← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 175

Sashe 117

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafin DIG ne ya dawo da hankalin Chief.. DIG da sauran ‘yansanda suka mik’e suna tafasa Inspector Gamji bisa wann k’ok’ari da yayi na kamo mai cin amanan aikin D’ansanda da kuma k’asa.

DIG yana tafawa yake fad’in “Impressive..! Gamji Mazan fama.. Well done Inspector Gamji.!”

Ai Chief ma tuni ya soma tafawa dan kar a zargesa. Yanayi yana Washe baki yana fad’in wann ba ci gaban Mu’azzam bane kawai ci gaban Team d’insu ne gaba d’aya tinda shine rahamar case d’in ke hannunsa.

Mu’azzam Sai duban Chief yake cikin zuciyarsa yana ayyana cewa saura kai Chief Jaja.. Sannu a hankali zamu iso Kanka Babban B’eran B’eraye.. Bayan mun gama da muk’arabbanka zamu iso kanka ne da izinin Allah.. B’eran banza sai na capko wuyanka In sha Allahu kafin na bar aikin D’ansanda.” Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai mik’awa DIG daketa faman mik’o masa hannu sukai masabaha. Yana kuma masa jinjina had’ida tabbatar masa samun goyon bayansa har a isa k’arshen wann case d’in.

Mu’azzam ya sara masa yana mai masa godiya “Wann nasaran mu ne gaba d’aya NPF Sir, dukda cewa ban kai yanda kake tunanin na kai ba amma na gode da kalaman yabo Sir.” Ya k’arashe yana sara masa dan yasan ba iyawarsa bane ko k’warewarsa ya kaisa wann matakin. A’a taimakon Allah ne da fawalla masa lamuransa da yayi.. Amma ko d’aya bai yarda akwai iyawarsa ko k’warewarsa a ciki ba.

Bayan sun fito daga Zauren taron kai tsaye cell d’in da akai detaining Yusuf nan cikin Headquarters d’in suka nufa shida Assad.

Hannayen Mu’azzam dafe da belt d’insa yake duban Yusuf yana tuna tsawon lokacin da ya kwashe yana cin amanarsu. Bai iya cewa komai ba sabida zafi da zuciyarsa ke masa. Ya tsani a raina masa hankali a ha’incesa.. Sun d’auki Yusuf d’aya daga cikinsu amma daga k’arshe yaci amanarsu..

Assad ne ya iya furta “Why did you do it.. Maiyasa ka aikata..?”

Yusuf ya mik’e ya k’araso gaba garesu yana sakin murmushi “I was only following orders.. Dear Team mate.” Ya k’arashe murmushin saman fuskarsa.

Assad ya girgiza kai yace “Waye yake baka umarni.. Was it Danger..?”

Murmusawa Yusuf ya kumayi “Ka bar shi wanda yake tunanin yanada brain d’in yayi tambayoyin amma ba kai ba wanda mace tai outsmarting naka.”

Izuwa lokacin ran maza ya b’aci, wani irin finciko wuyansa Mu’azzam dake aika masa mugun kallo yai.. Ta cikin kmarafunan cell d’in ya tura hannu ya capko Yusuf ya matsesa sosai kai kace zai fiddosa ta cikin matsin k’arfen ne. Dan wani irin damk’a ya masa ya shak’esa kaman mai shirin aikasa lahira har saida Assad ya k’waci Yusuf d’in da k’yar.

Yusuf ya zube nan wajen yana fidda numfashi da k’yar. Mu’azzam kam sabida b’acin ran abinda Yusuf yai kasa cewa komai yai saima ficewa da yai daga cikin ofishin gaba d’aya.

Assad ya dubi Yusuf ya girgiza kai disappointedly kafin yasa kai yabi bayan abokinsa Mu’azzam.

Saida Chief ya tabbata sun bar Ofishin kafin ya nufi wajen Yusuf.

“Kar ka damu zamu kula da iyalanka.. Sann zan samo maka hanyar da zakai escaping daga prison.. Kawai don’t rat us out.. Ka iya takunka ni kuma na maka alk’awarin zan maka komai..”

Yusuf ya tsaresa da idanu kafin ya murmusa da gefen baki yace “Kana tunanin yanda Inspector Gamji yai rantsuwa Sai ya kai k’arshen case d’in nan bazai kai bane.. Kana tunanin zaka iya dakatar dashi ne.. Idan ni da kai bamu b’ata ji da gani ba.. Inspector Gamji ya riga yasan da zaman Boss At the Top ko ince maka Babbanmu A Tushe..”

Murmusawa Chief yai kafin yace “Yasan abinda ya sani dai amma bazai tab’a sanin wanene Jemage ba. Yusuf ka iya takunka mu kuma zamu kub’utar dakai.”

Yusuf ya tsare Chief da idanu kafin ya soma jinjina kai yana fad’in “You better keep your words domin idan kai failing d’ina Chief believe me I won’t go down alone.. Ni ba kamar Maleeka bane.. You know I also have my own ways of doing things.. Zan baka mamaki idan ka zab’i juya mun baya.”

Chief ya kafesa da idanu kafin ya saki gajeriyar murmushi.. Lokaci guda yasa kai ya bar wajen.

Yusuf yai zaune yana tunanin makomar rayuwarsa data ahalinsa.

A haka har aka kwashe kusan sati biyu suna gudanar da bincike kan Yusuf.

Dik yanda Mu’azzam yaso ya fitar da wani abu daga bakin Yusuf abu yaci tura.. Duk kalan horon da za’aiwa mai laifi dan yayi magana anyi ma Yusuf amma yak’i sanar dasu komai.. Saima raina masu hankali da yai da fad’in Danger ne Boss d’insa.

Shi kaw Mu’azzam Chief yake so ya kama dan yasan Chief shine Babban b’era a Department d’in nasu saidai haka kurum ba tareda hujja ba baida ikon kamasa.

A wajen matarsa Sadiya kurum yake samun sauk’in abubuwan wajen aiki, saiko abokinsa Assad wanda Allah ya nufa ya tsallake tuggun azzalumai.

A b’angaren Sadiyar ma takan ziyarci Su Ummanta, saidai Umma ta hanata zuwa wajensu akai akai. A cewarta ba birgewa bane ace kullum matar aure tana gantali saman kwalta. Kamata yai ta killace kanta a gida ba taita fita barkatai ba hakan ba birgewa bane. Haka Sadiya zatai Ta ture turen bakinta babu dai yanda ta iya ne. K’arshe ma Umma wa Mu’azzam d’in tai magana tace ya daina biye Sadiya Wai idan zai fice aiki Sai ya kawota gida ya aje. Umma tace ya dinga barinta can gidanta idan abokan gira take nema za’a ke kawo mata su Ashir tinda ta kula kaman harda kad’aici ke damun Sadiyar. Dan a ‘yan kwanakin Mu’azzam na yawan jimawa wajen aiki ga fita bincike da suke shida Assad wasu lokutan ma har sukanyi dare sosai. Umma tace da ita ko wace mace haka tai hak’urin zaman gidan miji itama tai hakan tinda tasan ga yanayin aikin mijinta.

A b’angaren Safeenah da Mommy kaw, Mommy sai rainon cikin Safeenah take ba tareda Safeenar ta kula ba. Saidai yawan zazzab’i da k’anan ciwon kai dake damunta yasa Ta soma shakku.. Sai wann lokacin ma take tunanin Ta wuce kwanakin al’adarta tuntuni.. Calendar d’inta Ta duba tana mai kuma mamakin yanda abun ya canza da yawa.. Anya kuwa lafiya take.. Ta soma tinanin kwanaki biyu da suka shige taso zuwa asibiti amma sai Mommy ta hanata tace Malaria ce kawai no need taje a mata test zata bata anti Malaria tasha.. Ita dai cikin Magagin bacci ma ta amshi maganin tasha. Zata iya cewa batasan kalan maganin da Mommy ta bata tasha ba.. Anya bazata tafi asibiti ba.. Ta mik’e tana tunani.. Daidai lokacin Dattijuwar mai aikinsu ta shigo mata da farfesun kayan ciki da tace tana son ci.

Dubanta Safeenah tai tace “Iya nikam na tambayeki.”

Iya ta jinjina kai tace “Ina sauraronki.”

“Wai dan Allah meye alamomin mace mai ciki..?”

Iya ta zaro idanu waje tana tuna kashedin da Mommy ta masu. Ta kasa furta komai sai girgiza kai da take.

A kufule Safeenah tace “Bakiji tambayar da na miki bane..?!”

Daidai lokacin Mommy ta shigo.

Ta dubi Iya tace ta fice abinta.. Kana ta maidoda dubanta ga Safeenah “Mai kike son sani..?”

Safeenah ta kafe Mommy da idanu kafin ta girgiza kai tace “Kin sani Mommy.. Kinsan komai Kika zab’i ki b’oye mun.. Maiyasa Mommy..?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata.

Mommy Ta girgiza kai tace “Ban fahimci mai kike nufi ba..”

Safeenah ta mik’e zaune sosai tana kuma jinjina kai “Don’t play dump Mommy.. Kinsan komai.. Kinsan ina d’aukeda cikin Mu’azzam amma kika zab’i kiyi shiru kik’i sanar dani.. Mommy kina ganin yanda naketa faman shan wahala kan na karkato da akalar hankalinsa gareni.. Kina ganin yanda nake masifar son komawa gidan mijina amma duk kika zab’i kiyi biris sabida wani dalili naki.. Mommy shashanci nan ai bai kai yanda kike tunani ba.. Kina tunanin bana jin changes ne a jikina.. Kina tunanin bazan fahimci cewa inada ciki nan kusa bane.. Mommy abinda ban gane ba shine kan wane dalili zaki b’oye mun wann Babban makamin da zanyi amfani dashi wajen winning mijina back.. Haba Mommy Maiyasa zaki min haka.. Kinsan sarai Mu’azzam shine rayuwata shine cikar burina.. Maiyasa zaki hanani komawa gidansa..” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.

Mommy ta matso kusanta ta kamo hannayenta cikin nata, lallashinta ta somayi tana fad’in “Ba nak’i ki koma bane Safeenah.. Kuma ba nak’i sanar dake bane sabida wani manufa nawa.. Shin baki ganin yanda nake kulawa dake ne..? Irin tarairayar da ake wa mata masu ciki shi nake miki Safeenah..”

Cikin kuka Safeenah Ta fincike hannayenta daga cikin na Mommy tana fad’in “Ba ke kikeda alhakin kula dani da D’an ciki na ba Mommy.. Mijina shine zai tarairayeni ya kula dani.. Nayi imani da Mu’azzam yasan cewa inada ciki minti talatin bazan k’ara a gidan nan ba.. Haba Mommy wllhi ni kin cuceni.. Kinyi depriving mana right d’inmu nida d’ah na wajen kasancewa da mahaifinsa.”

Mommy ta girgiza kai “Safeenah ba haka bane.. Banda rashin wayo irin naki yanzu ai zai zaci k’Arya kawai kike masa babu wani ciki tattareda ke. Zaiyi tunanin so kike ya maidaki d’akinki sai kika b’ullo ta wann hanyar.. Kina tunanin zai yarda Kina da ciki ne.. Na bari cikin ya fito ne ya bayyana kowa ya shaida sai ki fi samun kulawar mijinki..”

Safeenah na hawaye take girgiza kai “Haba Mommy civilized world fah muke.. Kan wani dalili zaisa yak’i amincewa akwai gidan jininsa cikin jikina bayan ga prove na asibiti.. Mommy Mu’azzam needs to know.. He needs to know I’m carrying his child.. Kin fahimta..!” Ta k’arashe tana zaro idanunta dake jik’e da hawaye waje.

Ba tareda ta jira cewar Mommy ba ta janyo wayar salulanta ta soma dialing layin Mu’azzam..

Taita ruri ba’a d’aga ba. Ta soma k’ok’arin tura sak’o kenan Mommy ta kamo hannayenta tana fad’in “Mai kikeyi..?”

A d’an dak’ile take duban Mommyn “Text zan tura masa yasan da zaman D’ansa cikin jikina.”
Chapter 117 · 0% Book details