← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 175

Sashe 146

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’ayar mai suna Nazeeha tace “Wait Barr Ameer Dikko da na sani D’an gidan Mai Shari’a Sa’ad Dikko.. Toh ai cousin d’ina ne.. Wait ina yake..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa.. Tuni har ta fice ta riga Meeman ma.

Meema ta saki baki tana dubanta kafin Ta tab’e baki kad’an tabi bayanta.

Nan ta hangi Nazeeha da Ameer har sun b’ige da hira alamun dai ‘Yanuwa ne kuma sunsan juna sosai.

Meema na k’arasowa Nazeeha tai gyaran murya tace “Barr A ga k’awata ta k’araso ni zan shige na barku.. Please ka kular min da kawa wllhi zaku dace sosai..”

Meema ta saki baki tana dubanta cikeda mamaki.. sai kuma ta girgiza kai tana furta “You are crazy Zeeha..” Zeeha ta shige tana kashe mata ido.

Barr yai gyaran murya kad’an yana gyara tsayuwarsa yayinda Meema ta maidoda dubanta garesa tana fad’in “Ehen ina saurarenka.. Ka samu labarin Ya Mu’azzam sun rabu da Addah Feenah shine kazo ka fad’a mun bazaka janye k’udirin ka ba ko menene..?”

Ya d’anyi still yana dubanta kafin ya murmusa yace “Bansan da wann labarin ba.. Kuma a halin yanzu ban damu na sani ba..”

Meema Ta katsesa da fad’in “A’a da Allah Malam.. Babu abinda ya had’a ni da kai sai dalilin Adda Feenah. Ba court case nake ba balle nace Ina buk’atan attorney..” Ta k’arashe tana tab’e baki.

Ya kuma murmusawa kafin yace “Toh idan nace miki nazo na baki ansar Tambayar da kika mun ne fah, cewa na rabu da Safeenah rabuwa Ta har abada kuma na cireta daga zuciyata kaman yanda kika buk’ata..”

Meema Ta murmusa tace “Da yafi maka sauk’i dan kasan hausawa sunce soyayyar maso wani k’oshin wahala ne.”

Ya murmusa kad’an kafin yace “Ina son yanda kike magana.. Komai naki yana birgeni..”

Jin zancen nasa na neman canza salo yasa Meema kuma dubansa da mamaki “Bawan Allah shin lafiya..?” Ta tambaya tana dubansa.

“Lafiya sai alkhairi.. Bakiji mai Zeeha tace ba nida ke zamu dace da juna.. Kuma nima d’in na yarda da haka dan tin bayanda kika sa k’afa kika fice daga wann coffee shop d’in ban tab’a daina tunanin ki ba daidai da rana guda.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Quite alright naso Yayarki Safeenah, amma tin bayan da muka had’u nida ke muka tattauna sai na fahimci cewa kece wann matar da naketa nema ashe.. Kinsan wani sa’in baka tashi sanin ga abinda kake so sai kayi nisa kana chasing abinda ba Naka ba.. Wato Meema tin bayan da muka had’u muka tattauna wann ranan nida ke naji babu macen da ta kwanta min a rai nan duniya sama dake.. Yanda kika nuna kina son ‘Yaruwarki kuma kin damu da damuwarta Kina son Farin cikinta sai kika bala’in birgeni.. Kinada zuciya mai kyau mai cikeda k’aunan ‘yanuwanki tinda har zakiyi haka a bayan idon ‘Yaruwarki ba tareda ita d’in ta sani ba.. Burinki kawai shine ‘Yaruwarki ta kasance cikin Farin ciki..”

Meema da mamaki ya kasa sakinta saurin katsesa tai da fad’in “Give me break Mr Lawyer, will you. dan Allah kai shiru haka nan.. Kazo sai tsarani da zance kake irin taku na lauyoyi.. Ta yaya zaka so Yayata kuma kazo kace ni kake so.. Ni Meema nasan na iya jin zance da k’arawa a baya but I can never be a betrayal.. Besides wa yace maka ni Meema zan so ka.. Bana sonka bana k’aunarka dan Allah a k’ara gaba..”

Barr ya murmusa kad’an yace “Ni kuma wllhi ina sonki kuma tsakanina da Allah.. Ki bani dama na gwada sa’a na.. Please..” Ya k’arashe yana had’e hannayensa biyu alamun rok’o.

Meema tai murmushin takaici tace “Wai kai ko kunya bakaji.. Kaso Yaya kazo kana son k’anwa.. Who does that..?”

Barr ya kuma murmusawa yace “As far as I know yin hakan ba haramun bane kuma ba laifi bane.. Da yawa sukan so Yaya idan basu samu ba sai su koma kan k’anwa, wasu ma har basu k’anwar ake idan suka rasa yayar, ballantana in my own case ni ked’in nake so bama Safeenah ba ashe..”

“Aw sai yanzu ka fahimci haka.?” Meema ta katsesa tana dubansa galala.

Ya jinjina kai da sauri yace “Exactly.. Na d’au tsawon lokaci ina tausan zuciyata dan kar na sake samun heartbreak amma wllhi I couldn’t hold it back.. I love you so much Mims, like I never loved someone before..”

“Malam dan Allah ni ka cikani da surutu, ni kaw ko da ace baka so Adda Feenah ba mai zanyi da kai ni Meema..?” Tai maganar dafe da k’irji tana fito da idanu waje.

Ameer ya katseta da fad’in “Ke kin tab’a ganin Handsome Lawyer irina.? Ki tambayi Zeeha kiji yanda ake min tayin ‘Yanmata a family d’inmu Ina rejecting.. Kar kiyi wasa da wann damar yarinya..”

‘Yar bazaurar dariya tai kafin tace “Toh waye yace maka had’uwar ka ya dameni balle wani profession d’inka.. Kai baka san nasan kai criminal bane..?!”

Zaro idanu waje yai sosai wann karon kafin yace “Criminal fah Kikace.. Kinga ko a Kotu bana kare Criminal Allah is my witness.” Ya k’arashe yana kuma had’e hannayensa waje guda.

Meema tace “Idan kai va Criminal bane Maiyasa wann Police woman d’in take kiranka, abokiyar aikin Ya Mu’azzam. Wait what’s her name again..? Yauwa Maleeka.. Ka zaci bansan kanada connection da ita bane.. Kai da ita Kun had’a munafuncinku kuka haifar da fad’a tsakanina da Adda Feenah har ta daina min magana duk dan ta zaci Wai nice na tura wani sak’o da aka tura wayan Ya Mu’azzam.. Wai sak’on BAD.. Nasan ka sani dan ranan da muka had’u da kai na kiraka mu had’u ne dan na sami wani evidence akanka sann na wanke kaina.. Amma Adda Feenah bata saurareni ba.. Yanzu ka yarda nasan cewa kai Criminal ne tinda kai k’ok’arin had’a fitina tsakanin ma’aurata..!” Ta k’arashe hannayenta saman kunkumi tana sakin huci kai kace zata rufesa da duka ne.

Ga mamakinta dariya Ameer ya fashe dashi har yana dafe Mota kafin yace “Kinsan Allah wllhi bansan Maleeka ta tura wa Mu’azzam sak’on BAD ba.. Sai daga baya da na binciketa nasan da gaske ita ta tura masa kuma ta tura masa sak’on ne dan Ta haifar da zargi tsakaninsa da Safeenah.”

Meema tace “Ashe dai da gaske kai da ita Maleekar kunsan juna kenan.?”

Ameer ya jinjina kai yace “Bazan b’oye miki komai ba dan Ina matuk’ar k’aunarki.. Sanda Mu’azzam ya auri Safeenah sai na so na fara bibiyan rayuwarsa dan na samu na rabasa da Safeenah ni kuma na aureta.. Toh bibiyan rayuwarsa ba abu bane mai sauk’i, bayan kasancewarsa CID mutum ne maras hayaniya da shiga hidiman mutane.. Na fahimci shi mutum ne da ya bada mahimmanci sosai ma aikinsa, hakan yasa na fahimci cewa ta abokan aikinsa zan iya samun dama na cimma burina akansa da Safeenah na ganin na rabasu na mallaki Safeenah.. Toh sai nai amfani da Maleeka kasancewarta mace kuma mai tsananin k’aunar Mu’azzam.. Sai naga cewa nida ita abu guda muke so, ita tana son Mu’azzam ni kuma Ina son Safeenah.. Kinga zamu had’a perfect team kenan.. Maleeka ita take bani duk wani update da information na case d’in da suke handling.. Ita kuma Maleeka tana aiki ma Head d’insu na team d’in ne Wato Chief Jaja.. Daga wajen Jaja ta fahimci cewa Safeenah tanada alak’a da case d’in da suke bincike.. Ni kuma sai nai amfani da damar Ina jefawa Safeenah threats cewa nasan wani abu akanta.. Shiyasa naje a matsayin Lauyanta sanda aka kamata dan na samu daman kareta a kotu tinda nasan Mu’azzam dole zai iya rabuwa da ita ni kuma sai na aureta.. Bayan wann wllhi Allah shine shaidata banida wata masaniya akan case d’in kuma Kinsan sunce babu abinda soyayya bazai sa ba.. Nayi hakan ne sabida soyayyata ga Safeenah.. Kaman yanda yanzu na fayyace miki komai sabida soyayyar da nake miki.. Idan ma baki yarda ba inada duk records d’in wayar da mukai da Maleeka zan saka miki ki saurara.. Kinsan ni Lawyer ne so ina aje records sabida tsaro.. In case Maleeka tace zatai incriminating Kinga sai na bada shaidata.” Ya k’arashe yana murmushi kad’an.

Meema tai shiru tana jinjina wayo irinta Lauyoyi. Ashe duk yasan abinda yake bazai bari ai incriminating d’insa ba, idan ma ta fahimta amfani kawai yaitayi da Maleeka yana tatsan information daga wajenta ba tareda ta lura da hakan ba. Meema ta jinjina kai tace “Idan har kanada records hakan zai tabbatar cewa bani bace na tura wad’Ann sak’on wa Ya Mu’azzam, ina nufin sak’onnin BAD da aka tura masa cewa BAD yana lalata gidansa. Maleeka ita ce ta tura sak’onnin.. Yanzu inaso ka tafi ka samu Ya Mu’azzam ka sanar dashi komai duk abubuwan da suka faru.. Amma ka sani hakan ba yana nufin ni Meema zan so ka bane..”

Ameer ya jinjina kai yace “Zanyi duk abinda ya dace.. Kuma harta recordings d’in wayoyin da mukai da Maleeka zan sanar wa Mu’azzam.. Kinga hakan na nufin Mu’azzam zai fahimci akwai Rat a cikin department d’insu wanda ba Maleeka bace kawai harda Chief Jaja domin kuwa Maleeka ta kama sunan Chief Jaja da b’arnan da yake aikatawa a cikin wayoyin da mukai.. Na tabbata hakan zai taimakesa a case d’in da yake solving..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Idan haka kike so zanyi Meems.. Zanyi dik abinda kike so.. And ki sani ni ba mutumin banza bane obsession d’in da nakedashi akan Safeenah yasa nai kusan kauce hanya.. Kuma na gode ma Allah da yasa ban aikata wani abu mai muni ba in the process ba. Ban cutar da kowa ba Safeenah kawai naso karewa a kotu dan ta zamto tawa.. Sai Allah ya wanke Safeenah tun kafin na kareta.. Sann ya turo min ke naji cewa kece wacce zuciyata ya aminta da ita.. Ko Safeenah tana tareda Mu’azzam ko bata tareda shi a halin yanzu ke nake so Meema..”

Tab’e baki kad’a Meema tai kafin tace “Ni Zanje abokaina suna jirana.. And please don’t get your hopes up.. You might have another heartbreak.. Ah toh don’t say I didn’t warn you.” Tana ida fad’in haka tasa kai abinta.
Chapter 146 · 0% Book details