← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 175

Sashe 42

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duban Assad tai da idanunta masu zuban ruwa kafin ta samu kanta tana mai bin umarnin Assad d’in lokaci guda Ta juya suka koma gida.

Sauk’in abun su Ashir dik suna bacci da batasan yanda zatai tama yaran bayanin abinda ke wakana ba.

A nan veranda d’in Umma tai nuni ma Assad da tabarmar dasu Malam Liman suka tashi kafin Ta k’arasa saman kujera irin wanda mata ke amfani dashi a kitchen ta zauna, har lokaci sharan hawaye take da hijabinta.

Tsananin tausayin bayin Allahn ya rufe Assad. A hankali ya soma furta “Umma da farko Ina mai baki hak’uri kan abinda abokina ya aikata.. K’warai Mu’azzam bai kyauta ba sannan bai biyo ta hanyar da ya dace ba.. Ina baki hak’uri Umma on his behalf kiyi hak’uri.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam is not a bad person, yanada kurakurensa kaman ko wani d’an Adam, but I can assure you he’s not a bad person, and he’s not going to do any harm to your daughter.. Saidai ma ya d’auketa ne to give her protection daga mutanen da suke yunk’urin cutar da ita.. Mutanen da suke tunanin Sagir ya sanar da ita wani abu.”

Umma ta dubesa da mamaki wannan karon kafin tace “Amma ai mun sanar daku Jami’an tsaro Iyakacin abinda muka sani gameda Sagir.. Maiyasa abokin ka bazai k’yale d’iyata ba.. Na tabbata da wani dalili nasa da nufi ya aureta ya biya mana bashinmu.”

Assad ya jinjina kai kafin yace “Haka ne Umma, Kinyi gaskiya..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam ya auri Sadiya ne to keep her safe from danger, itace target d’in ‘yantaddan da muke nema muke kuma bincike kansu.. Nasan kinada masaniya akan irin mutuwar da mijinki kuma mahaifin Sadiya yayi..”

Umma ta d’ago tana dubansa wannan karon sai kuma ta katsesa da fad’in “Mijina had’arin mota yayi.. Mota ce ta bigesa.. Sannan tsautsayi ne kuma k’addara ne da bazai tab’a tsallakewa ba..” Tai maganar cikin tsananin rauni.

Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “K’warai haka ne Umma, Tabbas tsautsayi ne da bazai shige ranansa ba.. But mu jami’an tsaro hasashenmu da bincikenmu sun tabbatar mana accident d’in shiryayye ne.. Shiryawa akai Umma and Sadiya suke hari sai suka fara daga kan Wanda yake sama da kowa a family d’inta which’s her father.. Sun kawar da mahaifinta sabida shine mutum na farko da zai bata protection ya zamto garkuwa a gareta. Zaman Sadiya a taredaku had’ari ne a gareta da kuma gareku baki d’aya.. Na tabbata bazaki so wani abu ya sake samun wani cikin ahalinku ba.. Inada tabbacin wannan dalili shiyasa Abokina ya d’auketa sabida ‘yantaddan Ita suke hari they believe Sagir ya sanar da Ita wani abu wanda zai iya exposing nasu..”

Umma tai shiru tamkar mai nazari sai kuma tace “Idan na fahimceka Abokinka ya d’auke d’iyata ne domin yaja hankalin mutanen da yake nema.. Ba don ya bata kariya ba..”

Assad ya d’an shafi kansa kad’an yana mai sadda Kai k’asa “Umma bazan so kiyi ma abokina mummunan fahimta ba Dikda cewa kinada cikakken damar da zaki masa irin wannan fahimtar... Wato Umma Mu’azzam mutum ne da ya had’u da tarin iftila’i na rayuwa.. Dikda cewa ansan musulmi da d’aukan k’addara.” Ya d’an kuma nusawa kafin yaci gaba da fad’in “Ya rasa mahaifinsa tin yana k’arami sannan a daidai wannan lokacin jinya mai tsanani ya sami mahaifiyarsa.. Bayan wannan yazo ya rasa tilon k’anwarsa wacce aka kasheta aka kuma tsinta gawarsu tareda Sagir.. Kinji dalilin da yasa bincikenmu ya gangaro har kanku.. Sabida tarayyar Sadiya da Sagir... Amma kawai abinda nake so ki yarda dashi kuma ki amince shine Mu’azzam is never going to do any harm to your daughter.. And He’ll protect her with his life.. Ki kwantar da hankalinki Umma ki natsa zuciyarki kuma ki saka a ranki d’iyarki tana safer place.. Kiyi takabarki cikin kwanciyar hankali ki kuma rungumi yaranki.. I’ll be checking on you time to time in sha Allah.. Allah ya gafarta wa Abba yasa yana Aljannah..”

Jiki a sanyaye Umma ta amsa da Ameen tana mamakin tarayyar Assad da Mu’azzam, yanda wannan yakeda mutunci da sanin yakamata ba kaman abokin nasa ba.

“Ina mahaifiyar tasa take..?” Umma ta tambaya tana d’an dubansa kad’an.

Assad ya d’an risina kafin yace “Tana can garinsu ana mata magani. Shekaru goma sha biyar kenan tana kwance tana jinya..”

Jiki a matuk’ar sanyaye wann karon Umma tace “Allah sarki Allah ubangiji ya bata lafiya.”

Assad ya amsa da Ameen. Daga haka Assad sallama yai ma Umma kafin ya fito ya nufi bakin Babban kwalta..

Yana tafe yana dialing layin Mu’azzam.

Mu’azzam na driving yaga kiran Assad na shigo masa, yana d’agawa Assad ya soma fad’i daga d’aya b’angaren

“Do I always have to remind you that you are a big jerk..”

Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Say what you want to say quickly, I’m busy right now.”

“Who do you think you are Mu’azzam Gamji.! Ta yaya zakazo har gidan mutane ka d’auke masu d’iya.. Are you out of your mind.”

“No you’re out of your mind Assad, for as far as I know I didn’t do anything wrong. Matata na d’auko tareda ni.. Did I commit a sin..?”

“Is that how you take your wife..” Kafin Assad yakai aya ya katsesa da fad’in

“We talk tomorrow. I’ll send you some numbers.. Tracking nasu nake so ayi since you’ve access to the tracking room..”

Daga haka katse kiran yai yana k’ok’arin forwarding lambobin da aka turo masa sak’on BAD dasu..

Birki yai sakamon motar da bai kula wanda ke gabansa ba. Aiko nan Sadiya Ta hantsalo daga saman seat ta buga kanta.. A hankali ta soma k’ok’arin bud’e idanunta tana dafe goshinta dake mata zogi yanda Ta buga. Nan ta Ware idanu ta ganta cikin mota.. A firgice ta mik’e tana k’ok’arin bud’e k’ofar motar saidai tuni ya danna motar a central lock.

Sadiya ta dubesa yanda yake driving hankali kwance lokaci guda Take furta “Malam ina zaka kaini..? Ka maidani yanda ka d’auko ni ko na maka ihun b’arawo.!”

Shiru idan steering da hannayensa ke bisa ya amsa shima zai amsa.

Hawaye suka cika idanunta, cikin rawar murya take furta “Please ka maidani yanda ka d’aukoni.. I promise ban aikata komai ba.. Please don’t hurt me.. Ka maidani wajen Umma..!”

Nan ma shiru bai amsata ba. Lokaci guda Ta soma sakin huci tana dubansa, kaman wacce akanjefota haka ta tsallako ta dawo frontseat d’in.. Steering wheel ta shiga k’ok’arin janyowa tana fad’in “Either you take me back home ko kuma na jefamu a rami gaba d’aya.”

Ya juyo ya dubeta da mamaki ganin yanda take ta kokawa da steering.

Nan ma bai kulata ba bai sakar mata kan motar ba.
Idanunta na hawaye take dubansa “You’re merciless.. This is police brutality, Mr Inspector. Idan baka maidani ba wllhi zan maka ihun b’arawo.”

Ba tareda ya dubeta ba idanunsa naga street yake d’an rage girmansu, kafin ya saki murmushi kad’an yace “Go ahead and shout. Shout at the top of your voice.. Let’s see idan akwai wanda zai taimakeki..”

Hango check point na ‘yansanda da tai ya sanyata sakin murmushi tana hamdala, kafin ta juyo ta aika masa mugun kallo “You won’t get away with this.. I promise you..!”

Suna k’arasowa aiko yana zuge glass ta dubi ‘yansanda masu patrol d’in “Officers dan Allah ku taimakeni.. He’s a kidnapper, wllhi satoni yayi.. I know my Mum must be worried.. Dan Allah ku taimaka min.”

Mu’azzam ne ya katse zancen da fad’in “Officer all is well, I just found out my wife is pregnant. And you know how pregnant women are like..” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa

Daskarewa tai tana dubansa, for the first time da taga murmushinsa, sai kuma ta shiga girgiza kai tana fad’in
“K’arya yake Rankidad’e wllhi satoni yayi.. You need to arrest him please..”

Bata Kai aya ba taga ‘yansandan sun k’ame suna sara masa had’ida clearing masa hanya “SIR.!” Suka fad’i a tare suna masu nuna masa hanya.

D’ayan har yana fad’in “Congratulations Sir.!” Yana wani Washe baki yana k’anwata

Cak ta tsaya da bayanan nata kafin ta juyo tana duban Mu’azzam dake maida wallet d’insa cikin aljihu wanda ko shakka batayi ID d’insa masu patrol d’in nan suka gani.

Tabi ‘yansandan da kallo baki sake yanda Suka k’ame masa har motar Ta shige.. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in

“Do you think zanyi asaran wad’annan kud’ad’en kanki a banza ne,.. I’ll only dispose you when I’m done with you..” Yai maganan tamkar dai bashi yake maganar ba dan ko duban yanda take baya yi.

Cikin tsananin huci da zafin rai take dubansa, kalaman nasa masu zafi suna mata Yawo a dodon kunnuwarta. Wai zai disposing d’inta when he’s done with her saikace wata shara. Take kuma tsoro ya bayyana sosai saman fuskarta.. Ko lokacin da take Sady Pretty d’inta bata tab’a tsintar kanta da tsoron wulak’ancin d’a namiji irin wannan karon ba.. Tsoro take kar wannan mutumin ya mata babban wulak’anci.. Hijabin dake jikinta ta shiga duk’unkunewa ciki tana girgiza kai wasu hawayen na kwaranyo mata.
“Don’t hurt me please.!” Ta fad’i cikin tsananin rawar tana mai rintse idanunta.

Ko kallo bata isheshi ba saima bada mahimmanci da yai sosai ga tuk’in motar.

Suna isowa k’ofar gidan taga ya bud’e motar ya fito kafin ya zagayo ta yanda take zaune. Bud’ewa yai yace “Fito.”

Da rinannun idanunta take dubansa “No I won’t.!” Ta basa amsa kai tsaye.

Gajeren tsaki yai kafin ya fincikota ya fito da Ita ya soma k’ok’arin janyota tana tarjewa. Bai fasa janyota ba har saida suka shiga gidan. Saidai suna shiga taji haushin wasu irin k’artan karnuka irin breed d’in turawan nan. Ai bata San sanda tai tsalle Ta mak’ale cikin jikinsa ba.

Cikin tsananin rawar jiki take furta “Na shiga uku mai zaka mun.!”

Kai tsaye ya bata amsa “Zaki gani..!” Yai maganar yana mai tsare fuskarta da kallo wanda cike yake tab da tsoro.. Sai rawa jikinta yake ta kasa sakinsa.

Saitin kunnenta ya rad’a mata “Sakeni kafin ki Shafa min wani cutan zamani..”
Chapter 42 · 0% Book details