Sashe 34
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mamaki ya mugun cika Mu’azzam ganin yanda yarinyar nan ta tara masa jama’a sunata kallansa babu gaira babu dalili.
Aunty Shemau baki sake take duban Ajidde Cikeda takaici tace “Da sukayi mai..?”
Ajidde Ta dubi Inne sai ta kuma dubansu, lokaci guda take girgiza kai..
A kufule Safeenah tayo kanta tana fad’in “Ke yarinyar nan na kula kanki rawa yake.. Tin zuwanta gidan nan kike shiga hurumina.. Cikinmu wanene sa’anki da zaki tara mana jama’a.. Zo nan ki fad’a Uban mai mukai..”
Inne Ta tare Ajidde tana fad’in koda wasa kar Safeenah ta tab’ata..
Lokaci guda Ajidde dake tsalle bayan Inne take fad’in “ Inne wllhi Allah ne ya toni asirinsu, ni ba lek’ensu nayi ba k’ofa suka mance bud’e shine na gansu suna abinda ‘yaniskan turawa suke a tv.. Wllhi Inne Shi naga sunayi bari ma kiga..” Ta juya Ta manna ma garu kiss tace “Wllhi Inne haka naga sunayi...”Tai maganar cikeda gadara irin ita ga mai gaskiya. Cikin zuciyarta kaw duban Mu’azzam take tana ayyana dama dik wannan famkam famkam d’in nasa na K’arya ne da bogi iskancinsa yake a b’oye.
Meema baki sake take dubansu ta kuma dubi Ajidde ga wani irin dariya dake taso mata Wai abinda ‘yaniskan Turawa keyi a tv.. Kai wann yarinya anyi shashasha Ta bugawa a jarida. Babu hali Meema tai dariya ganin yanda Mu’azzam ya gumun had’e rai yana aikawa yarinyar razanannen kallo.. Sad’af sad’af Meema ta shige tana kuma k’unshe bakinta da dariya keta k’ok’arin kufcewa.
Uncle Salman ya girgiza kai kafin ya dubi Mu’azzam dake tsaye kaman wanda aka dasa idanunsa sunyi jazir, ya maido da dubarsaga matarsa Shemau yace “Ni na wuce Office.”
Musaddiq ya dafe goshinsa cikeda takaici kafin Shima ya juya d’aki dan yanzu kam ya gama yarda haukar Ajidde yafi k’arfinsa. Haka aka dinga barin parlorn cikeda takaici da kunyar abinda Ajidde tai.
Hindu ta janyo Ajidde tana fad’in “Zo muje Ajidde lokacin maganin Aunty Nuratu yayi..”
Ajidde ta saki baki tana duban yanda babu wanda ya kuma tankata a parlorn, ta dubi Mu’azzam da idanunsa suka kad’a sukai jajir yana aika mata razannan kallo.. Safeenah kaw ta Kasa yarda haukan yarinyar ya kai har wannan matakin.
Hindu ta janye Ajidde parlorn ya rage saura Inne Mu’azzam da kuma Safeenah.
Mugun kallo kurum Inne ke aika masu “Banaso naji wani ba’asi daga wajenku, ya maku kyau.. Ni bazan zuba maku idanu haka nan ba.. Na riga na gama magana, yau d’in nan zanyi magana da Salman a soma gyara maku b’angaren can gefen. Abin ya isheni haka..” Ta dube Safeenah dake ture turen baki tace “Tashi ki bamu waje kije ki saka sitira jikinki zanzo naji dake idan na gama dashi..”
Baki a ture Safeenah ta tashi ta bar parlorn tana kuma gyara zaman rigar baccinta ta nufi yanda takeda tabbacin Zata cimma shegiyar Ajidden nan.
Mu’azzam daketa faman murza zoben hannunsa yana sakin huci yana hango fuskar Ajidde sanda take nunasu tana fad’in asirinsu ya tonu, saurin d’agowa yai yana duban Inne data tasa sa gaba “Inne Yarinyar nan is a complete lunatic.. Mahaukaciya ce Inne. Bai kamata a barta ta kusanci Mamy ba in the first place, wayasan mai zata aikata mata idan haukarta ya tashi.. Gaskiya Inne lokaci yayi da za’a kori yarinyar nan daga gidan.”
Katsesa Inne tai da fad’in “Kai tafi can ka rufe mun baki dama tin can kana son kasancewa da matarka kak’i a Kai maka ita.. Kaketa wani hanya hanya.. Ai gaskiyar Ajidden ne da tace Allah ya toni asirinka..”
Mu’azzam ya shafa kansa kad’an yana kuma sakin huci “Inne, nifa bance Safeenah bazata tare ba, kawai banso a raba mun hankali ne a halin yanzu.. And Inne gaskiya yarinyar nan zata daina zuwa gidan nan daga yau ni ban ma yarda da maganin nata ba.. Idan har tana bada magani ma kanta ya kamata Ta fara yi.. Because she’s sick in the head.!”
Inne Ta kuma katsesa da fad’in “Kanka farau.? Nace Kanka farau..? Wane D’ansanda ne Aure ya hanasa bincike.. Kuma bari kaji da kyau na Fad’a maka Ajidde lafiyarta lau ehe, tanada hankalinta yarinta ce kawai ke d’awainiya da ita.. Sannan jikina na bani cewa maganin Nuratu na tattare da ita da izinin Allah..Babu wanda ya isa yasa a sallami Ajidde ko a hanata zuwa.. Ai Kai da matar taka kune manyan mahaukata da zaku shige d’aki ku bar k’ofa bud’e, ku ya kamata ayima magani ba Ajidde ba.”
Da mamaki Mu’azzam yake duban Inne yanda ta dage tana kare yarinyar nan da k’arfin gaske, ga gaskiya amma tana kaucewa.
Inne Ta mik’e tana ci gaba da sababi ta shige ta barsa nan zaune kaman an dasa sa .. Lallai zai karya yarinyar nan, zai mata horon da bazata sake gangancin shiga huruminsa ba. Idan ma wauta ne ko hauka duk sai ya cire mata Su. Ya mik’e a fusace ya fice daga parlorn. Banda iskanci gaban kowa da kowa harda ma’aikatan gidan zata dubesa tace ta kamasu suna aikata abinda ‘yaniskan turawa suke aikatawa a tv, wai Ta gansu suna suna kiss shida Safeenah harda manna bakinta jikin garu tana nuna yanda sukai Wato.. Lallai ma yarinyar nan Ta samu waje, kuma dik Inne ce ta sakar mata da yawa har wannan raini yake yunk’urin shiga tsakaninsu, yarinyar da yakeda tabbacin ko hak’orinsa k’wara d’aya bata tab’a gani ba..Aiko kafin ya bar gidan Sai ya cire mata haukar nan nata. Ji yake gaba d’aya ransa a jagule, ya kuma tsanar yarinyar fiyeda misali.
A can d’akin Aunty Nuratu kaw Safeenah ce keta kokawan kamo Ajidde Hindu na raba tsakaninsu “Yau sai na koya miki manners dan ubanki.. Sai na cire maki wannan k’auyancin naki..” Safeenah ta kuma fad’i tana kuma yowa kan Ajidde da tuni ta daka tsalle ta b’oye bayan gadon Aunty Nuratu. Hannayen Aunty Nuratu ta kama tana fad’in “Dan Allah kar ki bari ta daken kinji dan Allah.. Nice dai Ajidde mai baki magani.” Yanda take maganar kace Aunty Nuratu na sauraronta ne.
Hindu kaw Sai k’ok’arin dannar Safeenar take.. Daidai nan Inne ta shigo.. Ba tareda tace komai ba ta janye Safeenah tana fad’in “Shige muje kece ya kamata ki fara koyan manners d’in kafin ki koya mata.”
Inne tana janye Safeenah Ajidde ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana furta “Wai Allah na tsira..”
Hindu ta dubi Ajidde tace “Ajidde Maiyasa kika aikata hakan.. Kan mai kika kunyata Safeenah da Baban Hajiya a gaban jama’an gidan nan..”
Ajidde ta dubeta da mamaki irin ita batayi laifi ba sune masu laifi “Ah Toh ni mai nayi.? wayace su aikata tinda sunsan babu kyau.. Naga dai wannan jiya jiya tazo gidan nan.. Dodanniya.”
Hindu ta girgiza kai tana mai jinjina shashancin Ajidde “Toh ke baki San matarsa bace, bakisan sud’in sunyi aure bane..”
Baki sake Ajidde ke dubanta tana nanata kalman aure cikin zuciyarta.. Tinani take Meye ma auren.. Sai kuma ta kame baki ta rufe da duka hannayenta biyu tana zaro ido waje.
Hindu ta girgiza kai tace “Ai dai nasan a shekarunki Kinsan mai kalmar aure yake nufi.. Ajidde ke macece ya kamata ki rage wannan wautan naki Kinga kefa budurwa ce da wanann sakarcin naki babu wanda zaice yana sonki, nan gaba kad’an Kema auren nan zakiyi ya kamata kike natsuwa kinji koh..”
Baki sake Ajidde ke kallonta “Chabb kujita Wai nima aure zanyi.. Wllhi har kin bani kunya.. Tabb ni koda nake ce ma Inna Kyallu zata sami surki k’arya nake, ni wllhi kunya ma nake ji.. Ni dik kinsa inata jin kunyarki.. Ni yau Allah bazan iya duban fuskarki ba.. Na shiga uku.. Kujita Wai aure..” Ta k’arashe tana tura kanta tsakankanin cinyarta Wai kunya takeji..
Hindu ta girgiza kai kurum tana mai gauraya maganin kafin ta isa ta tallafo Aunty Nuratu tana fad’in “Kizo ki bata ko itama kunyarta kikeji yau..”
Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai kunyar Hindu take. Ta Kasa d’agowa ta tallafi maganin “Toh ni dan Allah ki daina kallo na wllhi kunya kika bani..”
Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai ita kunyar Hindu take, d’agowar da zatai kaw ta hangesa bak’in k’ofa fuskar nan tasa tamau kaman ma yafi na ko yaushe.. Wani irin tsalle Ajidde tai ta haye bayan gado jikinta sai rawa yake.
“Na shiga uku na mutu na lalace, shikenan harbeni zai.!” Tana maganan tana duk’e lungun Gado jikinta sai rawa yake idanunta a rintse.
Hindu Ta rik’e baki tana fad’in “Oh yau naga ikon Allah ni Hindu.. Wai meye yanzu kuma kika gani..?”
K’ofa Ajidde ke nuna mata tana fad’in “Gashi can a k’ofa Mama Hindu wllhi harbeni zai.. Ki ceceni..”
“Shi wane..Ni banga kowa ba..”
Sai sannan Ajidde ta bud’e idanunta a hankali sai kuma ta dubi k’ofar taga baya nan.. Toh kodai gizo ya fara mata ne.. Sabon tsoro ya bayyana a fuskarta.. Itakam tak’i jinin mutumin Allah ya gani tsoro yake bata.
A b’angaren Mu’azzam kaw tinda yaga ganinsa kawai da tai ya firgitata ya bata tsoro Sai ya shige d’akinsa dan yayi shirin tafiya masallacin Juma’a da shike ranan Juma’a ne babban Rana. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Ashe k’aryar rashin kunya da k’auyanci kike.. Tinda kika shiga gonar muazzma kin b’ata yarinya.’
Yana cikin shirin ne wayarsa ta soma ringing Assad ne mai kira..
Cikin sauri ya janyo wayar ya d’aga dan yasan update Assad zai basa gameda bincikensu.
Saidai baisan sanda cufflinks d’in dake rik’e hannunsa yana k’ok’arin mak’alawa hannun rigarsa ta fad’i ba.. Cikin rarrabewar kalma yake furta “What do you mean she’s getting married Assad..? I mean.. She can’t get married now.. We still need her for our mission..!”
Ya mik’e babu shiri yana mai zagaya cikin d’akin sanda Assad yaci gaba da fad’in “And that’s not the case Muazzma.. Mutumin nan idan ya aureta d’auketa zai daga garin nan, idan ma Danger bibiyarta da ahalinta yake kaga shikenan bazamu cimmasa cikin sauk’i ba..”
Muazzma ya fuzar da wani fuci yana girgiza kai alamun a’a “No Assad.. We can’t let this happen... Danger is still on the loose.. Hakan na nufin bazamu samesa nan kusa ba..” Ya d’anyi fasali kafin yace “Wai ma tsaya waye mutumin da zai aureta d’in..?”