← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 175

Sashe 107

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana jin sanda Shemau ta janyo k’ofa ta rufe. Still idanunsa a lumshe yake furta “Godiya nake Hajjaju yau bacci ko 5star hotel nake albarka.”

Musaddiq ya zame nik’ab d’in da ya rufe fuskarsa dashi had’ida yaye hijab d’in.. Cikin sauri ya k’arasa igiyan shanyan Su Mama Hindu yanda ya d’auki Hijab d’in da nik’ab d’in ya maida masu. Haraban gidan ya koma ya zauna yana jin zuciyarsa na masa zafi.. Maiyasa Safeenah da Shemau zasuyi tarayya wajen ruguza auren Mu’azzam.. Maiyasa ahalinsa suka zama mugaye irin haka..? Maiyasa ya fito cikin irin wann ahalin..? Ya k’arashe yana lumshe idanunsa had’ida girgiza kai. A fili yake furta “Monster.! Monster.! Monster.!!” Lokaci guda ya kame kansa yana jin zuciyarsa na masa tsananin k’una.

Daidai lokacin motar Uncle Salman ya shigo Gidan gonar.

Ya isa yanda yake parking ya ajiye motar, Musaddiq na nan zaune a mazauninsa har Uncle Salman ya ida parking.. Ya k’ura masa idanu yana tuna tsttaunawarsu da Daddy da ya sinkaya gameda sa’insan da Uncle Salman d’in sukai da Baban Mu’azzam kafin ya rasu.. Wani irin tsanar Uncle Salman na kuma taso masa.. Ya jinjina kai yana dubansa sanda ya nufi b’angarensa. A fili Musaddiq yake furta “I’m sure this will ruin you Uncle.. Kaida matarka baku da banbanci.. You both are monsters shiyasa kuka auri juna.. Na tabbata yau d’in abin da matarka tai niyyan yi zai tarwastaku gaba d’aya..!” Ya k’arashe yana ci gaba da dannawa Uncle Salman d’in mugun kallo..

Shigan Uncle Salman da kad’an Musaddiq ya soma jiyo ihun mutumin Uncle Salman na bugunsa.. Har waje suka fito Uncle Salman na bugunsa.. Yana ihu yana fad’in ya masa rai kar ya kashesa.. Musaddiq da securities suka nufo wajen babu shiri yayinda Uncle Salman yaci gaba da tokarinsa yana masa bugun zazzab’en dawa.. Ya mik’e zai arce a guje Uncle Salman na sakin huci yake fad’in kar Su barsa ya gudu..

Wann hayaniyar shi ya tashi hankalin illahirin mutanen dake cikin gidan gonar.

Musaddiq yai amfani da wann damar ya bawa Tj hanya, TJ ya arce a guje.. Uncle Salman na fad’in securities su bisa su kamasa. Saidai ina TJ gudun mutuwa yake dan tuni ya arce daga cikin gidan gonar.

Shemau jikinta na wane irin rawa ganin Uncle Salman cikin yanayin da bata tab’a ganinsa ciki ba.. Su Inne ma duk hankalinsu a tashe.. Kan kace mai ya kaiwa Shemau wata irin jahilar naushi.. Inne tai k’ok’arin dakatar dashi tana tambayarsa lafiya meke faruwa.

Bai amsa Inne ba ya kuma kaima Shemau wata tokarin.. Janyota ya shiga yi a k’asa tana ihu tana kururuwa.

Banda sakin huci baya komai “Dan Ubanki yau sai kin bar gidan nan.. Ni zaki kawo ma kwarto har cikin Gida.. Wllhi yau sai kin tafi Shemau.. Babu ni babu ke aurena da ke ya k’are matsiyaciya.. Wato dama dalilin da yasa kika tura yaranmu hutu kenan dan ki dinga kawo min maza cikin gida koh.. Toh yau Allah ya toni asirinki.. Kuma shima shegen da kike kawo mun d’in sai na bincikosa naci Ubansa..!”

Shemau na kuka take fad’in “Wllhi wllhi ba halina bane.. Wllhi bansan komai ba..!”

Uncle Salman ya rufe mata baki da wani naushin a tsananin hasale ganin tana k’aryata abinda da idanunsa ya ga hakan.

Sallalami da salati kawai su Inne suke, yayinda Mama Hindu da Sadiya suka koma cikin gida jiki duk babu k’wari.

Shemau taci gaba da kuka tana rantse rantse tana fad’in wllhi batasan komai ba.. Ita bata biye biyen maza..

Kaman dad’a tunzurasa take ya kuma harzuk’a ya yo kanta.

Inne tai saurin dakatar dashi tana fad’in “Kai Salman ka natsu nace abi komai a sannu.. Cikin hayyacinka kake jifan matarka uwar yaranka da wann mummunan k’azafi..?!”

Uncle Salman na sakin huci yana aikawa Shemau dake duk’e a wajen wulak’antaccen kallo yake fad’in “Inne k’azafi kike cewa bayan bani kad’ai naga d’an iskan da Ta kawo ba.. Harta masu gadi sunga hakan.. Inne d’akin bacci na fah naga wann D’aniskan saman gado na.. Wllhi yau idan ban kasheki ba Shemau sai na miki mummunan rauni.. Matsiyaciya zuriyar mastiyata.. Dama an fad’a mun gidanku ba gidan mutunci bane na toshe kunnuwana na aureki a haka na tsamoki daga yunwa da talauci shine bari ki saka mun da rashin arziki koh.. Toh dan Ubanki kin gama zama a Gidana.. Kuma babu ke babu ‘ya’yana..!”

Shemau dake duk’e wajen hannu aka take kururuwa tana fad’in “Na shiga uku.. Dan girman Allah ka mun rai wllhi rugar mu ko service d’in waya babu.. Na shiga uku ni Shemau.. Dan Allah ka mun rai kar ka sallame ni.. Wllhi ba kwarto na bane.. Bansan ya akai ya shigo ba.. Dan Allah ka tsaya na maka bayani..!” Bata kai aya ba Uncle Salman ya cire takalminsa ya shiga kai mata bugu dashi, ya rarumo katakon da ya daki TJ dashi ya shiga rapza ma Shemau kaman wanda aka Aiko Sa.. har saida Inne Ta kare Shemau.. Ya nufi cikin gidan yana huci ya soma firfito da kayayyakin Shemau yana watsi dasu yake fad’in “Yau zaki bar gidan nan Karuwar banza.. ‘Yar iska maras mutunci.. Yau bazaki kwana a gidan nan ba.. Maza a k’ara gaba aje aci gaba da tallan fura da nono.. Kayan ma a gidan nan kika samu.. Zo ki fita matsiyaciya.!” Ya shiga janyota a k’asa tana ihu tana fad’in Ita bazataje ko ina ba.. Ko sauraron Inne bai tsaya yi ba haka ya dinga janyo Shemau a k’asa har saida ya fitar da Ita har k’ofan gidan yai instructing masu gadin da cewa duk wanda ya bar Shemau Ta shigo gidan a bakin aikinsa. Ko mai kaman ta ne kuwa..”

Haka Shemau tana kuka tana rok’onsa ya k’yaleta ko sutura ne ta d’auka amma ko sauraronta bai ba saida ya fiddata har waje. Hannu biyu Ta saka aka tana kuka tana fad’in “Na shiga uku ni Shemau yanzu ya zanyi ina zanje.!” Ta mik’e da k’yar k’afafunta babu ko takalmi ta soma tafiya cikin d’ingishi dan da k’yar idan Uncle Salman bai ji mata rauni cikin k’ashi ba. Tana tafe tana kuka ba tareda sanin yanda ta dosa ba.

Uncle Salman yana komowa cikin gida zama yai a parlor zuciyarsa na tafarfasa.. Shine Shemau zataci amanarsa ta kawo masa kwarto har cikin gidan Mahaifinsa tsaban Ta maidashi D’an iska.. Shi abinda ya mata kawai ma bai ishesa ba ai taci banza ma kenan.. Idan sunansa Salman sai ta biya abinda ta masa.. Wane irin kishi na kuma turnuk’esa idan ya tuna ganin TJ da yai kwance saman gadonsa.

D’ago kai yai yaga Inne tsaye kansa tana dubansa, a hankali ta k’arasa saman kujera ta zauna.

Ta d’an girgiza kai kad’an tace “Kai yanzu abinda kai ba asirin kanka ka tona ba. Da Kayi komai cikin natsuwa ba cikin hauka da tashin hankali kaman yanda kayi ba.. Yau kaf fad’in gidan gonar nan kowa yasan abinda matarka ta aikata.. Haba Salman.. Wann ai kaman ka kwance ma kanka zani ne a Kasuwa..”

Uncle Salman ya katseta da fad’in “Inne mai zanyi idan banyi haka ba.. Cikin d’akin baccina fah na iske D’aniskan yaron nan.. Wllhi na mata da kyau da ban illatata ba..!” Ya k’arashe yana sakin huci.

Inne tai shiru kafin ta girgiza kai a hankali tace “Allah ya rufa asiri.. Ka natsu ka natsa hankalinka waje guda.. Har kullum tashin hankali baya kawo maslaha..” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta nufi nata b’angaren zuciyarta gaba d’aya babu dad’i.. Godiyar Allah ma da ya kasance yaran Shemaun basa nan abin bai faru gaban idanunsu ba. Dikda cewa jininsu dama sam baizo d’aya da Shemau ba sam bataji dad’in yanda al’amarin ya kasance ba. Ko Babu komai Shemau sirkarta ce kuma uwar jikokinta an riga an zama ahali.. Sam abu dai baiyi dad’i ba.

Tana isa parlor tasa Musaddiq ya mata kiran kaf mutanen da abun ya faru gabansu. Ta had’a assembly tace dan Allah abinda ya faru daren yau ya tsaya a iyaka nan.. Dik wanda ya rufa asirin d’an uwansa musulmi Allah zai rufa nasa ranan gobe k’iyama. Kowa yai mata Na’am da cewa in sha Allah babu mai d’ago zancen. Saidai maganar duniya dama ba mai b’uya bace.

Gaba d’aya gidan ranan wane irin bacci akai, abu ne da sam babu dad’in gani balle dad’in labari.

Washe gari jikkunansu duk a kace musamman Sadiya da Ta d’auki Shemau Tamkar sirkarta, sai taji sam babu dad’i, sauk’in abun sassafe dama suma zasu d’aga zuwa Abuja.

Ta rik’e hannun Mamy suna sallama. Fuskarta Sai Haske da shek’i yake, Ta shafi goshinta kad’an tace “Mamy yau zan tafi.. Amma na miki alk’awarin in sha Allahu zan kuma dawowa.. Ina fata had’uwar da zamuyi na gaba mu tarbi juna akan k’afafunki Mamy.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.

A hankali Sadiya Ta saka yatsun hannunta ta goge k’wallan da suka ciko idanunta.. Tana k’ok’arin mik’ewa taji Mamy ta rik’e yatsun hannunta.. Zuciyarta yaci gaba da harbawa da sauri da sauri.. Ta waigo domin tabbatarwa. Ai kuwa nan taga yatsun hannunta cikin tafin hannun Mamyn dukda cewa idanunta a lumshe suke. Sadiya ta kuma duk’awa a hankali tana kallon yanda hannayensu ya had’e waje guda sai taji wani k’wallan na kuma ciko idanunta. Ta jima tana duban hannayen nasu.. A hankali kuma taga hannayen Mamyn na k’afewa har dai ya koma a bud’e kaman yanda yake ko yaushe. Sai taga abin kaman imagination d’inta ne kaman mafarki kaman kuma gaskiya. Addu’an samun lafiya ta kuma mata sanda taji muryar Mama Hindu na fad’in ta fito su tafi.

Ta saka bayan hannunta ta share k’wallan kafi ta shafi kan Mamy tace “Zaki samu lafiya da k’udirar Ubangiji.”
Chapter 107 · 0% Book details