← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 175

Sashe 134

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wann karon bugun Zuciyar Daddy ya k’aru, ya dubi Mu’azzam yana girgiza kai, sai kuma ya dubi Mommy da kanta ke duk’e tana hawaye.

Musaddiq ma duk’ar da nasa kan yai yana hawaye.

Daddy ya kuma duban Mommy yace “Hajara mai Mu’azzam yake fad’i.. Shin kin cutar da Nuratu ne..?”

Cikin kuka Mommy ke girgiza kai ba tareda Ta iya furta koda kalma ba.

Jijiyoyin goshinsa da wuyansa sun fito sosai sanda yake furta “Daddy matarka Ta d’auko wa mahaifiyata ‘Yar rufa ido a matsayin majinyaciya.. Wann matar taka Daddy tana so ta raba tsakaninka da mahaifiyata ne.. Wann matar taka Daddy itace Ta fitar da mahaifiyata daga cikin gidan nan domin ta fice mata daga gida da kuma rayuwar mijinta gaba d’aya..!” Yaci gaba da jinina kai hawaye mai zafi na ganagrowa daga idanunsa guda, wann karon cikin sanyin murya yake ci gaba da fad’in “Duk tsawon shekarun nan Daddy, Mommy bata k’aunar mahaifiyata.. Bata k’aunar zamanta a gidan nan.!” Yaci gaba da duban Mommy yana furta “How could you Mommy.. Ta yaya zaki aikatawa mahaifiyata haka..? Banyi niyyan d’aukan mataki akan cire cikin Safeenah da kikai akan idanuna ba.. Amma ki sani when it comes to my Mother.. Bana sassauci kuma bana rangwame..!” Wani hawayen ya kuma gangaro masa.

Jiri ne ya kusan kai Daddy k’asa, yaji numfashinsa na k’ok’arin d’aukewa.. Yaci gaba da girgiza kai yana duban Mommy “Hajara.. Hajara.. Hajara da gaske ne.. Kin cutar da Nuratu.. Hajara ki mun magana..!” Ya k’arashe jikinsa na wane irin rawa hawaye suka gangaro masa.

Wann karon Musaddiq ne ya k’araso da sauri yana hawaye ya duk’a gaban Daddy dake nufo Mommy ya kare mahaifiyarsa yana fad’in “Dan Allah ku yafewa mahaifiyata she’s only Human..”

Wane irin duba Daddy keyiwa Musaddiq, yanayi ne da zasuce basu tab’a ganin Daddy ciki ba.

Hannayensa duka biyu ya saka ya finciko Musaddiq ya watsar dashi gefe, yaci gaba da takawa gaban Mommy “Hajara you answer my question. Shin kin cutar da Nuratu..?!” Yanda yake maganar dole ya baka tsoro ga numfashinsa dake sama sama, yana fita da k’yar, asthma attack d’insa na k’ok’arin tashi.

Cikin sauri Mu’azzam ya tafi ya tallafo Daddy dake k’ok’arin kaiwa k’asa. Ya juyo ya dubi securities yace su tare k’ofa Mommy bazata fice ba.

Tare Musaddiq da Mu’azzam suka tallafi Daddy suka shigar dashi parlor oxygen na k’ok’arin kasa masa, sai rik’e k’irjinsa dake masa zafi yake. Yana fitar da numfashi da k’yar.

Mu’azzam na masa fifita da hannu yake fad’in “Try to calm down Daddy.. Sit straight first.”

Musaddiq kaw a guje ya nufi upstairs ya d’auko inhaler na Daddy ya kawo ya saka masa a baki Daddy ya shak’a da k’yar yana mai sakin numfashi a hankali.

Su duka biyun sai sannu suke masa.

“Ina Hajara..? Where is she..?” Tambayar da yake masu kenan.

Musaddiq yace “Daddy please try to calm down first.”

Girgiza kai Daddy yake yana k’ok’arin mik’ewa “I need to talk to your Mom Musaddiq.. I need to ask her this question.. Maiyasa zata cutar da Nuratu irin haka.. How on earth Hajara zata aikata abu irin haka.. She spent 15 long years taking care of Nuratu.. Ta yaya za’a ce Ta aikata mata haka..?”

Girgiza kai Musaddiq yai yana hawaye “Daddy Mommy fansa take son d’auka kan abubuwan da Mu’azzam yai mata.. Mommy is not as bad as you all thought she is..”

D’agowar da Daddy yai da niyyan magana yaga babu Mu’azzam a wajen. Ya mik’e sosai yana tambayan Musaddiq Ina Mu’azzam.

Sai sann Musaddiq d’inma ya waigo yana duban b’angaren da Mu’azzam d’in ke tsaye amma baya cikin parlorn.

A tare Musaddiq da Daddy suka fito haraban gidan suna neman Mu’azzam saidai sam basuga Mu’azzam ba balle Mommy. Musaddiq ya k’arasa da sauri yana tambayan securities, nan suka sanar dasu Sun bar Mommy da Mu’azzam a parking lot amma basuga yanda suka nufa ba, sun tabbata dai suna cikin gidan basu fice ba.

Musaddiq ya girgiza kai kad’an yana furzar da huci, yasan wanene Mu’azzam tsaf zai tisiye Mommy da tambayoyi ne har sai yaji Gaskiyar komai.

Cikin madaidaicin store dake haraban gidan Mu’azzam ya titsiye Mommy. Mommy sai kuka take tana girgiza kai tana fad’in ita wllhi bata aikata wani abin cutarwa wa Nuratu ba. Taci gaba da fad’in “Mu’azzam wani dalili nakedashi na cutar da mahaifiyarka bayan na kwashe shekaru Ina jinyarta.. Mu’azzam ka yarda dani ‘yar uwa na d’auki Nuratu.”

Cikin k’unan zuciya Mu’azzam ya katseta da fad’in “Ke kike da dalilin cutar da ita..! Sabida baki son kasancewarta da mijinki.! Sabida baki son kasancewarta a gidanki..!” Yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Kece kike da babban dalilin cutar da mahaifiyata Mommy.. Now you tell me mai kika aikata wa mahaifiyata.?!”

Cikin kuka Mommy ke kuma girgiza kai “Mu’azzam mahaifiyarka accident Ta samu bani na cutar da ita ba kai kasan da hakan.”

Ya kuma katseta da fad’in “Nasan wann.. Amma bayan abinda kika tasamma yi mata.. I started to have my doubts.. Ban yarda idan jinyar tsakani da Allah kika mata ba.. Mommy tell me now.. Mai kika aikatawa mahaifiyata.!” Ya k’arashe hawaye na fito masa.

Mommy ta d’ago ta dubi Mu’azzam dake tsaye kanta hannayensa dafe saman belt d’insa, idanunsa tarau babu tsoro sam a cikinsu, kai kace a interrogation room yake.

Cikin kuka Mommy ke fad’in “Ni da Shemau ne.. Ni da Shemau muka tsara d’auko wa mahaifiyarka mai magani na bogi..”

“Aunty Shemau.?!” Mu’azzam ya katse Ta murya a hankali wann karon.

Mommy tai saurin jinjina kai kafin taci gaba da fad’in “Shemau ita ta d’auko mai maganin.. Ni ko sanin mai maganin banyi ba sabida wann duk shirin Shemau ne. Mun tsara haka ne bayan Shemau Ta zigani cewa na dena jinya ma Nuratu Wai Nuratu kishiyata ce, kuma na bar ganin Nuratu a nakashe kaman batada wani amfani ita kishiya sam bata kasawa dik randa ta sami lafiya rabani da gidana da mijina zatayi dukda kuwa wann sadaukarwar da Nayi mata na shafe shekaru masu tsawo Ina kula da ita ina mata jinya, da zaran ta samu lafiya bazataga wann ba k’ok’ari zatai Ta koremu nida yarana daga gidana ita kuma ta zauna tareda mijina.. Shine shedan ya rinjayeni na d’auki wann shawari na Shemau..” Mommy taci gaba da fad’i cikin rawar murya irinta wanda yaci kuka “Wllhi Shemau ce ta sanyani a wann hanya amma ba hali na bane Mu’azzam.”

Mu’azzam yai murmushi irinta rainin hankali kafin yace “Shemau ce ta sakaki kika aikata abinda kika aikata.?”

Mommy tai saurin jinjina kai alamun eh.

Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Haka kawai Shemau ta sakaki kika aikata hakan.. Haka kawai Shemau taji tazo miki da irin wann batu..? Ashe idan Shemau tace ki k’ona gidanki zaki k’ona.. Kodai Shemau ce Ta baki shawari ki kashe jikanki da kanki.. Gashi kin haukatar da d’iyarki in the process.. So you tell me, Ta yaya Shemau ta samu wann power akanki..? Ko nace ta yaya kukayi tarayya wajen ganin kun fitar da mahaifiyata daga cikin gidan nan.. Mai Shemau ta buk’ata daga wajenki.. Ko haka kawai taji ta miki wann sadaukarwan mai girma dukda d’imbin had’arin dake ciki..?!” Irin yanda yake tsare masu laifi da tanbayoyi haka yake jefowa Mommy tambayoyi.

Mommy tai saurin girgiza kai.

Wann karon Mu’azzam duk’awa yai gabanta suna fuskantar juna “Mommy tell me.. Menene sauran abinda kike b’oyewa.. Gashi nan Ina gani daga cikin idanunki akwai abinda kike b’oyewa. Tell me menene..?”

Mommy na hawaye taci gaba da fad’in “Shemau Ta sanar dani akwai aikin da take so na mata in exchange..”

Ya tsare Mommy sosai da idanu “Aiki in exchange..? Wane irin aiki.?”

Mommy Ta goge hawayenta kafin taci gaba da fad’in “Tace akwai wani takarda na yarjejeniya da mahaifinka da kuma Uncle d’inka Salman sukai..”

Zuciyar Mu’azzam yaci gaba da bugawa a hankali “Yarjejeniya..? Dad d’ina da Uncle Salman.?”

Mommy tai saurin jinjina kai kafin taci gaba da fad’in “Tace a cewar Uncle Salman wann yarjejeniyar mahaifinka ne yayi cewa ya mallaka wa Uncle d’inka Salman dukiyarsa gaba d’aya... Tace Slaman ya sanar da ita wann takardan na wajen Daddynku Marwan, tin bayan da Dad d’inka ya rasu Marwan Sai ya d’auke wann takardan to protect you and your inheritance from your Uncle Salman.. Shemau ta sanar dani Uncle d’inka Salman wann takardan kawai yake nema wanda akwai saka hannun mahaifinka akai.. Idan ya mallaki wann takardan shikenan ya mallaki dukiyarka.. Wann dalili ne yasa Shemau ta shiga jikina har Ta taimakeni.. Tace idan na samo mata wann takardan ita kuma zata kawar min da kishiyata daga cikin gidana.. A cewarta burin mijinta kenan ya mallaki wann dukiyar..”

Bibbiyu Mu’azzam ke gani.. Uncle Salman..? Takardar yarjejeniya..? Meke faruwa ne da ahalinsa..?

Muryar Mommy ya kuma sinkayo tana fad’in “Mu’azzam ka yarda dani wllhi sharrin Shemau ne da Salman.. Idanunsu ya rufe akan dukiya amma nida Nuratu lafiya muke zaune kafin Shemau da Salman suzo min da wann batu.. Wllhi ni ban tab’a nadama irinta yau ba bayan da naga halinda Safeenah ta tsinci kanta ciki.. Ko a haka Allah ya nuna min isharan cutar da Nuratu da na tassama yi Ta dalilin Shemau da mijinta Salman.

Ko tsayawa sauraron Mommy baiba ya fice yana ganin hanya na had’e masa, Mommy Ta nufo k’ofa tana rok’onsa ya bud’eta amma inaa ko takanta bai kuma bi ba, Tana nan kulle cikin store d’in mai tsananin duhuwa. Ta koma da baya tana muzurai saidai yana ficewa ta kece da wata irin muguwar dariya “Da sannu zaka bud’eni yaro dan zunubaina bai kama k’afan na ‘yan uwan mahaifinka ba.”

A haka Musaddiq da Daddy dake neman yanda suka shige a cikin gidan suka hangosa yana nufosu. Nan take suka nufosa Musaddiq na tambayan “Where is my Mom Mu’azzam.. Ina mahaifiyata.. Mai ka aikatawa mahaifiyata..? Police station ka kaita..?” Ya soma jijjiga kafad’un Mu’azzam yana fad’in “Answer me Mu’azzam Ina ka kai Mommy..?”

Fincikan hannun Musaddiq yai daga kafad’unsa ba tareda yace komai ba, ya k’araso gaban Daddy cikin wane irin yanayi “Daddy ina takardan yarjejeniyar.?”

Da mamaki Daddy ke dubansa, sai kuma ya girgiza kai yace “What agreement.?”

“Yarjejeniyar da mahaifina yayi cewa ya mallaka wa Uncle Salman dukiyarsa.. A ina ka adana wann takardan..?”
Chapter 134 · 0% Book details