Sashe 130
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Larai ta mik’e tana fad’in “Barin duba Assad a waje, ga kujera k’araso ka zauna.”
Godiya ya d’an mata kafin ta fice ta barsa da Sadiya.
Ya janyo kujeran dab jikin gadon nata kafin ya zauna yana mai kamo hannunta maras cannula.
Ya sumbaci hannun nata yana mai lumshe idanu a hankali. Dikda nauyin da k’irjinsa ya masa sai yana jin wane irin annashuwa da Farin ciki na fuzgansa.
Ya kuma bud’e idanunsa ya bud’esu tar kanta. A hankali ya d’aura d’aya hannun nasa yana shafan goshinta zuwa saman sumarta kad’an..
Sai kuma yakai dubansa ga shafeffen cikinta wanda kaman babu komai cikinsa, ya tuna yanda Mommy ta sanar dashi labarin cikin Safeenah da kuma yanda ta cire cikin akan idanunsa, take yaji wani abu kaman k’walla na yunk’urin ciko idanunsa. Ya matso a hankali yana mai kai hannu saman flat tummy d’in nata. A hankali ya janye rigarta kad’an ya soma shafa saman mararta yana kuma jin k’walla na ciko idanunsa. Kwantar da kansa yai gefenta had’ida lumshe idanunsa, still hannunsa saman cikinta yana shafawa yana tuna abubuwan da suka faru a rayuwarsa daki daki.. Sosai yake so yayi kuka, sosai yake so ya fitar da tarin damuwan dake k’unshe cikin zuciyarsa.
Yayinda Sadiya taji kaman mutum na shafata cikin baccin nata. A hankali ta soma bud’e idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi. Ta Ware idanun nata tas tana dubansa yanda ya kwantar da nasa kan gefen jikinta. Take ta soma tuna abubuwan da suka faru. Taji kuka na zuwa mata.. Yunk’urin da tai da zummar mik’ewa zaune yasa Mu’azzam ya fahimci ta farka daga baccin nata.
Saurin mik’ewa yai zaune yana dubanta, suna had’a ido taji kuka gadan gadan na zuwa mata. Nan kaw ta fashe masa da kuka tana k’ok’arin turesa daga jikinta. Bai saketa ba saima manne kanta cikin k’irjinsa da yai..
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*66*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Bai saketa ba dikda kiciniyar da take na k’ok’arin cire jikin nata daga cikin nasa, saima dad’a rungume kanta da yai cikin k’irjinsa yana k’ok’arin calming d’inta. Ta daina kiciniyar da take Tai lamo cikin k’irjin nasa tana fitar da sautin kukan hankali.
“Ni ka sakarni..”Ta fad’i cikin muryar kuka.
Sumar kanta yake shafawa a hankali kafin ya sumbaci kan nata yana mai lumshe idanunsa “Why haven’t you told me Beautiful..? Maiyasa baki sanar dani ba, that you are carrying my child.”
Saida taji k’irjinta ya buga da jin abinda yace, ta shiga tuna waima fah a asibiti ta tsinci kanta.. She fainted and they rushed her to the hospital.. Wai tanada ciki..? Sai kuma ta soma tunanin sabida Safeenah nada ciki ne yai mata duk abinda ya mata.. Wato yanzu itama da aka ce tanada ciki shine ya wani d’ibo k’afa yazo bayan da ya fita sha’aninta.. Kenan sabida cikin yazo.. Da ace batada cikin bazai tab’a waiwayanta ba. Gaba d’aya sai taji bata d’aukin cikin ma.
Bai saketa ba tana nan cikin k’irjinsa taji hannunsa guda saman mararta yana shafawa a hankali yana furta “Nasan Kema baki sani ba sai wann lokacin right.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Beautiful zamu zama iyaye.. Our Baby is in here.. Kina son Babyn..?” Ya k’arashe cikin wane irin siga mai kashe mata jiki lak’was.
Mu’azzam gwani ne wajen mantar da mace damuwa harma Ta mance fushi take dashi dukda kuwa zafin da yake dashi, idan suka kad’aice su biyun gaba d’aya mancewa take da cewa shine wancan Inspector mai tsananin tsaurin da ta soma had’uwa dashi.. Ita batai niyyan komawa gidansa yanzu ba balle ma data fahimci sabida wann cikin yake nuna kulawarsa akanta.. Wato da ace dai batada ciki da har yanzu yana can wajen Safeenah bazai ko waiwayeta ba. Aiko bazata koma ba idan dai dan cikin jikinta ne ya waiwayeta. Ta tura hannunsa daga jikinta tana girgiza kai alamun a’a “Ni bana so.. Kuma dan Allah ka fice ni ka k’yaleni..” Yanda tai maganar cikin fushi ne sosai wanda har saida ya tunowa Mu’azzam lokacin da take Sady Pretty d’inta, lokacin da yai mata lak’abi da Stubborn head, a ransa yace ‘Abin ya motsa, dama yaya lafiyar kura balle taci nama..’ Yasan halin kayansa balle kuma ga attitude na masu ciki.
Bai tak’ura ba, ya d’an janye jikinsa kad’an yana fad’in “Allah huci ran Maman Biyu..” Ya k’arashe yana gyara mata zaman hannunta mai cannula.
Ta d’an hararesa kad’an baki a ture jin sunan da ya kirata dashi.
“Akwai abinda kike so kici ne..?” Ya tambaya yana dubanta.
Ta mak’e masa kafad’a “Ni bana son komai.. Kuma ni bazanci koma ba, Kawai ni ka tashi ka tafi ka koma yanda ka fito..”
Da Mamaki yake dubanta yanda taketa fushi, Sai kuma ya tsime kad’an wann karon “Dole zakici abinci.. Bakiji abinda Dr yace bane.? Kan wane dalili zaki dinga zama da yunwa..? Baki San ba ke kad’ai bace.. What if something bad happens to either of you, and especially the Baby..” Yai fasali yana jinjina kansa kad’an kafin yaci gaba da fad’in “I know how stubborn you can be Sadiya. Kar ki kuskura.. Kinji na fad’a miki..!” Yanda Yai maganar cikeda gargad’i. Shi Gaba d’aya tinda ya rasa cikin Safeenah akan idanunsa sai yana ganin kaman zai kuma rasa na Sadiya ne.
Kuka ne taji na kuma zuwa mata, Wato dai sabida D’an cikinta ya waiwayeta.. Gashi har yana mata fad’a da kashedi kan cikin.. Ita gani take gaba d’aya ya sauya mata.. Da gaske yafi son cikin jikinta sama da ita, abin cikinta ne damuwarsa ba ita ba.. Kukanta a hankali yake fita maras sauti.
Mu’azzam duk sai yaji babu dad’i musamman da yaga yanda ta duk’ar da kanta tana hawaye. Lokaci ne da ya kamata ace suna Farin ciki da wann babban kyauta da Allah ya basu ba k’unci ba. Da tasan yanda hawayenta ke masa rad’ad’i a zuciya da ta daina kukan.
Ya d’an furzar da huci kad’an kafin ya mik’e daga saman kujeran ya zaune gefenta saman gadon, ya shigar da kanta cikin k’irjinsa yana k’ok’arin lallashinta.
Ita kaw kaman wacce aka ce ta k’ara sautin kukanta.
“Ya isa haka.. Hush now..” Yana maganar cikin sigan lallashi yana shafa kanta kad’an irin yanda ake ma yara idan suna kuka.
Suna a haka Dr ya turo k’ofan Aunty Larai na biye dashi. Mu’azzam yai k’ok’arin janye jikinsa, yayinda Sadiya tai k’ok’arin tsaida kukan nata.
Dr ya k’araso yai mata sannu had’ida tambayarta jikin nata ko akwai wani pain ko wani abu da takeji. Ta girgiza masa kai alamun batajin komai sai weakness da baza’a rasa ba..
Aunty Larai ta k’arasa wajen Sadiya tana mata sannu yayinda Dr da Mu’azzam suka fice suna tattaunawa.
Duba d’aya Aunty Larai tai mata ta fahimci Sun kuma haurawa da mutumin nata ne. Ta murmusa cikin zuciyarta tana mai mata uzuri, dan tasan mace mai juna abun fushi sam baya mata kad’an.
Bayan da drip ya k’are aka sallamesu, ana kiraye kirayen sallar isha suka iso gida. Har lokacin Sadiya a kumbure take, ko kallon yanda yake batayi.. Shi sam bai ma San ga laifin nasa ba, shi dai ya alak’anta fushin da take da kasancewarta mace mai k’aramin juna.. Dan yasan wann karatun na cewa mata masu ciki sunada saurin fushi. A haka kawai ma sai suyita fushi sann abinda bai kai ya kawo ba ma Sai ya sanyasu fushi.
Ya kula kaman space take so hakan yasan koda suka iso gidan bai buk’aci su tafi tare ba, Umma kaw dika Farin cikin da take na dadd’an labarin Jika da zata samu daga d’iyar nata hakan bai hanata cewa saidai Sadiya ta tattara tabi mijinta ba tinda babu wacce ciki ya hanata zaman aure baza’a fara a kanta ba.
Sadiya Ta fashe da kuka tana fad’in ita bazataje can gidan ba.
Mu’azzam ya d’an girgiza kai kad’an, cikin risinawa yace “Umma ai hak’uri a barta a nan d’in ta k’ara jin k’arfi..”
Umma tai k’wafa tana aika ma Sadiya dake faman ture turen baki mugun kallo “Ai kai kake biye mata take wani sangarcewa tana shagwab’e wa mutane. Kanta ne farau zata wani narkewa mutane.. Ta tashi ta wuce mu bamuda masauk’inta ma a nan..”
Mu’azzam ya d’an kuma duk’awa yana fad’in “A yi hak’uri dai Umma, a barta a nan d’in..”
Aunty Larai Ta janyo Sadiyar jikinta tana fad’in “Nifa a k’yale mun d’iya tinda an bamu lasisi.. Abi d’iyata a hankali dan D’an mutum ne sukutum cikin cikinta ehe.. Muje na sama miki wani abu ki saka a cikin koh..” Ta k’arashe rik’e da hannun Sadiyar wacce ke goge hawayenta da d’aya hannun.
Mu’azzam da Umma suka bisu da kallo Umma na yin k’wafa. Sosai Mu’azzam ke jin dad’in yanda Aunty Larai ke kular masa da Sadiyarsa.
Ya d’anyi gyaran murya yana mai mik’ewa “Umma ni zan wuce.. Zanjeni na taho mata da wasu ‘yan kayyayakinta.”
Umma ta girgiza kai tace “Kaida Larai dai Kun d’aure mata gindi.. Ni mai zance Tunda kunfi k’arfina.”
Murmushi kawai Mu’azzam keyi yana sosa kansa kad’an yana kuma bama Umma hak’uri. A haka sukai sallama da Umma ya fice.
Ya tadda Assad waje yana jiran fitowarsa.
Jikin motocinsu suka tsaya Assad na masa ‘yar tsiya da zolaya. Saidai gaba d’aya yanayin da yaga Mu’azzam d’in ciki yasan definitely akwai abindake faruwa.
“Wai lafiya duk na ganka haka nan..? Waima tsaya Ina ka shige ne mukaita neman wayarka.. Banjika ba Throughout the day. Nasan nasan dai munyi waya kace zaka duba Prison wajen Yusuf.. Ban sake jin d’uriyarka ba.. Ko wani classified mission d’in ne ya rik’eka..?”
D’an furzar da huci yai yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa “Komai ma ya faru yau d’in kaikam..” Ya fad’i yana d’an dafe motarsa kad’an suna fuskantar juna shida Assad.
Assad ya gyara tsayuwarsa “Ban gane ba.. Wane irin komai ma ya faru..?”
“Abubuwa da dama Assad..” Ya fad’i yana d’an rage girman idanunsa yana jinjina kansa kad’an “Na fad’a maka Safeenah nada ciki..?”