← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 175

Sashe 75

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’wafa Mommy tai kafin tace “Ba dai kin tare gidan miji ba.. Ke ga mai miji ya miki kyau Safeenah.. Ni mai zan ce miki bayan Allah ya kad’e fitina tinda kedai bakisan ‘yancin kanki ba.. Ke gaki ‘yar dad’i miji.”

Safeenah tace “Kai Mommy.. Let bygones be bygones.. My Halaal ma komai ya wuce wajensa.. And I don’t think yana tare da wancan shegiyar..”

Katseta Mommy tai da fad’in “Ke dallah rufe mun baki shashasha.. Wani Your Halaal kika samu.. Indai namiji ne Sai ya baki kunya gaki ga shi.. Kin karb’ar ma kanki ‘yanci ma ya kika k’are hannun namiji balle ke da kika kai masa kanki Bayan duk kalan rashin mutunci da ya zabga miki..”

“Mommy nifah bani na kawo kaina ba.. Daddy ne ya kawoni.. Mommy ni duk bama wannan ba.. Kira nai nace ki turo min d’aya cikin yaranki my Halal yace ina buk’atar Help..”

Ji tai kaman ta buge Safeenah ta cikin wayar “Kinci ubanki dake da Halal d’in naki.. Baza’a turo ba..” Tai maganar tana dak’uwa da hannunta kace Safeenar tana gabanta ne.

Safeenah Ta kuma turo baki tace “Ba damuwa Mommy zamuyi hiring a registered company.. Zan fad’awa My Halal..”

Katseta tai da fad’in “Kika k’ara ce mun wani My Halal zan fasa bakinki ta cikin wayar nan.. Doluwar banza ya gama cutanki kin d’ibi jiki kinje kina zama dashi.. Ina Mu’azzam d’in yake..?”

Baki a ture Safeenah tace “He’s having a shower.”

“Toh idan ya fito ki kirani ki sanya wayar a handsfree zan masa magana kinji koh..”

Safeenah ta jinjina kai tace “Alright Mommy..” Daga haka katse kiran tai ta kuma mik’e k’afafu nan saman gadon tana jiran fitowarsa. Jim kad’an ya fito yana tsane jikinsa, shi a zatonsa ma Ta fice a d’akin. Ya d’an dubeta da gefen ido kafin yaci gaba da abinda yake.

“Mommy tace tana son magana dakai yanzu..” Tai maganar tana mai nufosa.

“Tace idan ka fito I should call her back.”

Jinjina kai yai yace “Ehen.. Kirata mana.”

Safeenah Ta jinjina kai kafin Ta janyo wayarta ta soma dialing layin Mommy.

Bugu d’aya a na biyu Mommy Ta d’aga.

Safeenah tasa a handsfree kaman yanda Mommy tace d’in.

A zaton Safeenah Mommy zatai maganar ‘yar aikin da Mu’azzam yace a turowa Safeenah ce saiji tai Mommy ta soma fad’a ta yanda take shiga bata nan take fita ba “Kana jina Mu’azzam koda wasa kar ka kuskura kazo kusan d’iyata ba tareda ka kawo min shaida daga asibiti cewa baka d’auke da cutan zamani ba.. Wllhi kaji na rantse maka idan ka kuskura ko rik’e hannun Safeenah kai ba tareda ka kawo min shaida daga asibiti cewa baka d’auke da cutar kanjamau ba Allah ya isa ban yafe maka ba..!”

Safeenah Ta kame bakinta da hannu tana girgiza kai.. Kaman Mommy na ganinta tace “Idan kika katse wayar nan ke kuma sai na tsine maki.. Kuma Idan kika kuskura kika..” Basu k’arasa ji ba sai kururuwar Mommy suka jiyo tana fad’in “Dan na fad’i gaskiya.. Akan Mu’azzam ne yau zaka d’aga hannu ka ma...” Mu’azzam bai bari Mommy Ta k’arasa furta kalmar mari ba ya katse kiran d’if.

Ashe Daddy ne ya shigo yajita tana wannan maganganu shine ya fuzge wayar ya had’a mata da mari.

Safeenah ta sadda kai tana hawaye. Mu’azzam kaw kaman babu abinda akai yaci gaba da shirinsa. Zuciyarsa yana nanata kalaman Mommy wai shi Mu’azzam akema zargin cuta.. Har Mommy tana masa iyaka da d’iyarta bayan ma Safeenar albarkacin Daddy taci shiyasa aurensu bai k’are ba.

“My Halal please talk to me..” Safeenah tace tana k’ok’arin matsowa kusansa.

“Bakiji mai Mommy tace bane..? Kiyi hak’uri sai na kai mata takardan gwajin lafiyata kaman yanda tace..”

Saurin girgiza kai Safeenah tai tace “Dan Allah kai hak’uri da Mommy my Halal..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo hannayensa.

Dakatar da ita ya kumayi ta hanyar d’aga mata hannu “Don’t Safeenah.” Ya fad’i yana d’ago hannunsa guda.

Baki a ture Safeenah tace “But you are my Halaal..”

Ya jinjina kai yace “Of course amma Mommy bata yarda da hakan ba..”

Safeenah ta goge hawayenta tace “Amma ai Mommy batada hurumin da zata haramta mana juna.. Dan Allah kar ka azabtar damu kan maganganun Mommy..”

“Bazan saka ma ‘yarta cuta ba.. Zo ki fita ..” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa.

Kuka ta fashe dashi daidai sanda wayar Mu’azzam d’in ya soma ringing. Daddy ne mai kiransa.

Ya d’aga cikeda risinawa Safeenah Ta lab’e tana sauraron wayar.

Jinjina kai yai cikeda girmamawa yace “Alright Daddy.. Zan taho yanzu..” Daga haka k’arasa shiryawansa yai cikin k’anan kaya gray polo sai blue jeans..

Bai bari Safeenah taji fitarsa ba dan baida lokacin dramarta.

Yana isowa gidan Daddy ya hangi Musaddiq zaune balcony d’in side d’insu shida Musaddiq d’in. Ya k’urawa Musaddiq d’in idanu wanda ko ba’a ce maka ba cikin damuwa yake. Take tinanin hular B.A.T ya fad’o masa.. He needs to find out shin Musaddiq nada alak’a da Danger ne kokuwa dai wasa da hankalinsa Danger yake.. Da wannan tunanin ya nufi b’angaren Daddy.

Yana dosowa ya soma jiyo hayaniyar Mommy tana fad’in tinda Daddy ya d’aga hannu ya Matera kan D’aniskan yaron nan wllhi sai ta bar gidan.. Saidai duk abinda zai faru ya faru..

Fasa shiga Mu’azzam yai ya nufi b’angaren Musaddiq.

A balcony d’in ya taddasa.. Yai masa sallama. Da k’yar Musaddiq ya iya amsawa kana ganinsa zaka fahimci cewa he’s not himself.. Gaba d’aya a dama yake.. Ba komai yake tunawa ba face tattaunawar Uncle Salman da Daddy. Maganganun suketa Yawo a kwanyar Musaddiq kaman zasu tarwatsa masa kwanya ga Daddy yace ko da wasa kar ya sanar da Mu’azzam wani abu for their family’s sake.

Ya k’ak’aro murmushi daidai sanda Mu’azzam d’in ke zama kujerar gefensa “Detective.. Yaushe ka shigo.?” Musaddiq ya tambaya yana dubansa.

K’ura masa idanu Mu’azzam yai yana karantarsa kafin ya d’an girgiza kai yace “Are you alright..?”

Haka kurum Musaddiq yaji tambayar ta mugun razanasa.. Gani yake kaman Mu’azzam yana iya reading mind d’insa.. Gaba d’aya a daburce Musaddiq yake.. Wata zuciya tana ce masa ya sanar da Mu’azzam abinda yaji wata zuciya tana ce masa kar ya fad’a domin kaman yanda Daddy yace hakan can destroy Mu’azzam harma da ahalinsu..

Ajiyan zuciya ya sauk’e yana mai d’an fuzar da fuci kad’an lokaci guda ya kuma d’agowa yana duban Mu’azzam d’in wanda shima idanunsa k’ar akan Musaddiq d’in yake zuciyarsa fal tunanin hular da ya tsinta a business location d’in Danger.

“Musaddiq.. Are you alright..?” Mu’azzam ya kuma tambayarsa a karo na biyu.

D’agowa Musaddiq yai yana dubansa kafin ya furta..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*40*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Musaddiq ya girgiza kai kad’an yana mai sakin murmushi “I’m good..”

Jinjina kai yai a hankali kafin yace “Mun kwana biyu bamu kasance tare ba.. Do you have plans for tonight.. Let’s have dinner together..”

Musaddiq ya murmusa kafin yace “Anya kuwa yau d’in nan..”

Mu’azzam ya tsaresa da idanu sosai yana karantarsa, ya murmusa kafin yace “Why.. Ko Kanada wajen zuwa ne.?”

Ya kuma sakin murmushi kafin yace “No Fufore nake son komawa gobe.. Na gaji da garin nan nafi sabawa da can a halin yanzu.. Yanda babu tashin hankali babu damuwa babu komai sai kukan dabbobi da tsintsaye.. Idaniya bata kallon rikici da tashin hankali Sai ciyayi masu kyau masu sanya natsuwa ma zuciya..”

Mu’azzam yai masa K’uri yanda yake maganar. Jinjina kai yai a hankali kafin yace “Kayi gaskiya.. Tinda gobe kake son komawa ka tashi yanzu ka shirya sai Mu d’an fita tare maybe you can get rid of this negative energy.”

Musaddiq ya murmusa kafin yace “I can’t say no to my brother.. Ya mik’e yana murmushi. Idanunsa akan Mu’azzam d’in. Shima Mu’azzam d’in murmushi yake yana dubansa.

Musaddiq yace Bara ya shiga ya k’ara wanka.. Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin yace “Zan duba Daddy kafin ka fito..”

Musaddiq na shigewa bathroom Mu’azzam ya dawo closet d’in Musaddiq d’in yana duba ko zaiga hular Musaddiq mai d’aukeda rubutun B.A.T.. Bai gani ba dan cikin sauri sauri yake gudanar da komai..

Aljihunsa ya zira hannu ya zaro nylon k’arama ya zira hannayensa cikin gloves kafin ya isa yanda hair brush d’in Musaddiq ke ajiya ya zari gashi guda daga cikin hairbrush d’in yai saurin zirawa cikin ledar ya tura ledar a aljihunsa kafin ya fice daga d’akin yana zame gloves d’in da ya rufe hannayensa dasu.

Yana isowa b’angaren Daddy ya tadda Daddy shi kad’ai ne wannan karon. Ya zauna daga can gefen k’afafun Daddy suka gaisa.

Daddy ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kafin ya soma fad’in “Kai hak’uri da abubuwan da Hajara tai maka Mu’azzam.. Bata kyauta ba, kuma na maka alk’awari bazata sake shiga hurumin gidanka ba..”

Mu’azzam ya girgiza kai yace “A’a Daddy babu komai.. Ai komai ya wuce.. Kuma ko meye Mommy zata mun bazan tab’a daina ganin k’imanta a idanuna ba ko dan shekarun da Ta shafe tana jinyar mahaifiyata.. Abinda yasa take haka yanzu ba komai bane.. Fushi take dani sabida abinda naima Safeenah.. Daddy dan Allah kuyi hak’uri. Nasan ban kyauta ba amma dan Allah kuyi hak’uri..”

Daddy yai masa k’uri yana dubansa kafin ya girgiza kai yace “Dan kayi aure Mu’azzam bakai laifi ba.. Kuma bamu da hurumin da zamu haramta maka abinda Allah shi halatta maka. Ni wasilcin da zan maka shine adalci.. Tabbas Allah shine shugaban masu adalci, kowa saidai ya kamanta... Kai k’ok’ari ka kamanta adalci tsakaninsu.. Wannan shine nasihar da naso Yi maka.. Amma sai naji wani batu wanda ya girgiza ni Wai ka d’auki Salman ka wakiltasa ya karb’ar maka aure ina nan a garin nan.. Ka tsallake ni baka sanar dani komai ba sai ka tafi ka d’auko Baffanka Salman ka wakilta sa.. Mu’azzam ko na maka wani laifi ne..?”

Jikin Mu’azzam yai matuk’ar yin sanyi.. Ya d’ago yana duban Daddy, duk sai yaji bai kyauta ba.. A hankali ya sadda kansa kafin ya soma fad’in “Daddy kai hak’uri.. Bazan iya tunk’ararka nace ka amsar min aure bane alhalin ko tarewa Safeenah batai ba shiyasa na tafi wajen Uncle Salman.. Banyi haka dan k gaza ba Daddy.. Sai don gani nake hakan tamkar ya zama cin fuska ne..”
Chapter 75 · 0% Book details