Sashe 156
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Marwan yakan kai aike Daga wajen mahaifinsa zuwaga Baban Hajara Malam Ba’i wanda shi dama baida wani k’arfi. Abinka da mutanen da, ga yawan alheri da kamanta rik’o da uzumunci tsakani da Allah... Yawan aike gidan da yake kaiwa daga wajen mahaifinsa zuwa wajen Baban Hajara dake Birnin Yola dan dama su Hajara a cikin garin Yola suke, a nan Hajara Ta k’yalla idanu akan Marwan, nan taji gidan duniyar nan babu wanda take so irin Marwan, shi kuma tinda ya rasa Nuratu ya sadaukar da soyayyarta ma D’anuwansa sai magana soyayya da aure ya fita kansa, dan Nuratu ita d’aya ce sann tin sanda ya rasata zuciyarsa ta dasashe tai duhu indai abinda ya shafi soyayya ne. Baijin akwai fitilar da zata kuma haskata.. Baijin akwai wata mace da zata kuma haska zuciyarsa. Mahaifin Hajara ya nuna yana so ya basa auren Hajara. Ba d’abi’arsa bace cewa a’a ma Babba uwa Uba ga Inne ta taso masa da maganar aure ganin yafi son zaman Abuja tin sanda suka bud’e Gamji Dairy Factory a Abuja.. Shi kuma ba komai yasa yafi son zaman Abuja ba Sai dan baya so ya dinga ganin Nuratu tinda ita d’in matar D’anuwansa ce kuma ta haramta a garesa matuk’a D’anuwansa na aurenta..Sann ko tinaninta ma saida yai da gaske da addu’o’i kafin ya daina mafarkanta da tinaninta.. Koda ace ba D’anuwansa take aure ba haramun ne tunaninta a garesa kasancewarta matar aure. Da kyar ya samu Allah ya taimakesa tinanin Nuratu ya daina bijiro masa Amma har dai zai sakata a idanunsa dole yaji wani abu ya gifta masa, dole yaji wani haske ya haska b’angaren zuciyarsa koda na sakanni ne.. wann wani abu ne da Allah ya gani yayi iyaka k’ok’arinsa amma ya kasa, sann muddin Nuratu D’anuwansa take aure dole ya dinga ganinta lokaci zuwa lokaci.. Marwan ya shiga damuwa sosai yana tsoron kar Ubangijinsa yai fushi dashi. Nuratu ba tasa bace kuma ita d’in ta haramta a gareshi...Ya kamata ya amshi wann K’addarar kaman yanda ya amshi k’addarar sadaukar da soyayyarta. Cikin k’ok’arin ganin ya guje ma ire iren wann tunani da zuciyarsa ke bijiro masa yasa yai Na’am da auren Hajara d’iyar Malam Ba’i Watak’ila auren zai iya Sa ya mance Nuratu gaba d’aya. Toh ga Inne ma bata son zamansa a Abujan Babu aure hakan yasa bai k’asa a gwiwa ba, nan take ya sanar dasu Inne ya samu mata gashi kuma mahaifinta abokin Baffansa ne da sukai Tsangaya tare dikda cewa Inne ba wani san aurensa da Hajaran take ba amma hakan yafi mata zamansa a Abuja babu aure. Ita tafi so ya nemo ‘Yar babban gida kaman yanda shima yake D’an Babban gida, babu yanda ta iya tinda Hajaran ya kawo nan ta amince da batun auren.
Hajara Taita magiya wa Malam Ba’i cewa ayi a saka aurensu da Marwan dan gani take kaman Malam Ba’in ba wani son auren yake ba, kaman ma so yake a rushe maganar.. Hankalinta ya mugun tashi ganin tayi babban sa’a da dacen samun Miji irin Marwan Gamji wanda ya had’a komai da zai iya neman ko wacce irin mace.. Da k’yar Malam Ba’i ya amince zai saka Rana amma da sharad’in zai sanar da Marwan da iyayensa gaskiyan cewa ba shi ya haifeta ba shima a titi ya tsincesu itada D’anuwanta Muttaqa.. Aiko Hajara bataso ya tona mata asiri balle uwar Marwan tace an fasa auren tinda batada asali balle tushe. Ita kaw a yanda take jin son Marwan komai zata iya yi.. Wani rana K’aninta Muttaqa ya dawo gida yayi shaye shayensa ya taddata tana kuka nan take sanar dashi ga abinda Baba Ba’i yace kaman yanda suke kiransa.
Mutaqqa yace “Kam Burauba wann gidan masu kudin zaki bari wann D’anisakan tsohon ya miki sanadi wanda nasan ba ke kad’ai ba har ni zan warke idan kikai aure a ahali irin na Gamji.. Wllhi trailer na Wiwi zan dinga sauk’ewa a Birnin tarayya.. Kar ki damu babu wanda zai tab’a sanin ni k’aninki ne Sana’ata kawai zan dingayi idan kika bani jari.. Ai kawai mu murk’ushe D’anbanza mu gama dashi.” Ya fad’i yana wani bubbud’e hannaye yana tangad’i.
Hajara ta zaro idanu tace “Amma Muttaqa mutumin nan fah shi ya taimake mu sanda muka kashe iyayenmu da gobaran da muka kunna ni da kai kan Muna kokawa akan gayan tuwo.. Idan muka kashesa ai mun masa butulci..”
Tsaki Muttaqa yaja yace “Ina butulcin yake.! Ki kira min shi naci Buraubansa.. Ki tsaya kiyi ma kanki.. Yo mun kashe namu iyayen ma garin kokawa balle wani D’aniskan tsoho mai nema ya mana bak’in ciki.. Ke ni fah ko cikin abokai Danger ake kirana.. Billahillazi dik yanda na taka bala’i ne..! Wllhi tinda na tashi wutan da ya kashe iyayena babu uban da bazan kashe ba..”
Hajara Ta jinjina kai tace “Gaskiyanka ne Danger.. Bani mancewa garin kokawa ni da kai muka ture acibalbal ya k’ona iyayenmu har lahira cikin bukkansu muka rasasu.. Sann ‘Yan k’auyenmu suka koremu daga kauyen.. Toh kuwa da na rasa Marwan Gamji wllhi gwara na murk’ushe wann Shegen Dattijon kawai mahassadi mai nema ya min bak’in ciki.”
Muttaqa ya bushe da dariya kafin suka shirya yanda zasu kashe Malam Ba’i.. Dare yanayi suka shiga suka dannesa da pillow, Hajara Ta rik’e gefe d’aya Muttaqa ya rik’e gefe d’aya suka gama da Malam Ba’i.
Koda labarin mutuwan Malam Ba’i ya riski Marwan da ahalinsa basu janye k’udirin auren Hajara ba, dangin Malam Ba’i su suka bada auren Hajara ma Marwan Gamji bayan Muttaqa ya gargadesu da cewa dik shegen da ya tona ma ‘Yaruwarsa asiri Sai ya tsire masa wuya. Hakan kuwa akai ko tari babu wanda yayi akan asalin Hajara.. Akai aurenta da Marwan Gamji ba tareda sunsan tanada wani D’anuwa Muttaqa ba. A nasu tinanin ita kad’ai ce d’iyar Malam Ba’i. Anayin aure basu jima ba suka tafi Abuja.
Saidai duk irin soyayyar da takewa Marwan Gamji a nasa b’angaren ba haka bane. Yanda tai zaton zata iya canza miskilancinsa abu yaci tura ga wutan k’aunarsa kullum ruruwa yake cikin zuciyarta. Tana tsananin son Marwan Wanda dashi da dukiyar ahalinsu batasan waye tafi so ba, idan aka ajiye mata dukiya aka ajiye mata Marwan batasan waye zata zab’a waye zata bari cikinsu ba. A haka suna zaune ta kula Marwan bai faye son zuwa Adamawa ba. Saidai ita yakan barta ta tafi taje ganin gida.. A nan take samu taga D’anuwanta Muttaqa idan ta tafi Adamawa. Dik tafiya da zatai sai ta kai masa Aiken kud’ad’e da shike a wancan lokacin babu wani ci gaba na ture turen kud’ad’e through bank account masu asusun banki ma Sai wane da wane ba kowa da kowa bane. A haka Muttaqa ke bunk’asa kasuwancinsa na miyagun k’wayoyi har ya soma kafuwa kan k’afafunsa. Bayan lokaci k’ank’ani ya tattara ya bar zaman Adamawa yau shine can gobe shine nan yana kasuwancinsa na saida miyagun k’wayoyi yana ci gaba da bunk’asa had’ida zama rik’akk’en D’antadda.
A haka Hajara bata gane ma Marwan har suka fara hayayyafa.. Juyin duniya idan Hajara zatai Marwan ya sanar da ita abinda ke damunsa bazai sanar da ita ba. Ta rasa wani irin miji take aure wanda aikinsa ma ya fita mahimmanci a wajensa, ga azaban k’aunarsa da kullum yake ruruwa cikin zuciyarta tana jin babu abinda bazata iya ba Ta mallaki zuciyarsa kaman yanda Ta mallaki gangar jikinsa da katafaren gidansa. Ta soma tunanin ko wasu Matan ke d’auke masa hankali a waje amma ta kula kaman matan ma basa gabansa dan tasha gwadasa amma bata ganin komai.. Daga k’arshe ta yanke shawarin tambayarsa abinda ke damunsa tana kuka tana masa magiya cewa ya sanar da ita idan ta gaza ta wani waje ne Ta gaji da rayuwa dashi kaman hoto a cikin gida.. Ko hira basayi saidai idan ta buk’aci hakkinta ya bata.. Sann idan ba itace Ta kawo masa kanta ba bazai tab’a nemanta ba.. Ta kula ba don girman nauyin sauk’e hakki ba ma da bazai dinga kusantarta Ta ba.. Ta kula kaman auren manufa yayi da ita ba wai auren soyayya ba. Dan komai na jin dad’in rayuwa gashi nan amma babu d’igon soyayyar miji wanda take jin sonsa kaman zai hallak’ata. Ita ko a labarai bata tab’a cin karo da irin mijinta ba, mutumin da zasu rayu k’ark’ashin kalmar aure ko magana baya shiga tsakaninsu kuma ba wai gaba yake da ita ba, idan ba ita ta tambayesa abu ba toh ko Shekara za’ai a haka bazaiji muryar Marwan ba.
Amsar da yake bata ko yaushe shi ya sake bata cewa babu komai sann yaci gaba da aikinsa.
Hajara ta mik’e tana hawaye. Tana jin jinjirarta Safeenah na kuka amma tak’i tabi takanta.. Aiko nan taga Marwan ya shigo ya d’auki d’iyarsa yana lallashi dan dik wann rashin kulata da Marwan keyi baya haka da yaransa. Sosai yake nuna masu k’auna tare dasu ne ma take ganin murmushinsa mai mugun kasheta. Nan ta fahimci Lagon Marwan ‘Ya’yansa ne tai k’wafa tace zatai amfani da yaran nasa taji cikinsa da yake b’oye mata tsawon shekaru.
A haka wani rana ta k’yale Safeenah tana rarrafe ta kusan kama Dustin guga mai zafi.. A ranan taga b’acin ran Marwan irin wanda bata tab’a gani ba.. Ta fashe da kuka tana fad’in idan yana son ta kular masa da yaransa yanda ya kamata itama sai ya kular da ita yanda ya kamata. Taci gaba da fad’in “Ba fita k’asashen waje bane kawai.. Ba shiga jirgi da motoci masu tsada ba.. Nima Ina son kula daga wajen mijina kaman yanda ko wace mace ke samu.. Ka duba Hamma da Nuratu idan mukaje Fufore kaman zasu had’iye juna amma mu kaman mak’iya aka ajiye..”
Sunan Nuratu da Ta ambata yasa Marwan daka mata tsawa da fad’in “Ya isheki Hajara..!” Lokaci guda yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Na baki duk iya Farin cikin da zan baki Hajara.. Bazan iya baki fin haka ba.. Kinsan dalili..? Dalili shine Zuciyar babu wani Haske na soyayyar wata d’iya mace..Ni Marwan na rufe wann babin.. Ita d’aya ce wann Hasken.. Kuma haskenta ya disashe.. Har abada ya disashe..! Kin fahimta..” Ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa.