Sashe 175
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Saurin jinjina mata kai yai yana mai aje jaririyar gefenta a hankali “Go to Maama Jewel.”
Ta soma yunk’urin d’agowa yai saurin taimaka mata ta d’an karkato kad’an tana duban fuskar yarinyar. Sai taji hawaye na zuwa mata.. Batai zaton ita ko abin cikinta zasu tsira daga hannun Mommy da Danger ba. Allah sarki ashe da rabon zata bud’e idanu har taga d’iyarta. Ganin yanayin da Ta shiga yasa Mu’azzam d’an kifowa kad’an ya masu runfa ya rungumesu. Sai yana jin wani abu mai kama da rauni can k’asar zuciyarsa. Ahalin da Mommy taci burin tarwatsawa sai gashi Allah ya had’e fuskokinsu da alkhairi.. Sadiya ta d’ago tana duban fuskarsa hawaye na gangaro mata lokaci guda tana murmusawa. Shid’inma dubanta yake yana murmushi yana kuma duban d’iyarsu.
Ta kuma kai dubanta ga jaririyar daketa tsotson yatsun hannunta. Ta sumbaci goshin yarinyar tana mai lumshe idanu a hankali. Yayinda shima ya sumbaci goshin Sadiyar yana mai lumshe nasa idanu. Lokaci guda yana kad’aita Ubangijinsa cikin zuciyarsa da wann baiwa da yai masa.
Sadiya ta dubesa sai ta girgiza kai kad’an tace “Ina Safeenah..?” Dan ta kula tambaya na biyu kenan da tai masa gameda Safeenah bai amsa ba.
Sosai ta tsare fuskarsa da idanu, dan tuni fuskar tasa ta canza.
Hannunta ya kamo a hankali had’ida kwantar da murya ya soma da kwantar mata da hankali. A natse yake sanar da ita cewa sun rasa Safeenah ga abinda ya faru. Hawaye ne suka dinga ambaliya a fuskarta.
Lokaci guda take furta “She saved us all.. Safeenah ta sadaukar da rayuwarta ne garemu baki d’aya.”
Mu’azzam ya jinjina mata kai a hankali yana mai goge mata hawayenta. “Yes Safeenah ta mana sadaukarwa mai girma.,” Ya fad’i yana mai kwantarta jikinsa. Haka ta kwanta cikin jikinsa tana zuban hawaye mai ban tausayi da alhinin rashin Safeenah wacce basu tab’a samun jituwa ba sai ranan da Safeenar zata bar duniya.. Allah sarki rayuwa kenan, yau mune gobe ba mu ba. Ka zauna da kowa da alkhairi Dan baka San waye zai taimakeka a rayuwa ba.
Nan jaririyar ma ta soma kuka. Mu’azzam ya had’esu duka ya rungume, dai dai nan kuma Dr ya shigo. Yanayin da ya gansu ciki sai yaji tausayi ya rufesa shima.
Sadiya ta d’an zame jikinta tana gyara kwanciyarta. Mu’azzam ya mik’e yana k’ok’arin saita kansa had’ida bawa Dr hannu sukai masabaha.
Dr ya soma duba Sadiya yana fad’in Masha Allah. Jiki yayi kyau sai sallama.
Yakai dubansa ga jaririyar dake rik’e hannun Mu’azzam yace “An mata suna ne..?”
Mu’azzam ya dubi Sadiya sai kuma ya girgiza kai alamun a’a.
Baikaiga juyawa ba suka sinkayo muryar Sadiya tana fad’in “Safeenah.. Sunanta Safeenah..”
Mu’azzam ya juyo yana dubanta murmushi mai gauraye da tsantsan tausayi saman fuskarsa. A hankali yake jinjina kai yana duban Dr “Sunanta Safeenah Dr..”
Dr ya murmusa kad’an kafin yace “Allah sarki.. Allah ya raya mana little Safeenah ya kuma jik’an Safeenah babba.”
Dukansu suka amsa da Ameen.
Sunan Safeenah da Sadiya da Mu’azzam suka saka ma d’iyarsu sosai hakan yaima illahirin ahalin dad’i. Ranan suna Malama Hafsa wacce tai ma Mamy magani tin daga Fufore tazo dan an zama ‘Yanuwa, nan Tai wa’azi mai ratsa zuciya. Ta k’arada “Allah ya raya Safeenah ya kuma jik’an Safeenah.. Tabbas mutuwa wa’azi ce ga masu hankalta.. Mu sani cewa dukkanninmu a GIDAN ARO muke.. Yanda Safeenah ta tafi duk muma muna tafe.. Duk mai rai mamaci ne sann duk dad’ewarka a duniya akwai ranan da zaka barta ka shirya ko baka shirya ba. Gidan duniya gida ne na tanada guzuri domin tafiya gidan gaskiya ba gida ne na baje Koli ba kaman yanda da yawanmu muka d’auka har muna mance cewa aronsa aka bamu na wutin gadi akwai ranan da za’a amshe wann gida daga wajenmu muna so ko bama so.. Allah kasa mu dace duniya da lahira.. Ameen.”
A can b’angaren Mommy kaw tana prison babu k’afafu, duk wacce ta gani mai irin shekarun Safeenah a prison Sai ta hau rarrafawa tana binta tana k’ok’arin janyota tana fad’in “Safeenah Feenah na kar ki tafi ki barni.. Safeenah Safeenah na..!” Duk ‘Yar matashiyar da Ta gani cikin prisoners d’in haka take binta taita kiranta Da Safeenah tana fad’in bazata mutu ta barta ba. Abinka da gidan kasu wanda da yawansu b’ata gari ne suna jin ta fara jawosu tana kiransu da Safeenah sai kaga Sun taketa sun nausheta suna tattakata da shike ba k’afafu ne da ita ba.. Sai kaw kaji an saki shewa ana tafi dan dama wann d’abi’ar gidan kasu ya gada.
Yauma ta biyo wata kenan tana rarrafowa tana janyota tana kiranta da Safeenah budurwar Ta juyo babu ko tausayi ta shek’awa Mommy zazzafan kunun dake rik’e hannunta tana hankad’ata da k’afarta “Shegiya uwar naci mayya ni kar ki cinye ni.. wann da gani mayyace..”
Haba nan fah sauran Prisoners d’in suka d’auki shewa suna tayata aibata Hajara. Daga masu watsa mata gayan tuwo sai masu watsa mata zazzafan kunu da miyar kuka harda masu watsa ma Hajara najasa. Sunati suna tattaketa tana sakin ihu tana birgima da dungulumin k’afafunta a wajen ba abin Ta tashi Ta gudu ba. Haka sai sunyi mata lilis kafin jami’an gidan yarin su kawo mata d’auki kowa ya arce a guje a bar Mommy nan wajen tana juyi tana kuka. Haka dai kwanyar Mommy ya zama kaman ya tab’u kullum cikin ambaton Safeenah take tana fad’in Muttaqa ya kashe mata d’iya akan idonta. Har wak’an mahaukata prisoners suke mata suyita mata dariya su janyota toilet suna ce mata tazo ga Safeenah.. Sai Mommy ta rarrafo a guje zataga Safeenah sai su shek’a mata najasa ko ruwan datti ko wani abu mai muni su kuma kwashe dariya idan Ta fara mirginawa da gundulumin k’afafunta.
Rayuwa kenan, dama abinda ka shuka ko shakka babu shi kake girba. Allah ka bamu ikon shuka alkhairi domin mu girba da kyau Ameen.
**
Bayan shekara guda aka soma gudanar da shirye shiryen Bikin Musaddiq da Ajidde, Barr Ameer Dikko da Meema. Kafin nan saida akai Bikin Assad da Sabeera dan Assad bai hak’ura ba. Garin masoyi baya nisa saida yaje har Dutse ya nemi auren Sabeera ya kuwa yi sa’a Sabeera rabonsa ce. Sabon babin amintakansu ya kuma k’ullawa da Sadiya, suka mance komai suka d’aura k’awancensu daga yanda suka tsaya. Ga mazajensu ma Aminan juna abin sai ya dad’a k’ayatarwa.
Shirin biki ake kanyi gidan gaba d’aya a cike yake da bak’i.. Amaren gaba d’aya suna a nasu d’akin da aka ware dan shiryasu nan Sashen Inne dake Abuja kafin Su d’aga Fufore next week.
Sai zolayan Ajidde suke zata tarkasa ta tafi Turai susha iska da shak’iyancinta.
“Ni fah wllhi ba zuwa turai d’in bane kaje kaga ‘Yaniskan turawa..” Ajidde tace tana rapka uban tagumi. Suka dara kafin Meema ta d’anyi shiru cikin sanyin jiki dan sai ta tuna Addah Feenanta sanda sukaje Fufore Ajidde tace ta kama Safeenar da Mu’azzam suna sumbatan juna Wai abinda ‘Yaniskan turawa keyi ba tareda tasan mijinta bane.
Ajidde ma sai tunanin abin ya fad’o mata Ta d’an dafa Meema tace “Allah Sarki Safeenah.. Kema kin tunata koh..?”
Meema ta jinina mata kai a hankali tana goge k’wallan da suka ciko idanunta. Lokaci guda ta murmusa tace “My Addah Feenah.. Ina missing d’inta sosai..”
Ajidde tai k’ok’arin maida k’wallarta itama kafin tace “Kiyi hak’uri Meema kiyi mata addu’a duk sanda kika tunota.. Allah ya gafarta mata mu kuma idan namu yazo yasa mu cika da imani.”
Meema ta amsa da Ameen. Daidai lokacin Sadiya da bata jima da ficewa ba ta shigo rik’eda little Feenah. Aiko yarinyar tana ganin Meema ta soma d’ago mata hannu alamun tana so ta amsheta. Nan Ta tafi da sauri ta amsheta tana cillata sama yayinda Sadiyar ta kuma ficewa.
“Oh my Adda Feenah dole a bani Ke mu tafi Katsina tare.” Meema ta fad’i haka tana cilla yarinyar kasancewar Ameer d’an Katsina ne.
Ajidde tai karaf tace “Tabb waye zai baki Jewel d’in.. Badai Kofur Zalimu ba dan wann yarinyar zuciyarsa ce.”
Sadiya da waya Ke mak’ale kunnenta lek’owa tai ta dubi Ajidde tace “Gashi a waya yana jinki maimaita..”
Ai tuni Ajidde ta soma sakin salati tana fad’in ta shiga uku.. A d’ari ta duk’a saman gwiwoyinta ta bud’e murya tana fad’in “Yaya wllhi na tuba.. Na rantse da Allah ba dakai nake ba.. Da Kuran tashe nake..”
Musaddiq ne ya lek’o ya wani tsime yana fad’in “K’aramin danganki ko.. Zaki maimaita ne yarinya idan muka haye gajimare.”
Inne ta k’araso tana janye Musaddiq had’ida kamo kunnensa kad’an “Wann wane irin ango ne ni Mairo.. Wa ya gayyato ka nan..? Shige muje.. Kar na sake ganinka a nan har mu bar garin nan..”
Musaddiq ya saki k’ara yana kame kunnensa da Inne ta kame.
Haka sukaita dariyar Musaddiq da Inne har suka fice.
**
A can FCID kuwa Zaune yake cikin sabon ofishinsa wanda ya kasance Ofishin Chief Jaja a baya. Ya soma bud’e wani magazine nasu na Yansanda wanda aka raba masu a wani babban taro da suka gudanar , ciki harda hoton Chief Jaja Yusuf da kuma Maleeka. Dukansu dai gasu nan Sun bayyana cikin magazine d’in. Ya k’urawa magazine d’in idanu yana tuna gwagwarmayar da suka faru a baya, yau babu Chief Jaja babu Yusuf snn babu Maleeka... Yaita tuno abubuwan da suka faru, gwagwarmayar da suka kwashe taredasu Jaja harma da Yusuf da Maleeka wacce itama Ta zama victim na Mommy da Danger.. Ya furzar da huci a hankali yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. A haka Assad ya k’araso ya samesa, ya sara masa yana mai mik’a masa report na new case d’in da suke handling wanda Mu’azzam d’in Ke jagoranta. Assad ya sauk’e idanunsa kan magazine d’in wanda aka raba masu Yansanda a wani taro na musamman da suka gudanar. Dukansu suna sanye cikin Uniforms d’insu fuskokinsu cikeda annashuwa had’ida burin serving k’asarsu da Al’umman cikinta..
Assad ya d’an girgiza kai yace “Kalli fuskokinmu, ko wanne yana cikeda Farin ciki da burin bada gudumawa ma k’asarsa da Al’umman cikinta.. Saidai kash zuciya takan rinjayemu a wasu lokutan Ta sauya mana akalar tunaninmu har mu aikata aiki irin na danasani.. Allah yaci gaba da cire gurb’atattun Jami’an tsaro cikinmu domin kawo sauyi a k’asarmu baki da Al’umman cikinta.
Mu’azzam ya amsa da Ameen yana mai rufe mujallar.
Hakan yai daidai da na rufe nawa Labarin mai taken GIDAN ARO.
ALHAMDULILLAH!
_A nan na kawo k’arshen wann labari mai taken GIDAN ARO. Kurakuren dake ciki Ina rok’on Allah ya yafeni. Fad’akarwan dake ciki Ubangiji ya amfanemu dashi baki d’aya. Ameen thumma Ameen.!_
_To all my fans, na gode na gode matuk’a da nuna K’aunarku gareni.. Rabbi ya bar k’auna yasa mu gama da GIDAN ARO lafiya.. Ameen thumma Ameen. Sameena Ke maku fatan Alkhairi!_
SameenaAleeyou📚