← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 175

Sashe 26

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajidde tai zuru tana jiran taga ko Inne zata fice amma bata fice ba, dik addu’an da take cikin zuciyarta matar ta fice daga d’akin domin ta gudanar da abinda Kyallu ta turota tayi amma tak’i ficewa. Har Hindu ta k’araso da k’aramar kwano ta mik’a ma Ajidde. Ajidde ta amsa tana mata godiya. Har lokacin dai Inne na zaune saman kujera mai kallon gadon Aunty Nuratun Ita kaw Ajidde tana zaune gaban gadon tana k’ok’ari ciro had’in maganin.. Wani ruwa cikin gora irin wanda ake fafewan nan ta ciro.. A hankali ta soma zuba ruwan cikin kwanon.. Saida ta ida zubawa kafin ta ciro had’in maganin tana tina bayanan yanda ake had’a maganin daki daki.. Tana ida had’a maganin ta rik’e cikin hannuwanta guda biyu tana duban matar dake kwance, hannayenta sai rawa suke, zuciyarta na wani irin tsinkewa.
‘Ke Ajidde kiyi k’ok’arin saita kanki idan ba so kike asirinki ya tonu ba.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta.
Ta d’an juyo ta dubi Inne wacce itama Ajidden take duba “Inn Inne nace Ko za’a d’an tallafa mun kanta zan bata magani."

Dai dai lokacin Mu’azzam yai sallama ya shigo, kayan training ne jikinsa, ga dukkan alamu daga morning jugging ya fito.

A tare Inne da Ajidde suka dubi mai sallaman. Zuciyar Ajidde yai wani irin yankewa, k’iris ya rage bata tintsirar da ruwan maganin dake rik’e cikin hannunta ba, dikda ba da wannan shigar ta gansa ba fuskarsa bai b’ace mata ba, tana tuno sanda ya nunata da bindiga daga yanda yake a saman bishiya.

Gaisawa Mu’azzam yake da Inne amma Ajidde bata janye idanunta daga dubansa ba. Har saida Inne tace “Yauwa Modibbo na tinda ka shigo sai ka taimaka mata ta bawa Nuratu maganinta dama zan kira Hindu ne tinda ni banida k’arfin d’agata amma tinda ka shigo sai ka taimaka mata.”

Mu’azzam ya juyo yana duban yarinyar da zata bawa mahaifiyarsa magani, K’uri yai mata yana so ya d’ago a ina yasan fuskar tata.. Taso ta masa kamanni da fuskar da ya sani amma ya kasa tuna ina yasan fuskar. Haka kurum yanayinta yai masa Zubi dana criminals abinka da wanda ya saba cin karo da masu laifi.. Shi bama wannan ba mamaki yake Wai wannan k’aramar yarinyar ce zata bawa Maminsa magani..? Jiyo muryar Inne da yai tana fad’in ya tallafo kan mahaifiyarsa a bata magani kar lokaci ya k’ure ya dawo dashi daga duniyar tinanin da ya tafi. A hankali yake takowa har ya iso kusan Ajidde.. Ajidde dai sai kauda fuskarta take alamun bataso mutumin nan ya ganeta.
Idanunsa naga Ajidde yake k’ok’arin tallafo kan mahaifiyarsa. Dik iya tinaninsa dan ya tina a ina yasan wannan fuskar ya kasa.

Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai yana k’ok’arin d’ago kanta. Ajidde sai rawa hannunta yake tana k’ok’arin kai kwanon kusan bakin Aunty Nuratu.

“Dakata.!” Ya fad’i yana duban ruwan maganin da yake bak’ik’irin.

Cak Ajidde ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa.

“Wannan ruwan za’a bata.?” Ya tambaya yana kuma duban ruwan.

Inne tai karaf tace “Maganin kenan za’a bata. Kasan had’e had’e ne.”

“But Inne wannan zai iya cutar da lafiyarta dan bamusan da mai da mai aka had’a ba.. Sannan wannan yarinyar itace mai maganin dama.?”

Inne ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Banda abinka Modibbo jinjiri ma ai sai ya baka magani kuma a dace idan Allah ya nufa. Karka damu da yanayin wanda zai baka magani kawai kai add’uan dacewa.. Mudai fatanmu shine Allah yasa a dace.”

Ya jinjina kai a hankali yana mai maidoda dubansa ga ruwan maganin.

Idanun Ajidde naga hannayen Mu’azzam da ya tallafi mahaifiyarsa wanda suke fresh dasu. Ta kasa janye idanu daga duban yatsun hannunsa da suke dogaye tamkar dai yanda yake da tsayi... Tsaban kallon yatsun hannayensa da take k’iris ya rage bata d’urawa Mamy magani a hanci ba. Mu’azzam yai caraf ya rik’e hannun nata wanda ke k’ok’arin Kai magani hancin mahaifiyarsa.. Jin hannunsa saman nata ya sanyata d’agowa a zabure tana dubansa zuciyarta na wani irin yankewa.

Shiko yasha mur sosai yake dubanta “Concentrate.. Ki kula..” Ya fad’i fuska babu walwala.

Ajidde ta jinjina masa kai amma jin bai sakar mata hannu ba ya sanyata kai idanunta ga hannayen nasu.. Sai sannan shima ya dubi yanda take kallo. A hankali ya sakar mata hanunta kafin ya kuma tallafe kan Mamy sosai..
Wane irin nannauyan ajiyan zuciya Ajidde ta sauk’e kafin ta soma k’ok’arin bawa Mamy maganin, a daidai sanda ta kawo maganin dai dai saitin bakinta tana jin sanda Mu’azzam ya furta Basmala a hankali. Batasan dalili ba amma taji wani irin natsuwa na sauk’o mata a lokacin da yake ambaton Allah.

A haka Ajidde ke bata maganin, rabi na shiga bakinta rabi na zubowa jikinta. Inne ta taso ta gyara mata napkin d’in dake d’aure wuyanta har saida Ajidde ta ida bata ruwan maganin kafin Mu’azzam ya maida kanta ya kwantar, ya dafa goshinta da gumi ke tsartsafowa tin sanda aka soma bata maganin. A hankali ya share mata zufan yana mai kuma gyara mata kwanciyar. Ya jima yana duban fuskar mahaifiyar tasa yayinda Ajidde ke k’ok’arin tattare kayyaykinta.

“Allah baki lafiya Maami.” Ya fad’i yana maida mata sumarta cikin hulan da aka rufa mata.

Ajidde samun kanta tai tana mai furta “Ameen.”

Yai saurin dubanta dan yaji Ameen d’in data ce, ya soma k’ok’arin tino yanda yasan irin muryar amma nan ma shiru bai iya tuna komai ba. Ganin zai bawa kansa wahala babu dalili ya sanyasa mik’ewa yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu.

“Abinci fah ko sai zuwa anjima.?” Inne ta tambayesa cikeda kulawa.

“No sai zuwa anjima Inne, zanyi wanka yanzu dai.” Yana ida fad’in haka ya nufi k’ofa.

Inne ta jinjina kai tace a fito lafiya.

Ajidde kaw alla alla take ta gama abinda take ta fice daga gidan kafin wannan mutumin ya kamata dan ta lura sam bai d’auko kamanninta ba. Ta murmusa cikin zuciyarta tana fad’in ta Ina zai d’auko kamanninta bayan yau d’in gaba d’aya ta canza yanayi, yau d’in jan powder ta shafa Wanda ya k’ara ma bak’in fuskarta haske sannan bata cika kwalliya ba kad’an tayi kuma harda hijabi Ta saka ba kaman wancan ranan ba, gaba d’aya dai ta sauya yanayi yanda ba lallai a ganeta ba. Canza yanayi da kamanni dik na cikin d’abi’ar Ajidde tinda dama damfaran mutane Kyallu ke sanyata yi, mai Sana’a irin nata dole yanada dabaru na b’adda yanayi daban daban.. Ta kuma murmusawa tana fad’i cikin zuciyarta Wo ni Ajidde gaskiya na iya shashashantar da mutane tinda na shashantar da wannan k’aton.. Muryar Inne ta sinkayo tana fad’in “Ajidde idan kin gama da maganin nata sai kici abinci ko.. Hindu zata baki abinci.”

Ajidde ta girgiza kai tace “A’a Inne na gode, sauri nake akwai yanda zanje na kai magani.”

Inne tace “A’a ai kuwa dole zakici abinci dan ba’a zuwa gidan nan a fita ba’aci komai ba kinji koh.. Jirani a nan Ina zuwa.”

Ajidde ta jinjina kai tana murmusawa. Inne tana fita Ajidde ta mik’e tana k’are ma d’akin kallo.. Ya zama dole ta nemi abinda zata d’auka takaima Kyallu.. Saidai sam idanunta basu gane mata wani abinda zata d’auka ba. Sannan bata jin zata iya satar ma Kyallu wani abu a d’akin majinyaciya irin wannan.. Yanzu ya zatayi.? Bata isa ta koma ma Kyallu hannu banza ba dan Ta tabbata muddin ta koma mata haka a d’akin awakai zata kwana. Tana tsaka da tinanin ta hangi k’ofar d’akin a bud’e a hankali cikin sand’a ta fito daga d’akin. Doguwar corridor ta hanga da ya mik’e zuwa b’angaren hagu, ga wasu k’ofofin kana iya hangowa. Cikin sand’a Ajidde ta soma bin wad’annan k’ofofin.. Tana tafe ta hangi wata kaman bata ida rufuwa kirif ba. Ta Washe baki tana fad’i a hankali “Sa’arki tazo Ajidde.” Cikin sand’a ta isa jikin k’ofar tana turata a hankali. D’akin tas tas Sai k’amshin ‘yan gayun da take shak’a kaman dai yanda tace a cikin zuciyarta. Ta lumshe idanu tana shak’an k’amshin. “Kaji k’amshin Turawa.” Ta fad’i tana gyad’a kai. Ga kuma zuban ruwa tana jiyo daga wani wajen amma batasan daga ina bane. Kar dai ma ana kallanta.? Ta tambayi kanta cikin zuciyarta. Kafin takai ga nemo amsar tambayarta ta hangi wannan bak’ar jakan Ta mutumin nan data so masa sata dan sam bazata mance jakan ba, sannan shine mutumin da ya taimaka mata suka bama matar nan magani. Ajidde ta Washe baki tana fad’in “Jaka jin nace sai na sata ma Inna Kyallu abinda ke cikinki.. Watau yauma saida kika biyoni. Toh Bari dai muga Meye a cikinki.” Tana ida fad’in haka ta k’araso kusan jakan tana mamakin yau a bud’e ta sami jakan. Saidai k’arasowarta jikin jakan kenan taji an turo k’ofar d’akin an shigo.

Cak Ajidde ta tsaya ba tareda ta iya juyowa ba, jikinta sai rawa yake. Ta nemi layar zana da kyallu ta bata ta rasa. Tana cikin dibi dibin ta sinkayo muryar mutumin da ya shigo d’akin yana fad’in “Who are you.? What are you doing in here.?”

A slow motion Ajidde ke juyowa. Musaddiq ya ware idanu yana duban yanda ta zaro k’wayar idanunta, dikda babu janbaki da jagiran data zana wancan lokaci tsaf ya ganeta dan bazai mance wannan k’wayar idanun nata masu tsananin haske da kyau ba “You again.?” Ya furta yana nunata.

Daidai lokacin aka soma tab’a k’ofar bathroom alamun mutumin dake ciki zai fito.

Ajidde ta rikice ta rasa wanne zatai dan tuni Mu’azzam ya fito d’aureda towel, rufin asirin Allah hannunsa na rik’e da k’aramar yana goge fuskarsa zuwa sumarsa sam bai an kare ba balle ya gane da mutane cikin d’akin.

Cikin azama Musaddiq ya finciko hannun Ajidde da ta saki baki da hanci tana duban Mu’azzam ya turata cikin wardrobe.

K’aran rufe wardrobe Mu’azzam yaji ya d’ago fuskarsa yana duban Musaddiq dake tsaye wajen cikin wani irin yanayi na daburcewa.

“Hey are you with someone.? Ina wanka kaman naji murya..” Mu’azzam yace yana k’arasowa.

Musaddiq da gaba d’aya yake a rikice sabida Ajidde dake b’oye cikin wardrobe saurin girgiza kai yai yace “Me. A’a no.. Yanzu shigowarta.. Mu’azzam you need to come, wani mutumi ne naga ya dirk’o ta Katanga shine nazo kiranka.. You need to hurry kafin ya b’ace mana..”
Chapter 26 · 0% Book details