← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 175

Sashe 113

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu’azzam ya kaikaito kad’an had’ida k’ura masa idanu. Baice komai ba sai maida idanunsa kan gawan Maleeka da yai zuciyarsa fal tinani. Duk wanda su Jaja sukai amfani dashi wajen kashe Maleeka wani ne wanda ya sansu in and out.. Sann yasan dik yanda zai bi yayi ta’addanci ba tareda ya bar wani trace ba. Wani ne da yake da ilimin abun.. But who could that person be.? Tambayar da yai ma kansa kenan. He needs to solve this puzzle.. Kalman da Maleeka taso fad’i shi ya tsaya masa a rai BA..

Ya Tsuguna a hankali yana duban yanda harsashi ya huda a jikinta. Lokaci guda yana karantar irin harbin da aka mata da kuma yanayin da gangan jikin nata yake a kwance.

Wani abu k’arami mai kaman toci mai tsananin Haske ya Ciro cikin aljihunsa yana haska k’asan wajen kaman yana neman wani abu. Dik wani abu mai kama da trace baiga alamunsa ba. Yai shiru yana examining wajen.

A hankali ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihu. Wanene makashin Maleeka..? Shine tambayar da ya tsaya masa a rai.

**

A k’ofan prison d’in suka tsaya jingine jikin mota shida Yusuf suna jiran fitowar Assad.

Can suka hangosa yana nufosu kwantattun k’walla cikin idanunsa.

Yana k’arasowa ya shige tsakankaninsu Yusuf da Mu’azzam sai kuma ya rungumesu yana jin hawaye na zuwa masa.

Sameena Aleeyou📚

*GIDAN ARO*

*57*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Murmushi yake yana dubansu, su d’inma murmushi ne saman fuskokinsu.

“Thank you both for not giving up on me.. Thank you for believing in me.. Na gode K’warai..” Assad yace yana dubansu.

Yusuf ya dafasa kad’an yace “You don’t need to thank us.. This is what brothers are for.. Na maka murna” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’arsa murmushi saman fuskarsa.

Mu’azzam baice masu komai ba har lokacin, kaman baya wajen haka ya b’ace shiru.

Yusuf yai gyaran murya kad’an ya dubi Mu’azzam d’in yace “I’ll be heading to the headquarters.. Suna jirana akwai report d’in da zan basu.”

Mu’azzam ya jinjina masa kai kurum yana dubansa. Assad ya masa fatan sauk’a lafia.

Wajen ya rage saura Mu’azzam da Assad.

Assad ya d’an dube mutumin nasa cikin ransa yana ayyana yanda zasu kwashe. Abubuwan da sukaita faruwa shi yake zuwa zuciyarsa. Yai gyaran murya kad’an “Na yarda ka fini gaskiya a akasarin lokuta.. Kuma kaid’in ka fini sanin makamar aikinka.. A akasarin lokuta nakan yi zaton ka tsaurara.. Nakan yi k’ok’arin dakatar dakai.. Like you said, we have same profession but our personalities differ.. Mu’azzam aikin da kayi zan iya cewa kaid’in k’aararre ne a sanin makamar aikinka.. You proved me wrong.. Tabbas ba ko yaushe ake yarda da mutane ba.. Na d’auki darasin rayuwa bayan abinda ya faru dani.”

Mu’azzam ya d’an kauda kansa gefe kad’an yana zira hannayensa cikin aljihu “Ka zama mai bud’edd’en zuciya.. Ka yarda da mutanen da suka baka yarda.. It’s not a crime don ka zama mai sauk’in fahimta.. But it can be a crime idan ka zama wanda kowa zai d’ebo sharansa ya zuba..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kowa zai iya zama mai laifi.. Ban cire maka kowa ba.. Harta ni da kai zamu iya zama masu laifi.. People change, zuciya batada k’ashi.. Tsokace zalla da takeda tsananin rauni lokaci guda kuma takeda power a gangan jikin D’anadam.. Idan ka bata wann power d’in nan ne zata kaika Ta baro ka.. Amma idan ka barta da rauninta.. Sannu a hankali zata kasance a haka.. Sai ka samu power da zaka sarrafata..” Ya k’arashe yana juya coin d’in Black African Team dake rik’e cikin hannunsa.”

Assad ya kafe abokin nasa da idanu yana dubansa yana murmushi. Zuciyarsa fal jinjina ga abokin nasa.

Jinjina kai yai a hankali kafin ya gyara tsayuwarsa yace “Na gode da kalamanka... Na gode da bakai watsi dani ba.”

Kauda kansa gefe ya kumayi yana rage girman idanunsa kad’an. Dan bayan yaji statement d’in Assad a gaban Prosecutor yaji kalan tuggun da Maleeka taso k’ulla masa sam baiga laifin Assad na amsa laifin da bai aikata ba. Yayi ne to protect his reputation. Ko a shari’a idan aka maka barazana da b’ata suna bakai laifi ba don ka amsa laifin da ba Naka ba ka zab’i tafiya gidan kaso.

“Let’s get going Detective. Akwai aiki sosai gabanmu.” Mu’azzam ya fad’i yana bud’e marfin mota.

Assad ya d’an tsaresa da idanu kad’an yana duban Mu’azzam d’in, gajeren murmushi yai kafin ya jinjina kai yace “Yes Inspector.!” Yai maganar yana sara masa.

Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yaja motar suka shige bayan Assad ya shige cikin motar.

Suna tafe labarin mutuwar Maleeka ya kuma zuwa ma Assad “Dukda ta mun laifi naji zafin yanda mutuwarta ya kasance. Hak’ik’a ta zab’i turba maras d’aurewa.. Tanada k’wazo da sanin kan aikinta.. But still ta zab’i tabi hanya wanda babu komai cikinta face k’arya da tsananin duhuwa. I’m quite sure silencing nata sukai..”

Shiru Mu’azzam baice masa komai ba saima ci gaba da tuk’a motar da yake, idanunsa naga kwalta.

Assad yaci gaba da fad’in “So sad.. Sun kasheta bayan ta zab’i tai abinda ya kamata.. Na yafeki Maleeka..! Kuma ina fata ki samu rangwame wajen Ubangiji.. Allah yasa masu hali irin naki su hankalta su gyara.”

Sai lokacin Mu’azzam ya amsa da Ameen yana mai duban window d’in dake side d’insa.

Suna tafe Assad yaga ya d’auki hanyar Lafiya.

Da mamaki yake duban Mu’azzam d’in kafin yace “I thought kace aiki na jiranmu.”

Mu’azzam bai amsa sa ba yaci gaba da driving.

Assad ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza kai, yasan bazai amsa shin bane.

Suna isowa k’ofar gidansu Assad yaja yai parking.

“Hajiya ce tafi cancanta ta soma ganinka fiyeda Chief Jaja..” Yai maganar cikeda barkwanci wanda zaka iya cewa kaman ma ba daga bakinsa ya fito ba.

Assad ya kuma murmusawa yana girgiza kai yana duban abokin nasa lokaci guda yana bud’e marfin motar.

A tare suka jera suka nufi cikin gidan yayinda suka soma had’uwa da Shamsu zai fice shago dan dama yanada shago a d’an k’asa dasu kad’an.

Cikin sauri Shamsu ya k’araso ya rungume D’anuwansa cikeda jin dad’in ganinsa yana masa Barka da fitowa.

Ya k’araso yana gaisawa da Mu’azzam had’ida sake masa godiya kan d’awainiyar Assad d’in da yai. Assad kam tuni ya shige ciki yana ambato Hajiyarsa.

Hajiya harda hawayen murnan sake ganin D’an nata tai. Allah sarki D’ah da mahaifiya kenan. Yanda Assad da Hajiya suka rungume juna suna hawaye ya karya Zuciyar Mu’azzam. Tausayin kansa ya rufesa.. Allah sarki, rabonsa da yayi haka da tasa mahaifiyar shekaru ak’alla goma sha biyar. Ina ma shida Mamynsa zasu rungume juna wata Rana suna hawayen Farin ciki irin haka. Ya d’an sadda kansa k’asa yana k’ok’arin barin wajen.

Hajiya ta dakatar dashi tana kuma masa godiya.

Ya murmusa kad’an yace “Babu komai Hajiya.. Nida Assad ‘yanuwan juna ne.”

Hajiya ta murmusa tana goge k’wallanta “Allah yasa amincinku ya d’aure har Aljannah.. Allah ya rabaku da sharrin mak’iya na b’oye da na zahiri a dik yanda kuka kasance. Allah shi maku albarka.”

Daga Assad d’in har Mu’azzam Ameen suketa amsawa dashi cikeda jin dad’in addu’o’in Hajiyar a garesu.

Assad yace bari yai ma Mu’azzam rakiya.

Har mota ya rakosa. Ya saluting nasa yana fad’in “Idan Inspector yace kar nai reporting back to work Sai nan da sati ma bazance komai ba.”

Gajeren murmushi yai da gefen bakinsa kafin yace “I thought prison did change you..” Yana maganar yana shigewa mota.

“Sai munyi magana.” Mu’azzam ya k’ara da fad’in haka.

Assad na murmushi yake jinjina kai “Alright shikenan.. Da Allah ka bani update fah.”

Bai amsa sa ba sai key da yaima motar. Yasan ba lallai ya amsa d’in ba.
“Zan kira Yusuf kawai naji komai.. Drive safe.” Ya k’arashe yana d’an saluting nasa kad’an wanda kaman d’abi’ar aikinsu ne.

Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai masa horn alamun sallama.

Yana tafe saman kwalta yana tuna kalaman Maleeka na k’arshe “BA.. You..” Ya furta a hankali kafin ya fuzar da huci kad’an.

Kai tsaye gidan Maleeka ya kuma komawa yaci gaba da examining gidan yanda abun ya faru.

Tin daga k’ofa yake karanta. Ya d’aga kai yana duban yanda wasu frames irin mai guda biyar d’in nan Babba da k’ana... Nan yaga babu guda d’aya.. Ga wajen da yake makal’e harda alamun k’usa amma babu.. Take ya soma tinanin Maiyasa babu guda d’aya. “Garin kokawa ya fad’i glass d’in ya fashe.. Wanda yai kisan sai share komai kaman dai Babu abinda ya fashe.. Kenan Maleeka tayi fad’a da mutumin da ya kasheta kafin ya cimma kashetan.” Zuciyarsa ce take wann zancen. Yanayi yana kamanta yanda Maleeka sukai bata kashi da makashin nata. Hoton abubuwan na zuwa cikin k’wayan idanunsa.

K’aramar torchlight d’in ya ciro cikin suit pocket d’insa ya shiga haska k’asan wajen. A hankali ya duk’a yana kuma haska wajen nan ya hango k’anan broken glass alamun dai tinaninsa ka iya zama gaskiya, akwai k’aramar frame d’in a wajen garin kokawa Ta fad’i ta fashe. Yai shiru kaman mai nazari. Gefe kad’an ya haska nan ya hango shatin alamun k’asan takalmi saman farar tile d’in. Cikin tsanaki ya zaro Balck marker dake cikin aljihunsa. Take ya soma tracing shatin k’afan takalmin cikin tsanaki da k’warewa. Saida ya zana tsaf suffar shatin k’asan takalmin ya bayyana. Ya jinjina kai a hankali yake duban zanen tracing k’asar takalmin da yai. Wayarsa ya ciro yai hoton zanen k’asan takalmin da yai kafin ya mik’e yana kuma k’are ma gidan kallo yana karantar ko Ina a tsanake.

Dik iya binciken da yai gidan bai samu abinda zai linking Maleeka da Chief ba. Koda shike yasan hakan abu ne mai matuk’ar wahala, bazasu yarda su bar wani abu da zai nuna sunada wata alak’a ba. A fili yake furta “Sannu sannu bata hana zuwa Chief Jaja.. Da sannu zaka iso hannu.”

Daga nan ficewa yai daga gidan ya nufi gidan Daddy.
**
Chapter 113 · 0% Book details