Sashe 158
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajara dake lab’e akan idanunta komai ya faru.. Taga yanda mijinta yai tsaye yana kallon Nuratu sann ya shige cikin sauri kaman wanda ya tina wani abu.. Zuciyarta ya buga kardai Nuratu ce matar da Ta dasashe hasken Zuciyar mijinta.. Kar dai Itace wann Hasken da yace ta mutu tareda zuciyarsa.. Lallai kuwa idan haka ne ya zama dole Ta d’au mataki.. Ta wuce fuuu ta nufi cikin gida.. Saidai tana shiga ta hangi Marwan saman sallaya hannayensa biyu a sama yana rok’on Allah ya shiga al’amarinsa ya tsare masa zuciyarsa ya kareta daga sharrin shaid’an ya kuma basa ikon cin duk jarabawar da zai jarabcesa dashi.. A addu’o’insa na k’arshe ne Ta tabbata Nuratu dai itace wann matar da tasa Ta rayu da mijinta kaman hoto ko gunki.. Bata zaci matar da Ta kashe hasken fitilar Zuciyar mijinta tana raye ba.. Dama ta d’au alwashin gano wacece wann matar.. Lallai ya zama dole Ta taka ma hakan birki.. Meye abinyi..? Ta tambayi kanta..! Ta soma tinanin neman mafita.
Tana ganinsa ya shirya tsaf, kaman ko yaushe babu wani walwala yake sanar da ita zaije Company ya sami D’anuwansa.
Ta murmusa tace dashi a dawo lafiya. Sai girgiza k’afa take tana tinanin abin yi har ya fice.. Kafin hutunsu ya k’are a garin ya zama dole Ta fasa komai kowa yaji.. Kowa yasan Marwan son matar D’anuwansa ya hanasa samun natsuwa da nasa iyalin.. Tasan idan Abubakar yaji haka dole ya d’au tsartsauran mataki kan D’anuwan nasa.. Da wann tunanin ta yanke shawarin taje har Factory d’in Ta sanar da Abubakar a gaban Marwan d’in cewa K’aninsa na son matarsa. Allah Sa idan ta fad’I haka Abubakar ya d’auki matarsa suyi nesa yanda babu mai K’ara ganinsu cikinsu.
**
A can Factory kuwa Salman ya tasa Abubakar gaba, Ta yanda yake shiga ba Ta nan yake fita ba.. “Ka handame mana dukiya ka hanani sukuni ka hanani girma cikin company..Toh mai kake nufi kenan..?”
Tinda ya soma magana Abubakar kai tankasa ba, yanata rubutu cikin wata doguwar Takarda... Har ya gama ya saka hannu ya rufe envelope d’in ya rubuta BAT a saman takardan.
Salman ya dubesa ya dubi doguwar takardan kafin yace “Meye kuma wann.. Wane kutungwilar zakai da dukiyar mahaifinmu.?”
Murmushi Abubakar ya sakar masa kafin yace “Nawa kason ne a cikin nan..”
Salman yace “Ban gane ba..”
Murmusawa Abubakar ya kumayi kafin yace “Zan tafi da nisa.. Zan bar maka abinda kake mafarkin samu Wato shugabancin wann company... Ka kwantar da hankalinka Salman.. Kaga dukiyata dake cikin nan a rubuce bana son ko k’wandala.. Hasalima zanyi sadaukarwa ne da ita.. Ka fahimta.”
Salman ya murmusa irinta rainin hankali kafin yace “Ma waye zaka raina ma hankali..? Waye baya son dukiya.. Iyalanka mai zaka bar masu idan ka sadaukar da maka dukiyar..?”
“Zan nema masu da nawa gumin.. Amma wann bama so dani dasu..!” Ya k’arashe yana d’ago takardan da ya rubuta BAT yana nunawa a fuskar Salman.
Salman ya girgiza kai yace meye hakan ke nufi mai ka rubuta.
Abubakar ya dubi haruffan kafin ya murmusa yace “Bet Agreement Transaction.” Ka gamsu.
Salman yai tsaye cak yana duban takardan sai kuma yace “Toh amma ma waye zaka sadaukar da dukiyarka haka kawai..?”
Murmushi yai kafin yace “Wann ba hurumin ka bane D’anuwana.”
Dik tattaunawar da ake Hajara na bayan window tana sauraronsu tana lek’ensu dan ta riga Marwan isowa company da shike shi Marwan ya biya wani wajen.
Tana gani Abubakar ya janyo drawer ya tura Envelope d’in ciki, Salman yaci gaba da sa’insa da D’anuwan nasa yana fad’in kar dai dukiyar ahalinsu ya tattara zai handame dan shi sam bai yarda dashi ba.. Ana a haka Abubakar ya K’araso sai bai ya tsaya daga waiting shiga ba sabida yanda ya sinkayo muryar Salman ta yanda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Har cewa yake Abubakar ya rubuta ya ajiye Sai ya d’ale wann kujeran da yake bisa idan sunansa Salman Gamji.
Zai fice kenan ya hangi Marwan ya had’a tagumi yana zaune.. Tsaki yai kafin yasa kai ya wuce.
Marwan ya shigo ya sami D’anuwan nasa ya basa hak’uri kan abinda Salman yai masa.. Sai kuma ya mik’e yana fad’in “Hamma bazai yuwu a k’yale Salman ya dinga maka abinda yaga dama ba.. Zan fita yanzu nabi bayansa.. Zan masa magana.. Abin nasa is getting out of hand..”
Abubakar yai yunk’urin dakatar dashi amma sai Marwan ya girgiza kai dan ransa ya b’aci da ganin irin abinda D’anuwan nasu keyi ma Hammansu.. Cikin sauri yasa kai ya fice yabi bayan Salman ko zai cimmasa. Har lokacin Hajara na mak’ale bayan window.
Abubakar ya furzar da huci ya janyo drawer d’in yana kuma kallon takardan BAT.. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Haka shine daidai.. Kaman yanda ya sanar da matarsa zai nemo wann mutumin da duk abinda ya mallaka zai haka.. Hasalima bayan abinda yaji Inne ta aikata yaji gaba d’aya duniya da abinda ke cikinta ya fita ransa.. Baison komai face ahalinsa.’ Ya sauk’e ajiyan zuciya kafin ya tura hoton cikin envelope d’in ya saka envelope d’in cikin drawer d’in kafin ya maida ya rufe.
A haka ya mik’e ya nufi yanda kayan shiga d’akin k’ank’ara yake ya shirya tsaf dan yana so ya shiga yai ban kwana da Companyn nasu.
Yana shigewa Hajara ta fito daga mab’oyarta tana tinani.. Shin ta samesa ta sanar dashi abinda ya kawo Ta ne ko kuwa.. Toh amma ga takardan da ya rubuta zai sadaukar da dukiyarsa.. Shin ba gwara ta d’auki wann takardan ba Ta kulle Abubakar Gamji a cikin d’akin.. Idan ya mutu shikenan tasan dole Nuratu zata fice daga rayuwarsu ta koma yanda ta fito.. Ga dukiyarsa ta samu gashi Nuratu zata fice daga rayuwarta. Shikenan Ta jefi tsintsu biyu da Dutse d’aya. Ta saki murmushi cikeda jin dad’i lokaci guda ta soma waige waige ta k’arasa k’ofar D’akin K’ank’ara da Abubakar ke ciki.. Lokaci guda Ta janyo k’ofar Ta rufe kirif.. Tana jin sanda ya soma k’araso yana buga k’ofar yana neman d’auki amma sai ta saki dariya tana juya envelope d’in BAT dake rik’e cikin hannunta. lokaci guda take duban Envelope d’in tana furta BAT a fili.. Sai ta tuna lokacin da Abubakar ke sanar da Salman takarda ce ta Yarjejeniya. Ta kuma sakin murmushi tana fad’in “Dukiyar ya zama nawa ni Hajara.. Sann wann shegiyar matar zata tafi can da nisa tinda babu mijinta babu sauran zaman da zatai..” Ta kuma sakin murmushi kafin Ta nannad’e takardan Ta tura cikin rigarta ta fice.
Allahu Akbar wann shine sanadin mutuwar Abubakar Gamji. Hankula suka tashi, kowa na jimami, babu kaman Inne wacce tattaunawarsu na k’arshe da D’an nata bai mata dad’i ba.. Abubakar yaji Bak’in aikin da Ta aikata.. Allah sarki yayi k’udirin tafiya ya barsu ashe tafiya mai gaba d’aya zaiyi.. Ta d’au alwashin kular masa da bayansa, Ta d’au alwashin matarsa Nuratu bazata fice daga cikin iyalansu ba dan dama ita d’in batada kowa sai su.. Da wann k’udiri na Inne bayan Nuratu Ta ida takaba Ta bijiro ma Marwan da auren Nuratu. Hankalin Marwan ya tashi sai yake ganin kaman amanan D’anuwansa zaici idan ya auri Nuratu.. Toh amma saidai babu yanda ya iya haka Inne tace dole ya auri Nuratu ya kula da bayan Abubakar.. Domin Nuratu batada kowa dama sai su d’in.. Sai kuma ya tuna tatyaunawarsu na k’arshe da Abubakar d’in yanda yake ce masa ya kula da ahalinsu ko bayan baya nan.. Allah sarki ashe a ranan zai tafi ya bar duniya.. Basu samu sunyi tattaunawan da yace zasuyi ba.. Ko akan menene Allah masani.. Marwan ya shiga tashin hankali sosai da rashin D’anuwansa kuma amini a garesa. Nan ya amince da auren Nuratu sabida alk’awarin da ya d’auka amma dikda haka sai yana ganin kaman cin amana ne.. Inne taita masa nasiha cewa ba haramun a ciki dan ya auri matar D’anuwansa da ya rasu sann ya kular masa da yaransa.. Rufin asirin ahalinsu kenan.
Koda batun auren ya riski Hajara tashin hankali Ta shiga maras misaltuwa duba da cewa Ta kashe mijin Nuratu ne dan Nuratu Ta fice daga rayuwarsu.. Batasan cewa mutuwarsa ba komai zai k’ara mata ba face kusanci da Nuratu.. Wllhi wllhi bazata tab’a bari hakan Ta kasance ba.. Wllhi idan Nuratu tasa k’afa Ta shigo mata gida Toh kuwa Tabbas gidanta GIDAN ARO ne a wajen Nuratu.. Sai ta fice ta bar mata gida..
Aka d’aura auren Nuratu da Marwan hankalin Hajara duk baya jikinta, batai tariya ba auren kawai aka d’aura.. Wani ikon Allah tinda akai auren sai taga kaman am canza Marwan.. Ya fara sakewa da Ita har hira suke.. Abubuwan da a baya baya mata su ya shiga mata su.. Takaicin duniya ya cika Hajara.. Ganin Ta kwashe shekaru tana mafarkin ya bata irin wann rayuwar da take so bai bata ba saida Nuratu Ta zama matarsa.. Da tasan haka ne da bata kashe mijin Nuratu ba.. Sann yanzu idan Ta kashe Nuratu Ta kula Zuciyar mijinta zata k’ara kashewa a karo na biyu bayan Allah ya kuma raya Zuciyar kaman yanda take mafarki.. Da wann tunanin ta tafi gidan k’awarta Hajiya Faty suka tsara zuwa gidan Boka kan ranan da za’a kawo Nuratu gidan a tura mata bak’in Shaid’ani ya maye gurbin Marwan a wajen Nuratu.. Hakan kuwa akai.. Boka yai ture ma Nuratu had’ari ya samesu.. Driver da wata goggon su Marwan da zata mata rakiya zuwa Abuja suka mutu, Nuratu Ita kad’ai tai rai sann tinda tai had’arin ta kwanta jinya komai sai an mata.. Kula da Hajara ke bawa Nuratu yasa ta k’ara samun girma a Zuciyar Marwan, nan Hajara ta datse damtse ta d’aura d’amaran kula da Zuciyar Marwan Wato Nuratu.. Saidai duk kula da take bata hakan baisa Ta fasa sanar da ita Abubuwa masu zafi ba Dikda kuwa cewa tana kwance ne Ita ba a raye ba Ita baa mace ba.. Allah ne kawai keyin ikonsa akanta. Aka Fita k’asashe da dama neman magani amma Allah bai nufa za’a dace ba.