Sashe 5
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta juyo tana duban mahaifin nata “Daddy you need to stop her, nida Meema mun ce mata Bride bata Kai kanta gidan Groom shine tace zataje ta sami Inne ta kaita tinda ita bata koma Fufore ba..”
Mik’ewa yayi yana fad’in “Ina Safeenan take..?”
“She’s in her room, probably parking her stuff..” Kiki ta fad’i tana matsawa kusan mahaifiyarta dan bama mahaifin nata hanya..
Cikin sauri yasa kai ya fice..
Kiki ta dawo da dubantaga mahafiyarta tana yatsina fuska tana duban Aunty Nurah dake kwance..
“Wai Ke Mommy bazaki daina damuwa akan matar nan bane.. Matar nan fah kishiyarki ce amma ko asalin danginta iyakacin abinda zasu mata kenan.. Ni ban tab’a ganin kishiya irinki ba Mommy wacce take ma kishiyarta jinya. Ko a sch idan ina labarin Mommy ta ita take ma step mom d’ita jinya mamaki suke sha sai suce Lallai Ke ta daban ce..” Tai fasali tana mai zama gefen mahaifiyar tata kafin taci gaba da fad’in “And Mommy tun tasowarmu a haka muke ganin matar nan, ciwonta bai gaba bai baya Ke kuma sai faman wahala kike da ita dik tulun maids d’in dake gidan nan basu isa jinyar nata ba sai kin saka hannu..”
Murmusawa Hajia Hajara tai tana duban d’iyar tata “Kareema kenan, yaro dai yaro ne.. Bazaki fahimci komai ba yanzu sai nan gaba.. Mamarki kirki ne da ita bazata iya ganin wasu suna shan wahala ta k’yalesu cikin wahala ba.. Nuratu da kike gani ba kishiyata bace kawai, tamkar ‘yaruwa haka na d’auketa domin kuwa idan baki mance ba a baya Yayan Babanki mai rasuwa take aure.. Kinga nida Ita mun jima da sanin juna tun kafin Daddynki ya aureta..”
Kiki Ta d’an turo baki tace “Amma Mommy Maiyasa da nata mijin ya mutu ta aure miki naki mijin..? Mommy nan gidanki ne bai kamata ta aure miki miji ba..”
Murmusawa Mommy ta kumayi kafin tace “Nurah batada kowa a k’asar nan, batada dangi a nan.. Mijinta ne kad’ai danginta sai kuma yaranta, shiyasa koda mijinta ya mutu nawa mijin ya aureta..”
Shiru Kiki tai tana sauraren mahaifiyar nata kafin ta tab’e baki tace “Even so Mommy, she shouldn’t have married your own husband.. Ita ta aure miki miji ga kuma d’anta Ya Mu’azzam ya aure Addah Safeenah.. Um nidai duk bana son irin wannan had’e had’en kusancin tai yawa... Shikenan namu family d’in sun k’are a cycle d’aya..Ni gwara ma da Addah Ikram Ta mutu nasan itama da yanzu an soma maganan nata auren da Ya Musaddiq.”
“Ke Karimatu..!” Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa wanda ya sanyata zabura babu shiri..
Mommy taci gaba da fad’in “Kina jina.. Koda wasa koda wasan wasa kar na kuskura na kuma jin wannan kalma ya fito daga bakinki balle har kiyi gangancin furtata cikin gidan nan kinji koh..!” Ta k’arashe tana mai nunata da ‘yar yatsa cikin tsananin b’acin rai..
Kiki baki a ture ta mik’e tana fad’in “Fine Mommy, kema kinfi son wannan matar da yaranta sama damu yaranki.. Kaman yanda Daddy yake nuna yafi sonsu.. This is not something new a gidan nan.. Dama Daddy ya saba nuna yafi sonsu tun kafin Ikram ta mutu..”
“Kimin shiru da maganar Ikram nace and kindly leave this room kafin na b’ata miki rai..”
Fuu ta fice fuska a kumbure kaman zata kurma ihu..
Tana ficewa Mommy ta dafe k’irjinta tana Sauk’e ajiyan zuciya.. Ta maidoda dubanta ga Nuratu da fuskarta ke duban wani b’angaren.. A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tasa kai ta fice...
Tana fitowa d’akin Safeenah ta nufa yanda ta tadda Safeenar duk’e saman carpet tana fuskantar Daddy dake zaune bakin gadonta, kanta a k’asa da alama hawaye take..
“Daddy I’m sorry.. Kawai inaso na kasance da mijina ne.. Please understand me..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Cikin kwantar da hankali yaci gaba da fad’in “Na fahimceki Safeenah.. But don’t you think yayi sauri ayiwa Mu’azzam maganar tariya yanzu..I mean, he recently lost his sister.. And he’s looking into the matter right now...Kuma Kema ‘yaruwarki ce..”
Cikin muryar kuka Safeenah Ke fad’in “Daddy gani nake kaman Mu’azzam kufce min zaiyi.. Daddy kaga da k’yar ya yarda akayi aurenmu sabida jinyar Aunty Nurah toh mai kuma zai faru yanzu da Ikram ta rasu.. K’ila yace ya fasa auren ma gaba d’aya Daddy..” Ta k’arashe wani kukan na taso mata..
Cikeda tausayin d’iyar tasa yake dubanta dan yasan yanda take tsananin k’aunar Mu’azzam..
Hannunsa ya mik’o ya kamo nata kafin ya soma magana cikin kwantar da hankali “Safeenah an riga anyi aurenku da Mu’azzam kinji.. Shid’in mijinki ne, babu abinda zai rabaku ki kwantar da hankalinki kinji koh..”
Izuwa lokacin sosai take kuka tana fad’in “Daddy you don’t understand.. Daddy Mu’azzam ba kaman kowa bane. Bata soyayya yake ba balle aure, baida lokacinsu Daddy I’m sure of it, yafi bada mahimmanci ga jinyar mahaifiyarsa da kuma aikinsa na d’ansanda.. Ba don Inne ta dage sai anyi aurenmu ba nasan k’ila da ba’ayi ba.. And yanzu da ya sami dalilin da zaice ya fasa.. I know him zai iya cewa ya fasa auren.. Daddy please kar ka bari aurenmu da Mu’azzam ya sami matsala..” Yanda take maganar gaba d’aya tamkar mai son fad’in wani abu duk ta daburce tama rasa mai take fad’i.. Shi kansa Daddyn da mamaki ya soma dubanta..
Cikin sauri Hajiya Hajara ta k’arasa ta rungume Safeenah dake sharb’an kuka tana sunbatu..
Shigowar Meema a birkice tana fad’in “Mommy..! Mommy kizo ga cen Ya Mu’azzam ya dawo da Ya Musaddiq.. And... he looks high..”
Wani irin zafi Alhaji Marwan yaji zuciyarsa na masa, take ya shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Yai saurin ficewa daga d’akin cikin tsananin damuwa...
Mommy Ta dubi Meema dake tsaye daga bakin k’ofa tana duban yanda Safeenah ke cazgan kuka ta bud’e murya tace “Fita ki bamu waje..”
Turo baki gaba Meema tai cikeda haushi kafin Ta juya tai ficewarta tana k’walla kira ma k’anwarta Kiki..
Cikin sauri Mommy ta isa rufe k’ofar had’ida danna mata lock..
Ta juyo tana duban Safeenah dake tak’ure waje guda tana cazgan kuka tana fad’in “I can’t lose him.. I love him so much.. No.. No I can’t lose him..”
Jijjiga Safeenah take tana fad’in “Safeenatu Safeenah..Ke ki natsu nace..!”
Safeenah kaw kaman cewa ake ta k’ara..
Mari maiji da lafiya Mommy ta d’auketa dashi Wanda ya sanyata yin tsit kaman an d’auke ruwa..
Tana sakin huci take duban Safeenar..
“Kina jina ki fad’a min mai kike son fad’awa mahaifinki.. Talk to me now..!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya tana mai firfito da idanu waje..
Safeenah dake rik’eda k’uncinta wajen da Mommy ta mareta bata daina kukan ba take fad’in “Mommy idan Mu’azzam ya sani he will hate him.. Zai tsaneni Mommy.. Or he might even send me to jail..”
Izuwa lokacin Hajiya Hajara ta fara daina gane mai Safeenah ke fad’i.. Cikin daburcewa ta shiga bud’e hannuna tana fad’in “Safeenah.. Ke Feenah mai kike fad’i.. Ban fahimceki ba..”
Safeenah na hawaye take fad’in “Mommy I feel guilty.. I feel responsible..”
Girgiza kai Mommy Ta kumayi tace “Har yanzu ban fahimceki ba Safeenah.. You feel responsible for what.?”
“For Ikram’s death Mommy..!” Ta fad’i mata cikin tsananin rawar murya....
Izuwa lokacin bibbiyu Mommy Ke gani.. Cikin sauri ta janyo hannun Safeenah suka zauna saman gado
Wannan karon cikin tsananin sanyin murya take magana
“Safeenah.. Maiyasa kikace haka.. You did not kill Ikram, did you.?”
Cikin sauri Safeenah ta girgiza kai alamun a’a tana fad’in “No Mommy I didn’t..”
“Then how are you responsible..?”
Kallon mahaifiyar tata tai kafin tasa bayan hannu ta goge hawayenta. A hankali Ta soma fad’in “Mommy Ikram tana zargin ban daina aikata wasu d’abi’u da nake aikatawa a baya ba, Ta d’auki wayata ta karance Adress d’in a lokacin shagulgulan bikina..” Kuka sosai yazo ma Safeenah Mommy jikina sanyaye take dubanta,
Tai k’ok’arin saita kanta kad’an kafin taci gaba da fad’in “But Mommy abinda na sani shine I was to meet up with a client wllhi wllhi Mommy bansan Criminal bane... Bansan makashi bane..”
Girgiza kai Mommy tai tana fad’in “Ni duk nan wani fahimceki ba Safeenah “Toh Wai kan wani dalili Ikram zata zargeki..?”
Saida ta share hawayen da ya kuma gangaro mata kafin taci gaba da fad’in
“Kin tuna lokacin da aka kaita University of Salford ina ajin k’arshe ne Ita kuma tana year one d’inta Musaddiq na aji uku.. Toh gida d’aya muka zauna nida Ikram, Mommy a nan Ikram tasan duk wasu abubuwa marassa kyau da nakeyi, Ina kawo maza su kwana a gidan..” Kuka ya sanyata katse maganar..
Mommy tace “Ina saurarenki Safeenah ..”
Safeenah ta goge hawayenta kafin taci gaba da fad’in “Ikram witnessed everything, akan idonta komai yake faruwa.. Muka sami matsala a lokacin tace zata fad’awa Daddy da Mu’azzam duk abinda nakeyi.. Da k’yar na shawo kan Ikram nace mata friends d’Ina ne kawai and bama yin wani abu maras kyau.. Dukda haka Ikram bata yarda ba saida ta sanyani nai mata alk’awarin bazan sake yin abota da maza ba muddin Ina son kasancewa da Yayanta.. I promised her as she requested... And Mommy wllhi wllhi tin a Salford na daina bama Maza kaina..”
Batakai aya ba Mommy Ta Kai mata mari tana hawaye take furta “Ashe duk tarbiyan dana baki kinje kin watsar a turai.. How could you..” Ta k’arashe tana mai kuma Kai mata mari..
Zata kuma Kai mata wani marin ne Safeenah tai saurin rik’e hannunta tana fad’in “What do you expect Mommy.. Kun tura budurwa k’asar waje.. K’asar da babu kowa nata.. Kun bata gida da ko wacce irin Gata.. Meye wannan budurwar bazatayi ba.. Mommy wannan kuskure ne da da yawan iyaye suke aikatawa.. Tura mace tayi karatu a k’asar da babu kowa nata ba birgewa bace Mommy.. Bance duka ba amma akasari lalacewa suke kafin su dawo.. Mommy ko a addini ma Babu kyau tura mace taje uwa duniya da sunan yin karatu ba tareda wani nata ba..”
Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ai an tura Musaddiq.. Kuma Musaddiq d’an uwanki ne..”