← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 175

Sashe 50

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuzar da huci tai tana mai rausayar da idanunta ba tareda tace komai ba.

Lokaci guda Mu’azzam ya zaro shades d’insa ya rufe idanunsa dashi kafin ya zauna saman motar yana jiranta.

‘Yan matan dake zazzaune k’ofar wajen kuwa Sai awwn awwn suke masu dan sunyi bala’in burgesu yayinda wasu suka shagala da kallan mijin nata.. K’ananan maganganu na tashi musamman bayan rumor d’in abinda ya sami saurayin Sadiya Sagir ya isa masu wasu na gulman bata auri Baban Aminiyarta ba ta sami wani had’add’en matashi kuma daga gani He’s loaded . Da yawa cewa suke Lallai Sady Pretty nada sa’a.

Yanda taga anata kallonta yasa dik ta tsargu, haka ta shige sukuku kaman ba Sady Pretty da idan tazo waje sai kowa ya sani ba.. Haka nan da yawa ma shakkun magana suke mata.

Can ta hango Aminiyarta Sabeera zaune cikin lecture hall. Gabanta yai wani irin fad’uwa ganin irin kallon da Sabeerar ke mata.. Lokaci guda Sabeera ta wani d’auke kanta kaman bataga Sady ba.

Cikin sanyin jiki Sady ta nufi cikin hall d’in wajen k’awarta.

Sabeera tana Ganin Sady ta nufota ta mik’e zata fice.. Cikin sauri Sadiya ta k’arasa ta rik’o hannun Sabeerar.

“Dan Allah ki tsaya muyi magana Sabeera..”

A wulak’ance Sabeera ta juyo tana dubanta, lokaci guda tana duban sutiran dake jikinta had’ida wayar dake hannunta.

Murmusawa tai tace “Your true color has finally showed up, dear friend.. Bansan ya akai van fahimci haka ba tuntuni.. Dik ja min kunne da ake akanki ban tab’a sauraronsu ba amma yanzu na yarda.. Kuma Ked’in da alama tsautsayi binki yake Sadiya..”

“Shut up Sabeera..! You know perfectly well abinda kike fad’I ba haka bane...!”

“No you shut up.. Kin mance saura k’iris ki auri mahaifina.. I’ll never forgive you for that Sadiya..”

“But I didn’t marry him.. Did I.?”

“Badon ‘Yantaddan da suke bibiyan ki ba da tuni kin zama matar Babana.. How dare you..? You have no idea wane irin tashin hankali muka shiga nida Mama.. Bakisan yanda Baba ya juya mana baya ba duk akanki.. Sadiya Kinsan irin k’uncin da kika saka ahalina ciki.. My parents almost got separated all because of you Sadiya.. How could you expect me to forgive a betrayal like you..!” Ta k’arashe cikin kuka su dukansu biyun kuka suke.

“Sabeera hear me out first.. Kema kinsan idan ba dole ba bazan tab’a yin abu makamancin haka ba.. Kin sani Sabeera.. Please let’s talk this out first please..”

Girgiza kai Sabeera tai tana hawaye tace “Na yaushe Sadiya.. Bayan duk abubuwan da suka faru Baba yace bazamu ci gaba da zama a garin nan ba.. Dutse zamu koma kuma da zaran mun koma zai sami wani cikin family ya aurar dani..”

Sadiya taci gaba da hawaye tana girgiza kai. Lokaci guda Sabeera Ta jinjina kai tana murmushin da za’a kirasa da yak’e wanda yafi kuka ciwo..

“Kinfi kowa sanin yanda nake son karatuna Sadiya.. Yanzu shikenan bazanci gaba ba.. Dole na sato k’afa na fito domin nayi bankwana da karatuna na k’arshe.. Na tabbata mazajen zuri’ar mu basu bari matayensu suyi karatu.. But at least ke kin samu mai supporting d’inki.. Had’add’en miji mai sonki da k’aunarki wanda zai iya ajiye komai nasa ya biyoki har makaranta ya zauna ya jiraki.. Wacece ake mata haka Sadiya.. Da alama ke d’in kinada sa’a bayan duk abubuwan da kikai, mafarkin ki na auran mai kud’i ya tabbata, not only that he’s every girl’s dream..” Ta k’arashe maganar tana mata nuni da Mu’azzam dake zaune saman mota ya d’aura k’afarsa d’aya kan d’aya yana shafa waya.

Sabeera taci gaba da furta “I don’t know ko zamu sake had’uwa ko bazamu sake ba.. But for now, ni Sabeera ina ce miki Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai juyawa..

Cikin tsananin sanyin gwiwa Sadiya Ta silale ta zauna saman kujera.. Hawaye suka ci gaba da gangaro mata, cikin zuciyarta take furta “Allah sarki Sabeera bakisan abinda ke faruwa da rayuwata bane.. Baki San wane irin walak’antaccen aure nayi ba duk da bazaki fad’I haka ba.. A fili kuwa Fad’i take “Ki yafe min Sabeera.. I never wanted any of this to happen.. Ki yafe mun k’awata..” Ta k’arashe tana mai kifa kanta saman desk hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta.

Mu’azzam dake zaune waje waya ya samu daga Assad, lokaci guda yace “Alright I’ll be on my way..”

Yana katse kiran ya shiga kiran wayan Sadiya.

Sadiya da kanta ke kife tana mance da wani waya saida taji ringing har cikin kanta da shike wayar na saman desk d’in ne.

Tasan shi kad’ai ne zai kira tinda shi ya bata kuma bata saka lambar kowa ba sannan bata bama kowa ba.

Batace komai ba koda ta d’aga, daga d’aya b’angaren yace “Zanje yanzu ana nemana.. Don’t step a foot out of that hall.. Ki zauna a nan ki jirani kinji koh..”

Ya d’anyi fasali kafin ya k’ara jaddada mata “Kar ki fita ko k’ofa ne Sadiya.. You wait for me right there kinji koh..!” Daga haka katse kiran yai kafin ya shige Mota ya d’au hanya.

Yana katse kiran Ta kuma fashewa da sabon kuka.. Ai kuwa koda ta tabbata ya fice a makarantar Mik’ewa tai tana goge hawayenta “Ka rabani da kowa nawa Mr Inspector.. This is the perfect opportunity for me to escape..!” Tana ida fad’in haka tai fitowarta itama lokaci guda ta nufi gate tana neman abin hawa..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*28*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A cikin Mota suka had’u da Sabeera, saidai cikin dukansu biyun babu wanda ya fahimci suna cikin motar har saida Sady Ta fad’i destination d’inta. Sabeera ta waigo suna duban juna, sai kuma ta kauda kanta ba tareda tace komai ba. A haka har suka iso unguwar tasu babu mai cewa k’ala..

Da shike waje guda suka sauk’a Sadiya Ta dubi mai motar tace “Malam dan Allah kai hak’uri lungun can kawai zan shiga na amso maka kud’inka.. Akasi aka samu ban fito da Jaka ba.”

Mutumin ya dubeta ya girgiza kai yace “Hajiya Kinsan ba’a haka.. Ki biya kud’in ki kawai ki tafi..”

Zata kuma magana Sabeera ta ciro kud’i ta bawa mai taxi d’in tace “Malam namu ne mu biyu, ‘Yaruwata ce tare muka saba tafiya dama..” Daga haka Sa kai tai zata shige. Sadiya ta dubeta murmushi saman fuskarta “Na gode..”

Sabeeran batace mata komai ba sanda suka soma takowa daga nan bakin babban kwalta yanda aka ajesu.

Sadiya ce ta soma fad’in “Ina fata wata rana ki sami gurbi a zuciyarki ki yafe mun Sabeera.. Nasan Kinsan maganan bashin Hajiya Tabawa dake kanmu wanda Baba yace zai biya mana amma saidai idan zan amince da aurensa.”

Katseta Sabeera tai da fad’in “Basai kin maimaita ba na sani tinda har ya kiraki da Baby a gabana.”

Sauk’e ajiyan zuciya Sadiya tai kafin taci gaba da fad’in “Ba auren jin dad’i nai ba Sabeera. Dan ni ko a labarai ban tab’a karo da labarin irin aurena ba.. Auren Mission nai.. Sannan a GIDAN ARO nake zaune gidanda sam ba nawa bane kuma ko wane lokaci za’a iya sallamata.. Mr Inspector ya aureni ne ba wai dan yana k’aunata ba Sabeera.. Da zaran ya ida mission d’insa zai sallameni daga rayuwarsa Wanda zanfi kowa Farin ciki da hakan..”

Sai sannan Sabeera ta d’an dubeta da mamaki..

Sadiya ta murmusa Wanda yafi kuka ciwo taci gaba da fad’in “Sabeera amfani dani kawai yake domin ya cimma burinsa ya samu wani clue da zai had’asa da abokan ark’allan Sagir.. Yau da zai samu abinda yake nema zai rabu dani.. Amma idan bai samu ba haka zai Ta wahalar da rayuwata.. Kinji irin jarabawar da Sadiya ta sake samun kanta ciki..!” Ta k’arashe gajeriyar hawaye na gangarowa daga idanunta.

Sabeeran ma hawaye ne ya gangaro mata amma Sai batace komai ba.

Sadiya Ta k’ak’aro murmushi ta sakar mata daidai sanda suka iso layin gidansu Sabeeran dan dama sai an fara samun gidansu Sabeera dake sarari kafin a isa nasu Sadiya dake can k’asa.

“Ki gaida Mama Sabeera.” Ta fad’i murya can k’asa.

Juyowa Sabeeran tai ta dubeta kad’an kafin ta jinjina kai. Ba tareda tace komai ba ta shige hanyar gidansu.

A hankali Sadiya Ta lumshe idanunta tana ji can k’asar zuciyarta bazata tab’a bari abinda ya faru ya lalata zumuncinsu da k’awancensu itada Sabeera ba.. Tare suka taso tin suna yara bata da wata k’awa bayan Sabeera.. Tasan Sabeera na k’aunarta deep inside, kawai dai zuciya ce da batada k’ashi amma da yardar Allah zasu koma kaman da. Da wannan tinanin ta nufi layin gidansu.. Zuciyarta fari k’al zataga Umma dasu Ashir da Habeeb. Saidai murmushin nata ne ya tsaya Cak sanda Ta hango Mr Inspector tareda abokan aikinsa ga mutane sunyi cincirindo a k’wanan lungunsu da alama bayanai suke d’auka.

Zuciyarta yai wani irin tsinkewa dan dama tinda ta fito daga makarantar gabanta ke tsananta fad’uwa kaman dai wani mugun abu zai faru da ita.. Saurin girgiza kai Ta soma kafin ta nufi lungun nasu cikin sauri..

Kaman ance ya d’ago kai nan ya hangota ta nufo lungun..

“Oh no..! What’s she doing here..?” ya furta yana k’ok’arin nufota..

Bai tsaya saurarenta ba ya shiga janyota yana fad’in “Mai ya fito dake..? Didn’t I tell to wait for me there.. What exactly is wrong with you.. Baki jin magana koh.. What if something happens to you..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar.

Girgiza kai take tana duban lungun nasu “I need to see my Mom and my brothers.. Bazaka hanani ba wannan karon Mr Inspector.!”

Ya shafi goshinsa kad’an yana k’ok’arin rik’ota. Fuzgewa tai ta nufi lungun nasu a guje tana ambaton Ummanta..

“Damn it.! She can’t find out about this.!” Ya fad’i yana mai bin bayanta cikin sauri shima, lokaci guda yana kiran sunanta yana fad’in “Idan kika shiga gidan nan sabon mission zamu fara daga farko..! Just stay right there.!”

Ko sauraronsa batai ba ta tura k’ofar gidan ta shige a guje tana kiran Umma.. Su Assad tsaiwa kawai sukai suna duban Sadiya da Mu’azzam d’in wanda yabi bayanta cikin sauri.

“Umma gani nan na dawo. Ina kuke..? Ashir.. Habeeb.. Umma wai kuna ina..?” Tana maganar tana bud’e k’ofofin gidan Mu’azzam na biye da ita yana k’ok’arin dakatar da ita..
Chapter 50 · 0% Book details