← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 175

Sashe 151

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar ya iya zama saman kujeran har lokacin wani irin duba Mu’azzam d’in ke aika masa.

Yana zama Mu’azzam ma ya janyo kujera ya zauna ba tareda yace komai ba.

Hoton Danger ya aje saman table d’in yana duban Musaddiq “Tell me ina yake..? Ina zamu samesa.?”

Girgiza kai Musaddiq yake yana furta “Ban.. Ban sani ba.. Wllhi ban Sani ba.. Ban sanshi ba..”

Tsawa Mu’azzam ya daka masa yana mai buga table d’in “Shashantar dani dakai na tsawon watanni basu isa ba..!” Yaci gaba da huci a hankali yana furta “Kar ka kuskura..! Kar ka kuskura.!” Yana maganar yana jinjina kai a hankali.

Cikin zuban hawaye Musaddiq ke fad’in “Wllhi ban sanshi ba.. Ban san su waye suka kashe Ikram ba nasan dai ni ne mutumin da ya lalata mata rayuwa kuma yaci zarafinta amma wllhi Bansan su waye suka kasheta ba.”

“Shut up.! Shut the hell up.!” Ya kuma fad’in haka yana buga table d’in hawaye har na tsartowa daga cikin idanunsa. Lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Kar ka yarda ka raina mun hankali a karo na biyu.. Wann hular taka shaida ce da na samu wajen Danger..!” Ya k’arashe yana nunama Musaddia d’in hoton da sukai su biyu Musaddiq sanye da hular.

Musaddiq yaci gaba da girgiza kai yana hawaye “I was wearing it when the incidence happened.. Kuma na rasata ne tin ranan da abin ya faru.”

Mu’azzam yaci gaba da jinjina kai yana furta “Amma ranan na ga wann hular a d’aninka ya akai hular Ta dawo wajenka.?!”

“Mommy ce ta sake saya mun irinta exactly bayan na rasa wancan dan kar ka zargi wani abu..”

“Mommy.!” ya furta a hankali kafin yaci gaba da fad’in “Ya akai Mommy ta sani..? Tell me all the details.”

A hankali Musaddiq ya soma karanto masa duk abinda ya faru. Hawaye na gangaro masa.

Mu’azzam d’inma da k’yar yake saurara yanaji kaman zuciyarsa zata tarwatse.

“Ka tashi ka tsinci kanka a gida.?” Ya tambaya yana duban Musaddiq.

Musaddiq ya jinjina kansa a hankali alamun eh.

“Toh ya akai ka tafi gida..? Waye ya kaika gida..?”

Sai ya d’ago ya dubi Mu’azzam d’in dan harga Allah bayaso yai incriminating Mommy dan ko babu komai ita d’in mahaifiyarsa ce.

Mu’azzam ya kuma jefa masa tambayan cikin kaushin murya wann karon yana mai kuma buga teburin wanda har saida Musaddiq d’in ya firgita.

Ya rintse idanunsa yana hawaye yake furta “Mommy..! It was Mommy..! Mommy itace ta kaini gida..”

Mik’ewa tsaye Mu’azzam yai yana jinjina kai “That woman..! Itace.. Ita ce ta aikata komai..!” Lokaci guda ya soma jada baya yana k’ok’arin ficewa Daga interrogation d’in.

Musaddiq yaci gaba da hawaye yana furta “Please have mercy on her..”

Ko sauraronsa Mu’azzam bai tsaya ba ya fice cikin sassarfa kaman zai kifa k’asa yana neman layin Assad. Nan yaga kira da bak’uwar lamba na shigo masa.

Ya d’aga yana mai k’arawa kunnensa.

Daga d’aya b’angaren matar ta soma fad’in “Sunana Hajiya Faty Mijinyawa wacce kazo gidanta kwanaki kana neman Hajara.”

Mu’azzam ya jinjina kai yana fad’in ya ganeta.

Hajiya Faty taci gaba da fad’in “Akwai abu mai mahimmanci da nake so na baka, idan zaka samu hali maza maza ka fito ka taho Gidana dan Ina tsoron ficewa kar wani abu ya faru.”

Cikin sauri yake jinjina kai yana fad’in gashi nan tafe. Daidai lokacin Assad ya k’araso.

A gurguje Mu’azzam ke sanar dashi abinda ke faruwa lokaci guda yake fad’ida Assad “Maza maza ka tafi gidan Daddy kar matar nan tai escaping.. Kaje ka tabbata she doesn’t escape ni kuma zan tafi gidan Hajiya Faty yanzu..”

Assad yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Copy.” Cikin sauri ko wannensu ya nufi abin hawansa.

A can b’angaren su Sadiya kuwa fitowar Umma kenan zata nufi kitchen ta hango alamun coins guda biyu saman kujera. Gabanta ya yanke ya fad’i.. Ta soma takowa a hankali ta nufi yanda take hango coins d’in Sai k’yalli suke zuciyarta naci gaba da yankewa.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*76*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A hankali take duk’awa tana kuma duban coins d’in dake aje saman kujera hawaye na ciko idanunta lokaci guda hotunan abubuwan da suka faru dasu na gifta k’wayan idanunta.. ‘Yaruwarta Yayarta take hangowa da lokacin da Ta rasata... Takai hannunta dake tsananin rawa a hankali tana shafa coins d’in. Hawaye d’aya na bin d’aya suna gangaro mata.. Ta d’aukesu cikin hannunta tana kuma juyasu hawaye basu daina gangaro mata ba.

Tana nan zaune wajen Aunty Larai ta fito daga kitchen ta nufo parlorn, nan ta hangi Umma duk’e wajen tana hawaye. Aunty Larai ta k’araso da sauri tana tambayarta lafiya meke faruwa.

Coins d’in Umma ta d’ago ta shiga nuna mata hawaye d’aya na bin d’aya “Wann sisin kobon shine alama da aka d’aura mana.. Shine alaman da na jima ina ajiye dashi tsahon shekarun nan domin na dinga tuna ‘Yaruwata dashi.. Larai nasan nawa guda d’aya ne toh daga ina wann ya fito.. Ya akai na sake samun irin alaman.? Ya akai sisin kobon suka zamto guda biyu.?” Ta k’arashe cikeda kad’uwa tana nunawa Aunty Larai.

Sadiya da fitowarta kenan tai tsaye tana duban Umma rik’eda coins.. Sai ta k’araso da sauri tana duban coins d’in..

Ta shiga nuna coins d’in yatsarta tana fad’in “Umma dama wann shine alamar da aka d’aura maku a jelar gashinku keda ‘Yaruwarki..?”

Umma tai saurin jinjina kai “Wann alama irinshi aka d’aura mana dama duk wata budurwa dake cikin jirgin.”

Sadiya ta tina a hannun Mu’azzam jiya taga yanata juyasu. Ta d’an girgiza kai kad’an tana ci gaba da nuna coins d’in.

Muryar Umma ne ya katse mata tunaninta “Ya akai naga guda biyu..?”

Ta kuma dubansu tana murmushi kafin taci gaba da fad’in “Yaruwata.. ‘Yaruwata tana raye k’ilan.. Bata mutu ba..!” Hawaye sukaci gaba da gangaro mata tana hawaye. Lokaci kuma tai tsaye tace “Amma.. Ya akai suka zama guda biyu..? Waye ya ajiyesu a nan..?”

Sadiya Ta girgiza kai tana duban mahaifiyar tata sai kuma tace “Umma.. Wann ai hannun Mu’azzam na gansu jiya.. Shi ya mance a nan.” Ta fad’i tana duban Umma dan ita tama mance cewa bata so Umman ta d’ago nan gidan Mu’azzam d’in ya kwana.

Umma ta shiga girgiza kai tana duban Sadiya “Mu’azzam..! Mu’azzam fah kika ce.. Shi yazo da wad’ann..?”

Sadiya ta jinjina kanta a hankali “Hannunsa na gansu.”

Cikin sauri Umma ta mik’e tana fad’in “Ina Mu’azzam d’in.. Inaso na tambayesa ina ya samu wann alama.. Watak’ila ‘Yaruwata bata mutu ba.. Watak’ila Ta rayu... Watak’ila..” Yanda take maganar tana hawaye tana murmushi dole ta baka tausayi.

Sadiya ta kamo hannayenta tana k’ok’arin calming d’inta “Umma kince irin wann alamar aka d’aura ma sauran ‘yanmatan.. Umma shekarun da yawa mai zai faru idan wann alama ba na ‘Yaruwarki bane.”

Umma tai shiru tana hawaye tana tina sanda bomb ya tashi da jirgin, sai kuma ta soma girgiza kai tana fad’in “Ina so nasan yanda ya samu wad’ann shaidar ne.. Inaso naji mai ya faru da jirgin bayan bomb d’in ya tashi shin akwai wad’anda suka rayu ne kokuwa..? Sadiya Ina so naga Mu’azzam yanzu yanzu.. Dan Allah ku kaini yanda yake..” Ta k’arashe tana duban Sadiyar da Aunty Larai cikeda zak’uwa.

Sadiya da Aunty Larai suka dubi juna.
Sadiya zatai magana Umma ta soma girgiza kai tana fad’in “Bazan zauna a nan ba Sai naga Mu’azzam ya sanar dani yanda ya sami wann silallan.. Bazan zauna ba Sadiya sai na gansa.. Dan Allah ku kaini yanda zan sami Mu’azzam..” Ta k’arashe duk a dame.

Sadiya data tina cewa Mu’azzam a daren jiya ya sanar da ita yana fuskantar k’alubale da ahalinsa sai ta rasa mai zatace wa Umma, Aunty Larai ta dubi Sadiyar tace ta kira Mu’azzam a waya. Babu musu ta jinjina kai ta tafi d’auko wayarta. Saidai dik kiran da take bai d’aga ba. Umma tace a kira Assad.. Shi kuma wayarsa bata shiga.. Tuni sukaga Umma ta nufi d’aki ta d’auko mayafi tana fad’in wajen aikinsa zata tafi ta dubasa.. Aunty Larai da Sadiya sukai saurin nufota suna fad’in ta dakata har a samesa a waya. Inaa ko saurarensu Umma batayi tuni ta saka kai ta fice hakan yasa dole suma suka nufota, sauk’in abin su Asheer suna makaranta hakan yasa duk suka fice gana d’aya dan Umma dai ta dage sai taga Mu’azzam a wann ranan.

**
A b’angaren Mu’azzam yana isowa gidan Hajiya Faty ya fahimci wani abu baya tafiya daidai, babu kowa a gate, babu securities sann ga k’ofar gidan a bud’e. Take ya ciro intercom dake aljihunsa ya nemi backup.. Lokaci guda kuma ya ciro bindigarsa ya zama cikin shiri ya soma sand’a ya nufi cikin gidan. D’akin masu gadin ya soma dubawa yanda ya tadda an d’auresu an rufe masu bakuna.. Yai masu alama da hannu dake nunida suyi shiru.. Suka shiga jinjina masa kai a galabaice.

Mu’azzam ya kwancesu ba tareda ya tsaya sauraron bayanansu ba dan yasan hakan bazai wuce aikin Danger ba.

Yana isa cikin gidan ya dinga bud’e k’ofofin a hankali yanda ya tadda ma’aikatan gidan mata suma an rufe su a wani store a d’aure masu bakuna sai kuka suke. Yana bud’esu kenan ya soma sinkayo muryar Hajiya Faty tana fad’in “Dan Allah kar ka kashe ni.. ko nawa kakeso ka fad’a zan baka.”

“Shut up rufe wa mutane baki.!” Danger ya daka mata tsawa da fad’in haka kafin yaci gaba da nunata da bindiga yana fad’in “The document.. Ina yake..?”

Hajiya Faty jiki na rawa take fad’in “Wane document Kenan... Dan Allah ka mun rai wllhi ni bansan komai ba.”

Danger ya kuma harzuk’a yana nunata da bindiga “BAT.. Takardan BAT.. Ina yake..?”

Hajiya Faty ta kuma girgiza kai kaman batasan komai ba dan Ta d’au alwashin hannun Mu’azzam zata mik’a wann takardan, saidai rauni irin na mace ga bindiga da yake nuna mata yasa Ta bud’e wardrobe jiki na rawa ta zaro document d’in. Daidai lokacin Mu’azzam ya daki k’ofar d’akin ya shigo... Danger kaw jin an bud’e k’ofa ya sanyashi janyo Hajiya Faty ya danna mata bindigar akai yana fad’in kodai Mu’azzam ya koma da baya ko ya fasa mata kai da harsashi.

Mu’azzam ya d’aga hannunsa alamun surrender yana fad’in “It is over for you Danger.. Just surrender now..!”
Chapter 151 · 0% Book details