Sashe 167
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka mutumin yake k’arasowa cikin parlorn Sallama saman bakinsa. Muryar mutumin Baida banbanci dana mahaifinsu musamman kafin girma ya riski mahaifinsu.
Uncle Salman ne ya iya samun zarafin k’arasawa ya mik’a masa hannu sukai masabaha Daddy kam mamaki ya kasa sakinsa ganin fuskar Mahaifinsa tsaye gabansa.
Take mutumin ya soma gaida mutanen dake wajen, Mu’azzam ya k’araso Shima sukai masabaha yana hango kamannin Kakansa a tareda mutumin.
“Jauro..!” Inne ta furta tana dubansa lokaci guda tana nunasa da hannunta dake matuk’ar rawa.
Mutumin ya dubeta Sai yai murmushi ya girgiza kai “Sunana Ramadan ba Jauro ba..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Allah yasa nan ne gidan Alhaji Marwan Gamji..?”
Sai sann Daddy ya samu zarafin jinjina masa kai yana mai nuna masa wajen zama “Bismillah.. Ga wajen zama.. zauna ni ne Marwan Gamji..”
Kafin ya kaiga zama sai ganin Inne sukai ta duk’o gaban mutumin tana kuka tana fad’in “Ka yafeni.. Ka yafeni.. Wllhi kai jikinshi ne.. Wllhi kai d’ansa ne.. Fuskar nan tasa ce.. Dan Allah ka yafeni Bawan Allah ni ce na rabaka da mahaifinka.. Na tabbata kaine d’an Harira da Ta fice Ta tafi da cikinka..”
Gaba d’aya jikkunansu sukai sanyi ganin abinda Ke faruwa. Cikin tsananin sanyin jiki mutumin ya kamo Inne yana fad’in “Dan Allah ki daina.. Kar ki duk’a gabana.. Nida mahaifiyata mun yafeki..” Yai fasali sanda shima ya duk’a gabanta.
Lokaci guda ya d’ago yana dubansu “Tabbas ni d’in d’aya ne daga cikinku amma banzo nan domin na amsa sunan ahalinku ba.. Nazo nan ne domin na tafi da d’iyata wacce aka tabbatar min tana nan a nan..”
Da tsananin mamaki suke dubansa.
Daddy ya girgiza kai yace “D’iyarka kuma..? A nan gidan..?”
Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai d’iyata Jiddah..!”
Ganin basu gane ba sai kallon kallo suke ya sanyasa sakin murmushi kafin yace “D’iyata Ajidde wacce Kyallu ta rabani da ita..”
Sai snn Aunty Nuratu ta girgiza kai tace “Ajidde.. Ta ya ka zamto mahaifin Ajidde..?!”
Ya jinjina kansa kafin ya soma fad’in “K’warai Ajidde d’iyata ce wacce Kyallu ta rabani da ita da kuma mahaifiyarta..”
Mamaki ya cika illahirin mutanen dake parlorn. Ciki harda Mommy dake duk’e nan wajen wacce ake shirin tafiya da ita station.
Mu’azzam ya shiga nanata sunan Ajidde cikin kansa dan yama rasa wacece ma Ajidden.. Kai wann wani irin Al’amari ne daga wann sai wancan. Abubuwan al’ajabi dai bai k’arewa a wann ahali nasu.
Wajen zama Daddy ya nuna masa kafin ya mik’e ya zauna. Kowa ya zuba masa idanu alamun ana jira aji yanda al’amarin ya kasance.
Saida yai gyaran murya wajen ya kuma yin tsit kafin ya soma fad’in “Da farko dai sunana Ramadan.. Mahaifiyata mai suna Harira ta haifeni a wani gari dake can gabacin jihar Kaduna. Tinda ta haifeni sai ta tafi ta barni tareda mutanen da Ta zauna wajensu na d’an lokaci. Akai sa’a mutanen masu dattako ne da sanin ya kamata.. Koda aka wayi gari mahaifiyata ta tafi ta barni sai suka kula dani suka rik’eni amana har na kawo girma.. Tinda na taso sai kowa ya hanani aure a garin sabida a cewarsu babu wanda yasan asali na.. Mahaifiyata yada zango kawai tai ta haifeni ta k’ara gaba. Hakan yasa Iyayen rik’ona suka bani auren d’iyarsu wacce Ita kad’aice d’iyarsu mace sauran maza ne. Bayan na auri Hauwa muna zaune Ina tab’a kasuwanci na dan dama tinda na taso nakeda zafin nema da buga can buga nan.. Muna nan a haka muna zaune da Hauwa Allah bai bamu haihuwa ba tsawon shekaru.. A haka dai har na d’auki Hauwa tare dani muka taho cirani yanda muka yada zango a wani gari mai Sunana Fufore can jihar Adamawa. Tinda nazo garin naji hankalina ya kwanta a garin.. Naji Ina matuk’ar k’aunar zaman garin ba tareda nasan cewa wann garin shine Tushena da asalina ba.
Muka had’u da wata mata a kasuwa mai tallan magani mai suna Kyallu.. Kyallu sai ta bani masauk’i Nida iyalina.. Ashe tinda Kyallu ta k’yalla idanu akaina sai ta apka soyayya na.. wann dalili ma yasa ta bamu masauk’i.. Muna zaune nida matata Hauwa a nan gidan Kyallu mai warka warka tamkar dai muna a GIDAN ARO. Kyallu tace zata bawa Hauwa maganin haihuwa tinda ta fuskanci bata haihuwa, sai muka nuna rashin amincewarmu daga ni har Hauwa tinda munsan haihuwa abu ne wanda Allah Ke baiwa wanda yaso a lokacin da yaso. Kyallu dai bata janye kudirinta na cewa zata bamu magani ba, dan muna ganin masu amsar magani suna shiga da fice a gidan Kyallu.. A haka ta dinga hure wa Hauwa kunne ba tareda munsan cewa Hauwa na d’auke da juna biyu ba ma ashe.. Hauwa ta soma amsar tayin maganin kyallu a b’oye ba tareda tasan cewa tuni tanada juna biyun ba.. Koda na fahimci tana amsar maganin Kyallu raina Sai ya b’aci nace da ita zamu tattara mu tafi.. Kyallu taita magiya tace na tsaya na gani idan maganinta baiyi aiki ba Ta yarda na d’auki matata na tafi.. Hauwa ma ta nuna damuwarta na cewa saidai mu tsaya.. Nan kuwa Rahmatu ta fara nuna alamomin masu juna biyu.. Kyallu tace maganinta ne ya soma aiki.. Nace atafau ba maganinta bane domin kuwa ita bata isa ta saka ko ta hana ba.. Iko ne na Allah. Sann idan ma maganin nata yayi aiki ta sani ba yinta bane Allah zai iya nuna k’udararsa da isarsa ya sanya maganin nata yayi aiki domin yaga zatai imani ko zata tab’e. A haka na dinga k’ok’arin nusar da Kyallu tauhidi amma sai tai k’ememe tak’i d’aukan wa’azin da nake mata. Ni kuma na kasa barin garin na kasa d’auke matata mu tafi ba tareda nasan dalili ba.. Sai na alak’anta hakan da cewa Watak’ila Allah ya nufi nazo garin ne domin na had’u da wann mushirikar matar mai suna Kyallu nai mata wa’azi ko zata wa’aztu.. Tafiya yayi tafiya har lokacin haihuwar Hauwa yai wanda zai kuma tabbatarwa Rahamatu tanada juna biyu muka taho garin ba maganin Kyallu bane yai aiki, domin kuwa bamu cika watanni tara a garin ba Ta soma nak’uda.. Kyallu ita ta amshi haihuwar Hauwa yanda muka rasa Hauwa a wajen haihuwa. Ta haifo d’iyarta mai kama da ita na maida mata sunan Hauwa (Jiddah).. Nayi kukan rashin Hauwa dan bansan mai zanje na sanar da iyayen Hauwa ba.. Na yanke shawarin d’aukan d’iyata Jidda na tafi da ita, amma sai Kyallu ta dage saidai na zauna na aureta mu raini jidda tare.. Ni kuma Sai nak’i aminta da hakan.. Kyallu sai ta rik’e Jidda tace bazata bani ba.. A ranan taita min kururuwa ta had’a mun mutane tace ni b’arawo ne zan sace mata d’iya.. Inaji ina gani Kyallu tasa aka mun korar wulak’anci a garin Ta kuma goye d’iyata a bayanta Ta hanani d’iyata ta bini da sharri cewa d’iyarta ce nida ita munyi aure zan d’auketa ne na gudu na shiga duniya da ita. Kuma wani ikon Allah ban iya aiwatar da komai akai ba bansan wani k’ullin Kyallu tai akaina da d’iyata ba.
Koda na dawo gida na sanar da iyayen Hauwa cewa mun rasa Hauwa sai sukai tawakkali amma na kasa sanar dasu abinda ya samu d’iyarmu da Hauwa wacce muka haifa a garin fufore.. Tin daga wann lokaci sai aure ya fice mun a rai.. Naci gaba da neman kud’i gadan gadan dan sai inaji sakaci na ne yasa na rasa d’iyata da matata wacce na kasa komawa na k’wato ta.. Na d’au alwashin ko ba dad’e ko ba jima zan koma wann garin na k’wace d’iyata Jidda daga hannun Kyallu.. Ana haka shekarar da ya shud’e mahaifiyata Ta dawo garin da Ta barni.. Nan take sanar dani ga garin mahaifina.. Wann garin da na baro d’iyata ashe shine asalin garin mahaifina kuma tushena.. Asirin da akai wa mahaifiyata ya karye cikin ikon Allah nan take labarta mana duk abinda ya faru.. Ni kuma Sai na k’udiri niyyan bazan nemi dangina ba amma zan yafe masu kaman yanda mahaifiyata ta yafe.. Bayan Allah yayiwa mahaifiyata cikawa sai na tafi garin Fufore domin na d’auko d’iyata daga wajen Kyallu wacce ta azirta kanta da d’iyata.. Toh a nan ne Bayan naje da Jami’an tsaro sun tsare Kyallu take sanar damu cewa gidan Gonar Jauro Gamji take tura Ajidde kai magani wa matar Alhaji Marwan Gamji. Banyi niyyan taka gidan gonar ba amma sabida d’iyata dole naje.. Haka na shiga gidan Ina tina sanda mahaifiyata take sanar dani mammalakin wann gidan gonar shine mahaifina.. Koda na tambaya sai akace ai Matar Marwan Gamji dake jinya ta warke kuma ta d’auki Ajidde tafi can gidan mijinta dake Birnin tarayya tareda ita.. Wann shine dalilin da yasa na taho nan domin na d’auki d’iyata amma ba domin na kasance d’aya daga cikinku ba..!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa.
Al’ajabi da mamaki ya cikasu.. Kowa sai jinjina lamarin yake.
Aunty Nuratu na hawaye take jinjina kai tana furta “K’warai Ajidde itace mai kawo min magani amma ba maganin Kyallu take kawo min ba.. Ajidde da Musaddiq su suka shirya yanda zasu zubar da maganin Kyallu sann suke amso min ayoyin Ubangiji daga wajen Malama Hafsah.. Ajidde bata tab’a bani maganin Kyallu ba.. Maganin Malama Hafsah take bani wanda ayoyin Ubangiji ne da kuma magunguna na musulunci da suka Zo a sunnah. Cikin ikon Allah wad’ann ayoyi da nake sha su suka hana Shed’anin da Hajara ta turo min ci gaba da zama cikin jikina.. Tabbas Ajidde Alkhairi ce a gareni.. Abinda tayi mun Ubangiji ne kawai zai iya biyanta.. Ajidde yarinyar kirki ce kuma abin alfahari ga ko wani mahaifi..”
Hawaye suka ci gaba da zubowa, yayinda Mommy Ta saki baki da hanci tana jin yanda aka tarwatsa tsarinta cikin ikon Allah da buwayarsa.. Haka Aunty Nuratu ta d’aga waya ta kira Mama Hindu tace Azo da Ajidde parlorn Daddy.
Jiki a matuk’ar sanyaye Ajidde Ke takowa tana kallon mutanen daketa faman binta da kallo, Sai tananji kaman k’afafunta bazasu iya d’aukanta ba.. Idanunta suka sauk’a kan Mutumin da kukansa Ke k’aruwa tinda ta soma shigowa cikin parlorn.