← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 175

Sashe 90

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba nan fah Mommy ta hayayyak’ota da fad’in “Ni zaki ma sharri Ina mahaifiyarki..! Allah yasa ba ni kad’ai bace wajen.. Daidai kenan yanzu Kinga ranan zab’en namiji akan mahaifiyarki.. Gashi ya zab’i matar da yai auren bariki da Ita ya barki.. Yanzu zaki dawo cikin hayyacinki Safeenah..”

Mu’azzam dai bai kuma bi takansu ba ya janyo hannun matarsa suka fice suka bar Mommy da Safeenah sai rantse rantse suke gaban Daddy..

Safeenah tana fad’in Mommy ce ta zugota tazo Mommy tana fad’in hakkin abinda tai mata ne ya kamata.

A guje Safeenah tabi bayansu kaman sabuwar kamun hauka.. Mu’azzam zai shige Mota Safeenah ta rik’o rigarsa tana fad’in “My Halal.. Dan Allah kace sakin wasa ne.. My Halal you know I can’t do without you.. Please Mu’azzam kar ka tafi ka barni..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka.

Kallanta yai ya kalli yanda Ta rik’e masa riga kafin yace “A hukumance abinda kikayi za’a d’aureki akan hakan, Kinyi attempting murder.. Kin sake cin albarkacin Daddy bazan jefaki a cell ba.. Kaman yanda dama zaman auren da kikayi albarkacinsa kika ci.. Sakar min rigata.. You are not my wife..!” Yana ida fad’in haka ya finciki rigarsa yai shigewarsa Mota.

Safeenah tabi motar a guje tana fad’in my Halal.. Inaa tuni motar ta fice daga gidan.

Ihu ta kuma zundumawa ta nufi cikin gidan tana kuka tana fad’in wllhi sai ta bisu ta dawo da halal d’inta saidai ai duk abinda za’ayi.

Zata shige Mota kenan taga Daddy tsaye gabanta ya kai k’ololuwa wajen had’e rai.

“Give me the keys..” Ya fad’i yana mik’a mata hannu.

Girgiza kai take tana hawaye “Daddy please ka barni na bi mijina.. Daddy wllhi sharrin shaid’an ne.. Daddy zafin kishi ne bansan abinda nake aikatawa ba.. Daddy na tuba dan Allah ka barni nabi Mu’azzam.. Wllhi mutuwa zanyi Daddy idan har ya rabu dani.. Please Daddy dan Allah ka ceceni.. Daddy I’m your Daughter please..!” Ta k’arashe tana mai duk’awa had’ida rik’e k’afafun Daddy tana kuka sosai.

Abinka da d’a da mahaifi, Zuciyar Daddy ta raunana.. A hankali ya mik’a hannu ya kamo Safeenah ya tada ita tsaye.. Safeenah ta kuma fashewa da kuka tana mai fad’awa jikin mahaifinta. Bai hanata kukan ba, saida tai mai isarta kafin ya kamo hannunta suka nufi parlornsa. Zaunar Ta saman kujera yai yana dubanta cikeda tausayawa.. Shi kansa ya fara tsoron kardai Kwanyar Safeenah ya tab’u ne.

Ruwa ya mik’o mata yace tasha.. Babu musu ta amsa ta kafa kanta ta shanye still hawaye na gangaro mata.

“Safeenah inaso ki nastu ki nitsa hankalinki waje guda.. Safeenah da halayya irin wannan bazaki tab’a samun kwanciyar hankali a gidanki ba.. Bindiga Safeenah.. Kisan kai zakiyi akan wata ta auri mijinki..? Waye yace miki shi mijinki ne ke kad’ai.. Waye ya baki wann guarantee d’in..?!” Ya d’an k’arashe cikin tsawatarwa

Safeenah batace komai ba Sai kifa kanta da tai tana hawaye.

Daddy ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Mu’azzam yana d’aga miki k’afa, yana duba girman zumunci.. Amma ba don haka ba abinda kika aikata yau da ya kulleki a gidan Yari.. Why Safeenah.. Maiysa kike nema ki haukarta da kanki babu gaira babu dalili.. Kan rayuwar duniya da k’alilance ba tabbata za’ayi ba.. Idan kikayi hak’uri wataran babu ke ko Babu abokiyar zaman taki ko ma Babu mijin da ake ta faman tada jijiyan wuya akansa.. Rayuwar duka batada yawa Safeenah.. Har yaushe zakije ki jefa kanki a halak’a sabida soyayya.. Ai so ba hauka bane Safeenah..!” Ya d’anyi fasali yana dubanta. kafin ya d’ago yatsa yana nunata “Toh ki kula.. Ki sani rayuwar duka batada yawa.. Yau idan mune gobe ba mu bane.. Idan kuma baki natsu kin daina wann haukar naki ba Ina mai tabbatar miki ni da kaina zan d’aukeki na kaiki mental facility kin jini koh..?!”

Safeenah ta d’ago tana dubansa “Daddy asibitin mahaukata kuma..? Daddy wllhi da hankali na.. Kawai son mijina nake... Daddy na saba dashi bazan iya rayuwa babu shi ba.. Dan ka barni na bisu Daddy..”

Mik’ewa Daddy yai yana dubanta cikin tsananin b’acin rai “Idan kika sa k’afa kika fice daga gidan nan.. Ki nemi wani mahaifin amma bani ba Safeenah..!” Daga haka Sa kai yai ya haura upstairs..

Safeenah tai mutuwar zaune tana duban mahaifinta har ya haye sama.. Wani irin sabon k’unci da kuka ne taji sun taru sun bugi k’irjinta lokaci guda.. Ta mik’e ta fice ta nufi side d’un Mommy tana kuka kaman ranta zai fice..

Saidai tana zuwa Mommy ta haura sama ta k’yaleta ita kad’ai.. Tabi bayan Mommy da sauri tana kiranta.. Ko kallo bata ishi Mommy ba balle ta tankata. Tanaji Mommy ta banko k’ofar d’akinta da k’arfin gaske ta rufe akan fuskar Safeenar.

Juyowa tai ta dubi k’ofar d’akin Meema dake bud’e. Nan ta hangi Meema saman gadon tana karatun novel.. Suna had’a idanu Meema ta mik’e ta k’araso ta tura k’ofar d’akinta ta rufe..

Silalewa Safeenah tai a wajen tana kuka mai tsuma zuciya.

**

Assad kaw bashi ya farka ba Sai wajajen can bayan azahar, ya mik’e ya gansa kwance a d’aki babu riga jikinsa, daga shi sai shorts.. Mamaki ya cikasa.. Yai saurin janyo rigarsa yana rufawa, yana dafe kansa da yai masa nauyi lokaci guda yana tuno abubuwan da suka faru.. Innanlillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum zuciyarsa ke iya nanatawa.. Meke faruwa..? Mai ya faru dashi. Take ya soma tuna cewa Maleeka tazo tana neman taimakonsa.. Toh ya akai ya k’are a d’aki kuma undressed.. Cikin sauri ya mik’e yana duba lokaci.. Wai meke faruwa ne..? Mai ya faru..? Tambayoyi da dama cikin zuciyarsa da ya gaza samo amsoshinsu.

A fujajan ya fice parlor yana dubawa ko zaiga Maleeka a parlorn. Babu Maleeka babu alamarta saidai ga kayan karin kumallon da suka ci nan..

Cikin sauri ya suri wayar salulansa ya soma dialing layin Maleeka.

Ringing d’in wayar nata yaji a k’ofar parlorn, Ya tsaya cak yana sauraro.

D’ago kan da zai ya hangota ta shigo cikin parlorn muguwar murmushi saman fuskarta, Ta canza shiga wann karon cikin wasu sutura masu bayyana tsaraici.

“Wai har ka tashi a baccin..?” Ta tambaya tana fari da idanu had’ida bank’aro k’irji.

Shaye da tsananin mamaki kurum yake dubanta kafin yace “What really happened Maleeka..? Tell me mai ya faru..?” Yai tambayar cikin tsananin kad’uwa.

Murmusawa ta kumayi tana k’ok’arin matsowa kusansa. Ya dakatar da Ita ta hanyar d’aga hannu “Don’t dare.. Don’t you dare..!” Ya fad’i cikin d’acin rai.

Ta murmusa kafin tace “Idan kana son sanin komai.. Bani cell phone d’inka..!” Girgiza kai yai yace “Ke koda wasa don’t try me..”

Murmusawa tai kafin tace “Ashe ka mance da wa kake tare.. Ka mance profession d’aya garemu.. I won’t say a word.. I won’t explain anything to you.. Until you hand me over your phone..!” Ta k’arashe tana sakin huci.

Yana son yasan mai ya faru.. Baisan wani tuggu ta k’ulla masa ba.. Baida wani zab’i face ya mik’a mata wayar.

Ta saka hannu ta fuzge wayar nasa.. Aiko nan taga ya danna record Wato zai recording conversation d’insu ya sami evidence against her. Ta katse recording d’in tana sakin murmushi “Do you think I’m that fool Assad.. You might be my senior at the police academy.. Amma a wajen aiki you are my mate.. Nasan yanda abubuwan suke gudana..” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta.

Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda Maleeka take nufosa.

“Kar kizo kusana najasa kawai..!” Ya fad’i yana sakin huci..

Dariya tai kafin tace “Na yaushe kuma Assad.. Ai mun riga da Munyi Abinda Zamuyi..”

Dakatar da ita yai da fad’in “K’arya kike makira fasik’a.. Nayi imani babu abinda nayi dake..!”

Dariya ta fashe dashi wann karon kafin Ta dubesa tace “If I were you.. I wouldn’t be so sure..”

Cikin tsananin huci Assad ke furta “Na fad’a k’arya kike munafuka..!”

Ta kuma darawa kafin tace “What if I have a concrete evidenc that clearly shows ni da kai munyi abinda zamuyi.. Kamar dai haka..!” Ta k’arashe tana nuna masa fuskar wayarta hotonsu su biyu kwance saman gado babu tufafi ya bayyana a fuskar wayar.

Zuciyar Assad yai wani irin yankewa.. Ya shiga gani duru duru.. Jiri na neman kaisa k’asa.

Hannunsa na rawa haka ma muryarsa yake nuna hoton yana fad’in “Menene wannan.. Menene wannan Maleeka..?!”

“This is our photo Darling..Making love..” Ta k’arashe tana mai kashe masa idanu guda.

Girgiza kai ya soma cikeda jinjina kaidi irin na mace “What..!” Ya furta yana dubanta. Lokaci guda yaci gaba da girgiza kai yana fad’in “That’s not me in the picture.. Bani bane photoshop ne..!”

Ta murmusa kafin tace “Unfortunately kai ne cikin hoton nan.. Kai bama hoto guda d’aya bane ka gansu.. Hotuna ne.. Harda videos..” Ta k’arashe tana sliding pictures d’in..

Tsananin kad’uwa had’ida tashin hankali suka had’u ma Assad.

Maleeka taci gaba da fad’in “Kai jami’i ne na bincike.. Kasan hoton da aka had’a ka kuma San hoto na gaskiya kaman dai wann.. Munada na’urar da zai nuna cewa da model d’in wayar nan tawa akai hotunan nan.. Hotunan nan na gaske ne.. Kai kafi kowa sanin haka.. Sannan fuskarka da jikinka sun fito sun bayyana b’oro b’oro.. Babu wanda bazai ganeka ba cikin hoton nan koda kuwa yau ne ya soma ganinka.!”

Gumi mai tsananin zafi yaci gaba da tsartsafo ma Assad.. Ya shiga girgiza kai yana nunata da yatsa “How could you.. How could you Maleeka.. Banyi niyyan komai ba face taimaka miki.. Maiyasa zaki mun haka.. Mai kike nema a wajena..?!”
Chapter 90 · 0% Book details