← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 175

Sashe 4

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana k’ok’arin ficewa daga motar yake fad’in “No..MUSADDIQ ne... Daga yanda yake mun magana nasan ba cikin hayyacinsa yake ba..”

“Musaddiq kuma..? Na kwana biyu banji kana tare tare da gagaransa ba.. What really happened..?”

D’an tab’e baki Mu’azzam yai kafin yace “How would I know.. Abunda na sani kawai shine ya kasa karb’an k’addarar cewa Ikram ta tafi kuma bazata tab’a dawowa ba.. I’m afraid rashin Ikram ka iya jefa Musaddiq halinda ya riga ya bari a baya..” Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa..

Cikeda tausayawa Assad yake duban abokin nasa, yasan d’awainiya ne da dama zasu kuma hawa kan Mu’azzam d’in...

Daidai lokacinda cab ya tsaya.. Mu’azzam ya shige yana fad’in “Kaje kayi sauri ka isa location d’in zamuyi waya..”

Baki sake Assad Ke dubansa yana kuma juya ‘yar k’aramar Doguwar takardan mai d’aukeda address d’inmu.. D’an girgiza kai kurum yai kafin ya shige ya d’auki hanya...

**

-Star lake street, Maitama_

Tsaye tayi saman kan matar dake kwance saman gado wacce idanunta Ke bud’e tarau saidai gefen jikinta guda tamkar a shanye yake, bakinta dake karkace miyau na fitowa.. A tak’aice dai kallo guda zakai mata ka fahimci matar tana cikin tsananin jinya ne...

A hankali matar dake tsaye kanta ta duk’a tana mai ci gaba da k’are mata kallo, lokaci guda ta saki murmushi tana mai ciro tissue paper dake ake gefe cikin kwali ta shiga goge mata miyau d’in dake fitowa daga cikin bakinta. Lokaci guda take furta “Na shafe tsawon shekaru ina jinyar kishiya.. Shin zan samu riba nan gaba..? Shin hak’ata zata cimma ruwa.. They say everything in life has a price, Nuratu.. Could this be my punishment..?” Tai fasali tana mai duban matar wacce ta kirata da Nuratu kafin ta saki murmushi tace “No wait.. How could this be my punishment bayan ni ban aikata komai ba.. Kece kika aikata mun komai Nuratu.. Kece kika d’auke komai daga gareni.. A baya ked’in matar d’an uwan mijina wacce na miki lak’abi da kishiyar Dinga sannan Hausawa sunce ita d’in tafi zafi.. Kin kasance wacce tafi soyuwa cikin dangi musamman wajen Inne Mahaifiyar mazajenmu..” Ta k’arashe maganar tana mai disposing used tissue paper d’in kafin ta d’auko wani tana mai kuma goge wanda yake gangarowa, lokaci guda take ci gaba da furta “Nayi zaton idan mijinki ya mutu zaki fita daga rayuwarmu.. Zaki koma yanda kika fito.. But then I was wrong.. Ashe mutuwar mijinki ba komai zai k’ara mana ba face kusanci da juna..” Kukanta ya k’aru sanda taci gaba da fad’in “Kin aure mun miji Nuratu.. Kin aure mun miji bayan naki mijin ya mutu.. Kin zamto shalele mafi soyuwa a wajen mijina.. How could you.. Ta yaya zaki aikata mun haka..? Ta yaya Nuratu..” Tasa hannu tana goge hawayen da ya wanke mata fuska kafin taci gaba da fad’in “This is what you deserve.. Keda mijina bazaku tab’a kasancewa ba balle har Kuji dad’in yin rayuwar aure tare.. Bazan tab’a bari hakan ta kasance ba Nuratu.. Ked’in bazaki tab’a warkewa daga wannan ciwo ba.. Kar ki mance da furucina... Dama na gaya miki gidan mijina tamkar GIDAN ARO yake a wajenki... Babu Ke babu sukuni balle samun natsuwa a cikin gidan mijina.. Na fad’a miki aron gidan na baki na d’an wani lokaci.. Zaki fita daga gidan domin kuwa akwai babban shiri da nake miki.. Zaki fice daga wannan gidan kaman yanda na miki alk’awarin cewa shid’in GIDAN ARO ne a wajenki..” Tana kaiwa nan ta kece da wata irin dariya hawaye na fito mata.. Saida har dariyar nata ya koma tamkar kuka kafin ta kifa kanta gefen majinyaciyar tana kuma sakin kuka mai ban tausayi.

K’amshin turaren mijinsu da yaima k’ofofin hancinta sallama ya tabbatar mata cewa shid’in ne ya shigo.. Nan fah ta dad’a narkewa tana sakin kuka mai ban tausayi..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*03*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ya d’auki mintoci yana tsaye kansu kafin ya duk’a a hankali ya zauna gefen majinyaciyar, yai amfani da hannunsa guda ya dafa matar dake duk’e tana sharb’an kuka “Hajara kukan nan ya isa haka, shi majinyaci ba kuka yake buk’ata daga wajenmu ba.. Abinda yafi buk’ata shine addu’o’inmu.. Kiyi hak’uri ki daina kukan nan kinji..”

Ta d’ago fuskarta da tuni hawaye ya wanke ta janyo tissue paper tana share majinan da yazo hancinta alamun taci kuka.
“Daddy gaba d’aya hankalina ya gaza kwanciya, ace ko yaushe ahalin nan cikin tashin hankali muke.. Babu k’asar da ba’a fita da Nuratu ba amma jikinta yak’i dad’i kullum ciwon nata ma kaman k’ara gaba yake.. An gama Bikin SAFEENAH da MU’AZZAM Ko tarewa basuyi ba wani tashin hankalin ya kunno aka tsinci gawan Ikram..” Ta kuma saka hannu tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta, a hankali takai hannunta ta dafa saman na majinyaciyar, cikin rawar murya take furta “Poor Nuratu, bata San da labarin mutuwar d’iyarta ba.. I’m sure duk randa ta farka daga wannan jinyar nata ta tadda wannan mummunan labarin zata shiga tashin hankali ne maras misaltuwa.. Na kasa daina tunani, mai Ikram tayima wannan mutumin ya kasheta , sannan Maiyasa shima ya kashe kansa.. Da ace shi D’an Garkuwa da mutane ne da ya nemi Ransom.. Ikram yarinyar kirki ce mai tsananin kamun Kai balle ace biye biyen maza take.. Ko shakka babu mutumin nan saceta yayi...Bazan tab’a mance rawar data taka a rayuwar D’amu Musaddiq ba.. Ikram Ta zamto tamkar wata fitila data haska rayuwar Musaddiq, bani mance lokacin da ya dawo daga k’asar England bai dawo da takardan komai ba.. Baiyi karatun ba Sai yawo da abokan banza.. Bani mancewa har kusan koranshi kayi a gidan nan.. Amma Ikram da Mu’azzam basu cire rai akanshi ba.. Mu’azzam ya shawo kanka ka yafewa Musaddiq, sannan Ita kuma Ikram ta taimakawa Musaddiq wajen ganin rayuwarsa ta inganta.... And now that she’s gone.. I don’t know what’s going to happen to our son..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..

Alhaji Marwan Gamji ma hawayen da ya kasa rik’ewa ne ya sauk’o masa yana k’ok’arin dannewa..Ya rungume matarsa yana fad’in “Ya isa Hajara.. Allah yana nan da sannu zai daidaita mana al’amran ahalinmu kinji Ko.. Everything will go back to how it was before kinji koh..”

Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Ta yaya Al’amara zasu koma kaman yanda suke da bayan babu Ikram a halin yanzu, Ikram ta tafi yanda bazata sake dawowa ba. Al’amara bazasu kuma kasancewa kaman da ba.. Ikram Fitila ce a cikin gidan nan, kowa tasan yanda zata zauna dashi.. Na shak’u da yarinyar nan fiyeda yanda na shak’u da Karimatu da Meema, kusan kullum tare muke yini nida ita wajen jinyar mahaifiyarta.. I saw how dedicated she was to her ailing mother.. Yarinyar kirki wacce ko wace uwa zatayi fatan samun irinta.. Bata tab’a banbanceni da mahaifiyarta ba.. Ikram rashinta zai bar gib’i Babba a gidan nan...” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..

Hannu yasa yana mutsuke gajeren hawayen da ya mak’ale masa, lokaci guda yake furta “Wanda duk yayi ma Ikram wannan abun shine aiki yake gabansa domin kuwa itakam Ta sami shaida.. Sannan ita duniya dama takenta kenan GIDAN ARO, dik yanda ka kaiga sonta Ko k’inta wataran dole ka barta.. Yi k’ok’ari ka tanadi guziri mai kyau a GIDAN ARO domin ka inganta gidanka na lahira wacce itace tabbatacciyar GIDA...”

Mommy ta d’an dubesa kafin tace “Wai kaima baka yarda wannan mutumin da aka tsinci gawarsu tare shi ya kasheta ba.?”

D’an jan numfashi kad’an Daddy yayi yace “To be honest, I don’t know what to believe... Maiyasa mutumin nan zai kashe Ikram sannan ya kashe kansa..?”

Mommy tace “Maybe baiso a kamasa dan yasan dole a kamasa shiyasa da yayi garkuwa da Ita ya kasheta sannan ya kashe kansa..”

Daddy yai shiru kaman mai nazari sai kuma ya d’an girgiza kai yace “Still it doesn’t make any sense.. Maiyasa zai kashe kansa dan tsoron kar ya tafi gidan Yari..?”

Mommy tai shiru tana nazari itama..

Fasali ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Inada tabbacin Muazzam bazai huta ba har Sai ya zak’ulo su Wanene Keda alhakin mutuwar Ikram.. Sannan Ina fata kafin zuwa wannan lokaci Nuratu ta sami lafiya domin taga yanda za’a hukunta ko su wanene suka aikata ma d’iyarta haka..”

Wani irin bugawa k’irjin Hajiya Hajara yai lokaci guda.. Ta d’ago tana duban mijin nata Wanda da gani har cikin zuciyarsa yayi maganar.. A hankali ta shiga jinjina kai tana furta “Wannan gaskiya ne.. Ko su wanene suka aikata ma Ikram haka sun cancanci a gurfanar dasu gaban shari’a..”

Ta d’an nusa kad’an kafin tace “Yau ‘yan Fufore Sun koma gidan Sai ya dad’a mana girma da shiru..”

Jin baice komai ba ya sanyata kuma gyara zama tace “Jiya muke magana da Shema’u akan ciwon Nuratu, take ce min har yanzu Aunty Nurah dai shiru jiki yak’i dad’i nace mata wllhi anyi magani k’asashe da dama amma Allah bai nufa an dace ba.. Toh shine take ce min an gwada na gida.? Nace mata Ai baka faye yarda da maganin gidan nan ba.. Tace min akwai wata mata datayi shigen irin ciwonta, maganin wata bafulatana aka gwada dake wata Ruga cen gaba da Fufore.. Shine take ce min Ko za’a gwada nace mata gaskiya saidai idan na maka magana naji abinda zakace.. Magani kuma dace ne ba’a San yanda maganinta yake ba..” Ta k’arashe tana mai tsaresa da idanu cikeda kulawa..

Knocking d’in da akai a k’ofar d’akin ne ya katse masu tattaunawar tasu, Mommy Ta d’an janye jiki daga cikin nasa, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta bada izinin shigowa..

Wata budurwar yarinya ce da bazata gaza shekaru 16 ba ta turo k’ofar ta shigo..

Yanayin da suka ganta ciki ya sanyasu zuba mata idanu suna jiran suji yau kuma menene ya faru a gidan

“Kiki lafiya..?” Mahaifiyar tata ta tambaya

Alhaji Marwan Gamji kaw cewa yai “Come here baby.. Zo ki fad’a min mai ya faru..”

Cikin sanyi ta K’araso ga iyayen nata.. Ta dubi wannan ta dubi wannan..

Duban mahaifiyar tata tai tace “Mommy it’s Addah FEENAH.. Tace ita gidanta da Ya Mu’azzam zata tafi tinda ‘yan karb’an gaisuwar Ikram sun watse, ‘Yan Fufore sun koma itama zata tafi nata gidan..”
Chapter 4 · 0% Book details