← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 175

Sashe 66

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy harma da Aunty Shemau suka dubi Meema dake girgiza kai tana hawaye “Mommy na rantse da Allah ban aikata ba.. Wllhi banyi haka ba.. Maiyasa zan yiwa Addah Feenah haka.. Wllhi Mommy nasan dai na amsa kiran Ameer kuma na goge kiran amma wllhi ban turawa Ya Mu’azzam wani sak’o ba.. Mommy Addah Feenah fah ‘yaruwata ce Maiyasa zan mata haka.. Maiyasa zan rabata da mijinta..?”

Safeenah tace “Kunji munafuka koh.. Ita Tai incriminating d’ina da sak’on da turawa Mu’azzam.. Mommy Meema itace silan kaini police station har na kwana a cell.. Meema son Ya Mu’azzam take Mommy..”

Mommy ta darara masu tsawa da fad’in “Ya isa ni ko sunan D’aniskan yaron nan maras mutunci banson ji..!”

Meema taci gaba da kuka tana girgiza kai tana fad’in wllhi ba ita bace bata aikata ba.

Safeenah na huci take fad’in “Wllhi daga rana mai kaman ta yau ke ba ‘yaruwata bace Meema.. Babu ni babu ke.. Mommy kiyimin iyaka da d’iyarki mun raba jini daga yau..!” Tana ida fad’in haka ta shige fuuu..

Mommy Ta shiga salati tana tafe hannaye “Na shiga uku ni Hajara wannan wane irin Yaro ne haka..? Bayan duk abubuwan da yayi yanzu kuma ya shiga tsakanin yarana ya rabasu, Feenah da Meemah da ba’a rabasu sabida k’aunar juna yanzu saida Mu’azzam ya raba mun kan yara ya masu farrak’u.. Ga Musaddiq ma tin jiya da akace ana zargin Safeenah da kisan Ikram ni ban sake sakasa a idona ba.. Wannan duk laifin Mu’azzam ne.. Ya raba mun kan gida ya dasa gaba da tsana tsakanin ahalina.. Wllhi nima sai na masa farrak’u da duk wani masoyinsa..” Ta janyo hannun Shemau suka shige d’aki.

**

Yamma lis ya iso gidan, ya jima yana horn kafin Gateman d’in ya k’araso ya bud’e masa.

Yana sara masa yana gyara belt d’in wandonsa, hularsa ta ‘yansandan ma a karkace take ga uwar gumi duk ya wanke masa fuska.

Mu’azzam ya dubesa da mamaki kafin yace “Patrick is all well..? Ya na ganka haka..”

Patrick yace “Sir.. Sir cikina ne ya kunce amin afuwa Sir, zuwana toilet na goma kenan Sir.”

Mu’azzam ya girgiza kai kafin yace “Kasha magani..?”

“Eh..Eh.. Yes yes.. Sir, nasha ai..”

Yanda yake maganar gaba d’aya a birkice yake..

D’an Jim Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Idan cikin naka bai tsaya ba kana iya zuwa asibiti ai tinda ganin nan na dawo.. Ko barin kira azo akaika Asibiti.. Allah yasa ba abin naku kaje kasha ba..”

Patrick ya girgiza kai yace “Sir ai na daina sha tinda ka kawoni nan.. Ba sai ka kira kowa ba Sir.. I’ll be fine..”

D’an tab’e baki yai kad’an kafin ya jinjina kai yai masa fatan samun lafiya ya nufi cikin gidan.

Yana shigewa Patrick ya zame hularsa ya d’aura duka hannayensa biyu akai yana fad’in “You are a dead man Patrick.!”

Mu’azzam kaw yana shiga gidan bai tsaya nemanta ba dan yasan bazai wuce tana cikin d’aki ba.

Kai tsaye nasa d’akin ya shige ya soma rage kayan jikinsa, Cak ya dakata da abinda yake yana duban saman gadon yana tuna abubuwan da suka faru daren jiya. Murmushi ne yaji yana kufce masa, duk zafin kan da ya kwaso a waje sai yana jin kaman dai zafin kan yana yayewa a hankali, zuciyarsa tai masa wasai ba tareda yasan dalili ba. Ya kuma sakin murmushi yana d’an girgiza kansa kad’an, lokaci guda ya fad’a bathroom yayo wanka.

Ya fito yana goge sumarsa nan ya hangi takardan da yai mata rubutu gefen bedside. A hankali ya isa ya d’auki takardan yana dubawa. Wani abu ne yaji ya tsaya masa a k’irji a sanda ya soma karanta abinda ke cikin takardan.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*35*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Girgiza kai ya shiga yi yana furtawa a hankali “This is not happening.. No.. No.. Mai yarinyar nan ta aikata kuma yanzu.?” Cikin sauri yai jifa da takardan, a gurguji ya shirya cikin jallabiya ruwan toka kafin ya soma bincikata cikin gidan, babu ita babu alamunta hakan yasa ya nufo k’asa babu shiri. Patrick yana jin yanda Ogan nasa ke kiran sunansa cikin tsananin amo da gwab’in murya yasan mai aukuwa ya auku.

“Where.. is my wife.?!” Ya tambaya yana duban Patrick daketa faman rabe raben idanu yana girgiza kai.

“I ask you a question Patrick. Where is my wife.. Ina matata..?”

Patrick yaci gaba da girgiza kai gumi na k’eto masa “Sir.. Sir.. Ehm..”

Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Patrick, I’m at the edge of my patience.. Kar ka bari kaga other side d’ina.. Now you tell me. Where the hell is my Wife.?” Ya k’arashe idanunsa tar kan Patrick.

“I’m afraid she’s not here, Sir...”

Ya girgiza kai yace “What do you mean she’s not here..?”

Patrick yace “Ta aikeni na sayo mata magani na dawo na tadda bata nan,I.. I’m sorry Sir..”

Girgiza kai Mu’azzam keyi yana dubansa cikin tsananin tashin hankali “Aikinka ne sayo mata magani..? I thought I told you kar kaje ko Ina without informing me first.. What have you done now Patrick.?!”

Ya girgiza kai yana duban k’asa “Sir I tried calling you but I couldn’t reach you..”

Lumshe idanunsa Mu’azzam yai yana ambaton Allah. Bai San ta ina zai fara ba.. Baisan ta ina ta nufa ba.. Shin ta ina zai fara nemanta kafin ta fad’a cikin had’ari domin kuwa rayuwar tata na cikin had’ari ne.

Cikin sauri ya koma cikin gidan ya d’auko car keys d’insa da wayarsa. Ji yai sam bazai iya zama ba ba tareda yasan yanda take ba. Yasan bazai wuce tace zata fita ta nemi mahaifiyarta da ‘yanuwanta ba. Toh amma ta ina zata fara neman nasu.? What if taje Ta fad’a mugun hannu.? Yai saurin kauda tinanin yana fatan ta kasance lafiya a duk yanda take. A haka ya iso jikin motarsa ya bud’e zai shige amma Sai ya juyo yana duban Patrick “You stay here and don’t go anywhere.. Ban gama dakai ba..!” Daga haka ya shige motar Patrick na jinjina kansa dake kife. Lokaci guda ya isa gate ya bud’ewa Ubangidan nasa k’ofa.

Yana tafe a Mota yana kuma nanata sak’on da Ta ajiye masa cikin zuciyarta.. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furtawa a fili “Dear Stubborn head, please be safe..!”

Bai ida rufe baki ba wayar Assad ya shigo masa “A kasalce ya d’aga cikin rashin kuzari. Daga yanda Assad yaji muryarsa ya fahimci babu lafiya.

“Mu’azzam are you alright..?” Assad ya tambaya daga d’aya b’angaren.

“She has left..” Abinda kawai ya iya fad’iwa Assad kenan.

“Ta tafi kuma.? Wacece ta tafi..?” Assad ya tambaya.

“Who else Assad.? Wacece nake zaune tareda ita a gidan..” Ya basa amsa kai tsaye.

“Kana nufin Sadiya ta tafi..? Toh ina ta tafi..?” Assad ya tambaya daga d’aya b’angaren.

“Ta yaya zan sani Assad.. Ta bar gida bansan yanda taje ba.. Bansan yanda take ba..” Ya d’anyi fasali kafin ya k’arada “I don’t know what I’d do if something bad happens to her..”

Assad ya shafi fuskarsa yana mai jinjina lamarin “Don’t think like that.. Babu abinda zai faru Mu’azzam ka kwantar da hankalinka kaji.. Ka sanar dani yanda kake zan sameka.. And we’ll look for her together.. Just text me your location.”

Sauk’e deep breath Mu’azzam yai kafin yai parking gefen hanya yana mai turawa Assad location d’in. Lokaci guda ya kifa kansa saman steering wheel yana mai tuhumar kansa da alhakin ficewarta.. Da ace bai aikata mata abinda ya aikata a daren jiya ba maybe da bata tafi ba.. Idan wani abu ya sameta baijin zai tab’a yafewa kansa.. Ya lumshe gajiyayyun idanunsa yana nan gefen kwalta dan ji yai ma baida kuzarin tuk’a motar.

**

Mommy ta kasa ta tsare tace sam Safeenah bazata tafi gidan Mu’azzam ba sai anje Kotu an k’watar mata hakkinta tinda ita batasan zafin kanta ba sai soyayyar wann jarabban yaron maras mutunci.

Ana tsaka da wannan hatsaniyar Daddy ya shigo gidan.

Ya dubi Safeenah dake tsaye da trolley d’inta tana fad’in koma Mommy ta hana k’awayenta kaita gidanta ita zata kai kanta ehe. Dan a halin yanzu batada burin da ya wuce ta kori shegiyar can da Mu’azzam ya aje mata a gida ta kasance da mijinta.

Daddy ya kuma duban Mommy da Aunty Shemau dake tsaye gefe carko carko. Shemau tana ganin Daddy ya shigo ta shige ciki ta basu waje tana mai dialing layin mijinta, idanunta k’asa k’asa alamun zancen gidan D’anuwan nasa take sanar da mijinta Ta cikin waya.

Safeenah tana ganinsa ta fashe da kuka tana fad’in “Daddy dan Allah kace Mommy kar tayi k’arar Mu’azzam wllhi ina son mijina.. Daddy na gaji da tashin hankali I want peace with my husband.. Dan Allah Daddy kace kar tayi k’ararsa.”

Girgiza kai Daddy yai yana duban Mommy kafin ya dubi Safeenah yace “Ki kwantar da hankalinki babu wanda zaiyi k’arar mijinki..Kinji koh..”

Mommy Ta katse zancen da fad’in “Naji baza’ai k’aran Shelelenka ba amma Safeenah bazata tare gidan Mu’azzam ba sai an kirasa an zaunarsa a nan gamu ga shi ya sanar damu matsayin karuwar da ya aje gidan Safeenah tin kafin ta tare dan ni ban yarda aurenta yai ba ehe. Kai banda ma wannan yaron asirce zuciyarka yai har yaushe zaka kuma aminta dashi bayan yaje yayi aure ba tareda saninka ba duk wannan kulawa da kake basa wanda ko ‘ya’yan cikinka albarkaci.. Da ace ya d’aukeka Uba wllhi da ya sanar dakai.. Amma bai sanar dakai ba.. Ko Wanne uban ya tura ya amsar masa auren sai Allah..!”

Daddy ya jinjina kai yace “Kin gama..?”

Mommy batace komai sai jijjiga da take ci gaba da yi tana sakin huci.

Ya dubi Safeenah dake tsaye wajen tana goge hawayenta kafin yace “Safeenah zan kaiki gidan mijinki.. Amma zan hud’uba guda d’aya.. Kuma hud’ubar itace koda wasa kar ki d’auki halayyar wannan matar kije kina ma mijinki.. Kinji koh..”

Safeenah ta jinjina kai tana kuma goge fuskarta da mayafin dogon rigarta.

Mommy tai k’wafa tana kad’a kai “Eh yayi.. Dole ka mata hud’uba kar Ta d’auki irin halayyana.. Duk abubuwan arziki na alkhairi da nai a baya ba’a gani ba sai yanzu za’a sami bakin kasheni da shike na gama jinyar nakasasshiyar matarka ba..”
Chapter 66 · 0% Book details