← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 175

Sashe 137

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri Uncle Salman ya girgiza kai ‘A’a ai bani ne na kawo mata mai maganin ba.. Shemau ce da Hajara..’ Take zuciyarsa ta kuma basa amsa da fad’in ‘Harda kai Salman.. Hasalima sabida cimma burinka Shemau tai hakan.. Salman akan san duniya wacce ba komai bace face GIDAN ARO gidan da zaka tafi ka barta dik daren dad’ewa.. Gidan ba’a tabbata cikinta.. Ka zab’i ka salwantar da rayuwar Baiwar Allahn da bataji ba bata gani ba.. Bata aikata maka komai ba..’ Katse tinanin yai cikin sauri yana mai kuma ayyanawa cikin zuciyarsa ‘Dukiyar nawa ne ba nata bane da ‘ya’yanta.. Yayana shi ya saka hannu cewa ya mallaka min dukiyar.. Fad’a kawai nake akan abinda nawa ne tun usil.’ Da wann tunanin yasa kai zai fice Inne dake zaune parole ta bud’e murya ta kirasa.

Uncle Salman ya dawo da baya jiki duk a sanyaye.

Inne ta tsaresa da idanu sosai tana karantarsa dan ta kula a ‘yan kwanakin gaba d’aya Salman yayi sanyi kaman ba shi ba.. Taso ta tambayesa ko akwai abinda ke damunsa amma sai ta alak’anta shiga damuwar tasa da rabuwa da matarsa da yayi musamman duba da yanda rabuwar ta kasance.

Zamansa keda wuya wayar Daddy ya shigo masa..

Ya d’an d’aga wayar yana mai k’ok’arin zama, daga jin yanda suke gaisawa Uncle Salman ya fahimci Daddy ba k’alau yake ba.

Yai shiru yana saurara daga b’angaren Daddyn kafin ya girgiza kai kad’an yace “Gobe gobe.. Kasan ba jirgi gobe.”
Daga d’aya b’angaren Daddy yaci gaba da fad’in “Eh na sani Salman, Kai asubanci ka taho by road a goben idan Allah ya kaimu..”

Uncle Salman ya d’an dubi Inne da tin fara wayarsa ta tsaresa da idanu kafin yaci gaba da fad’in “Amma lafiya kake nemana urgently haka..?”

“Lafiya k’alau Salman, kawai dik tintsi ka taho a goben... Magana ne mai mahimmanci da ya shafi both companies.”

Jin ya ambaci Companies yasa Uncle Salman jinjina kai yace “Shikenan zanyi k’ok’ari na taho in sha Allah.” Daga haka sallama sukai Uncle Salman na duban Inne wanda tin fara wayarsa k’irjinta ke bugawa ba tareda tasan dalili ba.

“Lafiya Salman.. Meke faruwa ne.?” Ta tambaya tana duban Uncle Salman.

D’an girgiza kai yai kad’an kafin yace “Marwan ne ya kirani cewa lallai lallai yana son ganina gobe a Abuja.”

Inne ta tsaresa da idanu kafin tace “Gobe gobe kaman yak’i.. Abuja fah ba nan kusa ba.”

Uncle Salman ya jinjina kai yace “Nima nace masa babu jirgin Abuja gobe amma yace lallai lallai na taho koda a mota ne..”

Inne ta muskuta kad’an tace “Ikon Allah.. Toh amma Wai lafiya..?”

“Eh toh yace min dai lafiya lou, magana ce akan kamfanoninmu.. amma jikina na bani kaman akwai abinda bai sanar dani ba..”

Inne ta jinjina kai kad’an tace “Ni tinda Marwan ya taho garin nan ya kwana biyu sam ban gane masa ba, amma na alak’anta hakan da jikin Nuratu da ya gani.. Toh amma naga jikin Nuratu da kyaun gani balle ace hakan ne.. Kasan D’anuwanka Marwan fah da zurfin ciki, dik cikin yarana shine ke iya Had’iye damuwa dik girmanta kaga kaman babu abinda ke damunsa.. Amma a kwanakin nan ko waya mukai zakaji haka daga Muryarsa.. Gaskiya Marwan ba lafiya yake ba.. Babban dalili yasa yake nemanka bayan yau yau d’in nan ya koma gida..” Ta d’anyi fasali kafin tace “Salman, zamu tafi tare..”

Uncle Salman ya dubeta da mamaki Sai kuma yace “Inne ina ke Ina tafiya Abuja a mota..? Wahala kawai zaki sha.. Kiyi zamanki dan Allah ni zanje naji meke damunsa..”

Inne ta girgiza kai tace “Ni nace zanje, zan iya zuwa.. Ina son sanin halinda Marwan ke ciki.. Ka kira D’ahe tin yanzu ka sanar dashi zamuyi tafiya gobe idan Allah yakai rai.. In yaso a daren nan yajesa yasha mai..”

Uncle Salman yace “Inne jikin girma ne fah dake, zaman zai dameki..”

A d’an hasale tace “Yo a amalanke zanje da zaka wani ce zama zai damen.. Kai nifa ras nake ko ‘yan ciwon k’ashin nan na tsofi banayi.. Tafiya daga nan har legas sai naje maka a mota.. Dan haka zanje na gama magana, kawai kai abinda na umarceka.”

“Amma Inne..”

Bai Kai aya ba Ta katsesa da fad’in “Kai ban San wani magana.. Kai abinda nace..”

Ya jinjina kai a hankali yana mai amsawa da “Toh Inne.. Allah ya nufa ya kaimu lafiya.”

Inne ta amsa masa da “Ameen” kafin ya mik’e yana kiran layin D’ahe direban Inne.
**
Washe gari kaw asubanci sukai dan tun gari bai ida washewa ba suka fito, sallar asuba kawai sukai suka d’auko hanya. Yayinda aka baro Aunty Nuratu da Mama Hindu harma da Sauran ma’aikata.

Ajidde ma bata cimmasu ba ta tadda Sun tafi sanda ta iso gidan. Koda ta tambayi Inne Mama Hindu ke sanar da ita tafiya sukai can Abuja gidan D’an Inne na can d’in.

Ajidde ta fahimci gidansu Musaddiq Inne ta tafi. Ta dubi Mama Hindu tace “Zata gansa kenan..?”

Mama Hindu ta dubeta da mamaki tace “Shi wane..?”

“Kuran tashe..” Ta bata amsa kai tsaye.

Murmusawa Mama Hindu tai tana girgiza kai kad’an tace “Ajidde mai sunaye, daga Kuran tashe sai Dodanniya sai Kofur Zalimu.. Toh ni kuma wane suna kika saka min..”

Darawa tai kad’an tace “Ke ai ta amana ce Mama Hindu ke Mamata ce.” Ta k’arashe tana rungumar Mama Hindu.

Mama Hindu ma rungumeta tai tana fad’in “K’warai kuwa ke d’iyata ce Ajidde..” su duka biyun kyakkyawan murmushi ne saman fuskokinsu.

Aunty Nuratu dake fuskantar su idanunta akansu murmushi ta saki a hankali saidai basu kula da hakan ba sai hidiman had’a mata magani suke gwanin ban sha’awa.

**

A b’angaren Sadiya kaw rashin kiranta da baiyi ba a waya sosai ya kuma damunta, gashi gaba d’aya ranan bai Zo ba bai kuma kirata a waya ba, abin duk Sai ya dameta, haka ta tasa wayar gaba tana kallon ko zai kirata amma shiru bai kirata d’in ba. Sai ta d’aga wayar kaman zata kirasa sai kuma ta fasa. Ai shi ya kamata ya kirata yaji yaya jikinta ko bazai Zo ba amma bai kira ba, tasan yana can wajen Safeenah ne ita ya k’yaleta a nan bai ko waiwayeta ba, sai taji wani abu kaman kuka na zuwa mata.. Bayan dik abinda ya mata bai bata hak’uri ba saima k’arawa yake.. K’ila dai kawai ya daina sonta ne.. K’ila dai da gaske ita d’in matarsa ce ta mission. Take ta soma tuno had’uwarsu da yanda aurensu ya kasance, k’walla taji na kuma zuwa idonta.. Anya bata yaudari kanta ba da tai zaton zata samu miji irin Mu’azzam bayan batada tabbacin ko Mahaifinta ya yafe mata kafin ya bar duniya.. Anya bata rud’i kanta ba da tai zaton fairytale zai faru a duniyarta ba.. Rayuwa zai taho mata da sauk’i kaman dai a tatsuniyoyi irin labarun da ake baiwa yara dan suyi nishad’i.. A hankali taji bakinta da zuciyarta suna furta mata “Unfortunately, life is not a fairytale Sadiya..!” Ta lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka gangaro mata. Ta saka bayan hannunta tana goge hawayen da suka gangaro mata. Ta shiga tuna maganganun da Safeenah ta fad’a mata cewa ita d’in ba kowa bace face matar mission, da zaran Mu’azzam ya cimma mission d’insa zai sallameta.. Zata fice ta bar mata gidanta zata fice daga rayuwarsu itada Mu’azzam sabida a tsakaninsu itace bare kuma zata tabbatar hakan ya faru.. Taji kuka na zuwa mata gadan gadan, a hankali ta kwanta saman gadon tana danne kukanta. Lokaci guda tana addu’an Allah ya sassauta mata.

**

Basu suka iso garin ba sai yamma lis. Tin daga yanda sukaga ‘Yansanda sunyi ma gidan kawanya hankalin Inne ya soma tashi.

Fad’I take “Salman meke faruwa..? Mai nake gani haka.. ‘Yansanda ta ko ina..?!”

Uncle Salman wanda shima tsananin mamaki ne ya cikasa kasa furta komai yai sai duban ‘Yansandan da yake.

Motarsu na kutso kai cikin gidan suka hango Mu’azzam tsaye haraban gidan hannayensa sakale cikin aljihu yana duban motar tasu.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*70*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tsare motar yai da idanu yana duban Uncle Salman dake zaune frontseat yana tina tattaunawar su da Daddy Wanda Musaddiq yace ya sinkaya da kuma takardan yarjejeniya da Mommy tace sunyi shida mahaifinsa kafin ya bar duniya. A haka ya dinga tuna yanda tin tasowarsa basa jituwa da Uncle Salman, kaman dama tun can Uncle Salman baya wani k’aunarsa, shi zai iya cewa bayan gaisuwa babu abinda yake kuma had’asu sai lokacin da yaje masa da buk’atan karb’ar masa auren Sadiya da yai. A hankali yake jinjina kai cikin zuciyarsa yana fad’in sannu da zuwa Uncle. Zaka amsa min duka tambayoyi na kafin gari ya waye.. Yana tsaka da duban motar suka ida parking saidai hango mutum da yai zaune gidan baya ya sanyasa gyara tsayuwarsa sosai yana kuma duban bayan motar wanda ba kowa ya hango ciki ba face Inne.

A fili ya furta “Inne.?” Cikin zuciyarsa yaci gaba da fad’in toh mai ya kawo Inne.. Maiyasa ta taho.? Daidai lokaci suka soma fitowa daga motar securities d’in gidan dake zaune gefe dan an hutasarsu ‘Yansanda ke tsaron gidan, suka soma nufosu suna kwasan gaisuwa had’ida masu sannu da zuwa.

Har lokacin Mu’azzam na tsaye daga yanda yake yana dubansu.

Abin ya bawa Inne mamaki ganin Mu’azzam bai K’araso ba. A hankali take sauk’owa daga motar tana fad’in “Ikon Allah.. Shi kuma wancan mai D’amaran yana kallon mutane yana tsaye wajen kaman an dasa Sa..? Koda yake dama D’ansanda ne..”

Uncle Salman ya taho da niyyan taimaka mata saidai hakan yai dai dai da k’arasowar Mu’azzam murmushi saman fusakrsa.

Inne ta d’ago tana duban Mu’azzam d’in da tuni ya tallafo hannunta guda yana mai taimaka mata “Ai cewa nake daga can zaka tsaya kaita kallonmu kaman mai d’aukan hoto ba camera bazaka Zo ka tarbeni ba.”

Ya kuma murmusawa kad’an yana fad’in “Ni na isa ban taho na tarbeki ba Inne.. Sannu da zuwa Inne na.” Ya k’arashe hannunsa cikin nata.

Ta amsa masa tana karantarsa lokaci guda suna ci gaba da gaisawa, Mu’azzam yakai dubansa ga Uncle Salman wanda shima Mu’azzam d’in yake duba cikeda kulawa, saidai fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Chapter 137 · 0% Book details