← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 175

Sashe 145

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jaja ya d’ago kai yana murmusawa, a hankali murmushin nasa take juyewa zuwa dariya.. Yana dariya yana nuna Mu’azzam da yatsa ga jini dake fitowa daga hancinsa zuwa bakinsa “Don’t delude yourself Inspector.. And Stop acting like a Hero dan babu abinda zaka cimma a binciken da kake.. Sann bakada hujja da zaka ce inada connection da case d’in mutuwar ‘Yaruwarka.. Baka da shaida akaina. In fact baka kamani tareda Danger ba. I can still deny that in court.”

“Shut up you Bastard.!” Mu’azzam ya katsesa da fad’in haka yana mai buga teburin da ya raba tsakaninsu kafin yaci gaba da fad’in “Zaka amsa mun tambayoyi na and kasan menene Jaja.. Zaka k’are miserable life d’inka a gidan yari.. Bazan gajiya ba sai na tabbata ka tafi gidan Yari for the rest of your miserable life.”

Ya gyara zamansa kafin ya soma fad’in “Tell me how are you connected to Danger..?”

Chief ya murmusa yana duban Mu’azzam kafin ya tab’e baki yace “Ban sanshi ba, hasalima baka kamani tareda shi ba.. Dan haka bakada hujjan da zakace ni inada alak’a dashi..”

Ran Mu’azzam yakai k’ololuwa wajen b’aci ya yunk’ura zai kamo wuyan Chief amma sai hannunsa ya gauce, ya rintse idanunsa yana mai dafe wajen ciwo.

Chief ya murmusa kafin yace “If I were you da jinya ka tafi gida kai, ka samu hutu ko zaka samu energy na kamo masu aikata laifi..” Bai shiru ba Mu’azzam d’in ya damk’o wuyansa da hannu guda dudka zogi da ciwon nasa ke masa lokaci guda yake furta “And if I were you, I’d cooperate dan baka da wajen gudu Jaja.!” Ya k’arashe yana mai turasa da k’arfi.

Ya kuma daidaita zamansa kafin yace “What do you know about Black African Team.. Mai ka sani gameda wann Syndicate d’in.?” Ya d’an kuma gyara zamansa yana mai ci gaba da fad’in “Wanene Boss d’inku Ina nufin BAT..? The word BAT yana referring Syndicate d’in ne ko kuwa yana nufin Boss d’inku ne..?!”

Jaja ya kuma murmusawa kafin yace “Black African Team.. Wane Syndicate ne wann..? I don’t know what you are talking about Inspector.. Ya kake kauce hanya kai d’ayanka. Do I need to teach you how to question a suspect.?”

Mu’azzam zai kuma janyosa Assad ya dakatar dashi “K’yale shi for now..”

Ya kuma duban Jaja kafin yace “Jaja zaifi kyau ka bada had’in kai kaman yanda ka sani dole ka tafi gidan yari ko ka amsa cewa kanada alak’a da Danger ko baka amsa ba domin kuwa an kama dumu dumu kana drug business.. So da ka tsaya kana kare wani a banza gwara kai wani abu mai kyau for the first time na rayuwarka.. Kar ka bamu wahala kuma kaima kar ka bawa kanka wahala. Damuwar mu kawai shine la sanar damu yanda zamu sani Danger da kuma Boss d’inku.. Ina nufin wanda kuke ma aiki.. Dan tafiya jail kam kasan wajibi ne akanka Jaja. Gwara ma ka tona masu asiri ka samu abokan hira a jail.”

Yana ida fad’in haka yai umarni ma Sergeants dake tsaye gefe yace su tafi da Jaja Cell d’insa su kulleshi.

Jaja sai sakin huci yake yana aika masu mugun kallo.

**
A can gidan Daddy kuwa Al’amara sun kuma rikicewa, Mommy ta fayyace wa Inne komai cewa ‘Ya’yanta su suka kashe D’anuwansu Abubakar, d’aya dalilin matarsa d’aya kuma dalilin dukiyarsa da muk’aminsa.

Tin bayan da Mommy ta fad’iwa Inne haka take kwance sumammiya, Likita ya gama dubata ya d’aura mata drip a nan gida kafin ya juyo ya dubi Daddy da Uncle Salman da sukai tsaye carko carko.

Cikeda damuwa Daddy yace “Dr ya jikin mahaifiyata.?”

Dr ya d’an zame glasses d’in dake idanunsa kad’an yana kuma dubansu “Her heart is weak, zaifi kyau Ta samu hutu yanzun sann kar a kuma zuwa mata da wani zance mai girma koda na Farin ciki ne ko na akasin sa.. Zata d’an d’auki lokaci tana bacci yanzu.. Sann idan ta farka akwai pills d’in da za’a bata.. Zan rubuta maganin.”

A tare suke amsa masa suna jinjina kai ko wannensu na aika ma D’anuwansa wane irin kallo.

Daddy ya dubi Dr yace “I’ll walk you out.” Dr ya jinjina masa kai kafin sukai sallama da Uncle Salman.

Suna ficewa Uncle Salman ya k’arasa jikin gadon k’walla na ciko idanunsa, hannunsa guda ya d’aura saman na mahaifiyarsa ya d’an kifa kansa kad’an “Zan d’aukeki mu tafi bazan tsaya Marwan da iyalansa su kashe ki da bak’in ciki ba.”

Daidai lokaci Daddy ya shigo d’akin, Uncle Salman na aika masa mugun kallo. Lokaci guda yake jinjina kai yana furta “Maybe you planed all this.. Kai ka shirya haka Marwan tinda har ka kirani kace nazo da gaggawa.. Kawai ka fad’a ka shirya kashe mana mahaifiya ne.”

Daddy baice komai ba ya k’arasa saman kujera ya zauna, ya soma jinjina kai a hankali “Idan bincike ya tabbatar kanada saka hannu a tarwatsewar ahalinmu Salman.. Ka sani bazan tab’a yafe maka ba.. Kuma ka mance ni Marwan D’anuwanka ne..!” Ya k’arashe hawaye mai zafi na gangaro masa.

Uncle Salman ya jinjina kai kad’an shima yace “Likewise Marwan.. Idan har kanada hannu cikin mutuwan Hamma bazan tab’a yafe maka ba kuma ka mance kanada D’anuwa Salman.. Dan idan ban mance ba a ranan da mukai sa’insa da Hamma ranan da ya rubuta Bet Agreement Transaction kana cikin companyn.. Watak’ila kayi amfani da wann damar ne na sa’insan da mukai dashi ka hallak’a sa dan ka mallaki matarsa.!”

Daddy ya d’ago rinannun idanunsa masu zuban ruwa yana duban Uncle Salman lokaci guda yake girgiza kai kafin yace “Bazan tab’a kashe koda kiyashi ba ballantana D’anuwana mafi soyuwa a gareni.. Wanda mukai rabin k’uruciya har kawowa girma tare.. Kai ko kaima ban yarda zaka iya kashe D’anuwanmu ba Salman dukda kwad’ayinka na mallakan tarin abin duniya.. Kasan maiyasa..? Sabida nasan akwai Zuciyar musulunci a k’irjinka, kisan kai abu ne mai girma ballantana D’anuwanka.. Ko a da nafi bada zaton zafin maganganun da ka sanar da D’anuwanmu shine yasa ya yanki jiki ya fad’i cikin cold room har yai freezing hakan ya zama ajalinsa ba tareda an ankare ba.. Amma bayan abinda Hajara ta fad’i cewa kaida matarka kunyi amfani da ita da kishi irin na mace wajen cutar da Nuratu dan Ta mallaka maku takardan da ni banida masaniya akai.. Wann dalili yasa na fara shakku idan ba kashe Hamma akai ba. Dan babu yanda za’ai haka kawai ya rubuta yarjejeniya yace ya mallaka maka dukiyarsa Salman..!” Ya k’arashe yana mai tsare Uncle Salman d’in da idanu sosai.

Uncle Salman ya janye idanunsa da yake ta rarrabesu yana sakin huci a hankali.

Daddy ya jinjina kai kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Amma D’an marayan Zaki ya girma da sannu zai binciko gaskiyar komai.. Sann idan kashe mahaifinsa akai, zai farauto duk wanda yai wann kisan da izinin Allah.!”

Uncle Salman bai kuma cewa komai ba Sai kauda fuskarsa gefe da yai.

Musaddiq dake tsaye k’ofa yana dubansu, tafukan hannayensa ya saka ya shafi fuskarsa kafin ya fice cikin sassarfa kaman zai kifa k’asa yana jin zuciyarsa na masa tsnanin k’una. Kenan ahalinsu ahali ne mai cikeda ‘Yantadda. So yake ya fice daga gidan yasha iska saidai babu hali sabida house arrest da Mu’azzam yai masu gaba d’aya.. Shi ji yake bai k’aunan kasancewa cikin ahalin.. Bai k’aunan ganin kowa a ahalin.. Ya danne kansa tsakankanin gwiwoyinsa yana tuna Wai shine yaima Ikram fyad’e.. Take ya fashe da wane irin kuka yana kuma matse kansa, yaci gaba da dukan kansa yana fad’in “Man up Musaddiq.. Just do what’s right.! Do what’s right.” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

**
Nile University of Nigeria

Duk wainar da ake tuyawa gida Meema tana makaranta bata sani ba. Fushi take dasu gaba d’aya a cewarta tinda ta taho makaranta babu wanda ya tuntub’eta balle yaji ya take.

Zaune suke itada wasu k’awayenta a cafeteria. Guda d’ayar Ta dubi Meema tace “Wai ke Meems bazaki kira kiji ya suke ba.. Ko zaki bari sai weekend ne kije ki dubasu.”

Harara Meema ta aika mata kafin ta tab’e baki kad’an tace “Ai kuwa wllhi bazan kirasu ba idan dai su bazasu kira suji ya nake ba, kuma ko weekend d’inma bazanje ba.. Sai Sun nemeni da kansu.”

K’awayen suka dara kad’an suna sipping drinks d’insu daidai lokacin wayar Meema ta soma ruri.

D’ayar tace “Kinga kaman sunji k’orafinki gashi suna kira..”

Duban wayar dake aje saman table tai nan taga sunan Barr Ameer ya bayyana. Ta d’an kuma duban wayan da mamaki tana nanata sunan cikin ranta sai ta tuna lokaci da ta nemesa suka tattauna kan matsalar Safeenah cewa ya dubi girman Allah ya fice daga rayuwar Safeenah, Tabbas ya sanar da ita zataji feedback daga garesa.. Ita zama ta iya cewa har Ta mance da wann tattaunawar tasu sai yanzu da take ganin kiransa. Ta d’an tab’e bakinta kad’an kafin ta d’aga.

Daga d’aya b’angaren Barr Ameer yace “Barka da rana, Meema Gamji.. Zan iya samun kad’an daga cikin lokacin ki..?”

D’an rausayar da idanu tai kafin tace “Mai kake nema wajena..?”

Ya murmusa kad’an yace “Idan ban mance ba mun tab’a wani tattaunawa gameda ‘Yaruwarki Safeenah..”

Meema tace “And so.?”

Barr ya murmusa kad’an yace “I like the way you talk..” Ya fad’i cikin kashe murya kafin yaci gaba da fad’in “Anyways, amsa nazo na baki gameda buk’atar da kika Zo min da ita the other day.. Idan bazaki damu ba ina waje Ina jiranki.”

Meema ta d’an Ware ido tace “You mean kana cikin sch d’inmu..?”

Barr ya jinjin kai kaman tana dubansa yana sakin murmushi “You and I have pending business. Ta ina zan ganki.?”

Jinjina kai tai a hankali kafin tace “Alright bani minti kad’an.. Ka k’araso Cafeteria.” Tana ida fad’in haka ta datse kiran.

K’awayen nata da tin soma wayar suka tsareta da idanu d’ayar mai suna Fauzy tace “Aah Babes at las las zamuga Prince Charming d’in nan da kike mana rowarsa.”

Ta b’alla masu harara kafin tace “Kudai bakuda aikinyi.. Wann da mukai waya dashi sunansa Barr Ameer Dikko kuma ex d’in Yayata Safeenah ne, kuma yazo ne da magana akan Yayata bani ba.. So y’all should calm down.”
Chapter 145 · 0% Book details