Sashe 161
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy kam kasa motsawa yana jin kukan ma ya d’auke masa abubuwan da matarsa Ta aikata ne ko kuwa abinda mahaifiyarsu ta aikata ne zaima kuka... Wann wane irin tashin hankali ne wanda tinanin bazai iya lissafinsa ba..Shin wace irin duniya muke rayuwa ciki da son kai da abin duniya suka rufewa mutane ido har suke mance cewa gidan duniyar nan da suke zaune cikinta bafa matabbata bace GIDAN ARO ne da dik daren dad’ewa zaka tafi ka barta kuma kaje gidanka na gaskiya ka tarar da abinda ka shuka.. Ya Allah ka bamu ikon shuka alkhairi.. Ka kuma bamu ikon cin jarabawar da zaka jarabcemu da ita.. Ya Allah ka rabamu da mummunan k’addara..
Babu abinda Zuciyar Daddy ke iya ambaton sai sunan Allah.
Aunty Nuratu dake duk’e gaban Mommy hawaye kwance saman fuskarta, Ta d’ago tana dubanta “Kwantar dani da kikai tsawon shekaru bai d’aga mun hankali kaman abinda kika aikatawa Ikram da mijina ba.. Allah shi kad’ai zai miki hukunci Hajara.. Na barki dashi yayi ikonsa akanki Hajara.”
Mommy kuka yayinda har lokacin kan Mu’azzam ke kife.. Wai dama duk tsawon lokacin nan da ya kwashe yana bincike yana aikin D’ansanda ashe gasunk’umar ‘yartaddan tana nan cikin gidansu har yana kiranta da Mommy.. Lallai ya yarda wann azzalumar mata babu abinda bazata aikata ba domin cikar burinta.. Baijin akwai kotun da zai iya yanke hukuncin Hajara a duniyar nan. A shekarun aikinsa na D’ansanda yasha cin karo da criminal cases amma bai tab’a cin karo da ‘Yartadda irin Mommy ba. Harta ‘ya’yan cikinta ma bata barsu ba saida tai amfani dasu ta k’ulla masu sharri. Safeenah da Musaddiq. Ashe cire cikin Safeenah da tai ba komai bane cikin jerin abubuwan da Ta aikata.
Ji yai ko kallon yanda take baya son yi, bai tab’a kyamatan wani halitta irin Mommy ba. Ko shak’eta yai a wajen nan har Ta mutu bata biya abubuwan da ta aikata ba..
Ana a haka suka soma sinkayo murya daga k’ofa Sadiya tana k’ok’arin rik’o Umma take fad’in “Umma family meeting suke bai kamata mu shiga ba.. Ki bari har Mu’azzam d’in ya fito Sai ki tambayesa.”
Umma taci gaba da janye hannunta tana fad’in “A’a Sadiya.. Ki k’yaleni na tambayesa.. Bazan iya jira ba sai na tambayesa.” Ta k’arashe tana mai sako kai cikin parlorn Sadiya na biye da ita tanata k’ok’arin dakatar da Ita.
Gaba d’aya mutanen dake parlorn kallonsu ya dawo kansu.
Cak suka tsaya suma suna duban mutanen dake Parlorn yayinda idanun Umma suka sauk’a kan matar dake duk’e tsakiyar parlorn sanye da farar lafaya.
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*80*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali ta soma k’ok’arin mik’ewa tana duban matar wacce ke nufota hawaye na fitowa daga idanun matar. Wani haske mai kaman walk’iya taga ya gifta cikin k’wayar idanunta. Abubuwan da suka faru a wancan shekarun, rasa iyayensu.. Jinyar ‘Yaruwarta kwanciyarsu a asibiti har izuwa saidasu da mutumin da ya taimaka masu yai.. K’aran jiragen ruwa dake shawagi saman manya manyan tekuna take sinkayo cikin kunnuwarta.. Mutumin da ta mik’a masa ‘Yaruwarta tace ya kular mata da ita, bata hotonsa da kuma kamata da yantaddan suka kuma yi har izuwa jefata cikin jirgin ruwa da kuma tashin bomb da jirgin ruwan yai. Take take jin wasu memories d’in abinda suka faru a rayuwarta na baya suna Yawo a kwanyarta da k’wayar idanunta.
A haka Umman Sadiya ke K’arasowa itama hotunan abubuwan da suka faru sai gifta k’wayar idanunta suke.. Ta yaya zata mance wann fuskar.. Fuskar ‘Yaruwarta kuma Yayarta Halimatu wacce tai sadaukarwa da dama a sabida ita.. Hawaye sukaci gaba da gangaro mata yayinda su duka biyun suke duban juna, haka nan d’aukacin jama’an dake cikin parlorn idanunsu akansu ne harda Sadiya dake tsaye daga bayan parlorn.
Fuskokin juna suke duba hawaye naci gaba da gangaro masu, yayinda Aunty Nuratu takai hannunta dake rawa tana shafa fuskar Umman Sadiya a hankali tana kallon fuskar ya koma mata tamkar dai na k’aramar k’anwarta Aisha a lokacin da suke shekarun k’uruciya.. Kuka taci gaba da yi bata daina shafa fuskar nata ba yayinda Umma ma ke kuka tana duban ‘Yaruwar nata.
A hankali Umma ke d’ago hannunta, ta Ware tafin hannunta da coins d’in ke ciki.. Aunty Nuratu ta sauk’e idanunta tana duban coins d’in, kukanta ya k’aru itama.. Coins d’in da akai masu alama a sumarsa lokacinda Yantadda suka sacesu.
Cikin rawar murya Aunty Nuratu ke furta “Eassh...Easshaa...!” (Ita kad’ai ke ambatonta da wann sunan duk duniya).
Ai take Umma ta kuma bursting cikin kuka tana mai rungume ‘Yaruwarta “Didi.. Didi.. Deedeee..!” (Itama ta ambaceta da sunan da take kiranta) Kuka yaci k’arfinsu su duka biyun suna masu kuma k’ank’ame juna.
Gaba d’aya illahirin jama’a dake parlorn mamaki ne ya cikasu da ganin irin wann kayan al’ajabi da mamaki.. Babu kaman Sadiya da Mu’azzam wanda suke duban iyayen nasu cikin tsananin shock.. Mai hakan yake nufi.?
Wann dai Umman Sadiya yake gani rungume da mahaifiyarsa suna shek’an kuka.. Did they know each other from the past.? What exactly is happening.? Tambayar da zuciyarsa ke bijiromasa kenan.
Saurin juyowa yai yana duban bayan parlorn yanda Sadiya ke tsaye tana duban iyayen nasu cikin tsananin kad’uwa da mamaki. Ya kuma maidoda dubansa ga Mamynsa da Umman Sadiya wanda har lokacin rungume suke da juna tsakiyar parlorn suna kuka mai ban tausayi.
Kowa ya zuba ma Sarautar Allah idanu suna duban wann kayan al’ajabi, ciki harda Hajara dake duk’e wajen kaman mabaraciya.
Saida sukai kuka mai isarsu kafin Aunty Nuratu ta kuma kamo fuskar ‘Yaruwarta. Ta tallafo fuskar nata sosai da hannayenta duka biyu magana sukai cikin harshen yaren ‘Yan k’asarsu dan su kuma tabbatar ma juna sud’in ne. Murmushi mai gauraye da hawaye saman fuskokinsu suka kuma rungumar juna kaman zasu shige cikin jikin juna.
Suka d’ago suna duban mutanen parlorn da sukai masu k’ur yayinda Aunty Nuratu taci gaba da jinjina kai, hannunta rik’e cikin na Umman Sadiya take fad’in “‘Yaruwata ce.. ‘Yaruwata da muka rabu a lokacin da muka shigo k’asar nan.. ‘Yaruwata da na mik’ata amana hannun Ibrahim.. Ibrahim mutumin da ya mun alk’awarin rik’eta da amana.. Sann shine mutumin da Hajara Tasa aka kashe a sakamakon samun hotonsa da tai cikin takardan yarjejeniya.. Abubakar ya saka hotonsa ne cikin takardan domin dani da Abubakar duk bamusan mutumin ba, kawai munga hoton ne a tare dani sabida tunanina da ya shafe.. Abubakar Allah ya gafarta masu baki d’aya ya d’au alwashin nemo Ibrahim sabida tinanin da mukai na cewa Ibrahim zai iya zama D’anuwa a gareni.. Wann haruffa da ya rubuta jikin Yarjejeniyar ya rubutasu ne sabida kalaman dake jikin sisin kobon da muka kuma tsinta tattare dani..” Ta amshi coin d’in hannun Umman Sadiya tana nuna masu “Black African Team.. sune K’ungiya masu safaran mutane da suka sato mu daga k’asarmu wanda aka tarwatsa su tun a wancan zamanin.. Abinda yasa Abubakar ya rubuta BAT jikin takardan ba komai bane Sai dan Black African Team Wato sunan K’ungiyar shine zai zamto mabud’in sirrin sanin ko ni wacece da kuma yanda na fito..” Sai ta dasa aya ta juyo tana duban Umma dake ci gaba da hawaye “Hajara ta kashe Ibrahim..!” Ta furta cikin rawar murya.
Umma na hawaye take jinjina kai “Ibrahim ya rik’e amanarki Didi.. Ya kula dani da yaran da muka haifa tare dashi har izuwa lokacin da zai amsa kiran mahaliccinsa..” A tak’aice ta fad’i duk abinda ya faru aurensu da kuma yanda Sagir ya shigo rayuwarsu da yanda suka rasa mahaifin Sadiyar.
Aunty Nuratu na hawaye take duban Mommy dake duk’e wajen Al’ajabi bai saketa ba jin Wai ashe mutumin mijin k’anwar Nuratu ne.. Sann matar Mu’azzam da Ta tura Sagir ya aura bai aureta d’in ba Mu’azzam ya aureta ashe d’iyar k’anwar Nuratu ne.. Itakam bata K’ara ma Nuratu da ahalinta komai ba face kusanci.. Ashe Mu’azzam d’iyar ’yar uwar mahaifiyarsa kenan ya aura.. Wato dik yanda kaso ka rufe abu idan Allah yaso abun ya bayyana Sai ya bayyana.. Da ace tasan wann yarinya tanada jinin Nuratu tattare da Ita da ta umarci Danger ya kasheta a lokacin da ya saceta. Tinaninta ne ya Katse sanda Umman Sadiya ta duk’a gabanta tana tambayarta “Baiwar Allah Maiyasa kika kashe mun miji.. Maiyasa kika rabani da Ibrahim.. Maiyasa kika zab’i ki turo Sagir cikin rayuwarmu..? Maiyasa kika zab’i ki jefamu cikin tashin hankali wanda bamu santa a baya ba tun bayan aurena da Ibrahim..!” Kuka yaci k’arfinta ta shiga jijjiga Mommy dake duk’e wajen kanta a k’asa. “kin rabani da masoyina Ibrahim wanda bai tab’a gajiyawa da duk abubuwan da nai masa a rayuwa ba.. Ki amsa min mai muka maki da tsanani..!” Kuka yaci k’arfinta yayinda Aunty Nuratu Ta k’araso ta d’agata, ta rungumeta Umma nayin kukan cikin jikinta.
Tsananin Shock ya saka Sadiya silalewa a wajen hawaye naci gaba da gangaro mata. Ganin abin take kaman almara kaman a mafarki ne ba zahiri ba, Wai Mamy Mamyn Mu’azzam dai itace wann ‘Yaruwar Ummanta Haleematu da Umman ta basu labari.. Ikon Allah abun al’ajabi bai tab’a k’arewa a duniyar nan.. Ta shiga tuna yanda had’uwarsu ya kasance da Mr Inspector da irin auren da sukai.. Shin waye zai tab’a kawowa Su d’in sunada wata alak’a da dangantaka ta jini..? Kuka yaci k’arfinta idanunta a lumshe tana jin wani abu mai kama da rauni can k’asar zuciyarta.
Ji tai an dafata, ta d’ago tana dubansa shid’inma yau idanunsa duk a kod’e suke dukda jarumta irin tasa.
“Come with me..” Ya furta yana k’ok’arin d’agota. Babu musu Ta mik’e jiki a matuk’ar sanyaye Mu’azzam na janye da ita. Juyowa take kumayi tana duban Mamyn Mu’azzam da kuma Ummanta wanda suka tabbata ‘Yanuwan juna.. Ita har sai ta mance ma cikin jinya tasan Mamy bata San yaushe ta mik’e kan k’afafunta ba. A haka suka nufo wani d’an dogon hanya da farar k’ofar glass mai zugewa ta raba tsakani da parlorn Daddy wanda zai fitar da kai wani k’aramin parlor daga nan babban parlorn Daddyn.