← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 175

Sashe 85

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Marker ya kuma d’auka ya zana allon ya sake rubuta abinda ya goge. Maleeka tai masa K’uri tana dubansa, Toh ko bai yarda da sakamon gwajin bane.? Kodai shakku da kokonto ya fara..? Bata kai ga nemo amsar ba ta sinkayo muryar Yusuf yana fad’in “Sir menene B.A.T yake nufi if I may ask..?”

Mu’azzam na fuskantar allon yana karantar hotunan mutanen dake mak’ale jiki yake fad’i da Yusuf “Soon enough zamu gano wanene B.A.T.. But for now it’s classified..” Ya k’arashe yana mai juyowa had’ida tsaresu da idanu.

Yusuf ya d’anyi gyaran murya yace “Sir, is there any assignment da zaka bamu akan B.A.T..?”

Ya tsare Yusuf da idanu yana karantarsa kafin yace “For now akwai certain people a cikin Department d’in nan who are messing with our case.. And we need to find those people and make them pay..” Yana maganar yana duban Maleeka da tuni zuciyarta kaman bai wajen, kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin tsoro.

Mu’azzam ya tako zuwa gabanta idanunsa tar akanta “You will be the one to take this part..” Ya fad’i yana dubanta.

Saida ta d’an firgita kafin ta d’ago tana dubansa “Sir..?”

Mu’azzam ya d’an gyara tsayuwarsa kafin yace “Are you alright..?”

Saurin saita kanta tai kafin ta jinjina masa kai “I’m good, sir.”

Ya jinjina kai yana duban hannunta mai ciwo da aka harba “How is your wound.?”

Ta k’ak’aro murmushi cikeda jin dad’in ya tambayi ciwonta. Lokaci guda take duban hannun kafin tace “Na warke Sir, and I’m ready for another assignment..”

Ya jinjina kai kafin yace “Kinji abinda nace kenan..?”

Tai saurin dubansa sai kuma ta dubi Yusuf dake tsaye gefe yai Folding hannayensa yana dubansu. Saurin girgiza kai tai kafin tace “Pardon me sir, did you say something..?”

“About B.A.T..” Ya fad’i yana dubanta wanda ya kuma sanyata razana.

“Na zaci kace it’s classified, sir.” Ta fad’i a d’an daburce.

“I’ve changed my mind.. B.A.T is someone in our Department who is working hand in hand da criminals d’in da muke nema.. B.A.T is Danger’s Spy a cikin CID.. And If we want to catch Danger once and for all we must catch B.AT first dan shine zai leading namu to Danger..” Ya d’an soma takawa kad’an yana zagaye room d’in kafin ya tsaya jikin wani table da Maleeka ke tsaye gefe. Zuciyarta sai tsinkewa yake.. Lokaci guda Mu’azzam ke dubanta kafin yace “You will be the one to carry out this assignment.. ki nemo mana wanene B.A.T a cikin CID.” Daga haka d’aukan folder d’in dake wajen yai kafin ya fice daga office d’in.

Maleeka Ta fuzar da fuci tana duban Yusuf “Goddamn binciken cikin gida..? Ta ina zan fara.. Wa zan fara suspecting..? How am I going to carry out this assignment Yusuf..?” Ta k’arashe tana fuzar da fuci.

Yusuf ya d’an girgiza kai yana murmushi kafin yace “Tactics kawai zakiyi amfani da ki zak’ulo mana mai cin amanan K’asa da Al’umman cikinta.. Dan duk jami’in tsaron dake huld’a da ‘Yantadda maciyi amanan K’asa ne da Al’ummarta..” Yusuf ma ficewa yai ya barta nan tsaye a wajen gumi na tsartsafo mata.

Maleeka ta fuzar da fuci tana d’aura hannayenta saman table ko shakka babu ta fahimci Mu’azzam so yake ya kamata shiyasa kawai ya bata wann aikin.. Dan idan kana son kama mutum sai ka saka shi ya kamo kansa da kansa.. Yanzu mai zatayi..? Dole ta nemi taimakon Chief Dan idan ba haka ba tayi imani Mu’azzam Sai ya fahimci ita ce take masu zagon k’asa.. Da wann tunanin ta fice daga offishin tana sakin huci duk a dame take.

Kai tsaye Office d’in Chief Ta nufa tana yarfe gumi.

Chief ya tsareta da idanu yana girgiza kai alamun meke tafe da ita.

Fuzar da wani hucin ta kuma yi kafin tace “Ya fara zargina Chief..”

Chief ya girgiza kai yace “Waye kuma ya fara zargin ki..?”

“Waye kuwa idan ba Mu’azzam Gamji ba.. Can you imagine yayi assigning d’ina cikin team d’inmu na nemo masa wanene mai mana zagon k’asa a entire CID.. Idan ba zargina ya soma ba bazai tab’a assigning d’ina ba..” Ta k’arashe tana kuma shafe goshinta.

Chief ya murmusa kafin yace “Then give him what he’s asking for.. Ki kai masa mai yi maku zagon k’asan..”

Maleeka ta juyo tana dubansa shaye da mamaki kafin tace “Did you hear yourself..? Ni ce zan kai masa kaina ko kuma kai ne zan kai masa a matsayin wanda yake masa zagon k’asa.. Sanin kanka ne Chief binciken cikin gida yafi komai wahala a aikinmu..”

Chief ya murmusa kafin yace “Ku duka yara ne a aikin.. Baku San yanda al’amara suke gudana a wajenmu ba.. Especially Inspector Gamji.. Yaro mai k’waza mai kuma so ya kawo sauyi a al’amran tsaro na k’asar nan.. Saidai kash da irin wann k’wazon nasa ina mai tabbatar miki baza’a barsa yaje ko Ina ba.. Ko ni Jaja banyi eliminating nasa ba akwai manyan k’wari a sama da zasu shafe shi musamman idan suka lura zai kawo ma business d’insu cikas.. Su Waye ‘Yantaddan Maleeka..? Suna nan a cikin mu kuma ana dama hark’an mulki da tsaro dasu.. Kawo gyara ba abu bane mai sauk’i a k’asa irin namu saidai talaka yayita add’ua yana neman d’auki a wajen Allah dan shine kawai zai iya saita al’amran k’asar nan..”

Maleeka ta fuzar da fuci tace “Ni duk ba wanna ba Chief.. Ya zanyi da Inspector Gamji..?”

Chief ya murmusa ya matso yana shafan fuskarta kafin yace “Abu ne mai sauk’i.. Idan ya gwada yana son kamaki ke kuma sai ki tura makusancinsa cikin ramin.. Abinda nake nufi wannan shine perfect opportunity naki da zaki gwara kansa da abokinsa..”

Maleeka tai shiru tana sauraron Chief kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba Sir..”

Chief ya kuma murmusawa kafin ya saka makulli ya rufe ofishinsa ya janyo Maleeka yana fad’in barin na fahimtar dake.

Sai bayan tsawon d’an lokaci kafin Maleeka ta fito daga ofishin Chief tana kintsa kanta.

Mu’azzam da fitowarsa kenan daga wani dept d’in nan ya hangi Maleeka ta fito daga Office d’in Chief.. Sannan Ta fito dik a birkice sai waige waige take tana gyara zaman rigarta.

Jinjina kai yai a hankali kafin ya furta “Muje zuwa.. Sannu a hankali zamu kamaku..” Daga haka Sa kai yai ya fice daga ofishin gaba d’aya.

**

FUFORE

Yau ce Rana ta farko da ta soma shiga d’akin Inne, Inne ta aiketa ta d’auko mata k’aramar jakarta dake gefen bedside zasu fita zata raka Innen gaisuwan haihuwa jikar k’awarta ta haihu a cikin gari.. Nan Ajidde ta tsaya tana duban tsarin d’akin baki hangame tana fad’in “Kaga d’aki saikace ba na tsohuwa ba.. Masu shi dai suna abinda suka so.. An gaisheka d’aki kaci kud’in gidan gona gaskiya..” D’aga kan da zatai Ta hangi k’atoton hoto saman gadon.. Inne ce zaune a tsakiya sai Samaruka guda biyu Sun tsaya gefe da gefe sun sakata a tsakiya dukkansu sun dafa Innen murmushi saman fuskokinsu.

Ta gane d’ayan Mu’azzam ne wanda tasan jikan Inne ne saiko d’ayan da ko a mafarki bazatai kuskuren mance kamanninsa ba, Kuran tashe nata ne.. Toh ya akai sukai hoto irin haka kaman wasu ahali, a iyaka saninta Kuran tashe yace mata shi abokin jikan gidan ne.. Toh ma saida taga sunyi hoto haka taga kamanninsu ya fito.. Ikon Allah toh kodai ‘yanuwa ne..?

Bata kaiga samo amsar ba Mama Hinde ta shigo tana fad’in “Wai an aikeki Ajidde kaman an aiki Bawa garinsu.. Inne nata jiranki zaku fita..” Mama Hindu ta girgiza kai kurum ganin yanda Ajidde ta kafe tana kallon hoto..

“Ke Ajidde Wai bakiji bane..?”

Sai sannan Ajidde ta juyo tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta soma nuna mata hoton ba tareda tace komai ba..”

Girgiza kai Mama Hindu tai tace “Toh Sarkin shiririta wanene bak’o cikinsu a wajenki. Inne ce baki sani ba ko kuwa Mu’azzam da Musaddiq ne baki sani ba..?”

“Mana Hindu kika ce menene sunan wancan dake tsaye daga b’angaren hagu..?”

Mama Hindu Ta girgiza kai tace “Wai duk zuwanki gidan nan baki sansa ba.. Kwanakin baya ya koma can Abuja gidan Babansa amma ya jima a nan ai shi Musaddiq d’in..”

Ajidde tace “Kika ce sunansa Musaddiq.. Toh ai shine Kuran tashe.. Na rantse da Allah shine Kuran tashe.. Wllhi bazan tab’a mance kamanninsa ba.. Dama jikan Inne ne..?”

Mama Hindu ta girgiza kai tace “Adana tambayoyinki har ku dawo Inne na jiranki yanzu tintini Malam Sadi ya tada mota ke ake jira..” Ta k’arashe tana janyo Ajidden daketa faman waigowa tana kuma duban hoton Musaddiq daketa sakin murmushi. Mamaki fal Zuciyar Ajidde Wai jikan gidan ne.. Shine yace mata shi ba d’an gidan bane babu abinda ya had’asu Sai abota da yake da d’an gidan.. Wato k’arya ya mata kenan.. Toh Maiyasa ya mata k’arya.. Maiyasa ya b’oye mata asalinsa.. Duk sai taji babu dad’i.. Jikinta gaba d’aya sai taji kaman an zare mata laka.. Duk da wauta da shahshashanci irin nata sosai taji zafin abinda Kuran tashe yai mata na b’oye mata kansa da yai, sannan tana son sanin Maiyasa ya mata hakan.

Ranan haka Ajidde har Ta koma gida tunanin da take kenan b’oye mata kansa da Musaddiq yai.. Sunansa kuwa ranan kaman biya karatu haka taita nanatawa.. Yanzu Kyallu batada lokacinta sosai dan tana samun majinyata da take kwantar dasu a nan gidanta akai akai.. Idan ta baiwa Ajidde maganin Gidan Gona bata kuma bi takanta.. Hakan sai yafi ma Ajidde dad’i da bata yini a gidan balle taga yanda ake shirka ma Ubangiji da sunan magani. Ko safiyan Washe gari ma da zata fice taga wata mata an kawota bata cikin hayyacinta Kyallu tace a kawo Bak’in zakara da budurwa Baru a masu barbara sannan aka buga kan bak’in zakaran da dutse wanda saida ya mutu jini ya soma zuba Kyallu tace Jinin za’a baiwa matar sannan a shafe jikinta da sauran shine maganin ciwonta..

Ajidde Ta girgiza kai kurum kafin ta fice ta nufi gidan Malama Hafsah.

Daga yanda Malama ta ganta Jiki a sanyaye ta fahimci wani abu na damunta.

Malama ta tambayeta meke faruwa.?
Chapter 85 · 0% Book details