← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 175

Sashe 31

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya na kwance saman gado ta kasa cin komai har yamma, banda aikin kuka bata komai, harta k’annenta su Ashiru da basu wani fahimci wainar da ake toyawa ba saida suka taru suna bata hak’uri Ta tashi ta saka wani abu a cikinta.. A ‘yan kwanakin tun bayan fasa aurenta da Sagir idan kaga Sady Pretty sai ta baka tausayi musamman idan ka santa a lokutan baya lokacin da tashen kyaunta. Gaba d’aya Ta rame tayi duhu kaman ba Sady ba..

A haka Umma ta shigo ta taddata da k’annen nata sai aikin lallashinta suke. Umma ta shafa kansu tace su fita su basu waje. Babu musu Asiru ya ja hannun k’anins Habeeb suka fice. Suma yaran duk sun koma abun tausayi..

A hankali Umma ta zauna gefen kan Sadiya tana shafa kwantattun sumarta wanda suke a kwance luf ga sulb’i ga tsawo.

“Sadiya ki tashi kici wani abu kinji, zama haka bazai taimaka ba.. Ki tashi dan Allah idan nima ba so kike nak’I ci ba..” Umma tace tana kuma gyara mata sumar nata wanda ke zube saman pillown da take kwance bisa.

Bud’e baki tai da niyyar magana amma sai taji kuka na zuwa mata, da k’yar Ta iya furta “Sabeera gaskiya Ta fad’i Umma.. Nid’in tamkar macijiya ce.. An yarda dani nayi yaudara... An aminta dani naci amana.. Umma I’m nothing but a betrayal.. Tell me please Umma, am I really a bad person.?!” Tai maganar tana mai mik’ewa zaune had’ida fuskantar mahaifiyar tata.

Hannayenta Umma Ta rik’e tana mai share mata hawayenta “You are not a bad person Sadiya.. You are only human.. Dukkanmu muna kuskure, mafiya kyawun masu kuskure a cikinmu Sune wad’anda idan sun gane kuskurensu sai su tuba su gyara.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Inada tabbacin Sabeera will come to understand cewa baki ci amanan ta ba.. Da sannu lamura zasu daidaita kinji koh..” Ta k’arashe tana mai janyo Sadiyar cikin jikinta.
Sadiya bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin jikin mahaifiyarta tana mai lumshe gajiyayyun idanunta.
**

Yamma lis ana kiraye kirayen sallar magrib suka shigo gidan gonar, ko waya basuyi ba balle suce aje airport a d’aukesu dan dama tafiyar ‘yar solo ce. Motar haya suka yo shata suka taho garin. Meema sai mita take tana fad’in yau sai tayi ciwon jiki dan ita Allah ya gani bata tab’a shiga motar haya ba sai yau.. Safeenah tai gajeren tsaki tace “Toh wai da kika damen da mita nid’in na saba shiga ne.. Ni bama wannan ba Allah yasa muna shiga Inne tace duk mu tattara koma gobe gobe.. I’m sure zata goyi bayana wann karon.”

Meema ta danna mata harara cikeda takaici tace “Malama returning flight zuwa Abuja sai an shiga next week.. Zamuyi weekend mu kwashe kwanaki kawai kiyi shirin zaman garin nan..” Tai tsuka tana kuma jan suitcase d’inta “Ni wllhi Adda Feenah kin gama dani dan banyi niyyan zuwa ba ga jaraban wannan masifaffiyar tsohuwar na jiranmu..”

Feenah tabi bayanta cikin sauri tana kiran sunanta tana jan nata jakan da k’yar gashi babu kowa da alama ma’aikatan dik sun tafi sallah da alama. Safeenah Ta kuma sakin tsuka tana jan jakan.

A daidai mashigar da zai sadaka da k’ofar babban parlorn Ajidde dake rik’eda bak’in ruwa mai kaman black ink cikin kwano sukai karo itada Safeenah wacce shigowarta kenan tana kokawa da Jakarta, ai kuwa bak’in ruwan nan bai shek’e ko Ina ba Sai fuskar Safeenah da yake fari tas Wanda lokaci guda bak’in ruwan nan ya maidasa bak’ik’irin kaman tayi wanka da ruwan da aka wanke bayan tukunya..

Meema dake gefe baki sake take duban fuskar Safeenah da yai bak’ik’irin yayinda Ajidde ma ta saki baki da hanci rik’e da kwanon tana duban matar data wanke mata fuska da maganin Kyallu.

“Wow.! What a nice welcome gift you’ve received Addah Feenah.” Meema tace tana mai tintsirewa da dariya.

Ajidde kaw tuni Ta arce a guje tana fad’in “Kai wllhi Allah bazanyi dariya ni kad’ai ba.. Kuran tashe dole yaga wannan.”

Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsawa da tsananin mamaki take duban yarinyar kafin ta maidoda dubanta ga Meema da ke ta faman k’yalk’yala dariya harda ciro waya tana fad’in Ta tsaya tai mata video..

A daidai exit d’in da sukai zasu had’u ta taddasa, da alaman isowar Ta yake jira..
Musaddiq na hangota ya kuma duba agogon dake d’aure hannunsa yana girgiza kai “Ya na ganki haka.. Ina maganin..?”

Ajidde bata amsa sa ba sai dariya da take har tana zama a k’asa.

Takaici ya cika Musaddiq jin har an kusa sallamewa a masallaci “Ke Crazy Dove ki tashi kimin magana kafin su fito daga masallaci su samemu a nan.. Ina maganin yake..?”

Ta kuma tintsirewa da dariya tana fad’in “Ka tab’a ganin dodanniya..?”

Mu Sadiq ya girgiza kai yace “Dodanniya kuma..”

Ajidde ta mik’e tana fad’in “Kai sauri ka biyoni kar ta b’ace..”

Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, sai kuma ya girgiza kai yana furta “Crazy Dove, you truly are crazy..” Lokaci guda ya take mata baya.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*19*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin tsananin b’acin rai Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsa ‘yar yatsar k’afarta take duban Meema da har lokacin dariya take tana mata video sa waya “Meema you know I’m a very sensitive person, and I don’t take things lightly...Don’t make me take it out on you..!” Tai maganar tana bud’e hannayenta cikin tsananin b’acin rai da huci.

Daidai lokacin Ajidde ta k’araso hannu biyu aka tana dariya. Cikin tsananin mamaki Safeenah Ta karkato tana duban mahaukaciyar yarinyar wacce tai mata wannan aika aikan sannan bama tasan ta aikata ba balle Tai tinanin bada hak’uri waima dariyarta take tana duban fuskar tata..

Wani irin wawan birki Musaddiq yai ganin wacce Ajidde ta wanke da ruwan maganin nan ba kowa bace face Safeenah, dikda bai ganeta daga fari ba har saida yaji tana fad’in Meema ta damk’o mata shegiyar mai aikin nan taci uwarta ta koya mata manners.

Baki sake Musaddiq yake duban Safeenah da sam baisan da zuwansu ba yana duban yanda Ajidde ke dariya kaman sabuwar Kamu.

Meema ta yatsina fuska tace “Ni ce zan tab’a jikin wnn mahaukaciyar Adda Feenah.. Chabd’i God forbid.! You know I’ve a very sensitive skin. I might easily catch infection.. Kawai ki rungumi k’addara kizo muje ki wanke.

Ana haka Hindu ta k’araso jin hayaniya daga parlorn.

Musaddiq ya dafe goshinsa kad’an yana jinjina rashin hankalin Ajidde wacce taima Meema gwalo tana rataye jakarta tana fad’in “Ni kuma sai na tsaya ki kamani. Tab lallai kina ruwa.. Ko banza naci dariya wllhi.. Allah bamu Alheri dodanniya.” Tana ida fad’in haka Ta kuma arcowa a guje tana ma Meema gwalo.

Daga Meema har Safeenah da tsananin mamaki suka bita da kallo yanzu kam sun gama yarda Tanada tab’in hankali.

Saida tazo daidai yanda Musaddiq ke lab’e ya janyo jakanta da k’arfi ta dawo da baya.

Ihu ta saki tana fad’in “Dan Allah Dodanniya kiyi hak’uri.” Dik a zatonta Safeenah ce ta biyota.

“Ke Crazy Dove.!” Musaddiq ya fad’i cikin daka tsawa.

Jin Musaddiq ne ya sanyata sauk’e ajiyan zuciya ta bud’e idanu tana fad’in “Wllhi kallo ya shige ka.. Kaga..”

Katseta yai da fad’in “Waike lafiyarki kuwa.. Kinsan abinda kika aikata kuwa.. Yanzu idan ‘yanmatan nan suka biyoki suka lakad’a miki duka waye zai ceceki..?”

Ta sakar masa murmushi tana kashe masa idanu guda, abindake mugun basa dariya idan tai. Lokaci guda tace “Toh ba gaka nan ba.. Na San zaka tsare min kaman yanda ka tsare min sanda mugun abokin nan Naka mai bindiga ya biyoni wanda baya dariyar nan.. Mutum kullum kaman shed’an kasan d’azu ma na gansa ya fito wancan k’ofar fuskar nan babu annuri..”

Ya tsareta da idanu kafin yana mamakin halin Ajidde, lokaci guda ya girgiza kai yace “Watau sabida ina nan shine kike taro masifa ki gudu kice zan tsare miki koh.. Toh randa banzo aiki ba fah..”

“Zan jiraka har kazo ai..” Ta bashi amsa kai tsaye kayanta.

D’an girgiza kai yai yace “Kina jina idan baki daina shiga abinda babu ruwanki ba wataran zaki taro abinda yafi k’arfinmu daga ni har ke..” Yai maganar cikin yanayin b’acin rai.

Ta d’an dubesa da kulawa wannan karon “Kayi fushi ne..?”

“Banyi ba.. Inaso kimin alk’awari gobe zaki bama matar nan da kika b’ata mata fuska hak’uri.”

Tsuke fuska tai ba tareda tace komai ba.

Musaddiq ya tsareta da idanu babu walwala wann karon.

“Tau naji ince Dodanniya.. Anji anji.. Anji d’in.. Za’a bata hak’urin.. Hankalinka ya kwanta.”

Tsareta da idanu yai yana duban yanda take maganar tana duban wani b’angare. Harga Allah mugun nishad’i take saka sa, shirmenta da shiriritar ta mugun nishad’i yake saka Sa.

Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro kud’ad’en ya mik’a mata ”Oya take this..”

Bata karb’a ba sai dubansa da take a kaikaice alamun tana fushi dashi yace sai ta bawa Dodanniyar cen hak’uri wanda bama tasan ‘yanuwansa bane.

“Karb’a mana ya kuma fad’i yana dubanta.. Ko sai na baki hak’uri nima..?”

Wannan karon murmushi tai tana wani kad’a kai dan sosai take jin dad’in yanda yake damuwa da damuwarta abu ne da ba’a tab’a nuna mata ba a rayuwarta sai akansa tasan hakan.

Ta girgiza masa kai tace “Ai yau Inna Kyallu batace na sato mata wani abu ba, wanda ka bani jiya kace na bata kuma na bata..”

Tsayuwarsa ya gyara yace “Ke baki gane ba, Idan kika kai mata a jere kwana biyu a matsayin sato mata kike zata rage duk wasu abubuwan da take miki tinda imaninta kenan..”

Ajidde ta tsaresa da idanu tana dubansa “Toh randa bakadashi fah..?”

“Kar ki damu badai ina aiki ba.. Zan tara mana na baki ki kai mata..”

Ta murmusa kad’an tana mai rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shima kafeta da idanu yai yana mai sakin murmushin. Harga Allah Ajidde na d’aya daga cikin dalilin da yasa garin ke masa dad’i baya fatan abinda zaisa ya daina ganinta a gidan gonar.. Zaiyi dik yanda zai ya taimaka mata Ta daina mummunan d’abi’a na sata da Innarta ke koya mata koda hakan na nufin yayi aikin k’arfi ne ya samu Kud’i ya bata Ta fanshi kanta wajen Kyallu.

“Maza Jeki kar dare yayi.” Ya fad’i yana dubanta.
Chapter 31 · 0% Book details