← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 175

Sashe 51

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak ta tsaya sanda ta kula ga dukkan alamu babu kowa cikin gidan.. Babu Umma sannan babu Ashir da Habeeb.

Cikin rarrabewar murya tana Ganin gidan na juya mata take fad’in “Umm..Umma.. Umm.. Habeeb.. Ashir... Ina kuke.. Umma wasan b’oyo kuke mun.. Dan Allah ku fito gani nan na dawo gareku.. Babu abinda zai sake rabamu.. Umma dan Allah ki amsa mun.. Kinji na rok’eki..”

Kasa jura Mu’azzam yai ya shafi goshinsa a hankali kafin ya shiga janyo hannunta yana fad’in “Let’s go, we are going home now..!” Ya fad’i a tsare kaman yanda ya saba.

Bama tasan mai ke faruwa ba.. Bata gane mai take ciki ba, batama lura da Mu’azzam dake janyota ba har saida suka fito waje.. Sannan ne ta soma tuna wai babu kowa cikin gidansu. Babu mahaifiyarta sannan babu k’annenta guda biyu... D’agowa tai tana duban Mu’azzam wanda zata iya cewa yau d’in Ta hango tsananin damuwa cikin tsimammen fuskar nan tasa..

Wani irin fincika tai daga rik’on da yai mata, ta soma jada baya ta nufi gidansu tana fad’in “No.. I’m not going anywhere with you.. Ina Mahaifiyata da ‘Yanuwana..? Tell me.. Ina suke..?!” Ta k’arashe cikin tsananin tashin hankali jikinta na wani irin rawa..

Mu’azzam ya shafi kansa a hankali kafin ya k’araso ya kuma kamota “Shige muje nace..!”

Fincika tai tana huci take dubansa “Nace maka bazanje ba..! Ina Umma ta Ina Habeeb ina Asheer.. Ina suke.. Ka fada’a mun Ina suke.. Just tell me.. Tell me now ina suke..?”

“I don’t know..!! Ki wuce mu tafi nace miki.. Let me remind you, you still owe me.. You are still on your mission.. You must finish your assignment and help me catch Sagir’s accomplices.. Kin fahimta.!” Yai maganar cikin daka tsawa.

Shaye da tsananin mamaki take dubansa, bataga mahaifiyarta da ‘yanuwanta ba but he stills talk about his stupid mission.

Girgiza kai take wasu irin hawaye masu k’una na zubo mata cikin rashin yarda “My Mother and my two little brothers are gone missing.. Yet you still have the audacity to talk about your so called mission..!” Taci gaba da girgiza kai hawaye na zubo mata “You are so Selfish..You are so mean Mr Inspector..!” Daga haka gidan ta kuma komawa a guje tana kirawo Umma da ‘yanuwanta.

A guje shima ya bita ya fincikota “You will not find them here..Bazaki samesu a nan ba.. Just let the police do their Job..!” Cikin tsananin k’unan rai yake maganar.

Wannan karon da rinannun idanunta take dubansa “Damn the police..!” Ta fad’i tana dukan k’irjinsa.. Lokaci guda taci gaba da kai masa duka a k’irji da duka hannayenta biyu tana ci gaba da fad’in “This is all your fault..! Dik laifinka ne.. Laifinka ne na rasa kowa nawa..! Na tsaneka..! Na tsaneka.. I hate you l..! I hate you..!!”

Dikda zafin kalamanta da yake ji hakan bai hanasa kame duka hannayenta biyu da take dukansa dasu ba, lokaci guda ya rungumota ya kwantar da ita saman k’irjinsa, ya matseta sosai yanda zai iya hanata bige bige. Lokaci guda yake furta “I’ll find them..! I promise you I’ll find them..!” Yana jinjina kai still tana cikin k’irjinsa crying her heart out yake ci gaba da fad’in “Zan samo Su ko Ina suke..!” Ya k’arashe yana d’aura hab’arsa kad’an saman kanta.

Kuka take kaman ranta zai fice ba tareda tana iya fahimtar komai ba.. A haka ya rik’ota suka nufo waje yanda su Assad ke tsaye suna jiransu.

Mu’azzam ya dubi su Assad da jikkunansu gaba d’aya yai sanyi yace “Take care of things here.. I’ll take her home..”

Assad ya jinjina kai yace “Sure Inspector..”

Bata sake sanin meke wakana ba, bata sake sanin meke faruwa ba.. Farkawa tai kurum ta ganta a d’aki a kwance.. Ta mik’e cikin sauri tana jin kanta na wane irin sara mata.. Dikda rawar d’ari da jikinta keyi hakan bai hanata k’ok’arin fitowa daga d’akin ba ta nufo k’asa. Saidai tana fitowa ta hangesa a kitchen, yana sanye cikin armless shirt ruwan shud’i da bak’i irin kakin da police ke sakawa sai bak’in 3quater.. Ya bada baya da alama aiki yake kitchen d’in..

Cikin sand’a ta soma takawa a hankali da zummar guduwa.. Saidai tana tab’a k’ofar Parlorn ta jita a kulle.. Ta kuma ja da k’arfi taji bata bud’e ba.. Nan Ta shiga dage k’arfinta tana jan k’ofar kaman zata b’alla.

“Let me out please..! Dan Allah ka k’yaleni na tafi.. I need to find my Mom and my brothers.. Dan Allah ka k’yaleni.. Na rok’eka..!” Ta k’arashe sabon kuka na kufce mata tana mai juyowa.

Ido hud’u sukai dashi yana tsaye bayanta rik’e da plate noodles ne cikin plate d’in.

“Kinaso ki tafi..?” Ya tambaya yana dubanta.

Cikin sauri ta shiga jinjina masa kai tana hawaye.

Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Come here.” Yai maganar yana mik’a mata d’aya hannun nasa.

Ta girgiza masa kai alamun a’a tana mai ci gaba da hawaye.

Ya fuzar da huci kad’an kafin yace “Idan kinaso na barki ki tafi zakiyi duk abinda nace.. Kinji koh..”

Ta d’ago tana dubansa, sai taji wani kukan na zuwa mata gadan gadan.. Cikin muryar kuka take furta “Umma.. Ashir.. Habeeb.. They need me.. I need to find them.. Dan Allah ka barni na tafi yanzu..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

K’arasowa kusanta yai kafin ya kamota yace “I know.. But idan na barki kika fita haka bazaki iya komai ba.. You’ll collapse. You need to gain your strength idan kinaso ki samu energy d’in nemansu.. Come with me now..” Ya k’arashe yana janyota cikin jikinsa. Lokaci guda taji wane irin rauni gauraye da tausayin kanta cikin zuciyarta. Rik’eta yai b’angaren jikinsa guda yayinda d’aya hannun nasa ke rik’eda plate na noodle d’in.
A haka suka nufi upstairs tana binsa kaman rak’umi da akala.

Suna shigowa d’aki ya zaunarta bakin gado kafin ya aje plate d’in gefen bedside.

Kamo hannunta ya kuma suka nufi bathroom. Ya k’arasa wash bowl ya d’auki toothbrush d’inta ya wanke ya zuba mata toothpaste akai.. Lokaci guda ya soma k’ok’arin wanke mata bakin.

Saidai bata bari yakai ga hakan ba ta tsaresa da fad’in “I can do it myself.!”

Fuzar da huci yai yana mai kauda Kai gefe “Fine, do it then.” Ya fad’i a d’an hasale shima yana damk’a mata brush d’in cikin hannunta.

Ta aika masa mugun kallo kafin tace “I need some privacy.!”

Ba tareda ya dubeta ba ya fuzar da huci kad’an yana mai ficewa daga ciki bathroom d’in.

Yana fita ta wanke bakinta kafin ta soma lek’e lek’e ta ina zata iya gudu saidai babu wani hanya da zata iya tserewa.

Silalewa tai nan cikin bathroom d’in tana hawaye tana tina Ummanta da ‘yanuwanta.

Ganin ta jima bata fito ba yasa Mu’azzam matsowa bakin k’ofan bathroom d’in ya kasa kunnuwansa yana tinanin ko tayi collapsing cikin bathroom d’in ne.. Ya d’an saka yatsarsa guda ya k’wank’wasa “Kina lafiya..? Or should I come in..?”

Cikin sauri ta shiga share hawayenta tana fad’in “I’m almost done..” Ta mik’e tana d’auraye fuskarta da ruwa. Tsaki take cikin zuciyarta tana mamakin Wai duk jimawan nan da tai bai fice ba ashe, yana cikin d’akin yana jiranta.

Tana fitowa ta gansa tsaye gefen k’ofar bathroom d’in ya d’an jinginu jikin garu had’ida d’ingile k’afarsa guda alamun fitowarta yake jira.
Kallo guda tai masa ta d’auke kai. Shid’inma gajeren tsaki yai yace “Ke Zo ki zauna..” Ya fad’i yana mai k’arasawa had’ida d’aukan plate d’in noodle d’in.. Yai mata alama da ido kan ta k’araso ta zauna saman gadon.

Ba don taso ba ta k’araso ta zauna nan yanda yace ta zauna d’in.

“Eat up now..” Ya fad’i yana d’ebo abincin cikin fork ya mik’o mata saitin bakinta.

Mak’e masa kafad’a tai alamun “A’a.. Ka kaini wajen ahalina na rok’eka.. Suna buk’atata..!” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya.

“Zan kaiki amma sai kin cinye abincin nan.. You haven’t eaten anything since morning.. Kinga time kuwa yanzu..?” Ya k’arashe yana nuna mata smart watch d’in dake d’aure hannunsa na hagu.

Kauda kanta gefe tai tana jin wani kukan gauraye da tashin hankali na zuwa mata.

Mu’azzam yai gyaran murya yace “Police are doing all they can to locate them.. Na miki alk’awari zamu samesu.. Nasan baki yarda dani ba.. But please I want you to trust me on this..” Ya k’arashe yana tsareta da idanunsa.

Bazatace ta yarda dashi ba amma ta samu kanta tana mai sadda idanunta k’asa ba tareda taci gaba da duban cikin fuskarsa ba.

Ya kuma mik’o mata abincin lokaci guda yake furta “I cook for the very first time in my entire life. I hope you won’t disappoint me.. Zakici abincin nan koda babu dad’i.. Open your mouth now..”

Ta d’ago ta d’an dubesa yana mata alama da kansa irin yanda ake ma yara idan basu da lafiya ana so suci abinci.. Gaba d’aya ita gani take ma being nice doesn’t suit him at all gwara ma yaci gaba da zama tyrant d’insa.. Bata iya kauda kan nata ba wannan karon dan Ta kula bazai k’yaleta ba har sai taci d’in.. A hankali ta bud’e bakinta ya saka mata abincin ciki.

Saida tai spoon uku a na bud’u ta kauda kanta gefe alamun ta k’oshi.

“Last spoon.!” Ya fad’i yana tsimewa wannan karon.

Fuzar da huci tai kafin Ta furta a hankali “I’m ok..”

“No you are not.” Ya katse da fad’in haka, kafin yaci gaba da fad’in “Idan baki ci wannan na k’arshen ba bazan kaiki ba..”

Jin abinda yace ya sanyata bud’e baki a hankali ya saka mata.

Lokaci guda taga ya ciro magani pcm ya d’auki bottle water d’in dake gefe ya mik’a mata yace tasha.
Zata masa gardama taga ya tsareta da wad’ann idanun nasa.

Ta kauda kanta gefe tana amsan ruwan da maganin.. Saida ya tabbata tasha kafin ya mik’e zai fice.. Tai saurin bin bayansa tana fad’in “Nayi duk abinda kace.. Yanzu sai ka barni na tafi please..!”
Chapter 51 · 0% Book details