← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 175

Sashe 14

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safeenah tai saurin d’agowa tana duban Meema, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana fad’in “Itace.. Junior colleague d’insu ce a police Academy bani mancewa dik tare sukayi da best friend d’insa Assad.. And yanzu kuma tare suke aiki a CID.. Ta jima tana son Mu’azzam..”

Meema ta dara kad’an tace “Ahap wllhi itace take neman rabaki da mijinki..”

Safeenah tace “Toh amma ai shi baya sonta, kuma ita d’in ba ajin Mu’azzam bace..”

Gajeren tsuka Meema tai tace “Wllhi idan kikayi magana Sai naga kaman Bakida experience na rayuwa.. Shi namiji ina ruwansa indai zai samu abinda yake nema.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba itace tinda kullum suna tare wajen aiki..”

Safeenah ta jinjina kai tana huci “Wllhi sai na mata mugun wulak’anci.. Sai nasa ta soma jin kunyar kanta a ofishin nasu.. Sai naci mutuncinta a bainar jama’a..!” Ta k’arashe tana sakin huci..

Meema ta murmusa tace “Good. Now you’re talking like my real sister.. Ni ko a sch ban tab’a losing battle ba.”

Safeenah tace “Mai zan mata Meema ta fita daga rayuwar mijina..?”

Meema ta matso kad’an tace “Kawo kunnenki kiji..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*08*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Umma tana kallo Abba ya ida shirya yaransa Ashiru da Habib, tambayan duniya ta masa ya sanar da ita yanda zai kaisu yak’i kulata, ko kallon arziki ma bata ishesa ba balle ya amsata.. Har saida suka gama shiryawasu tsaf kafin yace suje waje su jirasa. Yaran sukai kaman yanda mahaifinsu yace..

Abba yai gyaran murya yana duban Umma “Uwani.”

Ta d’ago a raunane tana dubansa. Lokaci guda yaci gaba da furta “Bazan bar yarana suna ganin tashin hankalin da kuka janyo ma kanku Keda d’iyarki ba, a shekarun Ashiru da Habibu sunyi k’anana su dinga ganin ana sintiri cikin gidan nan ana Fad’a da mahaifiyarsu ana fad’in sai ta biya kud’ad’en data amsa, sannan bazan bar yarana sunaji ana cewa ‘yansanda na sallama da mahaifiyarsu ba.. Tsuntsun da yaja ruwa dama shi ruwa yake duka.. Kuma abinda ka shuka ko shakka babu shi zaka girba. Ashiru da Habib sun gama yini a gidan nan, idan Kinga mun dawo toh dare ne Yayi amma sam bazan barsu su yini a layin nan ana cewa ga abinda mahaifiyarsu da ‘yaruwarsu sukai ba.. Kunje can Keda d’iyarki ku warware abinda kuka sak’a..”

Umma cikin rawar murya take furta “Haba Abban Sadiya yanzu ficewa zakayi ka k’yalemu.. Idan ‘yansandan sukace zasu tafi damu fah..? Dan Allah ka tsaya ka zamo mana rumfa ka zamo mana Katanga.”

Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya murmusa yace “Wanda Allah ya zama gatansa shikeda cikakken Gata Uwani.. Amma yau naji dad’i da kika yarda duk talaucin miji da rashinsa akan iyalansa shi Katanga ne kuma rumfa ne..? Ashe yau kin amince ki tabbatar da hakan Uwani.. Na gode ma Allah da ya nuna mun wannan rana da kika furta hakan da bakinki kafin na bar duniya.. Ko kin mance abubuwan da kike fad’a mun a baya, cewa ni ban isa ba a gidan nan.. Idan inaso na zamto isasshe a gidana na maku abinda ranku ke so. Toh Alhamdulillah ban maku abinda ran naku ke so ba amma ku kunyi da kanku dan haka a wannan fanninma na kasa Uwani, saidai ku kuyi da kanku.. Ubangiji ya fiddaku..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai fice..

Sadiya dake mak’ale bayan k’ofa tana sauraren tattaunawan iyayen nata wane irin kuka ne taji na taso mata, tai saurin fitowa daga mab’oyarta ta nufi Mahaifinta.. Durk’usawa tai ta kamo k’afarsa tana kuka tana fad’in “Abba dan Allah ka yafe mun.. Abba nayi imani hakkinka da rainikon da muka maka nida Umma shike bibiyanmu.. Dan Allah ka yafe mana Abba, kar kayi fushi damu ka yafe mana.. Wllhi na tuba Abba bazan sake ba..”
Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai rungume k’afar mahaifin nata...

K’uri yai mata kaman zai magana, sai kuma ya duk’a ya zame hannayenta daga rik’on da tai masa, lokaci guda yasa kai ya fice daga gidan..

Sady ta d’aura hannu aka tana kuka da duka zuciyarta tana fad’in ta shiga uku..

Ficewan Abba da kaman wasu mintoci wani yaro ya shigo ya sanar dasu ‘yansanda suna sallama a waje..

Sady ta kuma fashewa da sabon kuka tana fad’in “Shikenan Umma k’ila kud’ad’en da Sagir yayita bamu na shan jini ne.. K’ila ma kud’in kan mutane yayita bamu bamu sani ba Umma.. Na shiga uku ni Sadiya ina zan saka kaina..”

Umma ta girgiza kai tace “Aikin gama ya riga ya gama Sadiya, shige muje mu sami ‘yansandan dan ko bamu fita ba zasu shigo su samemu..”

A b’angaren Sadiya Ita bama fitan bane, ganin wannan D’ansandan ne bata sonyi wanda kallonsa kad’ai ba komai yake haifar mata ba face tsananin fad’uwan gaba.. Addu’a take Allah yasa kar tayi tozali dashi..

Aiko tayi sa’a domin kuwa yau d’in babu wancan D’ansanda Sai d’aya abokin aikin nasa da sukazo tare jiya saiko wata mace wacce itama tayi shiga cikin bak’ak’en kaya..

Shi wannan Officer d’in kam nada kirki ba kaman abokin aikinsa da sukazo jiya ba, haka Sadiya tace cikin zuciyarta dan ko yanzu ma a natse yake masu tambayoyi shida abokiyar aikin tasa..

Tambayar k’arshe ne da yayi masu yasa Sadiya da Umma duban juna..
Assad yana hankalce dasu, d’an gyaran murya yai kafin yace “Zaki iya gane mutumin da ya turo a matsayin Uncle d’in nasa..?”

Umma Ta girgiza kai tace “Gaskiya nikam bazan ganesa ba, dan sau d’aya na gansa kuma da Mahaifin ita Sadiyar sukai magana..”

Maleeka ta d’an matso kad’an tace “Bazaki iya suffanta mana yanda kamanninsa yake ba..? Kiyi dogon tinani da nazari..”

Girgiza kai Umma ta kumayi alamun a’a.. Sadiya dake gefe ta bud’e baki tace “Officer idan kuka sami wannan mutumin zaku k’yalemu..?”

Assad ya dubeta kad’an yace “Kinga mutumin ne..?”

Jinjina masa kai tai kad’an tana furta “ Eh na gansa kuma zan iya ganesa.. A tsakar gidan nan sukai magana da Abba ni kuma ina lab’e kitchen ina hangensu.. Zan iya gane kamanninsa...”

Jinjina kai Assad yai yana mai zira hannayensa cikin aljihu “Da kyau, yanzu zaki bimu can ofishinmu dake headquarters, akwai masu ilimin zana kamanni cikin bayanan da aka masu wanda su aikinsu kenan.. Zamuje ofishinmu tareda ke zaki masu bayanin kamannin wannan mutumin su kuma zasuyi sketching d’insa..”

Sadiya jin ance zaa tafi da ita police station ya sanyata zaro idanu waje tana duban mahaifiyarta “Umma Wai tafiya dani zasuyi..?”

Maleeka da kanta ke kife tana rubutu cikin wata ‘yar k’amar littafi mai yanayi da jotter d’agowa tai Ta dubi Sadiya tace “Kar ki d’aga hankalinki ba tsareki za’ayi a can ba, wasu tambayoyi kawai zaki amsa mana sai kiyi bayanin wannan mutumin..”

Assad ya murmusa kad’an ganin yanda tsoro ya cika Sadiyar yace “Ki daina tsoronmu.. Police are your friends kinji koh.. Had’in kanki kawai muke buk’ata domin mu cire gurb’atattu cikin al’umma..”

A hankali Sadiya Ta jinjina kai har lokacin tsoro bai bar saman fuskarta ba..

Umma Ta matso da sauri tace “Rankaidad’e dan Allah zan iya raka d’iyata.. Dan Allah ku taimakeni ku barni na tafi tareda d’iyata..”

Shiru Assad yai yana dubanta kafin ya jinina Kai a hankali yana mai nuna masu yanda motar take pake..

Gaba d’aya suka d’unguma suka tafi police headquarters..

Zuciyar Sadiya sai tsinkewa take, ta d’aga idanu tana duban dogon ginin.. Oh yau kuma Ita Sadiya ce a ofishin ‘yansanda, abinda takeji take kuma ganina finafinai sai gashi yau yana faruwa da ita.. Tabbas a rayuwa kar kayi ma k’addaran wani dariya domin bakasan da mai gobe zata Zo maka ba.. Tana ganin yanda mutane ke shige da fice. Assad na gaba yana masu jagora yayinda Maleeka ke take masu baya.. Sady dai sai rabe raben idanu take tana kallon kanta a wajen da bata tab’a tsammanin zatazo ba..

Suna tafe ta hangosa yana tsaye k’ofan wani Office kansa kife yana duba wani file.. D’ago kan da zai suka had’a idanu.. Take taga annurin fuskarsa ya kuma d’aukewa, Ta lura mutumin kaman haushinta yakeji, Ta kula baik’i ya sami wani dalilin da zaisa ya jefata kurkuku ba.. Take ta shiga b’oyewa bayan Maleeka tana k’ok’arin b’oye fuskarta tana lek’ensa.. Tana ganin Assad ya isa garesa yana nuna masa wani k’aramin d’aki mai kaman office.. A tare suka shige Assad d’in nayima Maleeka alama da hannu kan su k’araso..

Office ne madaidaici mai d’aukeda table guda biyu, d’aya table d’in wani mutum ne zaune da computer gabansa wanda take tinanin shima d’ansandan ne.. Sai d’aya table d’in kuma wani mutum ne zaune da takardu gabansa da k’aramar cup wanda pens ne da dangin abin rubutu ciki.
Umma bata shigo office d’inba saiko Sadiyar. Addu’a take Allah Sa kar wannan mutumin ya shigo.. Aiko bata ida addu’an ba Ta gansa ya shigo yana amsa waya.. Assad yai mata nuni da wani kujera yace ta zauna.. Babu musu ta k’arasa ta zauna.
Mutumin dake gaban computer shike tattara bayanan da Sadiya keyi cikin computer d’in yayinda d’aya Mutumin dake zaune gaban table d ya shiga shirya takardunsa alamun yana jira ta suffanta masu kamannin Kawun Sagir..

Assad yai mata umarni data fara bayani..

Yanda take masu bayanin a tsorace yasa mutumin bai fahimci komai ba, tana kuma d’agowa idan ta dubi Mu’azzam sai ta kuma daburcewa ta rasa bayanin da take..

Assad ya lura da hakan, ya d’ago yana duban Mu’azzam ya kuma dubi Sadiya dake satan kallonsa.
D’an sosa kunnensa kad’an Assad yai kafin ya dubeta yace “Are you alright..?”

Girgiza masa kai tai alamun a’a..

“What’s the matter then.?” Ya tambaya yana dubanta.
Satan kallon Mu’azzam da ta kumayi yasa Assad murmusawa kad’an kafin ya k’arasa yanda Mu’azzam yake ya d’an janyo Mu’azzam d’in da har lokacin waya yake yana tsaye jikin window.. Cikin dabara Assad ya fiddashi daga cikin office kafin suka samu full attention d’in Sadiya..
Ai kuwa suna fidda Mu’azzam daga office d’in suka samu full attention d’in Sadiya, tai masu bayanin kamannin Kawun Sagir tiryan tiryan..

Mai zana hoto ya zano kamannin data fad’i.. A daidai lokacin Mu’azzam da ya ida wayan da yake ya turo k’ofa ya shigo.. Bai wata wata ba ya isa table d’in yana duba zanen wanda ba fuskan kowa bane ya bayyana face Danger..
Chapter 14 · 0% Book details