← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 175

Sashe 131

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assad yai saki baki yana dubansa, sai kuma ya zaro ido yana furta “Wow, da gaske..” Yai maganar yana murmushi lokaci guda yana k’arawada “Ah mutumina baka wasa, irin wann k’ok’ari haka lokaci guda.. Double goals at a time, Wa yake irin haka sai d’an baiwa.. Ce min zakai na soma Kiranka Yaya dan har zaka wuceni ni mai guda d’aya.. Kaga Baban ‘yan double..”

Shirun da yaga Mu’azzam yayi ne kansa kife ya d’an sanyasa dakatawa da zolayar tasa. Ya sinkayo muryar Mu’azzam d’in naci gaba da fad’in “She was pregnant kafin Mommy ta cire cikin..”

Assad ya tsaya Cak da ‘yar zolayarsa yana duban Abokin nasa, sai kuma ya girgiza kai yace “Ban fahimta ba.. Wane irin kafin Mommy Ta cire cikin.. I mean mai hakan yake nufi..?”

Mu’azzam ya jinjina kai yana duban Assad d’in “Eh kaji daidai.. Kafin Mommy Ta cire cikin right in front of me.. Assad Mommy Ta bawa Safeenah pills na cire ciki akan idanuna, Inaji Ina gani gudan jinina na fita yana bin k’asa And I couldn’t do anything to save my child.. I couldn’t do anything to protect that innocent soul that was only caught in the middle..” Muryarsa ya carke sabida tsananin b’acin rai.

Ya d’an lumshe idanunsa kad’an had’ida kauda FUSKA gefe yana sakin numfashi a hankali.

Assad da Mamaki ya kasa sakesa, girgiza kai yake yana duban abokin nasa “How is this possible.. Waima ta ya haka zai kasance.. Mommy tai aborting cikin Safeenah akan idanunka.. But Safeenah is her daughter right..? Ta yaya zata uwa zata cutar da d’iyarta irin haka..?”

Mu’azzam yaci gaba da jinjina kansa a hankali still yana duban gefe “Ta aiwatar da haka ne dan Ta d’auki fansa akaina, da duk abubuwan da na aikata masu itada Safeenah a cewarta..” Ya d’an maikaito yana duban Assad kafin yaci gaba da fad’in “Amma mai na aikata masu Assad..? Mai na aikata wa Mommy da tsanani da zata nuna min irin wann k’iyayya k’iri k’iri.. Shin kulle Safeenah da nayi ne lokacin da binciken mutuwar Ikram ya biyo kanta ko kuwa sakin da na mata akan idon Mommy ne..? Kodai auren da nayi ba tareda saninsu bane..? Assad cikin abinda na lissafo wanne ne yakai girman abinda Mommy Ta aikata mun.. Assad ban kashe mata kowa nata ba.. Maiyasa ta zab’i ta kashe bawa akan idona..? And bai tsaya a nan ba, yau d’in na kuma fahimtar wani abu gameda Mommy..” Yai fasali su duka biyun suna duban juna shida Assad kafin ya sanar da Assad dik abinda Musaddiq ya sanar dashi gameda Mommy.

Mamaki da tsoron mutanen duniya ya kuma kama Assad. Yayinda Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Assad matar nan tayi niyyan cutar da mahaifiyata bayan tsawon shekarun da ta d’iba da sunan tana jinyarta.. Allah kad’ai yasan mai ta aikatawa Mahaifiyata idan har zata iya kashe Jininta d’an Safeenah.”

Assad ya girgiza kai cikeda tausayin Abokin nasa “I can’t wrap my head around the whole thing. Da wani ne ya bani wann labarin bakai ba Mu’azzam, wllhi da zance k’arya ne ba gaskiya bane.. Ikon Allah.. Idan na tuna a lokutan baya yanda Mommy ke nuna maku k’auna daga kai har Ikram da Mamy wllhi da za’a ce zata aikata duk abubuwan daka zayyana min zance k’arya ne.. Toh amma kasan mutane suna canzawa.. Watak’ila b’acin ran da ka jefata ciki ne na duk abubuwan da ka zayyana kayi masu itada Safeenah ta iya yiwa hakan yasa take d’aukar fansarta akanka dan Ta bak’anta maka.”

A d’an kaikaice yake duban Assad d’in kafin ya girgiza kai yace “Haba Assad, Kai tunani mana.. Idan har Mommy zata so mahaifiyata ta fice daga gidanta da rayuwar mijinta bayan shekarun data kwashe tana hak’urin zama da Ita da yi mata jinya, Maiyasa tuntuni bata zab’i ta fitar da ita daga rayuwar nata ba sai yanzu.. Na tabbata wann matar akwai babban abinda take b’oyewa.. Kuma bazan gajiya ba sai na nemota yanda ta shiga ta fita ta amsa min tambayoyi na..”

Assad ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya. D’an matsowa kusan Mu’azzam d’in yai ya Dafasa kad’an yace “Mu’azzam kai hak’uri.. Na sani ka fuskanci k’alubale da dama na rayuwa, amma ka sani mai k’arfin imani shine Allah yake jarabtansa.. Yanzu da Mommy ta cire D’anka akan idonka sai gashi tun kafin wayewar gari ya maida maka waninsa.. Allah yana sakawa bawa idan an zaluncesa Ta hanyar da baiyi tsammani ba.. Sann gameda maganar neman Mommy kasan kanada full support d’ina.. Zamu binciko yanda take in sha Allah.. Nasan you are going through a tough time now, but please don’t do anything irrational.. Zamuyi komai a natse kaji..”

D’an kauda kai gefe kad’an Mu’azzam yai yana furzar da huci lokaci guda yana duba agogon dake d’aure tsintsiyar hannunsa na hagu.

Bud’e motarsa yai yana fad’in “Kaje kawai zamuyi magana goben in sha Allah..”

Assad ya jinjina kai yana dubansa, ya zira hannayensa duka biyu a aljihu kafin yace “Alright sai naji daga gareka.. Please take care Mu’azzam.”

Mu’azzam ya jinina masa kai yana mai k’ok’arin tada motar kafin Assad ma ya nufi nasa motar. Tare tare suka fice daga Foundation d’in.

Yana isowa gida yai tsaye jikin dining table yana kallon abincin data shirya masu wanda ko tab’awa batai ba, ya shiga bud’e abincin yana sakin murmushi a hankali. Shi kansa yasan idan yace bazaiyi kewar kasancewa da ita ba yayi k’arya. Sadiya ta zama wani b’angare na jikinsa, yana mata wane irin so wanda baisan yaya rayuwa zata kasance ba idan ya rasata. A hankali ya isa jikin hotonsu dake manne hanyar staircase. Ya shiga shafa fuskarta yana sakin murmushi yana tuno abubuwa da dama da suka faru, tin daga randa suka fara had’uwa har kawo wann lokacin da take d’aukeda juna biyunsa, murmushi ya saki a hankali still hannunsa na shafa hoton nata, sai kuma ya d’an stime ya harareta kad’an “Hey Stubborn Head, you better be careful now, you are carrying Mr Inspector’s child in your womb.” Ya d’anyi maganar yana nunata da yatsa had’ida d’an fito da idanunsa waje kaman dai yanda yake mata gargad’i a lokutan baya da basu jituwa. A hankali ya janye idanunsa yasa kai zai nufi sama. Har ya taka matakalan benen guda biyu sai kuma ya juyo still yana dubanta “Hey Beautiful, I love you.. I love you so much.” Ya k’arashe gajeren murmushi da yayita da gefen bakinsa saman fuskarsa kafin yasa kai ya nufi d’akin nata yanda ya shiga parking mata Kayyakinta.

**

A b’angaren Sadiya kaw dankalin hausa Aunty Larai ta soya mata taci da yaji mai dad’i maras zafi.. Ta kuwa ci sosai tai nak abinta. A nan parlorn ta d’an kishingid’a tana kallon labarun tara da aka soma nunawa a tashan NTA. Nan taga an hasko wani labari cewa Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina sunyi nasaran capke wata mata da ake tuhumarta da laifin safaran makamai wa ‘Yan fashin daji a garin Malumfashi na jihar Katsina. Matan mai suna Tabawa ta fito ne daga garin Suleja na jihar Niger dake mak’otaka da birnin tarayya Abuja.

Sadiya bata gama jin labarin ba ta shiga rangad’awa Umma kira “Umma..! Umma.! Umma Zo ki gani..”

A tare Umma da Aunty Larai dake kitchen suka nufo parlorn babu shiri suna tambayar Sadiya lafiya.?

Sadiya ta shiga nuna masu TVn wanda har lokacin labarin Tabawa ake nunawa “Umma Kinga Hajiya Tabawa ce duba ki gani.”

Umma ta shiga salallami tana tafe hannaye. Tabawa ce Tabawa da suka sha fama da ita, Tabawa da suka amshi rancen kud’ad’e wajenta lokacin auren Sadiya da Sagir da bai yuwu ba.

Umma taci gaba da salati tana fad’in “Tabawa ce.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Kar dai kud’ad’en Garkuwa da mutane Tabawa ta ranta mana.. Oh na shiga uku ni Uwani.. Allah mun tuba.. Allah ka yafe mana kurakurenmu.. Oh duniya ashe Tabawa ‘yar safaran makamai ne wa ‘Yanfashin daji..” Kuka ya kufcewa Umma tana fad’in “Yo ba dole muga ba daidai ba, ‘Yanta’adda suna kewaye damu.. Mun amshi Kud’i hannun Sagir Sann muka Zo muka amsa hannun Tabawa wacce itama ashe ‘yarta’addan ce ba dole muga babu kyau ba a rayuwa.. Son abun duniya baya kai Bawa ga komai face tab’ewa da halak’a..”

Sadiya ma hawaye ne taji na zubo mata sanda Ta tuna rayuwarsu a baya da yanda yanzu rayuwar nasu ya inganta bayan sun zab’i canza rayuwar da suka zab’ar ma kansu a baya.

Aunty Larai Ta rungume Umma tana bata baki da fad’in “Komai muk’addari ne daga Allah. Sann ku kanku baku San cewa Tabawa ‘yarta’adda bace da baku amshi rance daga hannunta ba.. Sann Kun maida mata kud’d’enta baku ci kud’in Tabawa ba, Allah ya ceceku ya fiddaku.. Allah baya kama mutum kai laifin da bai sani ba.. Kiyi hak’uri ki daina kukan nan haka kar ki d’aga hankalin Sadiya dubada lalurar da take d’auke dashi.. Sann Tabawa kuma an riga an capketa zata biya duk abubuwan data aikata, an kuma cire mugun iri cikin Al’umma.. Akwai ire iren Tabawa da dama ana rayuwa dasu cikin Al’umma amma ba’a sansu ba.. Allah yaci gaba da tona wa masu hali irin na Tabawa asiri dama sauran ‘Yantaddan da suka addabi k’asarmu. Allah ya kawo mana zaman lafiya ya azurtamu da shuwagabanni na gari ya kauda mana gurb’atattu.”

Gaba d’aya suka amsa da Ameen. Haka sukaita jinjina lamarin har Sadiya da Umma suka shige kwanciya aka bar Aunty Larai ita kad’ai a parlorn.

Misalin k’arfe 10:30pm yai sallama a k’ofar parlorn. Aunty Larai dake zaune ita kad’ai ta asma had’ida masa iso.

Ya d’an duk’a suna gaisawa yana fad’in tai hak’uri ya tadasu a bacci ya Zo late.

Aunty Larai ta murmusa tace “Ai yanzu kam nasan mu saka ran ganinka ko tsakan dare ne tinda mun d’auke matar mission.”

Murmusawa yakeyi yana shafa kansa dan yanzu kam zai iya cewa ya soma Sabo da barkwancin Aunty Larai, ba’a rabonta da barkwanci saikace ita ta haifi abokinsa Assad.

Ta d’an murmusa itama kafin tace “Kaga saki jikinsa sirkarka tayi bacci nidai kasan ba sirkarka bace. Ka shiga ka sami matarka bata jima da shiga ba. (Sadiyar dama a d’akin Aunty Larai Ta sauk’a).
Chapter 131 · 0% Book details