← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 175

Sashe 106

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba zata Sadiya taji batun.. Sai bata ce komai ba ta amsa ma Inne da fad’in “Toh Inne.. Can k’asan zuciyarta kaw dikda tana son kasancewa da mijinta dan tayi kewarsa amma wani b’angare na zuciyarta sam bai son rabuwa da Mamy.. Ta saba sosai da ita d’an zaman da sukai tare dan tare suke kwana sann kusan rabin d’awainiyar da Mama Hindu ke mata Sadiyar ke mata su yanzu.

Shemau kaw ji tai kaman an dab’a mata mashi.. Abin yayi kusa bazata samu Ta cimma Alk’awarin da taima Safeenah cikin gaggawa ba.. Ya zama dole Ta b’ullo da dabara.. Ya zama dole kafin wayewar gari tai executing plan d’inta.

D’an murmusawa tai tana fad’in “Allah Sarki Amarya zata tafi Ta barmu da kewa.. Gashi bata zaga taga dangi ba.. Dama Mu’azzam ya kamata ya zaga da ita toh gashi baya nan.. Har lokacin tafiyarta tayi..”

Inne ta d’anyi shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne.. Ya kamata ta d’an zaga ta gaida dangi ta masu sallama.. Shemau sai ki mata rakiya zuwa yamma..”

Shemau ta jinjina kai cikeda jin dad’i “Tau Inne zan zaga da ita In sha Allah..”

Inne Ta dubi Sadiya tace “Tinda gobe zaku juya da yamma idan rana tai sanyi sai ki shirya Shemau ta rakaki gari kiga dangi koh..”

Sadiya Ta jinjina kai tana amsa dama Inne da “Toh Inne.” Lokaci guda Ta mik’e tana fad’in bari ta duba Mamy.

Inne ta jinjina mata kai tana mata izinin tafiya.

Suka bi bayanta a kallo daga Innen har Shemau. Murmushi saman fuskar Inne take fad’in “Yarinyar a natse take.. Modibbo yai sa’an iyali.. Allah ya nuna min d’iyoyinsu kafin ya amshi rayuwata.”

Shemau Ta murmusa tace “Zaki ga d’iyoyinsu in sha Allah Inne..”

Inne ta murmusa tace “Allahu yashaa.”

Shemau Ta amsa da Ameen kafin Ta mik’e tace bara ta duba taci kaman shigowar motar Uncle Salman k’ila ya dawo.

Inne ta jinjina mata kai tana mai gyara zaman k’afarta dake d’an mata ciwo. Ta bud’e murya tace “Ki fad’a wa Salman d’in Ina nemansa.”

Shemau Ta amsa da “Tau Inne.”

**

ABUJA

_National Police Headquarters (Force Criminal Investigation and Intelligence Department FCID)_

Carko carko sukai shida Yusuf bayan sun fito daga Babban meeting d’in da ya k’unshi manyan ‘yansanda daga cikinsu. An kuma d’aukan statement d’in Assad an basu kwanaki k’alilan su zak’ulo Danger yanda ya shiga ya fita.

Mu’azzam ya fuzar da fuci a karo na babu adadi yana shafan sumarsa, dole yai interrogating Assad koda bai yarda cewa Assad d’in mai laifi bane dan a halin yanzu abin ya fi nasa k’arfin ya isa yanda baiso ya isa ba.. Idan yana son wanke Assad dole sai ya kamo asalin b’eran dake cikin Department d’in.

Jikin Farin allo da hotunan mutane da case d’in ya shafa ya k’arasa ya manna hoton Assad jikinsa a matuk’ar mace.. Ya janyo arrow yai linking hoton Assad dana Danger yana jin kaman hannunsa na shaking.. Abotansu da abubuwan da sukai going through a rayuwa kawai yake tunawa kama daga lokacin da police academy har zuwa nasarori da k’alubale da suka fuskanta a aikin na D’ansanda.

Yusuf ya dubesa cikeda tausayawa kafin ya k’araso yana basa k’warin gwiwa.

“Komai zai shige.. Zamu wanke Assad, bazai losing aikinsa ba saidai ma ya samu k’arin yarda da matsayi.. In sha Allah zamu fitar da gaskiya daga cikin k’arya.. Nasan zaka iya Mu’azzam.. Kar ka karaya.. Kar ka nunama Azzalumai gazawarka.. Zaka kawar dasu da yardar Allah.”

Duban Yusuf kurum yai da idanunsa da suka kad’a sosai kafin ya maida dubansa fa hoton Assad da aka had’a da na Danger.

Ya d’an shafi sumarsa kad’an kafin yace “Kaje wann asibitin.. Mai ka samo so far.?”

Yusuf ya d’an ware idanunsa yana mai fuzar da fuci kad’an yace “I couldn’t find anything until now.. Na sa an min playing CCTV footage tin daga ranan da ka kai samples d’in asibitin amma wann ranan da ka kai samples d’in security Cameras d’in asibitin sun sami matsala..”

Mu’azzam ya dubesa yace “Kenan ba’a sami footage d’in wann ranar ba.?”
Yusuf ya jinjina kai alamun Eh..

Murmusawa yai da gefen bakinsa yana jinina kai kad’an “Na wann ranan ne kawai ya zama missing.. Why..? Maiyasa sai a ranan zai sami matsala..? Don’t you think this is too much of a coincidence..?” Yai maganar yana d’an bubbuga table d’in da marker dake hannunsa.

Yusuf ya jinjina kai yace “I thought as much.. Nayi tunanin haka nima..”

Mu’azzam ya d’an sosa hancinsa kad’an kafin ya dubi Yusuf yace “K’arya suka maka.. Wann footage d’in na nan kawai basu maka playing d’insa bane.. Wani wasa suke so su buga, but believe me we’ll turn the table on them.. Wann Rat d’in da muke nema shi ya shiga wann asibitin Yayi Sabotaging DAN Samples.. Idan muna so mu kamo b’eran nan sai mun fitar da wann footage d’in daga hannun securities d’in. I’m pretty certain footage d’in na nan biyansu akai dan Su b’oye dan na tabbata by now b’erayen sun san muna hunting d’insu.”

Yusuf yace “What if sunyi deleting..?”

Mu’azzam yai shiru yana nazarin Yusuf sai kuma yace “Ai asibiti ne bazasu goge record haka kawai ba.. Sannan sunsan test d’in is somehow related to police case. Dole akwai abinda sukai.. Nafi tunanin biyansu akai.. Amma kar ka damu zamu buga wasan sai mun samo wann footage d’in.”

Dai dai lokacin Maleeka ta shigo Office d’in. Mu’azzam ya mik’e daga saman table d’in da yai zaune bisa ya dubi Yusuf yace “I’ll interrogate Assad..”

Yusuf ya jinjina masa kai kafin ya shige.. Maleeka kaw sai dubansa take k’asa k’asa zuciyarta ba wane irin yankewa sabida taga irin firgitaccen duban da Mu’azzam d’in ke mata.

Yana ficewa Ta dubi Yusuf tace “Bansan mai naima Inspector Gamji ba. Ko kallo ban ishesa ba.. Na rasa shi wane irin mutum ne sam da yakeda tsananin ra’ayi.. Ba hurumin kowa yake shiga ba koda aiki tare ya had’aku idan ba dole ba Sai yaga dama yai involving naka.” Ta k’arashe tana zuba files d’in hannunta saman table.

Yusuf yaci gaba da tattara reports d’in dake saman table d’insa yace “I don’t blame him idan ya zab’i yai minding business d’insa.. Nowadays mutane ba abin yarda bane.. Kana tare da mutum ne bakasan yana cin dunduniyarka ba.. Excuse me..” Ya fad’i yana d’aukan folder d’in.

Tabi bayansa da kallo cikeda takaici dan Ta kula magana ya fad’a mata a dunk’ule..

Zuciyar Maleeka yai wani irin tsinkewa sanda wani tunani ya d’arsu mata cikin zuciyarta. Yanzu idan teburin ya juya fah..? Idan aka fahimci Assad baida laifi kenan fah itace zata tafi kurkuku alhali babu abinda ya had’ata da Danger tinda Ita dai masu Chief take aiki.. Toh amma babu Ta yanda za’ayi a wanke Assad dan sun rufe duk wata k’ofa da za’a ratsa a wanke sunan Assad bugu da k’ari Assad da bakinsa ya bada statement d’insa bama wani ne ya bayar ba. A sabida wann Assad Baida k’ofar ficewa.. Dole ya tafi prison. Ta murmusa kad’an tana duban hoton Assad da akai linking da na Danger.

**

A can Fufore kuwa yamma lis kusan goshin magrib suka dawo daga gaishe gaishen nasu, gaba d’aya a gajjiye take dan saida Aunty Shemau tasa driver ya d’an zagaya dasu Sadiyar taga gari. Hakan yasa tana dawowa gida Ta fad’a wanka kafin Ta fito Ta shirya tsaf cikin doguwar riga cotton mai Laushi da fad’i, Ta zira hijab d’inta ta gabatar da sallar magrib dan already anyi kira kafin Ta fito ta nufi sashen Inne wajen Sirkarta..

Shemau na ganin ficewarta Ta d’ago wayarta ta soma dialing wata number..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*53*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Shemau taci gaba da fad’in “Yauwa kana jina koh.. Kana isowa ka kirani a waya ni zanzo na shigar dakai.. Karfa kazo Ta main gate.. Eh ta k’aramar k’ofar baya... Yauwa kana zuwa kawai ka kira wayata ni sai na taho na bud’e maka na shigo dakai.. Toh sai ka iso sai na jika..” Tana katse wayar Ta soma murmushi Ta kusa cika burin mijinta, Ta tabbata idan taima Safeenah wann aikin shikenan Safeenar ta sami abinda take so sann zata nemo masu BAT cikin gaggawa. Hakan na nufin abinda mijinta ya jima yana nema zai tabbata nasa.. Ta murmusa tana juya idanu lokaci guda tasa kai ta nufi nata b’angaren.

Shigarta da kad’an Ummilo ta shigo ta sanar da ita Inne na nemanta.. Bataso zuwa ba dan tana tsaka da mission ne bata fatan abinda zai b’ata mata wann mission d’in nata.
Gashi babu abinda yafi bata takaici kaman da kiran ya kasance Wai hidiman Nuratu ya shafa.. Takaicin duniya kaman ya kar Shemau ba abin ta silale ta gudu ba kafin bak’onta ya k’araso. Hankalinta gaba d’aya kan wayarta yake tana jira taji kiransa.. Gaba d’aya kana ganin Shemau zaka fahimci ba cikin hayyacinta take ba.

Can after like 1hr mutumin ya k’araso location d’in da Shemau ta sanar dashi. Ya k’araso Bakin k’ofar yana ‘yan dube dube. Ya soma k’ok’arin ciro waya kenan zai kirata sai hangota yai tana tahowa cikin shiga bak’in hijabi harda mayanin rufe FUSKA mai kaman nik’abi.

Ya murmusa yace “Rankidad’e harda nikabi kika rufa a daren nan..”

Ta jinjina masa kai tana masa alama da hannu kan ya k’araso cikin sauri.

Ya d’an ci gaba da waige waige yana fad’in “Dole ki b’adda kama dukda dare ne sabida tsaro..”

Shemau dai bata ce komai ba tana gaba yana biye da Ita har suka k’araso b’angaren.

Ta bud’e masa k’ofofi suka isa har bedroom. Ya haye saman gado ya zauna yana d’an tsalle daga zaune kad’an nan saman katifar yana fad’in “TJ yau zakai bacci mai rai, bacci maiji da lafiya saman tattausar katifar nan.. Dad’i ya maka yawa... Ga kud’i an tura maka account ga bacci saman katifa mai taushi.. Safiya nayi idan an maka ihun kwarto Sai ka arce a guje kafin a capkeka..” Ya k’arashe yana zame rigarsa ya rage daga shi sai singlet ya maida kansa ya kwanta saman pillow harda lumshe idanu yana jijjiga k’afafunsa kad’an yana shak’an k’amshin ‘yan gayun dake cikin d’akin ga taushin katifar da yake jinsa har cikin b’argonsa.
Chapter 106 · 0% Book details