← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 175

Sashe 74

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Idan akan abinda ya shafi takardun kud’i ne babu wanda ya isa yama D’anuwanka wayo.. Dik k’ok’arina na rasa ina takardun suke.. Kuma da alama baya sanar da matarsa wasu abubuwan.. Amma mai zai hana ka cire idanunka akan dukiyar Mu’azzam tinda yanzu company dake Adamawa kai kake rik’e dashi harma da gidan gonar..”

Katseta yai da fad’in “Samun mahimman takardun nan su zasu sa Company ta zama nawa gaba d’aya amma muddin ba’a samesu ba baza’a daina cire kason Mu’azzam da ‘yar uwarsa harma da mahaifiyarsa a cikin dukiyar ba. Wann takarda shaida ce zai tabbatar cewa basu da kaso cikin dukiyar.. Inada tabbacin lokacin da Yayanmu ya mutu Marwan shi ya d’auke takardun nan..” Ya k’arashe yana kuma zagaye d’akin lokaci guda yana kurb’an shayi.

Aunty Shemau ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tace “Yanzu kam da ka d’auko ni ai ka b’ata komai saidai mu dake gwada sa’an wani lokaci.”

Fuzar da fuci yai yana mai jinjina kai a hankali.

**

‘Yansanda ne tin daga k’ofar asibitin har cikin asibitin. Tuni an shiga da Assad d’akin operation.. Sadiya ma Ta k’ara fainting a asibitin dole aka bata Gado dan gaba d’aya babu k’arfi da kuzari jikinta gashi har lokaci bata daina razana ba sabida abinda ya faru da Ita. Da alama tin safiyar ranan da aka d’auketa bata saka komai a cikinta ba.. Kwana guda kenan tai babu abinci ya tsoro da razana dole aka d’aura mata ruwa a nan asibitin.

Mu’azzam yana zaune gefenta yana dubanta idanunta a lumshe, da gani baccin azaba take da kuma tsoro. A hankali yakai hannunsa saman goshinta yana shafawa a hankali “Bazasu k’ara samun damar cutar dake ba.. Na miki alk’awari..” Ya fad’i idanunsa akanta

Lokaci guda kuma yai shiru yana nazari.. Maiyasa suke bibiyanki da ahalinki.? Maiyasa suke so su shafeki Keda ahalinki..?

Zuciyarsa Ta basa amsa da fad’in ‘Sabida suna tsoro kar Sagir ya sanar da ita wani abu tinda har saura kad’an ya aureta.. Zasuyi tunanin yarinyar tasan duk wani shirinsu daga wajen Sagir.. Watak’ila harta ahalinta ma sun sani..”

Shafe fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kafin ya mik’e yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu.

Fitowa yai daga d’akin ya dubi ‘yansanda guda biyu dake tsaye k’ofar d’akin yace su kula sosai babu mai shiga Sai likitan nan da suka gansu tare..

Suka jinjina kai suna sara masa. Lokaci guda ya shige nan ya hangi Maleeka ana rufe nata wound d’inta a dressing room.

Kaman zaisa kai ya shige sai kuma ya dawo da baya. Da wutsiyar idanu Maleeka take dubansa.. Ganin ya tsaya yana dubanta ya sa Maleeka marairaicewa kaman yau ne bullet ya soma kuskuranta.

Mu’azzam ya nufo d’akin still idanunsa akanta, daidai lokacin da aka fama rufe mata ciwon.

Ta d’ago tana dubansa, k’warjininsa ya hanata duban k’wayar idanunsa, hakan yasa Ta sadda kanta a hankali.

Hannayensa dafe da kunkumi yake dubanta “You shouldn’t have done that, you know..”

Ta d’an d’ago a zabure tana dubansa jin abinda yace

Mu’azzam ya kuma jinjina kai kafin yace “Maisa zaki karb’a mun harsashi.? Next time kar ki sake abu makamancin haka Maleeka.. Get well soon..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige.

Maleeka Ta saki baki da hanci tana dubansa, Ta tare masa harbi harsashi ya sameta maimakon ya samesa amma ya rasa abinda zai fad’a mata sai wad’ann kalaman.. Maimakon yai mata godiya ko ya nuna kulawarsa akanta amma abinda zai iya fad’i kenan sabida tsaban girman kansa da isansa.. Tai k’wafa tana jin zuciyarta na mata wani irin k’una.. Nurse d’in ta k’araso tana fad’in bari a k’arasa rufe mata ciwon.

Tsaki Maleeka tai tace “Barshi bana buk’ata..”

Nurse d’in tace “But infection zai iya shiga ki tsaya a k’arasa rufewa.”

A kufule Maleey tace “Ank’i a tsaya d’in.. Baza’a tsaya ba.. Infection d’in ya gama shiga a daidai lokacinda wanda akaji ciwon dominsa ya nuna rashin kulawarsa.” Tana ida fad’in haka ta mik’e tana huci.

Chief ne ya shigo yace ma nurse d’in ta d’an basa Moment da Maleeka. Babu musu nurse d’in ta basu waje.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*39*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Chief ya k’ura mata idanu yana girgiza kai “Ban yarda baki sanar dashi komai akan BAT ba.. If you can take a bullet for him na tabbata zaki iya masa komai.. So you better tell me the truth right now.. Mai kika sanar da Inspector Gamji gameda BAT.?” Ya k’arashe kaman zai shak’ota.

“Wane irin rantsuwa kake so na maka..? Na rantse maka da Allah ban sanar dashi komai ba.. Yanda kaga ya rubuta B.A.T jikin board haka nima na gani.. I’ve no clue mai hakan yake nufi..”

Jaja ya jinjina kai ya d’an kuma matso da fuskarsa kusan na Maleeka. Cikin yanayi na gargad’i yake furta “You better be telling the truth.. Because once I find out k’arya kike mun Maleeka..?” Ya murmusa kafin yace “Ki fara k’irga kwanakinki..”

Har ya juya zai fice ya kuma dawowa “Ki tabbata kin samo mai Mu’azzam ya sani gameda BAT.. Wannan shine next Assignment d’inki..”

Murmusawa Maleeka tai kafin Ta girgiza kai tace “Da alama har yanzu bakusan da wa kuke dealing ba Sir.. Do you think this is an easy task..? We are talking about Mu’azzam Gamji here..” Ta gyara tsayuwarta kafin taci gaba da fad’in “Guy d’in nan is a complete savage. I risked my own life for him.. I took a bullet for him.. But a simple thank you ya gaza fad’a.. Irin wannan mutumin nan ne kuke tsammanin shiga jikinsa abu ne mai sauk’i..? Mu’azzam Gamji is not like every other guy.. Kuyi hak’uri amma zai matuk’ar wuya ku kaisa k’asa..”

Chief ya murmusa kafin yace “Ko bai fad’a miki ba yasan he owes you a huge of gratitude.. And deep down ya gode miki.. Kuma bazai tab’a mance sacrifice d’in da kika masa ba.. Kawai kaman yanda kika ce ji da kansa bazai barsa ya nuna miki hakan ba ko ya furta.. But believe me kin samu yardarsa daga yanzu.. Mu’azzam Gamji will never doubt you bayan sadaukarwa mai girma da kika masa.. Ki ringa da kin samu yardar Mu’azzam, yanzu abinda ya rage miki shine kisan mai yake ciki, kiyi uncovering duk wasu abubuwan da ya sani especially akan BAT.” Ya murmusa kafin ya kuma furta “Get well soon sweetheart..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice.

Huci Ta kuma saki kafin Ta fito waje, nan ta hangi motar Mu’azzam a wajen. Ta d’an d’aga gira guda sama tana duban motar.. Toh kenan bai tafi bane ko k’ak’a.? Wata Zuciyar ta bata amsa da fad’in Ina zai tafi tinda Queen of his heart tana kwance anyi admitting nata.. Ta fuzar da fuci mai zafi tana furta “Goddamn your pride Inspector Gamji..!” Tana ida fad’in haka Ta nufi motar tasa dan a zatonta ko zata hangosa ciki.

Tai tsaye tana k’are wa motar kallo.. A backseat ta hango wani abu cikin transparent nylon.. Tai saurin matsowa tana duban abun.. Hula ce d’auke da rubutun B.A.T a fuskar hular.. Take ta soma tina abinda taga Mu’azzam ya rubuta saman allon bincikensu.. Kenan wannan ne clue d’in da ya samu gameda BAT ko menene.. “I need to find out what he knows.” Ta furta a hankali tana mai ficewa daga asibitin lokaci guda ta tari Cab ta shige tana dialing layin Chief..”

**

Kai tsaye bayan ya fito daga asibitin gida ya wuce dan ya samu yai wanka ya sake fitowa. Bud’e k’ofar parlorn da zai ya hangi used tissue papers baja baja a k’asa wanda Safeenah tasha kukanta ta goge fuskarta dasu, ya hangi dining table nan ma yaga a wargaje, ko ina very scattered.. Ga plates a saman dining table d’in ga abinci har saman table d’in tin daga cikin takeaway pack har k’asa.. Ga ledojin da aka sayo abincin ciki suma suna nan a wajen ba’ai disposing nasu ba.. Fuzar da fuci yai a hankali kafin ya nufi upstairs cikeda k’yank’yanin gidan gaba d’aya kaman ba kwana guda Safeenah tai cikin gidan ba ko Ina kaca kaca..

D’akinsa ya nufa ya soma rage kayan jikinsa. Daidai lokacin Safeenah ta shigo taci uwar gayu kai kace ba itace tai kaca kaca da gidan ba tsaban yanda Ta tsara gayu ma jikinta. Fuskar nan Sai k’yallin kwalliya take an zubo da gashi sai zuba k’amshi ake.

Saurin K’arasowa tai tana k’ok’arin b’alle masa botiran rigar nasa. Ganin bai gwasaleta ba ya sanyata kuma rausaya idanu tana ci gaba da b’alle masa botiran cikin salo na jan hankali “My Halal banji zuwanka ba..” Ta fad’i cikeda shagwab’a.

Kauda fuskarsa yai kad’an kafin yace “Ina zakiji kina can kinata tsara kwalliya ma jikinki kin bar gidanki kaman bola..”

Ta d’an turo baki tace “Yanzu zan gyara.. Na kawo maka abinci ne... Nayi order online d’azu..”

Girgiza kai yai yace “I’m Ok.” Ya d’anyi gyaran murya kafin yaci gaba da fad’in “Everywhere is scattered Safeenah.. Ya kamata ki kira gida kice a turo miki yarinya da zata ke tattara gidan nan.. Kinsanni, I’m obsessed with tidiness..”

Safeenah ta kuma turo baki cikeda shagwab’a tace “My Halaal kasan bana son wata tazo ta zauna a gidana.. Ni kawai bana son wata ‘yar aiki a gidana, I can handle everything here..”

Girgiza kai yai yace “No Safeenah, you can’t.. Bazaki iya kula da gidan nan ba.. Ki kira Mommy right this moment ki fad’a mata kina buk’atar help.”

Ta kuma turo baki cikeda shagwab’a, kafin tai magana ya tsareta da rikitattun idanunsa yace “Now Safeenah..!”

Babu musu ta d’auki wayarta da ta aje saman gadonta Ta soma dialing layin Mommy tana addu’an Allah yasa ta d’aga.

Kaman kaw bazata d’aga ba, can ta d’aga ba dan tayi niyya ba Sai dan Aunty Shemau ta kirata ta sanar da ita halinda Safeenar ke ciki bayan taje gidan Safeenar.

Bai tsaya sauraren wayar ba ya fad’a bathroom.

Safeenah ta zauna nan saman gado tana gaida Mommy, Mommy na amsa mata da k’yar.

Safeenah ta d’an kuma turo baki tace “Mommy are you still mad at me..?”
Chapter 74 · 0% Book details