← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 175

Sashe 6

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka itama tace “But kafin Musaddiq ya tafi Mommy I was all alone.. Har saida nayi shekaru biyu a UK kafin Musaddiq ya tafi.. Kuma Mommy Musaddiq shima nashi watsewar yake tareda ‘yanmatansa har saida Ikram ta taho Salford kafin ya rage wasu abubuwan da yakeyi sabida Ikram da nasihar da take masa... Mommy ki yarda akwai naku laifin daga ke har Daddy...”

Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ke ni Kimin shiru ba guntun wa’azi nace Kimin ba tinda kin riga kin gama watsewarki da mazan turawa a turai.. So nake ki fad’a min Ta yanda alhakin mutuwar Ikram ya rataya a wuyanki..”

Safeenah ta kuma k’unshe bakinta tana jin wani kukan na taso mata..
Daidai lokacin aka soma knocking..

Jin muryar mai k’wank’wasa k’ofar ya sanya Mommy da Safeenah ware idanu suna duban juna.. Cikin sauri Safeenah take k’ok’arin saita kanta Mommy na aika mata wane irin kallo.. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kina jina..”
Safeenah tai saurin jinjina kai

Mommy taci gaba da fad’in “Koda wasa kar giyan soyayya ya d’ibeki ki bud’e baki ki sanar da mijinki wani abu.. Ke bama shi kawai ko Daddy bazai sani ba, sannan babu wanda zai san wannan maganar.. Daga ni sai ke kin fahimta..?”

Nan ma saurin jinjina kai Safeenah tai kafin Mommy taci gaba da fad’in “Kisan yanda zakiyi ki b’oye wannan rawar jikin naki dan idan kika bari ya fahimci wani abu kashinki ya bushe Safeenah, Kinsan Wanene Mu’azzam kin fi kowa sanin zafin zuciyarsa.. Ba ke kad’aiba inaga har zuri’arki kaf Sai ya tura kurkuku muddin ya fahimci you’re somehow related to case d’in mutuwar ‘yaruwarsa..” Ta gyara tsayuwarta tana mai kuma yin k’asa da murya “ Kina jina..Zaki natsu kuma zaki nitsa kanki yanzu sannan kiyi abinda ya dace..” Ta k’arashe tana ware idanunta a fuskar Safeenar..

Cikin sauri Safeenah ke jinjina kai tana mai k’ok’arin saita bugun zuciyarta.. Lokaci guda ta koma kan Gado ta zauna tamkar marainiya...

Mommy ma ta saita kanta kafin ta dubi Safeenah tace “Nidake bamu gama magana ba, zaki sanar dani komai..” Tai maganar tana kad’a d’an yatsarta a Fuskar Safeenar..

Safeenah Ta lumshe idanunta tana jin sanda Mommy Ta isa ta bud’ewa Mu’azzam k’ofar..

Haka kurum yaji wani iri da yanayi da yaga Mommy ciki dikda k’ok’arin saita kanta da take.. Sai ya jingina hakan da iftila’in da ahalinsu ke fuskanta a d’an kwanakin..

Gaisawa sukai da Mommy kafin tace “Gwara daka k’araso.. Gata nan kowa yayi shiru ya daina kukan rashin Ikram amma ita bata daina ba.. Nayi nasihan nayi lallashin duk tak’i dainawa nace k’ila sai kazo.”

Haka kurum yaji bai gamsu da abinda Mommy tace ba abinka da Detective dukda cewa tin a waje Meema ta sanar dashi Addah Feenah nata kuka ta kulle kanta cikin d’aki, ya jinjina kai kad’an yace “Zan mata magana Mommy.. You can go now.. I think Musaddiq needs you..”

Mommy Ta jinjina kai kafin tace “Mu’azzam.. Thank you for bringing him home..”

Jinjina kai kurum yai ba tareda yace komai ba har Mommy Ta fice..

Cikin yanayin tafiyarsa yake takowa cikin d’akin, saida ya d’auki lokaci yana dubanta yanda ta tak’ure saman gado kanta kife saman gwiwa, a hankali yake takowa cikin d’akin.. Gefenta ya zauna har lokacin kanta na kife tana matsan hawaye..

Ya d’an fuzar huci yana shafe goshinsa kad’an, kana ganinsa kasan he must be completely stressed out.. Hannu yakai kaman zai tab’ata sai kuma ya janye hannun nasa yana mai d’an janye fuskarsa idanunsa a lumshe.. Jin alamun haka yasa Safeenah k’ara sautin kukanta..

Ya d’an rintse idanunsa kad’an kafin ya dad’a matsowa kusanta, hannayensa duka biyu yasa ya d’aura saman kafad’unta.. Kaman yace ta k’ara nan Ta kuma sake masa wani kukan..

D’an kauda kansa gefe yayi still yana rik’eda ita, kaman bazaice komai ba Sai kuma ya rungumota cikin jikinsa ga kukan nata dake k’aruwa “It’s okay Feenah.. Ya isa haka.. Ki daina kukan nan haka..” Yanda yake maganar tamkar wani d’an koyo sosai zai baka dariya..
Jin haka yasa Safeenah lafewa cikin k’irjinsa tana mai kuma sakin kuka.. Ba kukan tashin hankalin da take ciki takeyi ba.. A’a kukan Farin ciki da murna take yau Allah ya cika mata burinta Gata nan cikin jikin Mu’azzam d’inta kuma a matsayin matarsa.. Shid’in halaliyarta ne.. Cikin zuciyarta Ta furta _My Halaal_ .
Tina haka da tayi ya sanyata had’e hannunta ta rungumo bayansa sosai tana kuma kwantawa cikin jikinsa tana kuma sakin kuka...

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*04*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

K’aran da wayarsa tai ne ya sanyasa k’ok’arin zame jikinsa daga nata, Safeenah kam da alama bama taji sautin wayar ba har saida taji Mu’azzam na k’ok’arin cire hannuwanta daga rik’on da tai masa.Ta d’ago tana dubansa idanunsa naga fuskar wayarsa yana ganin mai kiran nasa, caraf itama ta sauk’e idanunta kan screen d’in wayar tasa.. Sunan Assad data gani ya sanya gabanta wani irin fad’uwa.. Tasan Assad amininsa ne sannan abokin aikinsa ne a CID Office.
Haka kurum taji wayar da Assad Ke masa nada alak’a da case d’in mutuwar Ikram..

“Excuse me, I’ve to take this call..” ya fad’i yana mik’ewa tsaye, lokaci guda ya tura dogon k’ofar glass da ya raba d’akin da balcony ya shige yana amsa kiran Assad.. Cikin sauri Safeenah tabi bayansa cikin sand’a ta d’an lab’e ta kasa kunnuwa tana san sauraron wayar tasa..

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “What do you mean Negative...?”

Daga d’aya b’angaren Assad yace “You heard me right, negative..”

Lumshe idanunsa yai kad’an kafin ya soma fad’i cikin b’acin rai “Assad kana so na koyar dakai aikinka ne.. you need to get ya act together, I have no time to babysit you..”

“Mai kake so nayi Mu’azzam. Ka bani location without going through the details.. Naje wajen and guess what.. Wannan location d’in is an open waje, nothing suspicious.. Ba kowa babu komai a wajen.. Ban San mai zanyi a wajen ba..”

Girgiza kai Mu’azzam yai cikin rashin yarda yace “No.. There must be something in that particular location,.. Danger ne ya bani location d’in nasan haka kawai bazai bani ba dole akwai dalili.. Look around, babu wani daba da mutane ke zama wajen, babu wani shago kodai wani abu..?”

Assad yai shiru yana duban wajen da babu ko alamun mutane kafin ya fuzar da huci yace “He played you.. Wasa dakai kawai yayi Mu’azzam.. There’s nothing suspicious here.. Ga Maleeka ma ta taho tare muke da ita.. But we couldn’t find anything..”

“Damn it..!” Ya furta yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una, idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a raina masa hankali.. Fuzar da huci yai kad’an kafin yace “I’ll give him what he’s asking .. I’ll play his games.. Ka gane ku bar location d’in zamuyi magana..”

Assad ya amsa masa da fad’in “Copy sir..” Yai maganan yana sarawa kaman Mu’azzam d’in na ganinsa..

Safeenah tana jin ya ida wayar tai saurin komawa mazauninta dikda cewa ba wai ta fahimci mai yake cewa bane cikin wayar amma kam ta tsinci wasu kalmomi kuma Ta fahimci bincike yake...

Saida ya tsaya ya ida abinda zaiyi cikin wayar tasa kafin ya dawo cikin d’akin, Safeenah tana ganinsa ta mik’e tsaye, fuska fal damuwa take fad’in “Are you leaving now..?”

K’arasowa yai kusanta hannayensa saman waist d’insa, ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai duba wristwatch d’insa “I have to.. Aiki na jirana..”

Rau rau tai da idanunta tace “But you just got here.. Can’t you stay a little longer..” Tai maganar cikeda shagwab’a

K’uri ya d’anyi mata kafin yace “Why..? Do you need something..?” Yanda Yai maganar yana bud’e idanunsa Sai ya koma mata Mu’azzam d’insa wanda a baya yake gwaleta a mafi akasarin lokuta.. Idan da Ta barsa ya gwansaleta sam bazata bari yanzu hakan ya kasance ba, shid’in mijinta ne kuma zatayi komai domin taja hankalinsa gareta.. Zatayi what ever it takes ta tabbata ta gina soyayyarta cikin zuciyarsa..

Matsowa ta kumayi kusansa.. A hankali ta isa ta d’aura kanta saman k’irjinsa, cikin raunanniyar murya tace “I need you here.. Please stay with me kaji..”

D’an kauda kansa gefe yai yana son tureta daga cikin jikinsa amma sai yaji ta sakalo hannayenta saman waist d’insa ta rungumesa sosai tana ci gaba da fad’in “Please stay..”
Tai maganar tana mai d’ago fuskarta idanunsu cikin na juna..

Bai iya tureta daga jikinsa ba sannan bai iya furta koda kalma ba saima samun kansa da yayi yana mai tallafe bayanta da hannunsa kad’an..

Inne Kakarsu mahaifiyar Daddy itace Ke k’ok’arin shigowa d’akin dashike Mu’azzam bai rufe k’ofar d’akin ba sanda zai shigo.. Safeenah tana hango Inne na dosowa d’akin Ta kuma mak’alewa cikin jikinsa dan tasan idan Inne ta gansu a haka zata hura wuta su tare a cen gidansu...

Aiko Inne tana hangosu haka sai bata shigo d’akin ba tayi juyawarta..
Saida suka kwashi mintoci a haka kafin Mu’azzam yai gyaran murya yace “Safeenah, I need to go now.. They are waiting for me..” Yai maganar yana mai cireta cikin jikinsa..

D’ago fuska tai tana dubansa kafin tace “How long will you take..?”

Ya d’an tab’e baki kad’an “I can’t say for sure.. It depends.. Kinsan yanda yanayin aikin namu yake..”

Ta d’an rausayar da idanu kad’an lokaci guda tana mai kuma rau rau da idanun cikeda shagwab’a “My Inspector, nasan yanda yanayin aikin nan naku yake, very dangerous..Sannan kana bada mahimmanci sosai ma aikinka... Please promise me you’ll take care of yourself.. Always..”

Yanda tai maganar sosai ya sanyashi jin sanyi can k’asar zuciyarsa, ya saki murmushi kad’an yana mai tallafo fuskarta da tafukan hannayensa, a hankali yake furta a hankali ya jinjina mata kai kafin yace “Zan iya tafiya..”

Wani irin dad’i da mamaki ne ya cika zuciyar Safeenah Wai Mu’azzam ne yake mata magana softly haka ba tareda ya gwansaleta ba harma tambayarta yake zai iya tafiya.. Dad’i ya mamaye zuciyar Safeenah tabbas lokaci k’ank’ani zata d’iba ta dasa soyayyarta mai tsafta cikin zuciyar Mu’azzam..
Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Zan duba Mamy first daga nan zan shige..”

Ta jinjina masa kai a hankali tana sakin murmushi.. Hannunsa guda dafe da b’angaren fuskarta yaje furta “You take care..”
Chapter 6 · 0% Book details