← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 175

Sashe 33

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assad ya d’anyi gajeren tsaki yace “Things are getting tougher here, tinda ka tafi.. And Chief Jaja ya bud’e mana wuta mu kawo Danger within 2 days... Jiya ya mik’a team report d’inmu office d’in Chief Superintendent a General meeting d’in da akai, and babu wani progress har yanzu and he was even insisting bamuda case against Danger.. Saifa da nai presenting final report d’inmu ne ya tabbata Danger’s involved toh shine ya hura mana wuta mu kawo masa Danger yanda ya shiga ya fita..Ga dukkan alamu so yake case d’in ta lalace a haka ba tareda an sami wani improvement ba.. And Danger is no where to be found.. Dik wani hideout da muke tinanin zamu samesa bamu samesa ba, duk wasu masu criminal records da muke tunanin zasuyi linking d’inmu to Danger still babu wani haske har yanzu..”

Fuzar da huci Mu’azzam yai yana tura yatsunsa a sumarsa da suke wet.. “That scumbag I’m pretty sure he’s up to no good again.. Babu wanda ya isa ya rufe case d’in matuk’a ina numfashi.. Sai mun Kai har k’arshe yana so ko baya so.. Assad yarinyar nan itace kad’ai key d’inmu.. Inada tabbacin Babanta kashesa akai ba ordinary accident bane da ya saba aukuwa.. They’re after her family, I’m pretty sure bazasu k’yalesu haka nan ba.. Ya kamata muyi monitoring duk wani abinda ahalinta ke ciki.. Sannan Kai zaka fara tinda ni bana nan.. Go there, find out everything about them.. Dik information d’in da ka samu nasan zai ma investigation d’inmu amfani.”

Assad ya jinjina kai kaman yana ganinsa “Copy Sir..”
Lokaci guda ya k’arada “Baka tambayeni mutuniyar ka Maleeka ba.. Ita kaw kullum cikin missing d’inka take.. Tana counting days har zuwa randa zakai Reporting back to work.”

Gajeren tsaki Mu’azzam yai yace “Banida lokacinku daga kai har ita..”

Assad ya tintsire da dariya dan dama tsokanan abokin nasa yai niyya.

Sallama sukai kafin Mu’azzam ya zauna saman gado rik’e da wayar yana fuzar da fuci.. Zama bai gansa ba, yasan da biyu Chief yasa aka dakatar dashi dan ya samu sauk’in cimma burinsa cikin sati biyun idan baya nan, yasan muddin yana nan sai yanda k’arfinsa ya k’are bazai tab’a iya stopping d’insa ba.. Fuzar da fuci ya kuma yana jin zuciyarsa na masa zafi.

A b’angaren Safeenah kaw kafin ta isa d’aki wayarta ce dake cikin jakarta tai ruri, Meema da fitowarta kenan daga shower taji sautin waya na tashi daga cikin jakan Feenah. Kaman bazata d’aga ba dan tasan bazai wuce Mommy ba k’ila sunyi waya da Inne. Bata shirya ma fad’an Mommy ba. Amma jin wayar ta k’ara ruri ya sanyata k’arasawa jikin jakan ta d’ago wayar tana dubawa. Lamba ce Babu suna..

Meema dai samun kanta tai tana mai sliding kiran da ake.. Lokaci guda ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba.

Daga d’aya b’angaren Barr Ameer ya murmusa yace “Kin zaci zaki gudu mun ne Safeenah.. Dik yanda kikaje sai na biki.. Bazan tab’a barinki ma D’ansandan nan ba Safeenah.. You are mine.. Ked’in tawa ce ni Barr Ameer.!”

D’if Meema ta katse kiran tana kuma duban wayar k’irjinta na wani irin bugawa. “Barr Ameer..?!” Ta nanata a hankali.

Daidai lokacin Safeenah ta turo k’ofa ta shigo da jik’akk’un kayanta sai rawar d’ari take.
Da mamaki take duban Meema da tai tsaye rik’eda wayarta. Ta soma saurin nufo Meemar tana fad’in “Meye kikai wani tsaye a wajen sororo haka.. And why are you holding my phone.. bani kayata..”

Saidai kafin ta mik’awa Feenah wayar saida ta tabbata ta goge kiran.. Feenah ta fuzge wayarta tana aikawa Meemar mugun kallo “Waye ya kira..?”

“Babu mana.. Naji kaman wayar tayi ringing ne nazo zan d’auka, nayi tinanin Mommy ke kira Kinsan tawa babu charge.. Nasan dole zata nemu..”
Meema tace tana mai bud’e suitcase d’inta.

Tsaki Feenah tai tana mai neman towel take fad’in “Sabida kin mata sallama sanda zamu taho Ko..”

Meema ta d’an tab’e baki tana duban ‘yaruwar tata. Sai sannan ta kula da jik’an dake jikin Feenar..

“Addah Feenah.. Ya haka..? Ya na ganki a jik’e..?”

Tsaki Safeenah tai tana mai nufa hanyar bathroom..

Dariya Meema Ta soma tana fad’in “Kardai horon watsa ruwa yai miki a sanyin daminar nan.. Amma wannan miji naki anyi bak’in mugu wllhi duk wani salon mugunta ya Sani.. Koda yake ba laifinsa bane dama D’ansanda ne ya karanci sharri Da mugunta.. Allah ya cecen wann karon ba’a had’a dani ba..”

Ko amsata Safeenah batai ba ta shige toilet kayanta.
**

Washe gari sassafe Safeenah ta nufi d’akin Mu’azzam, dan tasan ya fice sallar asuba. Tana shiga ta fad’a kan gadonsa ta lume cikin bargo ta lumshe idanunta kaman mai bacci. Tasan babu yanda za’ai idan ya dawo sallar asuba ya samu tana bacci d’akinsa ya koreta dole ya k’yaleta su k’arasa kwanan tare.

Aiko koda ya dawo yasha mamakin ganin Feenah na bacci saman gadonsa, bai tasheta d’in ba ya kwanta daga can gefenta dan jiya bai wani samu bacci ba kusan kwana yai yana tinani tin bayan wayar da Assad yai masa yanda zai b’ullowa al’amarin Danger da Chief Jaja wanda idan yayi wasa zai iya rasa case d’in mutuwar k’anwarsa da ya d’aukarwa mahaifiyarsa alk’awarin kafin ta farka daga wannan jinya nata da izinin Allah sai ya gano waye ya kashe mata d’iyarta. Hakan yasa tuni bacci yai awon gaba dashi.

Safeenah tanajin alamun bacci yayi gaba dashi ta mirgino ta dawo jikinsa, zuciyarta fari k’al ta mak’ale cikin jikin mijinta tana shak’ar k’amshinsa dake rikitata.. Baccin ne itama yai gaba da ita.. Ba ita ta farka ba sai wajajen k’arfe bak’wai da rabi na safe sabida iska da aka soma sosai alamun za’ai ruwa hadari ya rufe sama gaba d’aya.. Ta saki murmushi tana duban yanda Mu’azzam ya rik’eta sosai cikin jikinsa alamun shi kansa yana enjoying baccin nasa. Ta k’ura ma kyakkyawan fuskarsa idanu tin daga sumarsa da suke kwance luf har zuwa idanunsa da suma suke a rufe, ta gangaro da idanunta tana duban hancinsa zuwa lips d’insa.

Iskan da akeyi shi ya bud’e k’ofar d’akin.. Ajidde da Ta biyo corridor d’in dan zuwanta kenan, nan tazo zata shige k’ofar d’akin Mu’azzam dan kafin ka isa d’akin mahaifiyarsa sai ka wuce wasu k’ofofi ciki harda d’akin Mu’azzam.. Da mamaki take hangan k’ofar a bud’e ta tina sanda ta shiga zata masa sata ya kusa kamata.. Ta soma sauri tana fad’i cikin zuciyarta bari tai sauri ta shige k’ofar d’akin kafin ta hango wannan jakar tasa.. Tana tafe bata fasa lek’en d’akin ba aiko nan ta hango matar nan ta jiya data watsa mata ruwan magani zaune gefensa saman gado tana shafa sumarsa zuwa fuskarsa.. Ajidde ta saki baki da hanci tana duban ikon Allah.. Ji tai bakinta na furta “Kaga ‘yaniska.. Toh asirinku ya tonu tinda kuka mance k’ofa a bud’e..” Bata ida shan mamaki ba saida taga matar nan ta kifa fuskarta kaman dai sumbatar juna suke.. Jikin Ajidde ya d’auki rawa babu shiri ta kwasa a guje ta nufo parlor..

Tana k’arasowa tsakiyar parlorn ta saki wani irin azabebben k’ara wanda idan akwai masu bacci da basu tashi ba ma tabbas sai Sun tashi.. Ihu Ajidde take tana tsalle tsakiyar parlorn tana fad’in ta shiga uku.. Inne dasu Hindu dake kitchen suna karin kummalo Inne na monitoring nasu kaman ko Yaushe, babu shiri suka nufo parlorn..

Mu’azzam cikin bacci shima yaji ihun har tsakar kansa.. Ya mik’e yaga Feenah tareda shi itama da alama ta firgita da ihun da ake.. Cikin sauri ya mik’e yana janyo jallabiyar sa yana fad’in “Mamy.. Mamy na.. Something happened to Mamy..” Abinda yake fad’i kenan yana k’ok’arin zira rigar dan itace maras lafiya a gidan dole kowa yai tunanin jikinta ne ya tashi koma aka rasata gaba d’aya. Ko tsaya bi takan Feenah dake tambayarsa Ina zaije bai ba ya matsarta gefe kad’an ya nufo yanda yake jiyo ihun cikin sauri.. Tuni Feenah ma ta take masa baya tana mai rufa siririn rigar baccin nata da na saman.

Musaddiq ma dake bacci a nasa d’akin babu shiri shima ya fito a birkice..

Aunty Shemau da tayo rakiya wa Uncle Salman zai wuce Factory dan wataran da wuri yake zuwa, nan Suma suka soma jiyo ihu daga sashen Inne. Babu shiri suka nufo sashen suma duk a birkice dan a tinanin Shemau Nuratu ce Allah ya mata cikawa.

Harta Meema dake ta faman susa ta kasa bacci dan dama tanada allergy irin na daminan nan balle tazo gidan Gona ga dabbobi ga shuke shuke tuni allergy d’inta ya tashi.. Ta d’an samu baccin kenan itama ta soma jiyo ihun.. Ta fito rai b’ace tana soshe soshe..

Gaba d’aya aka hallara parlor ana duban Ajidde dake ihu tana tsalle idanunta a rintse.

Musaddiq kam daga nesa yaja ya tsaya yana jiran yaji ruwan da Ajidde ta b’allo wannan karon.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*20*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ikon Allah, wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan kowa na mamakin haukar yarinyar. Inne Ta k’arasa ta rik’eta tana fad’in “Ke Ajidde.. K’alau kike..? Lafiya kiketa zunduma ihu haka..? Ko wani abu ne ya faru..?”

Ajidde ta Ware idanu tana kallon mutanen da sukai cincirindo a parlorn Kowa ya zuba mata idanu. Ta kai dubanta ga Mu’azzam wanda yakai mak’ura wajen had’e rai kafin ta maidoda da dubanta ga Safeenah wacce ke tsaye tana aika mata mugun kallo ko ba’a ce ba kasan shak’e take da ita.

Inne ta dubi Mutanen da Ajidde ke duba Wato Safeenah da Mu’azzam, sai kuma ta maidoda dubanta ga Ajidden “Ajidde lafiya kike.. Wani abu ya faru ne..?” Ta tambaya tana mai tsareta da idanu.

Cikin sauri Ajidde ta jinjina kai alamun Eh.. Inne tace “Mai ya faru.. Ko wani abin ne ya sami Nuratu..?”

Ta girgiza kai a hankali tana duban Safeenah da har lokacin huci take tana aika mata mugun kallo ga Mu’azzam dake gefe shima yana aika mata razanannen kallo hannayensa hard’e ta baya.

Matsawa bayan Inne tai cikeda tsoro still idanunta naga Mu’azzam da Safeenah take fad’i a hankali “Inne Allah ne ya toni asirinsu..”

Inne ta kuma dubanta da mamaki “Asirin Su Wanene ya tonu..?”

Ajidde tai saurin shigewa bayan Inne tana lek’en Mu’azzam da Safeenah wanda kallon mutanen parlorn ya dawo kansu.
Chapter 33 · 0% Book details