← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 175

Sashe 150

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin dakatar da ita yai yana mai girgiza kai “No.. Don’t blame yourself, ba sabida ke Mommy ta mun haka ba. Dama ta jima da k’udirin haka cikin zuciyarta.. She never cared .. Duk kulawan da ta bamu a baya na k’Arya ne.. Sai kwanan nan na fahimci hakan..” Ya kuma sak’alo hannunsa ya d’aura nasa sama kafin ya d’aura hannayen nasu saman cikinta yana fad’in “And a wann ranan da Mommy ta cire cikin Safeenah a ranan na samu labari mai dad’i da yaye min wancan bak’in cikin cewa matar da nake tsananin k’auna tana d’auke da gudan jinina..” Ya d’ago idanu yana dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa kafin yace “Thank you.. For being mine Beautiful.” Ya k’arashe yana mai sumbatar hannunta.

Ta murmusa kad’an tana goge hawayen da suka gangaro mata. Lokaci guda yake furta “Babu wacce ta bani tausayi irin Safeenah.. She’s the one who’s been hurt the most here.. Abinda Mommy tai yayi affecting d’inta sosai.. She’s loosing her mind..”

Sadiya taci gaba da girgiza kai cikeda tausayawa, dukda cewa basa jituwa da Safeenah sann basu wani zauna tareda juna ba sosai taji tausayin abinda ya sameta, abinda ciwo ace kuma mahaifiyarta ce tai mata haka.. Lokaci guda take furta “Ta yaya uwa zata aikata wa d’iyarta mugun abu irin wann..!”

Mu’azzam ya girgiza kai kad’an kafin yace “Sadiya.”

Ta d’ago idanunta da k’walla ke cike tab tana dubansa dasu, lokaci guda yake ci gaba da furta “Bazan b’oye miki ba.. A halinda ake ciki yanzu, abubuwa basa tafiya daidai tareda ahalina.. Maganar da nake fad’a miki my family is a complete mess a halin yanzu..” Ya d’an ja numfashi kad’an yana furzarwa, lokaci guda yana jinjina kansa “Abubuwa da dama sun faru kuma suna kan faruwa...”

Jikinta ya kuma yin sanyi.. Ta matso kusansa ganin ya k’ura ma waje guda idanu, a hankali ta d’aura hannunta guda saman nasa “Are you alright.?” Ta fad’i a hankali.

Ya sakar mata murmushi kad’an kafin yace “Hey.. I’m not that fragile.. I’m good.. Bana so ki saka ma ranki damuwa a halinda kike ciki.. Komai zai daidaita in sha Allah.. And idan komai ya daidaita na miki alk’awari zan sanar dake komai..”

Ta d’an tsaresa da idanu kafin tace “I’m here for you.”

Ya jinjina mata kai yana mai janyota cikin jikinsa “I know, shiyasa nazo nan neman shelter... I hope za’a bani..” Ya k’arashe yana kasheta da salon k’aunarsa.

Jin hannunsa cikin rigarta ya dawo da ita daga duniyar tunanin da Ta tafi. Kaman wacce aka zabura tai k’ok’arin turesa tana fad’in “Mai kakeyi na shiga uku kasan ina muke kuwa.. What if Umma ko Aunty Larai suka fito suka taddamu a nan koma Asheer da Habeeb. Dan Allah kai hak’uri ka k’yaleni..” Tai maganar Cikeda shagwab’a.

Bai saketa ba bai daina abinda yake ba “Relax Beautiful I’m not doing anything I promise..” Ya fad’i cikin wane irin siga mai kashe mata jiki yana kuma shigar da ita jikinsa.

Turesa ta soma k’ok’arin yo nan Taji ya saki k’ara kad’an yana dafe wajen ciwonsa. Sai kuma ta razana ta soma basa hak’uri tana tambayarsa ko da zafi.

Dikda ba zafin yake ji ba amma yanda yaga dik ta damu yasa yaci gaba da yi kaman dai yana jin zafin ne “It hurts..!” Ya fad’i yana kuma tamke idanu kad’an.

“Da gaske..? Ko asibiti zamuje..” ta fad’I tana k’ok’arin mik’ewa.

Janyota yai yana fad’in “No ba sai munje ba, besides bazan iya driving ba..”

Ta jinjina kai a hankali tana dubansa lokaci guda tana kuma masa sannu.

Saitin kunnenta ya rad’a mata “A amince za’a barni na kwana.?”

Ta d’an turo baki gaba kad’an tace “Do I have a choice.. Amma nidai Allah saidai ka kwana kai kad’ai cikin d’akin ni kuma na kwana nan dan wllhi kunya nakeji mu kwana d’aki d’aya a gidan nan.. Kuma da sassafe zaka tafi kafin Umma tasan ka kwana a nan..”

Ya d’anyi gyaran murya yace “Ni fah patient ne aji tausayin Bawan Allah.. Ya za’a bar patient ya kwana shi kad’ai a d’aki what if emergency ya taso..?”

Shiru tai kaman bazatace komai ba Sai kuma tai rau rau da idanu tana dubansa “Haba mana Inspector...that’s not fair fah..” Ta fad’i kaman zatai kuka.

Ya kwaikwai yanda take magana kafin ya k’arada “I’m hungry Beautiful, amma banjin zan iya cin komai..” Ya fad’i yana d’an kishingid’a kad’an.

“What do I serve you.?” Ta tambaya tana dubansa.

Lips d’insa ya shiga turo mata yana fad’in “Some kisses will do..”

Pillow ta janyo ta d’an turesa dashi tana fad’in ita bata tab’a ganin irin wann patient d’in ba.

“Na kawo maka abinci.?” Ta tambaya tana dubansa.

Ya d’an tab’e baki kad’an had’ida girgiza kai “Im good, besides it’s late already..”

Ta d’an tsaresa da idanu kafin tace “No way.. You must eat something.. Nasan ka sha magani since you’re wounded.”

Ya d’an tab’e baki kad’an kafin yace “Banida appetite.. But since you insist anything liquid will do.”

A hankali ta jinjina kai kafin ta mik’e ta nufi kitchen ya bita da kallo yana murmushi. Lokaci guda ya zira hannunsa guda cikin aljihun wandonsa ya ciro coins guda biyu na black African team d’aya wanda ya samu cikin kayan mahaifinsa d’aya kuma wanda ya samu hannun Habeeb k’anina Sadiya.

**

Ita kad’ai sai safa da Marwa take cikin d’akin, ta kira wayan Hajiya Faty yafi sai abinda yafi amma Hajiya Faty bata d’agawa, mai hakan yake nufi..? Badai juya mata baya zatai taci amananrta ba lallai ya zama dole Ta fice a gidan Ta cimma Hajiya Faty ta karb’i documents d’inta tin kafin ta gudu da dukiyar, taci gaba da zagaye d’akin tana tinanin yanda zata fice daga cikin gidan, idan akwai ‘yansanda kaw hakan na nufin bazata iya ficewa ba kenan.. Meye abinyi..? Take ta soma jinjina kai tana furtawa a hankali “Ciwo.. Dole na k’irk’iri ciwo da zaisa a fice dani daga wann kurkukun.. Sann Musaddiq shine zai goyi bayan a fice dani..” Bata kai aya ba wayarta ya soma ringing.

Ta jinjina kai tana murmushi kafin Ta d’aga kiran “Yanzu nake tunanin nemanka.. Hajiya Faty bata d’aga kirana kuma BAT yana hannunta..”

Daga d’aya b’angaren Danger ya murmusa kafin yace “Haba Hajiya mai BAT .. Idan dan wann ne kar ki samu damuwa minti nawa ne na shiga har cikin gidanta na d’auko miki. Abinda kika mun a rayuwa ai bazan tab’a mancewa ba.. Ke kika bani jari da arziki har hark’an saida miyagun k’aayoyina ya bunk’asa..” Ta murmusa kad’an kafin tace “Da kyau Muttak’a.. Saima na dafe wann dukiyar kafin kaga abinda zan maka.. Munada saka hannun Abubakar Gamji akan takardun hakan na nufin dukiyar Ta zama nawa.. Hanyar gudu kawai muke nema yanzu idan yaso daga baya sai mu dawo muyi claiming dukiyar..”

Ya murmusa kad’an kafin yace “Kar kiji komai, zaki mallaki wann dukiyar idan har Sunana Danger.. Saidai mun sami matsala guda an kama babban yaronmu a police headquarters Wato Jaja..”

Mommy ta zaro ido kad’an tace “Garin ya hakan ta kasance..? Kai Muttak’a kar fah mutumin nan ya tona mana asiri..”

Dariya Danger yai kafin ya girgiza kai yace “Bai sanki ba.. Bai tab’a sanin ma waye nake aiki ba.. Idan akwai wanda ya sani toh ni kad’ai ne.. Iyakacin kalmar da ya sani shine akwai BAT amma baisan wacece Ked’in ba, saidai yakan kirani da wann sunan a akasarin lokuta..” Yai fasali kafin yaci gaba da fad’in “Zanje gidan Hajiya Faty na amso BAT..”

“Toh ni ya za’ayi na fice daga wann kurkukun da Mu’azzam ya rufemu, house arrest fah yaron nan yai mana.”

Ya kuma murmusawa kafin yace “A halin yanzu Ai ‘Yanuwan mahaifinsa yake ma kallon ‘Yantadda bake ba.. Dan haka mai sauk’i ne.. Ki bari da safe zanje gidan Hajiya Faty ma amshi wann sak’on Kema Sai ko tada ciwo da safe zan sanar dake yanda zamu had’e.”

Mommy ta jinjina kai tace “Na gode Muttak’a.. Sai naji daga gareka.”

Daga haka katse kiran tai tana darawa a hankali. Lokaci guda take furta “Akan na mallaki dukiyar nan babu abinda bazanyi ba kuma wanda bazan kawar ba.”

**

Tare sukai bacci cikin jikin juna, saidai kaman yanda yai mata alk’awari Umma bazata San yana gidan ba kiran asuba na farko ya gyara mata kwanciyarta ya sumbaceta kafin ya silale ya fice daga gidan. Ko da Sadiya ta farka sai tana ganin kaman a mafarki yazo mata, ya tafi ya barta da k’amshinsa. Ta lumshe idanunta tana mai shak’an pillown da yai matashi dashi, cikin zuciyarta take masa addu’an nasara da dacewa.

K’aran shigowar sak’o da taji a wayarta ya sanyata saurin janyo wayar tana dubawa. Shid’in ne ya turo mata sak’o kaman haka

_It is your smile that fills my world with pleasure.. I need nothing more in life than you being around me.. I love you so much Beautiful.. Take care of yourself and our unborn for me_

Tana ida karantawa ta saki murmushi a hankali tana mai kuma shigar da kanta cikin pillow. “I love you too my Detective.. Please be safe..” Ta furta a hankali
**

K’arfe takwas a Ofishinsu yai masa, ya jima sosai a k’ofar interrogation d’in yana tinanin abinda zai tadda ciki. Saida ya furzar da huci a hankali kafin ya tura k’ofar ya shiga.

Can ya hango Musaddiq tsugune ya tak’ure can k’asa kansa kife.. Sai ya soma tuna Safeenah ma ta shigo d’akin nan sanda Bincike ya fad’a kanta.. Tabbas wann ya kuma tabbatar masa da abinda yaketa gujewa yana k’in aminta.. Kaman yanda makashin mahaifinsa ka iya zama d’aya daga cikin ahalinsa haka nan makashin Ikram na cikin ahalinsa.. Hular Musaddiq d’in da ya tab’a tsinta a business location d’in Danger ya kuma tunawa.. Yai saurin rintse idanunsa yana mai kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na masa wane irin d’aci.

Saida yai k’ok’arin saita kansa kafin ya k’arasa wajen Musaddiq d’in. Fuskarsa a matuk’ar tsume. Ya tura masa kujera da k’afarsa yace “Tashi ka zauna.”

Musaddiq dake rawan d’ari ya d’ago da k’yar yana duban Mu’azzam d’in Sai yaga kaman an canza D’anuwan nasa ne. Jikinsa yaci gaba da kyarma cikin wane irin yanayi mai cikeda tsananin tsoro.
Chapter 150 · 0% Book details