← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 175

Sashe 47

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci guda ya kuma janyota cikin jikinsa sannan ya rufa masu lemar akansu.. Ta dubi hannunsa yanda ya rungumota ya rik’eta, zafin kalamansa akanta kurum take tunawa da wulak’ancin Sa take tunawa.. Lokaci guda taji wani irin k’arfi yazo mata.. Tai k’ok’arin turasa dashi da lemar tasa.. Saidai sam bai saketa ba saima dad’a matseta da yai.. Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Don’t get wrong ideas dik cikin acting ne..!”

Lumshe idanunta tai hawaye na gangaro mata.

Ganin tana rawar d’ari ya sanyasa zame jacket d’insa ya rufa mata.. Still saida ya sake tina mata cewa a cikin acting ne.

Ruwan na k’aruwa dole suka nufi mota, ya bud’e ya shigar da ita.. Nan wani mutumi mai hoto ya tsallako a guje yana tare Mu’azzam d’in.. Envelope ya mik’o masa yana fad’in “Yallab’ai hoto aka maku d’azu kaida Madam baku Sani ba.. Yayi kyau sosai bud’e ka gani..”

A hankali Mu’azzam yasa hannu ya amshi envelope d’in.. Lokaci guda ya soma zaro hoton kaman mai tsoron ganin hoton.. Fuskokinsu ya gani su duka biyun suna murmushi sanda yake ce mata ta nastu tayi acting d’inta da kyau idan tana son komawa gidansu..
Sunyi kyau sosai like a real couple.. Kud’in hoton ya zaro ya mik’a wa mutumin kafin ya saki tsaki a hankali ya tura hoton cikin aljihunsa.. Ya kaindubansa ga Sadiya dake zaune cikin Mota ta kifa kanta da alamun kuka take. Ya d’auke kansa yana sakin gajeren tsaki.. Lokaci guda ya shige cikin motar ya tada suka tafi.. Sam baiji dad’I ba dan babu wani abinda suka samu gameda Su Danger ko masu bibiyan Sadiya.

Suna isowa gida tai shigewarta tana matsan k’walla.

“My jacket.” Ya fad’i yana dubanta.

Babu musu ta cire ta mik’a masa abunsa kafin tai shigewarta. Shima shigewar yai nasa d’akin dan yin wanka dan duk a jik’e suke.

Yana cikin rage kayan jikinsa yaga hoton da akai masu a park.. Ya jima yana duban hoton, lokaci guda ya k’arasa dustbin zai disposing sai kuma ya tsaya kaman wanda ya tina wani abu.. Drawer ya janyo ya jefa hoton ciki kafin yai shigewarsa bathroom..

Yana fitowa daga wanka yaga kiran Assad na shigo masa.

Daga d’aya b’angaren Assad ke sanar dashi Sun sami wani clue regarding the search for Danger..

“Are you serious Assad.. Did you find his whereabout..?”

“No not really... But mun samu abinda zai iya leading namu to his hideout..” Assad yace yana juya flash drive d’in dake hannunsa. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “I’ll tell you about the details idan muka had’u.. Yanzu dai ya kamata muyi aiki akaine.. Ina zamu had’u..?”

“Let’s meet up here at my place..” Mu’azzam yace yana k’arasa shiryawa.

Assad yace “Alright zamu taho tareda Yusuf dan d’aya location d’in shi yaje yai spying mana..”

“Alright sai Kun k’araso..” Daga haka sallama sukai kafin ya ida shiri a gurguje ya fito ya nufi masallaci dan kiraye kirayen sallar magrib ake.

Yana dawowa daga masallaci d’akinta ya nufa ya tadda Ta ida sallah kenan tana k’ok’arin linke darduman.

Bata ko dubi yanda yake ba taci gaba da abinda take.

“My friends are coming over tonight, kar ki damu ba masu kud’i bane balle kice zaki samu wani attajirin cikinsu.. ‘Yansanda ne irina masu fafutuka.. So karki kuskura ki sauk’o downstairs har sai Sun bar gidan nan...” Daga haka Sa kai yai ya juya ya fice a d’akin..

Ta girgiza kai ba tareda tace komai ba. Zama tai nan saman carpet tana tinanin abinyi.. Take taji ya kamata Ta karanta Alk’ur’ani dan zuciya da karatun alk’urani ne kawai take samun nastuwa.. A hankali cikin tsanaki ta soma rero karatun ta cikin suratu Maryam daka dan dama ta haddace suran.

Bayan su Assad da Yusuf sun iso tuni sukai connecting na’urar aikinsu a nan parlorn gidan. Mu’azzam yai masu offering coffee da tea Assad yace “Tab Inaa wannan ai sai ku turawa.. ni wllhi yunwa nakeji.. Idan zan samu something solid I’ll be glad..” Bai kai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “The kitchen is right there Sai ka shiga ka girka dan dai nikam k’asan ban iya girki ba.”

“Toh matar gidan fah.. Haba Malam Officer gidan Amarya fah muka zo.. Ni wllhi kafin a fara aikin nan sai an bani abinci idan ba haka ba bazaku tab’a gane kaina ba..”

Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yasan da gangan Assad yai maganar nan kawai dan dai ya had’asa magana da yarinyar ne..

Car keys d’insa ya d’auka yana fad’in “Barin sayo maka a nearby eatery..”

“A’a wllhi.. No gaskiya bazanci na restaurant ba na Amarya nake so idan kuma ba rowar abincin gidanka zaka mana ba.. Ko ya kace Yusuf..?” Ya k’arashe yana duban Yusuf wanda tinda suka fara tattaunawar murmushi kurum yake yana k’ok’arin connecting computer.

Fuzar da huci yai kad’an yana aikama Assad mugun kallo “Damn you..!”Ya fad’i yana hayewa upstairs.

“Oho dai naji koma menene..” Assad yace yana darawa kad’an.

Mu’azzam na hayewa ya tadda karatu take. Ya d’an tsaya jikin k’ofa yana sauraronta. K’amshin nan nasa da taji ya tabbatar mata yana tsaye wajen. Ta dasa aya ma k’aratun nata kafin ta juyo a hankali. Cikin zuciyarta tai tsaki tace mutum kaman goyon maguzawa Sai ya ringa shiga waje babu sallama.

“Abokaina suna jin yunwa.. I told them ba’a dafa abinci a gidan nan amma sunk’i amincewa.. Can you cook something simple for them..?”

Jin bata amsasa ba ya sanyasa fad’in “Nasan kin San matsayin girman miji a wajen matarsa. So idan har kinada karatun addini kaman dai yanda naji kina karatun nan zakiyi abinda mijinki ya umarceki.. Idan kuma Bakiyi ba Kinsan mai hakan yake nufi.. And please do not embarrass me.”

Daga haka ficewa yai ya barta nan zaune ba tareda ta tankasa ba. Watau yanzu kuma da Ubangijinta zai had’ata bayan ya gama mata barazana da mission. Taji wasu k’walla masu zafi suna zuwa mata... Tasha jin ana cewa ko Wanne gidan Aure da nasa k’alubalen wata nata dangin miji ne wata uwar miji ne nata k’alubalen wata kuwa shi mijin kansa ne k’alubalen kaman dai yanda nata ya kasance dikda kuwa Auren nata ba mai d’aurewa bane. Tina cewa da tai koda auren na d’an lokaci ne shid’in mijinta ne kuma umarni yake bata ya sanyata mik’ewa ba dan taso ba. Ta nufo wardrobe d’in tana duba mai zata rufa akanta.. Wani shud’in mayafi ta d’auko yalwatacce ta rufa akanta kafin ta nufo k’asa ta shige kitchen d’in.. Tana jin hayaniyar su shida abokan nasa har tana mamaki ashe dama ana jin muryar sa haka.. Wata zuciya tace ai indai bincike yake kam tsaf zakiji muryarsa.. Ta tab’e baki kad’an kafin Ta nufi kitchen d’in.

Store ta soma dubawa taga store d’in shak’e da kayan abinci. Ga dangin su pasta da couscous.. Tai tinanin dafa masu abinci mai sauk’i kaman yanda yace. Couscous d’in ta d’auko ta dawo kitchen d’in ta bud’e fridge ta duba groceries nan taga gasu veggies sealed cikin leda irin yanda ake saidawa a super markets harda minced meat dasu sausage dik Suma sealed... Minced meat d’in ta d’auko kafin ta dafa white couscous tai garnishing d’insa da veggies sannan tai soma had’a masu sauce d’in minced meat d’in wanda za’aci white couscous d’in dashi..

Suna zaune parlor suna aikinsu k’amshi ke dakan k’ofofin hancinsu. Assad yace “Kai wannan k’amshi ai sai ya cika mana ciki kafin muci.. Gaskiya da alama Amarya ta iya girki..”

Gajeren tsaki Mu’azzam yai ya kuma duban Yusuf dake k’ok’arin saka flash jikin computer yace “Ina sauraranka Yusuf go ahead.”

Yusuf yaci gaba da fad’in “Kaman yanda na fad’a maku shi wannan footage d’in wajen security d’in da suke kula da restaurant d’in na samu bayan na shafe kwana biyu ina bincike ina tambaya people around the area ko sun tab’a ganin mai kama da Danger wajen.. Toh shine na samu har mutum uku suka ce Sun tab’a ganinsa sau kusan uku yana zuwa wannan restaurant d’in yana sayan abinci.. Da alama Danger yana son abincin wannan restaurant d’in.. Toh sai na tambayi CCTV Footage daga wajen securities bayan na sanar dasu matsayina da binciken da nake.. Bari mu gani gaba d’aya mu tabbatar..”

Suka jinjina kai a tare sanda Yusuf ya soma playin videos d’in har kashi Uku wanda yake tabbatar da cewa Danger ne yake zuwa Restaurant d’in sayan abinci dikda yana saka rigar sanyi mai hood dan kar a ganesa.

Sanda akazo daidai fuskar mutumin Mu’azzam yace “Stop. Yi zooming muga.” Yusuf yai kaman yanda yace d’in.

Jinjina kai yai yace “It’s him.. Danger ne.. So Ta tabbata yana zuwa wannan restaurant d’in tinda har yaje sau uku..”

Yusuf ya jinjina kai kafin Assad y ciro wani flash drive d’in yace “Wannan kuma wani super market ne da aka ga wani mai kama dashi once.. But nima I’m not sure idan shi d’in ne domin wannan kaman yafi Danger girman jiki saidai kuma idan camera ce ta k’ara masa girman jikin.. Footage d’in na k’ofar super market d’in ne wanda fuskarsa ta d’an fito amma is not that clear..”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Saka mu gani..”

Lokaci guda Assad ya saka ya soma playing..

“Wait.” Mu’azzam ya dakatar dashi yace masa yai zooming.. Lokaci guda ya k’ura ma lambar motar da mutumin zai shiga idanu a nan k’ofar super market d’in..Lambar motar tayi daidai da motar da aka basu bayanan cewa itace motar data buge Baban Sadiya.

Mu’azzam ya shiga jinjina kai yana fad’in “That Scumbag.! Shi ne.. Shine ya kad’e Babanta.. Danger ne ya kad’e mahaifin Sadiya..!”

Ya shafa sumarsa a hankali yana jin zuciyarsa na masa zogi.. Cikin sauri Yusuf ya shiga d’aukan plate number d’in motar dan suyi comparing da wancan...

Assad yace “Yanzu ya tabbata Danger yana nan cikin garin nan yana hunting dik wani wanda yakeda alak’a da case d’in nan.. By all means yake so ya rufe bakin kowa.”

Ya dubi Mu’azzam yace “Surely Danger will come after your wife..!”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “I’ll kill him if he attacks her..” Yai maganar yana murza hannunsa a hankali.

“What’s plan now.?” Assad ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in.
Chapter 47 · 0% Book details