← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 175

Sashe 7

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jinjina masa kai a hankali su duka biyun suna masu sakar ma juna murmushi kafin Mu’azzam ya fice..

Yana ficewa Safeenah ta fad’a kan gado tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali.. Ta janyo pillow Ta kwanta ciki tana shafe fuskarta yanda Mu’azzam ya d’aura hannunsa.. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin bazata tab’a bari wani abu ya datse mata wannan farin ciki da take ciki ba.. Zata kare aurensu no matter the cost..
Tana tsaka da tinanin wayarta dake gefen bedside Ta soma ruri.. Tai saurin d’agowa tana duban mai kira, lamba ce Babu suna..
Batasan dalili ba amma ta tsinci kanta da fad’uwan gaba... A hankali ta d’aga wayar tana mai k’arawa a kunnenta..

Lokaci guda ta mik’e tsaye sanda take receiving wayar “Barrister Ameer..Ina ka samu sabuwar layina..?”

Daga d’aya b’angaren mutumin data kirada Barr Ameer murmusawa yai kad’an kafin yace “Ba damuwa bace sanin yanda na samu sabuwar layinki... Kawai na kira ne na miki murnan aure tinda ba’a gayyace mu biki ba..”

Murmushin da yafi kama yak’e ta d’anyi kafin tai masa godiya Ta muka rok’esa da kar ya sake kiran layinta bata san duk wani abinda zai haifar da zargi tsakaninta da mijinta... Barr Ameer yace babu komai kawai dai dama ya kira ne ya mata murna tinda Allah bai k’addara shid’in zai aureta ba dukda tsananin k’aunarta da yake..

Barr Ameer Dikko yaso Safeenah sosai tun tana makaranta a Salford, da aure yaso Safeenah bada wani shashanci ba, tun Safeenah bata kulasa har saida yayi amfani da dabaru nasu na lauyoyi wajen iya tsara zance da kuma tsananin nacinsa da soyayyar da yake mata har dai ta soma kulasa, bata b’oye masa d’anuwanta Mu’azzam take so ba dukda kuwa cewa a lokacin bata gaban Mu’azzam d’in.. Barr bai karaya ba yace zai gwara luck d’insa.. A haka dai har Safeenah ta d’an basa dama cikin rayuwarta sabo ya shiga tsakaninsu sosai dukda cewa ita ba irin son da yake mata take masa ba, zuciyarta na Mu’azzam ne batajin zata iya had’a soyayyarsa da wani cikin zuciyarta, Barr Ameer yasan da haka amma bai damu ba a cewarsa nasa sa’an yake gwadawa.. Koda aka saka aurenta da Mu’azzam kuwa tuni tai cutting ties da Barr, ta yanke duk wata alak’arta dashi, dan sabida shi ma da nacinsa Ta canza layinta..

Bazata tab’a mancewa da furucin da Barr yai mata ba wata rana suna firan Mu’azzam shida Ita, tana sanar dashi irin soyayyar da take wa Mu’azzam d’in, Barr yace ‘Na saka a raina zaki zauna a gidan Mu’azzam ne na d’an wani lokaci tamkar dai kina a GIDAN ARO ko bajima ko na dad’e bazan tab’a cire rai ba, nasan watarana zaki dawo gareni..’ Batama d’auki maganar tasa da mahimmanci ba dan tasan irin son da takewa Mu’azzam zata iya shanye duk wani miskilancinsa ta tabbata aurensu ya d’ore har k’arshen rayuwarsu..
A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai kuma kwanciya saman gado..

Mu’azzam kaw a parlor ya hangi Inne Kakarsu da Daddy harma da Mommy, yanda yaga Mommy da Daddy sun gurfana ya tabbatar masa assembly Inne take, shi sam bai zaton ma bata koma Adamawa ba, hango Musaddiq da yayi duk’e gaban Innen ya sanyasa k’ok’arin janye jiki da niyyan ficewa ba tareda wani yayi noticing d’insa ba dan yasan fitinar Kakarsu..

Yana cikin sand’uwa zai fice ya sinkayo muryarta da girma ya d’an kama tana fad’in “Kai Kai Dansanda ina zakaje..? Zo nan kaima akwai namu da kai.. Bari na gama da wannan shashashan d’anuwan Naka..” Ta k’arashe tana dungure kan Musaddiq da yai zaman rak’umi gabanta, ya kuwa cika yayi fam kaman zai fashe...

Dan dole Mu’azzam ya dawo ya tsaya daga bayan parlorn can wajen staircase..

Inne Dattijuwa da sam bazaka bata shekarun da take ba sabida kyaun k’ira da Allah yayi mata, ta dubi Musaddiq dake duk’e gabanta k’iris ya rage bai fashe ba Ta kuma dungurinsa tana fad’in “Sokon banza, ai bansan shashashancinka kawai kake a nan ba.. Mu dik zuri’armu babu mashayi baza’a fara samu cikin jikokina ba.. Kana jina Gida zan tafi dakai cen Fufore kaje kayi noma da kiwo naga alama gata ne yai maka yawa a nan shiyasa ka sangarce..”

Musaddiq ya d’ago yana mata wani irin duba, Ta kuma dungure masa kai tana fad’in “Daina kallo na da wannan jajayen idanun naka.. Sabida azaban shan kayan maye jibi dik yanda kayi duhu ka lalace..”

Mommy ta k’walolo idanu waje jin Inne tace zata tafi da Musaddiq Fufore yaje yayi noma da kiwo, ta dubi Daddy tana jiran taji mai zaice amma shiru baice komai ba...

Musaddiq ma ganin iyayensa ba suce komai ba ya sanyasa soma girgiza kai yana fad’in “No.. No way.. Gaskiya bazan koma Gidan Gona ba..Ai dai kinsan ina makaranta Inne..”

Ta kuma Kai masa bugu a kafad’arsa yana karewa, lokaci guda take furta “Rufe mun baki shashasha.. Yo makarantarka har wani makaranta ne, inji kaje can k’asar wajen ka gama yawon shashashancin Naka babu abinda ka tsinana, na tabbata nan d’inma ba abun arziki kake ba.. Idan ba an rabaka da shashashan abokan naka dake nan ba bazakayi hankali ba.. Ni tuntuni nasan cewa shashashancinka yakai har ruwan kwalba kake sha da ban Barka ka girma a bariki ba..” Ta dubi Daddy da kansa Ke kife k’asa tace “Kana jina Marwan, yaron nan zamu tafi tare.. Kayi magana da D’anuwaka Salmanu tinda shike kula da Gidan Gonar, ya samar wa Gidado aiki a nan Gidan Gonar.. Ya dinga kula da shanun dake gidan gonar..”

Musaddiq baki sake yake dubanta shaye da tsananin mamaki.. Katseta yayi da fad’in “Amma Inne kinsan ni ba karatun kula da Dabbobi nayi ba koh..I’m not a Vet Dr..”

Carbinta da ko yaushe yake nad’e hannunta wannan karon ta warb’a masa tana fad’in “Rufe mun baki idan bakayi karatun kula da dabbobi ba ai ka gada kiwo... Ubanka ma ya gada.. Gidan Gonan da Kakanka ya mutu ya bari arzikinsa kake ci..”

Ta d’ago tana kuma duban Daddy “Kana jina ka kira Salmanu ka sanar dashi tun kafin mu koma Adamawa..”

Jinjina mata Kai Daddy yai yace “Za’ayi yanda kikace Insha Allah Inne..”

Mik’ewa ta soma k’ok’arin yi ta dubi Mu’azzam tace “Kai kuma shige muje..”

Cikin rashin yarda da batun Musaddiq Ke fad’in “Haba Daddy.. You can’t be serious.. Daddy this is unfair.. Dan Allah kar ka bari hakan ta kasance..” Ya d’ago ya dubi Mu’azzam dake k’ok’arin bin bayanta yace “Officer dan Allah ka mata magana, you’re her favorite zata saurareka..” Ya k’arashe yana bin bayan Mu’azzam d’in cikin gudu gudu...

Saitin kunnensa Mu’azzam Ke fad’i a hankali “Hakan yafi idan dai halinda zakaci gaba dayi kenan a nan..”

Musaddiq ya girgiza masa kai yace “Wllhi na daina..”

“Proof it then..” Mu’azzam ya fad’I yana mai bin bayan Inne..

Cikin sauri Musaddiq ya take masu baya..

Suna ficewa Mommy Ta dubi Daddy tace “Yanzu bazakace komai ba.. Haka zaka zuba ido Ta tafi dashi..”

“Mai kike so nace Hajara.? Nace mata ba haka ba.. Ko kin mance cewa matar nan mahaifiyata ce.. Sannan idan hakan shi zaisa d’anki ya dawo cikin hayyacinsa I’d welcome the idea d’ari bisa d’ari.. If he stays here babu wani abinda zai tab’uka ma rayuwarsa..”

Shiru Mommy tai tana mai kwantar da kai, hawaye ya ciko idanunta, k’ok’arin saita kanta tai sanda Daddy yaci gaba da fad’in “He’ll be better off there, tinda a nan dai kina gani yanda muke tare tare dashi, idan aka canza masa environment d’in na d’an wani lokaci k’ila Allah yasa hakan ya zamto sanadin shiriyarsa... Muyi masa addu’a kawai da fatan hakan ya zamto alkhairi..”

Mommy dai bata ce komai sai mik’ewa da tai ta haura sama tana tinanin hukuncin cikin ranta.. Ita tanadinta shine Nuratu ta fice mata daga gida tayi nesa da ita da ahalinta ba Wai d’aya daga cikin yaranta yai nesa da Ita ba..

Daddy ya bita da kallo yana mai kwantar da kansa cikin kujera had’ida lumshe idanunsa kad’an..

Inne na gaba Mu’azzam da Musaddiq na biye da ita, Musaddiq naci gaba da magiyan cewa ta janye k’udirin ta..

“Kai Gidado (Kaman yanda take kiran Musaddiq d’in) bari kaji na fad’a maka.. Ko Marwan Ubanka bai isa ya hanaka komawa Gidan Gona ba.. Na riga na gama magana ehe, bazan zauna inaji Ina gani ka zame mun zakka ba.. Banyi shirin sallameka ba.”

Musaddiq ya dubi Mu’azzam da yai kaman bashi a wajen a hankali kaman mai rad’a yake furta “Aren’t you gonna say anything.. Talk to her please.. She can’t do this to me... I mean she’s turning my life into a nightmare.”

Bai Kai aya ba yaji sauk’ar ‘ya’yan carbi a k’eyarsa, yai saurin sosawa yana d’an sakin k’ara.. Kunnensa ta kamo dikda ratan tsawo dake tsakaninsu.. Nanma k’ara Musaddiq ya saki yana k’ok’arin k’watan kunnensa..

Inne Ta dage k’arfinta ta matse kunnen tana fad’in “Ni na gayyaceka d’akina..? Maza a k’ara gaba.. Fita ka bani waje jarababbe..” Ta k’arashe tana turasa waje..

Dik tsimewan da Mu’azzam yake saida yaji dariyar Inne da Musaddiq ya taso masa.. Ya sunkuyar da kansa gajeriyar murmushi saman fuskarsa..
Inne na hankalce dashi sannan sosai taji dad’in ya d’an saki ransa dan zata iya cewa tinda tazo bataga murmushinsa ba.. Abubuwa da dama Sun faru dashi d’in.. Ga mutuwar k’anwarsa bayan jinyar da mahaifiyarsa Ke ciki...

Musaddiq na ficewa Inne ta K’araso ta zauna bakin gado, tai nuniwa Mu’azzam da kujerar dake fuskantar gadon “Modibbo zauna kaji muyi magana.”

Ba musu Mu’azzam ya k’arasa ya zauna yana “Inne na zata kin tsufa a Adamawa..”

Ta tab’e baki kad’an tace “Ina zanje bayan ban kai maka Matarka d’akinka ba..”

Ba zata yaji maganan nata ya d’ago yana dubanta, dan shi harga Allah ya mance da wani maganan tariyar Safeenah..

“Kana jina.. Yau d’in zuwa dare.. Kokuma a barshi gobe yarinyar nan ta tare a d’akinta.. Zaman baida wani amfani..”

D’an tura yatsunsa yai kad’an cikin sumarsa kafin yace “Inne Wai dama da dai an barshi sai zuwa gaba kad’an..”
Chapter 7 · 0% Book details