← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 175

Sashe 35

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assad ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Bazaka yarda da abinda zan fad’a maka ba.. Amma bari na baka labarin komai in details..”

Mu’azzam ya k’urama window idanu yana sauraren Assad dake labarta masa yanda auren Sadiya da Alhaji Isyaku zai kasance a gobe Asabar..

Wani irin gumi ne ke tsartsafowa Mu’azzam, Wai gobe auren yarinyar da Alhaji Isyaku “Wait Assad mutumin nan ba shine ya dinga sanar damu munanan halayyar yarinyar na kwad’ayin abin duniya da bin maza masu abin duniya ba.. Ba shine ya sanar damu irin shaidar da akai ma yarinyar na rashin kamun kai a unguwar ba.. Ba shine ya rabata da d’iyarsa ba..? Idan duka yayi wad’anann abubuwan Maiyasa zai zago yace zai biya mata d’inbin bashin dake kansu idan za’a bashi aurenta.. Ni fah ban yarda da mutumin nan ba Assad, idan baka mance ba bincikenmu ta Kansa ya fara biyowa kafin mu isa ga yarinyar domin kuwa Danger sunansa ya soma mentioning mana.. Assad I won’t let this happen.. I’ll stop this marriage from happening no matter the cost.”

Assad ya nusa yace “Bashin zaka biya masu kokuwa d’auke yarinyar zakai..? Muazzma kar fa ka mance You’re still on your suspension, you’re not allowed to go to work ko kuma Kai wani abu ba tareda umarnin NPF ba.. Nasanka Mu’azzam, I know exactly how your mind works.. Don’t get yourself into another trouble.. Mubi hanyar da ya kamata musan yanda zamu b’ullo wa al’amarin..”

Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Idan bazan Yi da yarda da amincewan NPF ba then I’ll have to do it my way..”

Daga haka katse kiran yai ya k’arasa shiryawa a gurguje yana tina Wai auren gobe gobe ne.. Baisan mai zai aikata ba, baisan mai zai iya faruwa ba. Ya San yayi nisa da garin. Hakan na nufin baisan ko zai iya dakatar da wannan aure ba..

Yana ficewa bai zarce ko Ina ba sai Factory.. Nan ya nemi ganin Uncle d’insa Salman. Sectary d’insa ya ma Mu’azzam iso..

Mu’azzam yana zaune yana k’are ma Factory d’in kallo, yana kallan workers sai shige da fice suke, yakai dubansa ga office d’in Uncle Salman wanda Office d’in Mahaifinsa kenan a baya.. Ya tina sanda yake k’arami mahaifinsa na zuwa dashi Factory d’in wasu lokuta, lokaci guda kuma ya tuna a wannan wajen ya rasa Mahaifinsa.. Ya tina sanda aka kawo masu gawan mahaifinsa a daskare ya k’ank’are bayan yayi jamming kansa a D’akin K’ank’ara da ake aje nama.. Lokaci guda yaji wani irin rauni na ziyartar zuciyarsa.. Sam sai yaji baison kasancewa cikin Factory d’in.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa kenan Sectary d’in Uncle Salman ya k’araso yai masa iso yace ya shiga.

Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin ya nufi office d’in.

Can saman kujerar mahaifinsa ya hango Uncle Salman yana zaune yana juyi cikin kujerar.. Wannan murmushin tasa saman fuskarsa.

“To what do I owe the honor..?My dear Nephew..” Ya k’arashe yana mai daidaita zaman nasa saman kujerar lokaci guda ya nunawa Mu’azzam d’in kujera mai duban table d’insa.

Mu’azzam ya k’araso ya zauna “Uncle, Barka da rana..” Ya fad’i yana mik’a masa hannu alamun musabaha.

Babu musu Uncle Salman ya mik’a masa hannu suka gaisa kafin yace “Har ka gama da commotion d’in da ka tayar a gidan..?”

Mu’azzam ya fahimci mai Uncle Salman yake nufi amma Sai ya kawar da zancen da fad’in “Uncle ever since my father passed away, ban tab’a tambayar wani alfarma daga wajenka ba.. Wannan karon nazo na tambayeka alfarma If I’m really your nephew..”

Gyara zama Uncle Salman yai yana duban Mu’azzam d’in wanda ga dukkan alamu magana ce mai girma yazo masa da Ita. Sannan babu tsoro ko kad’an cikin idanunsa wanda kusan ko yaushe idan ya dubi idanun yaron abinda yake iya hangowa kenan.. Rashin tsoro.

Ya kuma gyara zamansa kafin yace “Allah yasa ba Kud’i kazo nema ba dan idan kud’i ne zan iya cewa wanda Sirkinka ke tara maka yayi yawan da har zai iya fin nawa. You know you’re lucky Mu’azzam, dikda ka zab’i career wanda ba wani kud’in arziki zaka tara da wannan career d’in Naka irin D’ansanda, You still have your inheritance a wajen Baban matarka.. Saidai kuma idan kaima baka yarda dashi bane..”

Mu’azzam ya d’an murmusa kad’an kafin yace “I trust Daddy with my life.. Ko mai zaiyi da dukiyata na yarda dashi d’ari bisa d’ari kuma na yarda bazai tab’a yin abinda zai cutar dani ba.. Kar ka mance Wannan shine karo na farko da zan tambayi alfarma daga wajenka, Uncle Salman. And inaso ya tsaya between us.. Juts the two of us.. Let’s call it uncle to nephew gift tax..” Ya k’arashe idanunsa akan Uncle Salman d’in, gajeriyar murmushi wacce yake yinta da gefen bakinsa saman fuskarsa.

Lokaci guda ya kuma gyara zamansa cikin kujerar kafin yaci gaba da fad’in
“If you consider me your Blood, Uncle.. Zaka min wannan alfarmar.. Just this once..!” Wannan karon gumi ne ke gangarowa daga cikin gashin sa zuwa goshinsa sanda yai maganar.. Kana gani zaka fahimci har cikin zuciyarsa yake maganar.

A hankali Uncle Salman yake jinjina kai tamkar wanda ya tina wani abu yana duban Mu’azzam d’in wanda shima dubansa yake.

“Alright fine.. Yes.. Zan maka wannan alfarmar my dear nephew, and you have my word it will stay between us.. Babu wanda zaiji, not my mother, not my brother, not even my wife..”

Mu’azzam ya sakar masa murmushi da gefen bakinsa su duka biyun suna duban juna “Thank you.. Uncle..” Ya fad’i still yana dubansa.

A hankali Uncle Salman ya jinjina masa kai shima murmushin ne saman fuskarsa.

**

Aunty Shemau ta d’an girgiza kai tana mai saita zaman wayar a kunnenta “Wai dama Aunty Hajara kinaso kice min Safeenah da Meema basu sanar daku zuwan nasu ba.. Toh mai Daddy yace.?”

Mommy ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Wllhi nasan bazai wuce shawarin Meema ba dan Safeenah dai bata amfani da k’wak’walwarta sai abinda Meema tace shi takeyi.. Tin jiya Daddy ke fad’a Maiyasa ba’a sanar dashi ba sai bayan Sun tafi. Nadai samu nace munyi ta neman wayar Office d’insa ance yana meeting nasa wayar kuma bata shiga.. Sannan da nace Mu’azzam ne yace saidai Safeenah taje can ta samesa sai baice komai ba, Kinsan wannan d’aniskan yaron yacce kika San ya lashe zuciyar Alhaji ne.. Duk abinda za’a ce indai Mu’azzam ne bai cewa komai.. Sami’ina wa’ad’a’ana ne. yanda kika San ya masa asiri wllhi.. Wani irin so yake ma Mu’azzam wanda tuni ya rufe masa idanu baya ganin laifinsa duk kalan laifin da zai..”

Aunty Shemau Ta nusa tace “Yanzu dai Kakar tasu zata masu section a nan, jarabebbiyar tsohuwa.. Kuma sanin kanki ne Aunty Hajara zaman Mu’azzam a nan ka iya kawo mana cikas..”

Mommy ta share gumin dake goshinta tace “Dik Safeenah ce da jarabar tsiyarta ta ja mana, amma inada tabbacin zaman Mu’azzam a Fufore bazai yuwu ba domin kuwa bazai tab’a barin aikinsa ya tare can ba.. Kafin ya ankare sai mun Kai uwarsa rami..”

Aunty Shemau tace “Bakida wannan matsalar Aunty Hajara.. Aiko maganin Kyallu zai mata aiki mahaukaciyar yarinyar dake tareda Nuratu Itace zatayi ajalinta..”

Suka shek’e dariya a tare kafin Aunty Nuratu taima Mommy sallama, Mommyn na cewa Ta saka mata idanu akan yaranta.

**

SULEJA

A daren ranan ma iya cewa Sadiya kwana zaune sukai daga ita har mahaifiyarta, Umma na saman sallaya tana kai ma Ubangiji kukansu yayinda Sadiyar ta kasa tab’uka komai dan tuni zazzab’I mai zafi ya rufeta tsaban kuka da tsananin tashin hankalin da take ciki.. Muassman idan Ta tina Washe gari Wai Ita d’in Ta zama Matar Alhaji Isyaku Baban Aminiyarta Sabeera.. Haka ta tak’ure cikin bargo tana rawar d’ari dikda tasha pcm amma kaman bata sha komai ba.. Tak’i daina Kukan tak’i taci komai.. Kallo guda zakai mata ta baka tausayi. Lallashin duniya Umma tayi amma abu yaci tura haka dole ta hak’ura ta fawalla wa Ubangiji lamarinsu dan shi kad’ai ne zai iya kawo masu d’auki a halin da suke ciki..

Washe gari sallar asuba ma da k’yar Sadiya ta tashi tai, ko k’wakk’waran tsayuwa bata iya yi sabida yanda take jin jikinta babu k’arfi.. Haka ta jima saman sallaya tana kai ma Ubangijinta kukanta..

Wasu almajirai ne sukai sallama rik’eda manya manyan kwalayan juice da dangin ruwan gora da dai abubuwan tab’awa irin na tarban biki.. Dikda Umma ta hanasu shigowa da kayan hakan bai Sa Almajiran sun fasa dire masu kayayyakin ba..

Sadiya tana jiyo yanda Umma ke fama da almajiran kukanta ya k’aru.. Shikenan da gaske yau ne aurenta da Alhaji Iskyaku.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*21*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Rana ce mai tsayi ta kasance a gidansu Sadiya, wajen Sadiya da mahaifiyarta. Ga duk wanda ya sansu zai fahimci tashin hankalin da suke ciki ya ninka wanda suka shiga a lokacin da Sagir ya tafi ya bar Sadiya a ranan bikinsu. Aure ne da basu san Mecece makomar auren ba. Iyakacin abinda suka sani shine K’addarar su rubutacciya ce tuntuni. Kuma bazasu tab’a tsallake K’addarar da Ubangiji ya gindaya masu ba. ‘Rabbi yassir wala tu’assir’ shine kad’ai abinda bakin Umman Sadiya ke iya nanatawa a wannan rana mai matuk’ar tsawo a garesu.

Wai abin mamaki saiga Tabawa gidansu Sadiya harda d’ibo masu kid’an k’warya..

Da baya da baya ta shigo gidan tana tik’an rawa, tin daga lungun ma take tik’an rawa har suka iso gidan..

Baki sake Umma ke dubanta da tsananin mamaki. Tabawa kaw ko ajikinta, sai tik’an rawa take tana sabada harda k’awayenta ‘yan rakiya su Asabe mai kayan Koli.

Umma ta zuba tagumi tana duban Tabawa da k’awayenta daketa faman juya mazaunanai suna tik’an rawa. Masu kid’i da rawan da Tabawa ta kawo kaw tuni yaja hankalin mutane akai cincirindo a gidan.

Tabawa taci d’amara ta shiga rabon drinks da ruwa ma bak’i harda snacks danginsu cake da donuts Tabawa tazo dasu kwali kwali tana rabo wa mutane.
Chapter 35 · 0% Book details