← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 175

Sashe 123

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya murmusa kad’an sai kuma ya girgiza kai yace “Bansan komai gameda wann Syndicate d’in ba.. BAT yana nufin Babbanmu A Tushe.. Ko kuma nace maka Boss At the Top.. Kaje ka nemo shi Mu’azzam.. Ka nemi BAT duk yanda ya shiga ya fita.. Idan ka kamo shi ka gama cin nasara.. May God be with you, Dear Friend..” Daga haka Sa kai yai ya shige Mu’azzam yabi bayansa da kallo.

Furzar da huci yai a hankali yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. A fili ya furta “BAT.!” ‘Is this another mission.?’ Zuciyarsa tai masa wann tambayar. A fili ya kuma furta “Where are you Danger..? Ni da kai ya kamata mu sake had’uwa..!” Ya k’arashe yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. Lokaci guda ya zira coin d’in cikin aljihunsa kafin yasa kai ya fice yana jin wayarsa na ruri. Ya d’aga yana amsa kiran Assad.

**

A sace Safeenah ta d’auki car keys Ta fice daga gidan dan dama Mommy ta mata kashedi Ta hanata fita ko k’ofa sann ta k’wace mabud’an motar ta. Saida ta tabbata Mommy ta Shige wanka kafin ta saci k’afa ta fice.

Bata zarce ko ina ba sai gidan Mu’azzam.

Patrick ya ganeta saidai da mamakinsa wann karon bata masa hauka ba. A mutunce ta masa magana harda cewa ba shiga zatayi ba sak’o tazo badawa ya shiga yai mata iso da uwar D’akinsa.

Patrick ya amsa mata kafin ya nufi cikin gidan.

Sadiya na tsaka da bacci taji ana knocking.. Ta mik’e tana mutsuka idanu lokaci guda tana duban agogon dake manne Parlorn, tana Mamakin yanda bacci ya saceta nan da nan gashi har ta jima tana bacci nan wajen. Gashi baccin ba wani mai dad’i tai ba, bacci ne da babu komai cikinsa face wasu irin mafarkai sarara marassa kan gado.. Gashi ta farka da wani irin azabebben ciwon kai.

Nan ta sinkayo Muryar Patrick yana kuma knocking. Da k’yar ta mik’e tana jin duk jikinta ya mata nauyi.. Ita sai lokacin ma take tuna yau ko azkar na bayan sallan Asuba bata samu tayi ba, duk hankalinta baya jikinta. Ta mik’e tana fad’in gata nan zuwa.

Haurawa sama tai Ta d’auko mayafi ta rufa kafin ta k’araso ta bud’e k’ofar.. Nan Patrick ke sanar da ita ana sallama da ita waje.

Ta d’an rage girman idanunta tana dubansa cikeda mamaki “Ni kuma sallama Patrick.. Ni kaw wa na sani a nan..?”

Patrick yace “Matar Oga ce da take gidan nan da..”

Yanzu kam ta fahimci Safeenah ce tazo. Ta d’an lumshe idanunta kad’an tana k’ok’arin saita kanta dan saida taji gabanta ya fad’i da Patrick yace Safeenah ce mai sallama da ita, ta shiga tuna jiya Mu’azzam wajen Safeenar ya tafi bai kuma waiwayanta ba har safiyar yau d’in.

“Ma’am should I go and tell her you are not available..?” Patrick ya tambaya cikeda risinawa.

Sadiya ta girgiza kai tace “Maiyasa bata shigo ba tace ka mata sallama dani..?”

Patrick ya d’an girgiza kai kad’an yace “Nima ban Sani ba Ta dai ce na miki magana bazata shigo ba.”

Ta jinjina kai kad’an tana fad’i cikin zuciyarta ‘K’ila ta tuna arangamarta da Karnuka ne kwanakin baya Shiyasa ta zab’i kar ta shigo d’in.. Da wann tunani Sadiya ta nufi waje da zummar ganin Safeenah..”

Safeenah tana hangota ta bud’e motar ta fito muguwar murmushi saman fuskarta. Sai faman k’are ma Sadiyar Kallo take yanda ta wani k’ara cika da kyau an samu duniya an baje Koli a Gidanta.. Saima rage girman idanunta Sadiyar take tana kare fuskarta da hannayenta sabida hasken rana irin mai zafin nan da ya bayyana. Kana ganinta kasan ba fitan take ba, hutu da jin dad’i sun zauna a wajen. Fatarta kad’ai ka kalla zai tabbatar maka da hakan.

Safeenah taci gaba da tab’e baki tana dubanta.

Yayinda Sadiyar ta sakar mata murmushi tace “Ya kika tsaya daga waje.. Mu k’arasa ciki mana.. Allah yasa da alkhairi kika Zo..”

Safeenah taci gaba da k’are mata kallo tin daga sama zuwa k’asa kafin ta murmusa tace “Ba shiga nazo yi ba. Zuwa nai na baki sak’o..”

Sadiya ta murmusa kad’an tace “Toh banda abinki nan fah gidan Yayanki ne kinga ai bazan hanaki shiga ba matuk’a ba da tashin hankali kika Zo ba..”

Safeenah ta murmusa mai sauti tace “Kar ki nuna mun bariki yarinya.. Tar nake kallonki.. Ki gama duk wani iskancin da kutungwilarki na d’an lokaci ne.. Naji dad’i da kika San cewa ni da shi tushe guda ne.. Kece bare a tsakaninmu.. Har abada mu zamu tab’a rabuwa ba.. Domin kuwa akwai jini mai k’arfi da ya had’amu..” Ta saki murmushi tana mai d’aura hannunta saman flat tummy d’inta da kaman babu komai ciki.. Lokaci guda take ci gaba da fad’in “Shin kin tambayi mijinki jiya da wa yake tare a daren jiya..?” Ta wani rausayar da idanu kafin taci gaba da shafa cikin nata tana fad’in “Koda yake naga kinata kiransa amma yanata katse kiran naki.. Toh Maiyasa ma bazai katse ba alhali yana tsaka da jin dad’insa..”

Izuwa lokacin k’wallan da Sadiya keta k’ok’arin dannewa Sun gama ciko idanunta..

Safeenah tai murmushin cin nasara ganin yanayin Sadiyar ya sauya gaba d’aya. Lokaci guda taci gaba da fad’in “My Halal bazai tab’a rabuwa dani ba.. Ni da shi are one.. Haka kikazo kika samemu kuma haka zaki fice daga rayuwarmu ki barmu tare kaman dai yanda kika samemu tare.. Kinsan Maiyasa..?” Ta k’arashe tana kuma matsowa kusan Sadiyar kafin ta janyo hannun Sadiya guda ta d’aura saman cikinta.. Murmushi bai bar saman fuskarta ba take duban Sadiyar wacce ta daskare tana kallon hannunta da Safeenah ta aza kan cikin ita Safeenar “Akwai ajiyar shi a cikin nan.. Zan bashi abinda babu wata mace da ta tab’a bashi a duniyar nan.. Product na soyayyarmu ne a cikin nan.. Tab’a kiji da kyau ki tabbatar da hakan... Kar kiga laifinsa , Kinsan mace mai juna tana buk’atar kulawa na musamman sann jariri na buk’atan d’umin mahaifinsa dole ya katse kiranki..”

Sadiya tai azaman fincike hannunta daga saman cikin Safeenah tana goge hawayen da suka shiga gangaro mata.

Safeenah Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “ Dama na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Mijina nawa ne.. Ni kad’ai.. Ki fara k’irga kwanakin ki a gidan nan domin kuwa kwanakin ki a gidan nan K’ayaddadu ne.. Zaki fice ki bar mun Gida kaman dai yanda na miki alk’awari.. Bari dai muga mai zai faru yanzu..” Ta k’arashe a daidai sanda ta hangi motar Mu’azzam ya karyo layin.. Safeenah Ta silale nan wajen, tai saurin jifa da takalmanta gefe.. Ta kama k’asan rigarta ta keta.. Ta d’aura hannunta guda akai d’aya kuma ta aza saman kwamkwasonta daga nan ya da take duk’e gaban Sadiya. Ta shiga zunduma ihu tana kame cikinta tana kuka “Wayyo sun kwance mun karnuka.. Wayyo cikina.. Wayyo zan mutu.. My baby.. I don’t want to lose my Baby.. Wayyo Allah na..!”

Sadiya tai tsaye Cak cikeda mamaki tana kallon wani irin makirci da bata tab’a arangama da irinsa ba..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*63*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Hango Safeenah zaune darshan a k’asa da yai ya sanyasa saurin taka birki. Babu shiri ya bud’e marfin motar ya fito ya nufosu cikin sassarfa, ga Sadiya tsaye gabanta tamkar wacce aka dasa.

“Feenah.. Ke Safeenah lafiya.. What’s going on here..?” Ya tambaya yana k’arasowa.

Safeenah ta kuma kame bayanta tana nishi da k’yar “Wayyo.. Wayyo Allah na.. Karnuka Ta sakar mun.. Wayyo na shiga uku.. Wayyo zan mutu.. Bayana.. Marata..” Cikin kuka taci gaba da nuna Sadiya tana fad’in “Gata nan.. Itace tasa mai gadinka ya kwance mun Karnuka.. Ni banyi niyyan zuwa gidanka ba amma dashike inada appointment da Dr tau shine na taho muje tare tinda kaima Kanada iko akan D’anka kuma ka canci kasan dik abinda ake ciki... Shine wann matar taka tasa security man ya kwance mun Karnuka.. Dama ba yau bane kawai Ta tab’a mun haka.. Ranan ma ta mun haka harda cewa ni mayya ce Ina bibiyanka bayan ka sakeni.. Ai ko da ace Babu aure tsakaninmu nan fah gidan D’anuwana ne zan iya zuwa gidan nan..Amma shine ta kwance mun Karnuka saikace wata b’arauniya, wllhi da k’yar nasha.. Wayyo cikina..!” Ta kuma kurma wani ihun daidai sanda Patrick ya fito da Karnuka.. A nasa tinanin Safeenah ta tare Sadiya ne da fad’a shine ya fito da Karnukan dan ya mata barazana kaman yanda suka mata wancan ranan. Patrick ya turo gate yana rik’eda Karnukan yake fad’in “Ma’am Ta tafi ko na sakar mata su Danny su tayata shawagi..” Yai birki wa kalamansa sakamakon hango Mu’azzam da yai.

Safeenah ta kuma sakin ihu tana rarrafawa Ta isa bayan Mu’azzam Ta rik’e k’afafunsa tana b’uya tana fad’in “Ka gani ko.. Kaga abinda nake fad’a maka koh.”

Wani irin tsawa ya dararawa Patrick wanda saida yasa Patrick sakin chain d’in wuyan Karnukan dan tsoro dan shi sam baisan Mu’azzam d’in ya iso ba..

“Are you stupid.. Ashe kai mahaukaci ne..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar wanda zai tabbatar maka ransa a b’ace yake. Patrick fad’i yake “Sorry Sir.. I.. I didn’t know.. You..”

“Shut up.. Just shut up.!” Mu’azzam ya kuma daka masa wani Tabawan.

Sadiya dake Hawaye bud’e baki tai da niyyan magana ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu “Banson jin komai, ki shige gida yanzun nan.!”

Ta saki baki tana kallon ikon Allah. Ta girgiza kai tace “Amma...”

“Bakiji mai nace bane..? Ko kurma ce ke..? Kina iya adana bayanan ki har na dawo..Please.” Ya k’arashe yana mai janye idanu daga barin dubanta.

Take taji hawayen na zuwa mata gadan gadan, Jiki babu laka Ta nufi cikin gidan, yayinda Patrick keta k’ok’arin basa hak’uri yana janyo igiyan wuyan Karnukan.

Ta jikin gate Sadiya Ta mak’ale tana hange Safeenah dake kuka Mu’azzam na tambayarta ko zata iya tashi.. Wani sabon kuka ne taji yazo bakinta.

Safeenah ta girgiza masa kai tana hawaye “I can’t.. I can’t walk.. Wllhi bazan iya ba.. Ni da nasan Karnuka za’a kwance mun a gidanka wllhi da bazanzo ba in the first place..” Kuka ya hanata ci gaba da magana, tana hawaye tana shafa cikin take fad’in “Our Baby Mu’azzam.. I don’t want to lose our child.”
Chapter 123 · 0% Book details