Sashe 132
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mu’azzam ya murmusa kad’an yana fad’in “A’a Aunty ai munyi sallama d’azu, dama wasu ‘yan kaya ne na kawo mata... Bara na shigo dasu..” Ya k’arashe yana mai ficewa. Ya shiga sauk’o da kayyakin daga mota yana shigo dasu, ciki harda sayayyan da ya tsaya yayo masu.
Aunty Larai ta saki baki tana dubansa tace “Oh Mu’azzam ba’a rabaka da hidima, naga dai shopping d’in da kai ai ko rabi bamu ci ba, ko dai D’an naka acici ne, da alama manomi za’a haifo shiyasa Kayo wann cefane haka..”
Ya kuma murmusawa yana sadda kai kad’an.
Aunty Larai tace “Allah sarki sannu da k’ok’ari kaji.. Allah ya k’ara rufa asiri ya k’ara arziki.”
Ya amsa da “Ameen Aunty.”
“Shiga kaga matarka tana ciki, shiga kuyi sallama.” Ta k’arashe tana nuna masa k’ofar d’akin daga bakin corridor d’in da take tsaye.
Zuciyarsa cikeda son ganinta ya nufi d’akin yana amsawa da “Toh Aunty..”
Aunty Larai ta shiga tattare kayayyakin da ya shigo dasu wanda kayan kwad’ayi irin wanda mata masu ciki ke so yafi yawa. Sai murmushi take tana ayyana irin k’aunar dake tsakanin Mu’azzam da Sadiya. Fatanta Allah ya barsu tare ya kad’e masu duk wani fitina.
Da sallama saman bakinsa ya tura k’ofan d’akin.
Can ya hangeta saman gado tana rufe da bargo idanunta a lumshe irinta mai bacci. Ya k’araso a hankali cikin sand’a kaman mai tsoron kar ya tada ita daga baccin nata. A haka ya zame pillown dake rungume cikin k’irjinta tayi matashi ma kan nata da pillow d’in, ya yaye bargon kad’an kafin ya d’ale saman gadon ya janyo masu bargon ya rufa masu, ya janyota cikin k’irjinsa had’ida lumshe idanunsa yana shak’an k’amshin nan nata mai mantar dashi duk wani tarin damuwar da ya kwaso.
Yana jin yanda ta mak’ale kan nata cikin k’irjinsa, cikin baccin nata take shak’an had’add’en k’amshin mijin nata. Harda wani sakin ajiyan zuciya yaga tayi a cikin baccin.
Ya murmusa kad’an yana mai sumbatar tsakiyan sumarta. Bai cireta cikin k’irjin nasa ba ya k’yaleta Ta sami bacci mai natsuwa dan shi kansa yasan ya sabar mata da bacci cikin jikinsa.
Saida suka kwashe kusan minti shabiyar a haka kafin ya d’ago tsintsiyar hannunsa yana duba lokaci. Cikin dabara ya cire nasa jikin yai mata matashi da pillow d’in. Ya karanto mata addu’o’in bacci na tsari ya shafe jikinta dasu, sanda ya gangaro zuwa mararta ya jima sosai yana shafa wajen a hankali kafin ya mik’e ya sumbaci goshinta. A hankali ya fice yaja mata k’ofar d’akin.
A parlor ya tadda Aunty Larai sai hamma take alamun dai baccin itama takeji.
“A’a Inspector har zaka wuce.” Ta tambaya wani Hamman na kuma karyo mata.
“Eh Aunty zan wuce, ta riga tayi bacci ma.. Sorry for the inconvenience fah..”
“Kai haba babu komai dik sanda kake son ganin matarka kazo ka ganta abinka.. Nan Abuja ne babu wani surkunta ehe, Abuja style.. Idan munje Can Fufore sai muyi surkuntanmu kaji koh..” Ta k’arashe dai kaman ko yaushe cikeda barkwanci. A haka Sukai sallama Mu’azzam ya fice na murmushi.
**
Washe gari Sadiya k’amshin mijinta ne ya tada ita sallan asubahi, wanda tuni ya kama jikinta harma da abin rufuwan nata kai kace a mayafi guda suka kwana. Ta dinga shinshina jikinta jikinta da abin rufuwan tana mamakin ya takejin k’amshin Mu’azzam, toh kodai cikin mafarki ne yazo mata.. Ita kad’ai sai sak’awa da warwarewa take tana mamaki. Har saida ta fito da safe taga tulin kayan da ya kawo a daren jiya tasan dik yanda akai Mu’azzam ya shiga d’akin ne kuma ya kwanta saman gadon. Sai ta shiga jin kunyar kanta da kanta, batasan ya akai ya shige d’akin ba amma ita gani take kaman ma gaban Su Umma da Aunty Larai yai hakan.. Lallai da ya gama da ita.. Tai k’wafa cikin ranta a hankali dan har yanzu haushinsa takeji tin kan abinda ya mata gashi bai bata hak’uri ba har wann lokacin.. Dik wann rawar k’afan da yake ta riga tasan sabida abinda ke cikinta yakeyi kaman yanda yakewa Safeenah. Ko kula expensive kayyayakin da ya kawo d’in ma batai ba sai cewa da taiwa Aunty Larai ita k’osai da kunu take so. Babu b’ata lokaci Aunty Larai tace an gama uwar biyu..
Taji sunan da Aunty Larai Ta kirata dashi amma sai ta basar dan ita ko zance tanada ciki bata so ayi.
**
Yamma lis Daddy ya iso garin. Adnan ne yaje Airport ya d’aukosa. Tin daga gate ya tabbata gidan nasa babu lafiya.
Yana isa cikin gidan kuwa ya tadda wani tashin hankali..
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*67*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Safeenah ce zaune tsakiyar parlorn rik’eda ‘yartsana tana jijjigasa tana fad’in “Kai hak’uri little champ Daddynka baizo ya ganmu ba ko nasan zaizo sa ne, wancan shegiyar da ta rabamu zata fice mana daga gida zata koma can yanda ta fito...”
Kiki da Musaddiq sun had’a uban tagumi suna duban ‘yaruwar tasu cikeda tausayawa. A haka Daddy ke motsa k’afafunsa da k’yar yana shigowa parlorn.
Safeenah tana hangosa ta saki murmushi tana ci gaba da jijjiga d’antsana dake rik’e cikin hannunta, Ta mik’e da sauri ta nufi Mahaifin nata “Daddy.. Welcome..” Sai kuma ta dubi D’antsanan dake rik’e cikin hannunta wanda akai masa dressing irin na d’anmutum hardasu diaper da overall. Tana duban D’antsanan tana murmushi take fad’in “Your Grandpa is here.. Oya go and say hi to Grandpa..” Ta k’arashe tana mik’awa Daddy D’antsanan.
Daddy ya dube d’iyar tasa cikin wane irin tausayawa yayinda Musaddiq da Kiki suke duban mahaifin nasu suma cikin wane irin yanayi na tausayin ‘yar uwar tasu.
Safeenah ta dubi Daddy yanda yai tsaye yana binta da kallon tausayi “Daddy look, kalla kaga.. Your Grandson.. He’s saying hi Daddy..” Tana maganar tana kuma jijjiga babyn robar..
A hankali Daddy ya saka hannunsa ya amshi D’antsanan yana dubawa. Safeenah taci gaba da fad’in “Oya little champ say Hi to grandpa..”
Yanda Daddy yai tsaye yana dubanta ya sanyata d’agowa itama tana duban Daddyn. Sai kuma ta soma girgiza kai tana fad’in “Kaima baka yarda ba koh..? Daddy did you know I was pregnant..?” Hawaye suka gangaro mata, ta jinjina kai a hankali kafin taci gaba da fad’in “A nan parlorn Mommy ta bani abortion pills..” Muryarta ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da fad’in “Daddy.. Daddy Mommy terminated my pregnancy right in front of Mu’azzam.. Mommy is not human.. Bazan tab’a yafe mata ba.. Bazan tab’a yafe mata ba..”
Saurin rungumota Daddy yai yana jin kukan da yake k’ok’arin dannewa na kuma taso masa. Safeenah ta fad’a jikin Mahaifinta tana kuka sosai yayinda kukan Kiki ma ya k’aru, Musaddiq ya kifa kansa kad’an shima hawaye na d’igowa daga cikin idanunsa.
Daddy ya rik’o hannun Safeenah suka zauna saman kujera, ya kwantar da kanta cikin jikinsa kad’an yana lallashinta. A haka aka samu tai shiru amma yana rungume da D’antsananta.
Kiki tai k’ok’arin tsaida kukanta kafin ta nufo yanda suke zaune ta dafa Safeenah tace “Addah Feenah Daddy just got home ki barshi ya huta kinji, sai ki nuna masa little Inspector..”
Safeenah ta dubeta sai kuma ta jinjina kai tana murmushi “Sunansa little Mu’azzam.. That’s how much I love his Dad.”
Daddy ya cire jikinsa daga na Safeenah a hankali da taimakon Kiki kafin ya kirawo Musaddiq suka fice.
Daga shi har Musaddiq jigum jigum sukai Musaddiq na karanto masa duk abinda ya faru saidai bai sanar dashi cewa Mommy ta d’aukarwa matarsa mai magani na bogi ba. Cire cikin Safeenah da Mommy tai kawai ya sanar dashi.
Tsananin mamaki ya cika Daddy “Hajara ce tai wann aika aika.. Kuma a cikin gidana.. Right in front of Mu’azzam, Ta kashe masa D’a.. Hajara duk ta aikata wann..?”
Musaddiq ya jinjina kansa a hankali.
Daddy yai shiru cikeda mugun al’ajabin irin wann al’amari. Ya kuma d’agowa yana duban Musaddiq d’in “Kuma kace Hajara is nowhere to be found..?”
Musaddiq ya jinjina kansa a hankali.
“Badai ta aikata abinda take so ba, ta k’untatawa Mu’azzam ta kuma haukatar da d’iyarta Toh meye na guduwa.. Idan tsoron tafiya gidan yari take kan abinda ta aikata da Ta daina wahalan gudu dan idan Ina numfashi Hajara sai ta biya abinda ta aikatawa Mu’azzam da kuma Safeenah.”
Musaddiq ya d’an dubesa kad’an sai kuma ya sadda kansa k’asa.
“Su waye k’awayen Hajara a garin nan..?” Daddy ya tambaya yana duban Musaddiq.
“Je ka sanar da Adnan kar ya tafi ko Ina zamu fita yanzu..”
Musaddiq ya jinjina kai a hankali yana mai amsawa kafin ya fice sanar da Adnan sak’on Daddy.
Daddy ya mik’e ya haura sama dan shiryawa sabida dawowarsa kenan daga tafiya.
**
A b’angaren Mommy kuwa wani sunk’urumin D’aki ne dake underground a gidan Hajiya Faty ta b’oyeta, Hajiya Faty ta nusa tace “Nifa a gaskiya Hajara na fara tsorata da lamarinki, Kinga ko d’azu ma saida D’an kishiyarki yazo gidan nan shida wani abokinsa D’ansanda suka tiistiyeni da tambayoyi.. Kinsan dai mijina D’an siyasa ne, and he has a reputation to protect, bazai yuwu ‘Yansanda su dinga masa zarya a k’ofar gida ba, rufin asirin Allah ma baya k’asar a yanda nasan Abba da yanzu nima ya sallameni dan dik abinda zai kawo ma siyasarsa cikas Abba zai iya rabuwa da wann abun koda kuwa uwarsa ce.. So kawai ni gaskiya ki canza wajen b’oyo.”
Mommy ta jinjina kai tace “Kar ki damu nasan mai zanyi, badai ni Mu’azzam yake nema ba, toh zan bayyana masa kaina.. Kuma wann karon da labari mai dad’i da ya jima yana nema zan bayyana masa.. Amma zan baki ajiyan wani abu..”
Hajiya Faty ta dubeta da mamaki yanda take murmusawa “Ajiyan mi zaki bani..?”
“Dukiya..” Mommy ta bata amsa kai tsaye. Lokaci guda ta zaro doguwar envelope cikin Jakarta tana nunawa a fuskar Hajiya Faty, murmushi saman fuskarta take ci gaba da furta “Kinga wann.. Shine ummulhaba’isin komai.. Kinga wann takardan shine ya haddasa duk wani tashin hankali.”
Hajiya Faty ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba, meye cikin takardan..”