Sashe 125
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin zuban hawaye yake fad’in “Zan sanar dasu yanda kuka had’a baki keda Aunty Shemau kuka d’aukowa Aunty Nuratu mai magani na bogi dan kawai Aunty Nuratu ta fice daga gidanki da kuma rayuwar mijinki.. Naji wayar da kukai keda Aunty Shemau Tun kafin mu tafi Fufore.. Na riga nasan shirinki Mommy..” Muryarsa ya soma rawa sosai yana ci gaba da hawaye yake fad’in “Kin San Maiyasa ban tona miki asiri ba Mommy..? Because you are my mother.. And I love you so much.. Kuma nayi zaton zaki tub’a... But then... Yau d’in nan na yarda cewa Ke baki cancanci a kiraki uwa ba..!”
Mommy da duniyar ya soma juya mata, hawaye Ta soma tana rok’on Musaddiq “Musaddiq don’t please.. You are my son Musaddiq..Don’t do this to your Mom.. Musaddiq Kurku fah za’a jefa mahaifiyarka..!”
Cikin tsananin daka tsawa hawaye na tsartsafowa daga idanunsa yake fad’in “No..! I’m not your son Mommy.. Kin kashe D’an Safeenah da kanki Mommy.. Wace irin uwa ce zatai ma d’iyarta haka.. Idan zaki iya kashe D’an Safeenah wanda yake jininki ne Mommy Tabbas zaki iya kashe kowa sabida bak’in zuciya irin naki..!” Hawaye yaci gaba da gangaro masa ana ci gaba da fad’in “You don’t deserve to be a mother.. Baki canci zama uwa ba Mommy.. Babu uwan da zatai abinda kika aikata yau, son zuciyarki yakai mak’ura..!” Ya k’arashe yana mai kuma girgiza kai hawaye basu daina ambaliya a fuskarsa ba.. Lokaci guda yasa kai ya fice cikin sassarfa.
Mommy ta biyo bayansa a guje tana kuka tana k’walla masa kira amma inaa tuni ya fice.
Zubewa Mommy tai a wajen ta d’aura hannayenta biyu aka tana k’walla wani irin ihu had’ida kiran sunan Musaddiq da tuni ya fice.
A d’ari Mommy Ta mik’e Ta nufi d’aki ko takan Safeenah dake murk’usoso a d’aki batabi ba Ta suri mayafinta da jaka ta fice daga gidan hankali tashe.
**
Mu’azzam kaw tinda ya fice daga gidan da k’afafunsa kurum yake tafiyar yanaji kaman ba’a saman k’afafun nasa yake tafiyar ba, maganganun Mommy sai Yawo suke a kwanyarsa, hannayensa sakale cikin aljihunsa. Mommy ta kashe masa d’ah a gaban idanunsa. Matar da ya d’auketa uwa Itace tai masa hakan.. Shi duk tunanin duniyar nan ma ya rasa wane dalili ne zaisa Mommy ta aikata abinda ta aikata Wai kawai dan Ta rama abubuwan da yai mata.. Toh ma Wai shi mai yai mata da tsanani da zata d’auki wann d’anyen hukuncin.? Ya k’arashe tunanin nasa yana zama saman wasu kujerun shak’atawa dake d’an k’asa da layin masu kad’an.
Mu’azzam yai zaune yana tunanin lamarin nan ya hango Musaddiq na tahowa.
D’an kauda fuskarsa gefe yai kad’an har lokacin yana jin zuciyarsa na masa zogi.
Musaddiq ya k’araso jikina sanyaye ya zauna a gefensa ba tareda yace komai ba.
Sun b’ata lokaci a haka babu mai cewa komai kafin Musaddiq ya soma fad’in “I’m sorry.. I’m sorry Mu’azzam.. Please forgive me..!” Kansa a k’asa yake maganar.
Da mamaki Mu’azzam ya d’ago yana dubansa, Maiyasa yake basa hak’uri bayan bashi yai masa laifi ba.
Hannun Musaddiq dake aje gefen Mu’azzam d’in saman kujeran da suke zaune bisa Mu’azzam ya dafa, Musaddiq ya d’ago idanunsa masu zuban ruwa yana duban Mu’azzam d’in.
D’an girgiza kai Mu’azzam yai yace “Maiyasa kake bani hak’uri Musaddiq.. Baka aikata mun komai ba.. Mommy ita ta aikata laifin ba kai ba..”
Kuka sosai yazo wa Musaddiq ya rungume Mu’azzam yana kuka yake ci gaba da fad’in “Nayi shiru ne sabida ita d’in Mahaifiyata ce.. Mu’azzam ka yafe mun.. Ka yafe mun it I kept this from you..”
B’anb’aresa daga rik’on da yai masa Mu’azzam yai yana binsa da kallon mamaki yake girgiza kai “What do you mean Musaddiq..? What are you trying to say..?” Ya tambaya cikin rud’ani.
Cikin zuban hawaye Musaddiq ke fad’in “Mommy ‘yar damfara ta d’aukawa mahaifiyarka a matsayin mai magani Mu’azzam.. Ba don komai ba Sai dan ya fice mata daga gida da kuma rayuwar mijinta gaba d’aya..”
Bibbiyu Mu’azzam ke ganin Musaddiq zuciyarsa na wani irin harbawa.
SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*
*64*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kauda kansa gefe yai yana d’an shafa sumarsa kad’an cikin rashin yarda da abinda Musaddiq d’in ke fad’i “Kamin magana da yaren da zan fahimta Musaddiq..” Ya fad’i cikin rarrabewar kalamai.
Musaddiq da har lokacin bai daina zuban hawaye ba, yaci gaba da jinjina kai “I’m sorry Mu’azzam.. I really I’m sorry brother.. Dan Allah ka yafe mun.. Ban zaci Mommy zata kawo wann lokacin bata hankalta ba.. Had I known abubuwa zasu kasance haka da nayi magana tuntuni koda ta kasance mahaifiyata.. Inajin laifina ne daka rasa D’anka, Watak’ila da nayi magana tuntuni da an d’auki mataki kan Mommy.. Watak’ila da baka rasa D’anka ba..!” Kuka ya hanasa ci gaba da magana yayinda Mu’azzam yai zaune yana ganin duniyar na jujjuya masa.
Ya k’ura ma waje guda idanu, cikin wane irin yanayi da zai iya cewa bai tab’a kasancewa ciki ba, a hankali cikin kwantacciyar murya yake fad’in “Tell me everything Musaddiq.. Ka sanar dani duk abinda ka sani..”
Musaddiq dake duk’e wajen tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu, kafin ya shiga jinjina nasa kan shima.. Lokaci guda ya shiga karanto wa Mu’azzam duk abinda suka faru harda yanda suka juya maganin Kyallu shida Ajidde da k’udirin Kyallu na turo Ajidde gidan dan tai mata sata.. Musaddiq na labarta masa abubuwan da suka faru Mu’azzam d’in na tuna komai daki daki harda lokacin da Ajidde taso masa sata farkon zuwansa gidan.. Allah sarki ashe ba b’arauniya bace kaman yanda ya zata.. Ashe tilasta mata yin satan akayi.. Shin wace irin duniya muke rayuwa ciki..? Haka Musaddiq ya dinga karanto wa Mu’azzam duk abubuwan da suka faru gameda jinyar Aunty Nuratu da rawar da Ajidde ta taka wajen watsi da maganin Kyallu tana kuma karb’o mata ayoyin Allah daga wajen Malama Hafsah.. Yarinyar da yake ma kallon shashasha mahaukaciya, yarinyar da yake ma kallon bata cancanci kasancewa kusan mahaifiyarsa ba balle tai mata jinya.. Yarinyar da yai mata lak’abi da Mahaukaciya.. Ya kuma lumshe idanunsa a hankali yana jin zuciyarsa na wani irin harbawa..
Muryar Musaddiq ya sinkayo yana ci gaba da fad’in “Shisa a lokacin da ka dage sai Ajidde ta bar gidan nima na dage cewa bazata tafi ba.. Shisa nima nai duk yanda zanyi nabi duk hanyar da zanbi domin na tabbatar Ajidde bata bar gidan ba..Nida Ajidde tuni mun had’a Team wajen ganin munyi watsi da maganin dasu Mommy suka so d’aura Aunty Nuratu akai..” Muryar Musaddiq yaci gaba da rawa “This is the least I can do bayan cutar da Aunty Nuratu da mahaifiyata taso yi..”
Musaddiq ya had’a hannayensa biyu alamun rok’o ya duk’a saman gwiwoyinsa yana fuskantar Mu’azzam still hawaye ne saman fuskarsa “Mu’azzam dan Allah kai rangwame wa Mahaifiyata.. Dan Allah ka mata rangwame..!”
Cikin sauri Mu’azzam ya kamo Musaddiq ya rungumesa yana jin wasu k’walla masu zafi suna ciko idanunsa yayinda kukan Musaddiq ya k’aru.
Cikin wane irin yanayi Mu’azzam ke furta “Mommy ta tafi da nisa Musaddiq.. Ka sani, banyi niyyan d’aukan mataki akan Mommy ba sabida kisan d’ah na da tai akan idona..” Ya d’anyi fasali yana duban Musaddiq d’in kafin yaci gaba da fad’in “Kasan Maiyasa..? Sabida Sadaukarwa mai girma da tayi na jinyar mahaifiyata tsawon shekaru.. Amma bayan labarin da ka bani yau Ina shakkun idan Mommy tsakani da Allah ta shafe shekarun nan tana jinyar mahaifiyata.. Musaddiq kai hak’uri, bazan tab’a sassauta ma duk wanda ya cutar da mahaifiyata ba.. Ina buk’atar ganin Mommy.. Akwai tambayoyi da dole zata amsa mun.. Idan ta aikata wani abu domin ta cutar da mahaifiyata, I’m sorry Musaddiq.. But I won’t spare her..!” Ya k’arashe hawaye mai zafi na gangarowa daga idanunsa guda zuwa k’uncinsa. Daga haka Sa kai yai ya nufi hanyar da zai kaisa gidan.
Musaddiq yai saurin take masa baya suka nufi gidan a tare.
Saidai suna shiga gidan suka tadda wani tashin hankalin Safeenah suka hango saman k’arafan dake balcony d’inta Ta kama ginin Ta d’ale zata fad’o k’asa ga ma’aikatan gidan sunyi cincirindo Sai rok’onta suke tai hak’uri Ta sauk’o.
Shigowarsu Mu’azzam yai daidai da shigowar Kiki itama ta dawo daga makaranta kenan ta tadda wann badak’ala dake tashi cikin gidansu.
Musaddiq fad’i yake “Feenah don’t.. Don’t jump please..”
Safeenah na kuka take fad’in “Mutuwa zanyi Musaddiq.. Meye amfanin rayuwar.. Bata da sauran amfani.. Ka barni na mutu nima..!” Tana maganar tana kuka tana kuma yunk’urowa kaman zata duro k’asa.
Ko kulawa da Mu’azzam da tuni ya haye sama basuyi ba.. Dukan k’ofan d’akin Safeenah dake kulle ya dinga ti da k’arfasa har saida ya bud’e d’akin.. Yai azaman shigowa balcony d’in yanda Safeenah ke tsaye tana fad’in zata fad’o k’asa Musaddiq na bata hak’uri, Kiki kam ma school bag d’inta Ta d’ora aka cikin tsananin daburcewa tana kuka.
A daidai sanda Mu’azzam ya shigo Safeenah har ta saki k’arafan ta nufo k’asa, ya daka firgitaccen tsalle daga yanda yake ya tallafo Safeenah had’ida janyosa ta dawo cikin jikinsa.
Ganinsa da tai sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan ta fad’a cikin jikinsa tana fad’in “Our Baby.. Our baby Mu’azzam.. Mommy killed our child.. Ta kashe mana D’a.. Mommy ce ta kashe mana D’a Mu’azzam.. Bazan tab’a yafe mata ba..”
Sosai ya rik’eta cikin tsananin tausayi yana furta “Ya isa Safeenah.. Kiyi shiru haka nan.. Ya isa..”
Safeenah ta kuma fashewa da wani kuka daidai sanda Musaddiq da Kiki suka k’araso wajen. ‘Yanuwan suka k’arasa a guje suka rungume Safeenah babu kaman Kiki wacce Ta mak’alk’aleta sosai tana fad’in “Addah Feenah don’t please.. Don’t ever try that again.. Wllhi muna sonki..”
Fincika Safeenah tai daga rik’on da Kiki tai mata, tana kuma jada baya bata daina hawaye ba take fad’in “Baku nake so ku soni ba.. The only person da nake so shine wann..!” Tai nuni da Mu’azzam dake tsaye gefe yana dubanta.