← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 175

Sashe 144

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka suna bata kashi tsakaninsu da jami’an tsaron muka samu zamu arce gudu muke suna biye damu.. A haka muna cikin gudu nida Yayata muka had’u da wani mutumi shima gudu yake kowa na Ta kansa.. Yayata Ta a tambayi mutumin ko wata k’asa ce wann sai mutumin yace mata nan k’asar Nigeria ne kuma jihar Lagos..

Muna gudu mutumin yake tambayarmu mu kuma daga Ina muke.. Yayata tace masa sato mu akai daga K’asarmu Eritrea.. Sai ta tambayesa shi kuma mai yake a nan.. Saurayin yace shi daga Arewacin Nigeria yake zuwa jihar Lagos suna kawo fatu na dababbi ana fitar dasu k’asashen waje Ta jirgin ruwa.. Muka ci gaba da gudu na kasa gudu sabida ba wani k’oshin lafiya bane dani.. Sai saurayin ya d’aukeni ya azani a bayansa yana fad’in muci gaba da gudu kar mutanen Su cimmamu.. Muna cikin gudu muka hangi mutanen suna biyomu a guje suna fad’in ko mu tsaya ko su harbemu.. Yayata Ta karaya dan bata fata mutanen su kama ‘Yaruwarta bata fata wad’ann azzaluman su cutar dani ‘Yaruwarta.. Sai Yayata ta dakata da gudun, ta dubi matashin mutumin wanda a lokacin bazai gaza shekaru 24 ba tace dashi Bawan Allah ga amanan ‘Yaruwata ka taimaka ka tseratar mun da ita daga hannun azzaluman nan.. Bansan ko zamu sake had’uwa a gaba ba.. Amma ga amanan ‘Yaruwata na bar maka.. Wann saurayi mai Sana’an Safaran Fatun dabbobi daga arewacin k’asar nan zuwa kudanci mai suna Ibrahim ya amsa amanar da ‘Yaruwata Ta bashi muna kuka daga ni har ‘Yaruwata.. ‘Yaruwata tace mecece alama da zanyi amfani da ita na iya ganeka gaba idan Allah ya nufa zamu sake had’uwa.. Sai Matashin ya ciro hoto cikin aljihunsa ya mik’a mata yace wann hoto na ne bansan wata shaida ko alama da zan baki ba amma ki rik’e wann hoton nawa ki nemeni da ita a gaba.. Yayata Ta amsa hoton tana hawaye tana masa Godiya. Ina gani Ta k’ulle hoton Ibrahim cikin zaninta kafin mukaci gaba da gudu nida Ibrahim.. Juyawan da zamuyi muka hangi ‘Yantaddan nan sun kame Yayata sun jefata cikin jirgin ruwan.. Suna jefata kuwa muka hangi wuta ya tashi a cikin jirgin ruwan dan dama bata kashi suke tsakaninsu da jami’an tsaro...!”

Umma taci gaba da hawaye yayinda Aunty Larai ke hawaye..

Umma taci gaba da fad’in “Akan idona jirgin ruwan da Yayata ke ciki ya kama da wuta.. Ibrahim yaci gaba da gudu dani Ina fad’in ya k’yaleni naje na duba Yayata amma bai sakar ni ba, haka ya dinga gudu dani Ina kuka yana lallashina.. A haka Ibrahim ya tseratar dani da taimakon Allah amma alhinin rashin ‘Yaruwata yana nan tare dani.. Ya kawo ni garinsu Birnin Kebbi yanda ‘Yanuwansa sukai masa chaa da fad’in Ina ya samo yarinya.. Ibrahim ya sanar dasu cewa ni d’in amana ce a gareshi.. Babu yanda danginsa basuyi ba cewa ya fitar masu dani a cikin gida dan basu San daga wata duniya nake ba amma fir Ibrahim yak’i aminta yace idan zasu koreni saidai Su had’a dashi.. Ba dan sun so ba suka k’yaleni Sai dan Ibrahim ya dage cewa ni d’in amanarsa ce kuma zai rik’eni amana kaman yanda yaima ‘Yaruwata alk’awari.. A nan gidansu Ibrahim da shike family house ne kuma iyayensa sun rasu dangi ke rik’e dashi a nan suka saka min suna Uwani dan sunana Wato Aisha sunan Kakarsu Ibrahim ne sai suna kirana da Unwani.. Aka Zo za’a saka yara sa’annina a makaranta a nan family house d’in su Ibrahim d’in, kowa ya saka d’ansa a makaranta amma ni babu wanda ya waiwayeni balle ya sakani.. Wariya babu irin wacce ba’a nuna min amma haka Ibrahim yake lallashina yace nai hak’uri wataran komai zai wuce kuma nima zanyi karatu kaman ko wacce yarinya a cikin gidan.. Haka da ‘Yar sana’arsa Ta safaran Fatun dabobbi ya samu ya tara ‘Yan kud’ad’e ya sakani a makaranta.. Harta da tufafi babu mai saya min a dangin komai shi yake mun, wajen kwana da abinci kawai suke bani suma d’in sai nasha gori.. A haka suka soma bijiro ma Ibrahim da maganar aure lokacin ni ina k’arama ban wani girma sosai ba tinda dama ya d’an fini da shekaru masu d’an yawa.. Akwai wata d’iyarsu a cikin gidan da suke son had’asu auren Dangi Amma sam Ibrahim yak’i amincewa yace dasu shi baida lokacin aure kula dani yake ba aure bane a gabansa, kula da amanarsa yake.. Wann soyayya da kula da Ibrahim ke nuna mun yasa suka k’ara tsanata k’arshe suka ce saidai na fice masu a zuriya nasan yanda dare yamun Wai zan raba masu kan ahali sabida Ibrahim yaro ne mai biyayya amma bai tab’a bijire masu ba sai akaina.. Sukace ya zab’a ko su ko ni.. Ibrahim yace ya zab’eni zai aureni kuma zaici gaba da kula dani.. A haka akai aurenmu da k’uruciyata.. Ibrahim ya d’aukeni ya taho dani garin Suleja yanda yake bugabugansa..” Muryar Umma yaci gaba da rawa tana ci gaba da furta “Ibrahim bai kusanceni ba sabida k’arancin shekaru na yaci gaba da bani kula irin wanda ya kamaceni musamman a b’angaren karatuna na boko da Islama. Har sai lokacin da na kai matakin cikakkiyar budurwa wacce komai na matantaka ya bayyana jikina wacce zan iya d’aukan d’awainiyar d’ah namiji kafin ya soma kusantana a matsayin mijina.. Ibrahim shine uwana Larai kuma shine Ubana.. Ya mun komai a rayuwar nan.. Amma nazo na masa butulci na raina arzikinsa.. Na had’u da k’awaye da suka hure mun kunne cewa yanda nakeda kyau nafi k’arfin ajin Ibrahim.. Dan da na k’ara girma sai kyauna ya kuma bayyana.. Naita shek’a masa rashin mutunci ko zai gaji ya sakeni amma bai sakeni ba a cewarsa ko mai zan masa ni d’in amana ce a gareshi.. Sann ba kyaun halitta na bane ya rud’esa dan tun bansan kaina ba yake k’aunata.. Kuma ni amana ce a gareshi.. A haka har na saduda na dangana lamarina ga Ubangiji nace tawa k’addarar kenan zan k’are da wahalan auren talaka bayan tulin iftila’ain da na fuskanta a rayuwa, koda na haifi Sadiya sai na k’udiri niyyan d’iyata bazata auri Talaka kaman yanda mahaifiyarta ta had’u da k’addaran auren Talaka ba.. Nasan zafin talauci da rashi Larai nasan wahalan da muka sha a rayuwa sabida rashin gata a lokacin da nake cikin jinya, amma na mance komai Allah keyi.. Komai muk’addari ne daga Allah.. Sann lafiyar da Allah ya bani bayan na shafe lokaci Ina jinya.. Larai inaji ni ce sanadiyar da yasa na rasa ‘Yaruwata domin kuwa Ta dalilin jinyana muka rasa komai namu har muka tsinci kanmu hannun ‘Yan ta’addan nan.. Kaicon zuciya maras godiya..! Kaicona.. Kaicona Larai.. Ni ce na hure ma Sadiya kunne da San abin duniya.. Na nuna mata mahaifinta baya dashi.. Alhalin Ibrahim shine mutumin da yamun arziki a rayuwa.. Shin Larai ta yaya zanga da kyau a rayuwa.. Mutumin da ya mun wann irin sadaukarwa Larai.. Zan jima Ina jin ciwon abubuwan da na aikata masa..!” Kuka mai k’arfi ya kufce mata.. Aunty Larai ta rungumeta tana kuka itama cikeda tausayawa.

Sadiya dake lab’e jikin k’ofa taji labarin da mahaifiyar nata Ta sanar da Aunty Larai wani irin kuka itama Ta fashe dashi tana mai silalewa saman gwiwoyinta...

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*73*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Umma da Sadiya suka kifa kawunansu suna kuka mai ban tausayi Aunty Larai na tsakaninsu na matsan k’walla dan itama Ta kasa tsagaita nata kukan balle Tai tunanin dannarsu.. Allah sarki rayuwa, a wann ranan Sadiya Ta kuma yin kukan rashin mahaifinta, a ranan taji sadaukarwan da yaiwa mahaifiyarta, mutuwar Abba Sai ya dawo masu Sabo. Haka suka sha kukansu gwanin ban tausai.

Sadiya da kanta ke bisa cinyar Umma taci gaba da shafa kan Sadiyar a hankali tana fad’in “A lokacin da aka haifeki sai Abbanki ya bani zab’in sunan da nake so a saka miki.. Ni kuma na sanya miki sunan ‘Yaruwata Halimatu..”

Sadiya ta murmusa kad’an wasu hawayen suka gangaro mata “Zanso na ga takwarata.. Zanso naga wann ‘Yaruwar taki da tayi sadaukarwa mai girma ma ‘Yaruwarta.. Da ace zan ganta da na mata godiya mai yawa.. Allah sarki da ita da Abba duk sun tafi sun bar duniya.”

Umma ta jinjina kai tace “Maraicin rashin Ibrahim harda ni ya shafa domin kaw shine gatana ya d’aura kula dani daga yanda ‘Yaruwata ta tsaya.. Ubangiji ya gafarta masu kurakurensu ya kyautata namu bayan nasu.. Halinsu na k’warai ya bisu.”

Sadiya ta amsa da Ameen tana mai kuma lumshe idanunta.

Tabbas Sadiya ta kuma yarda ba tarin dukiya bane jin dad’in rayuwa, samun mutanen kirki masu k’aunarka tsakani da Allah a rayuwarka shima wani babban arziki ne.. Wadatar zuci da kwanciyar hankali shine babban arziki a rayuwan duniya.
**
FCID

Chief Jaja sai sakin huci yake shi kad’ai cikin interrogation yana furta “Damn it..! Damn you Mu’azzam Gamji..!”

Daidai lokacin Mu’azzam ya turo k’ofa ya shigo hannunsa da aka harba lank’aye cikin Arm holder, yai tsaye yana k’arewa Jaja Kallo yayinda Jajan ma ke dubansa.

Hannunsa mai ciwo lank’aye yake nufo Jajan, still bai janye idanunsa daga duban Jaja ba, duk tulin abubuwan da yai masa kurum yake tunawa harda suspending d’insa da yasa akai.. Wasa da hankalinsa da ya dinga yo da kuma cin amanan k’asa da aikin D’ansanda da yai.. Assad na biye dashi suka shigo kan Jaja.

Daga Mu’azzam har Jaja fuci suke suna duban juna.. Kan kace mai Mu’azzam ya dunk’ule hannunsa ya kaima Jaja wani irin naushi wanda saida yakai Jaja k’asa dukda cewa ba k’oshin lafiya bane dashi sabida hannunsa da harsashi da huda wanda ke lank’aye cikin arm holder.

Assad yai saurin rik’o Mu’azzam yana k’ok’arin janyesa.

Jaja ya kifa kansa jini na fitowa daga hancinsa da bakinsa.

“I told you so.. Kafin kaga bayana sai na gama da kai Jaja.!” Yai maganar yana jinjina kai a hankali kafin ya turama Jaja kujera da k’afarsa yace “Tashi ka zauna kuma ka amsa mun tambayoyina dalla dalla..!” Ya k’arashe yana mai zama gaban teburin da ya raba tsakaninsu.
Chapter 144 · 0% Book details