← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 175

Sashe 159

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka suka ci gaba da rayuwa yaran Abubakar Mu’azzam da kuma Ikram suna hannun Marwan da Hajara sun had’esu da nasu yaran suna kula dasu baki d’aya har bazaka banbance ba sabida yanda Hajara ke basu kulawa, wann ma sosai yasa Marwan yake kuma k’iman Hajara, har saida yaji babu dad’i kan abubuwan da yai mata a baya. Tinda Nuratu da yaranta suka dawo wajen Marwan Hajara Ta fahimci kaman an dasa wa mijinta wani Sabon rayuwa ne Dikda tashin hankali da yake shiga idan yaga yanayin jikin Nuratun da yanda akaita neman magani Allah bai nufa za’a dace ba. Daga nan Hajara ta k’udiri niyyan sai yanda k’arfinta ya k’are wajen ganin Nuratu bata sami lafiya ba.. Balle ma tasan ba samun lafiyar zatai ba haka zata k’arashi wahalarta rai yayi hali.

A can b’angaren Salman baida damuwar da ya wuce wann takardan yarjejeniyar da Hammansu ya rubuta.. Burinsa shine ya mallaki takardan ya mallaki dukiyar tinda da bakinsa ya sanar dashi cewa shida iyalansa basa buk’atar dukiyar.. Yasan bazai wuce D’anuwansa Marwan bane ya d’auki takardan tinda iyalan Abubakar d’in gaba d’aya sun koma hannunsa.. Shi bazai bari dukiyar nan ta tafi hannun kowa ba face shi.. Watak’ila ma Marwan azirta kansa zai da dukiyar dan haka zai bi ko wacce hanya zaibi dan Ganin ya mallaki wann takardan. Hanya mafi sauk’i shine matar Marwan, zaisa Shemau matarsa ta shiga jikin matar Marwan dan su mallaki wann dukiya. Ba tareda sun San cewa takardan na hannun Hajara ba.. Ita kaw Hajara da Ta fahimci suna neman wani abu a wajenta shiyasa Shemau ke shishige mata.. Dariyarsu kawai take a gefe dan tasan bazai wuce takardun dukiyar Abubakar Salman yake nema ba tinda akan idanunta komai ya faru.. Su a nasu wautan amfani zasuyi da Hajara su buga wasansu basu San cewa itace zatai amfani dasu Ta buga nata wasan ba. Tar Hajara ke kallonsu da sunan zasu mata wayo Ta samo masu takardan yarjejeniya daga wajen mijinta.. Suna ma Hajara kallon biri tana masu kallon ayaba.

Marwan da baisan duk anyi wata yarjejeniya ba hakan yasa yaci gaba da kula da dukiyar su Mu’azzam musamman da ya kula Salman na yawan damunsa kan cewa Ina yake kai dukiyar su Mu’azzam tin kafin Mu’azzam d’in ya mallaki hankalinsa. Saidai Marwan bai tab’a sanar dashi komai gameda yanda yake adana masu Kason su ba. Hakan ya kuma tabbatarwa Salman cewa Marwan ya hau kan dukiyar ne yayi k’ak’a gida, Tabbas wann takardan Yarjejeniyar tana hannunsa. Dik yanda zai Sai ya mallaki wann takardan.
**
Mommy Ta ciro takardan tana juyawa tana murmushi, a fili take furta Salman kenan, ka zaci kai kanada wayo.. Ta kuma murmusawa kafin ta bud’e envelope d’in tana juya takardan wanda Tabbas Abubakar ya rubuta zai sadaukar da dukiyarsa amma babu sunan kowa bisa sai hoton wann mutumin da Ta jima da sanar da Danger ya nemo masu wann mutumin.. Toh anyi sa’a Danger ya samu mutumin da iyalansa, yana zaune a garin Suleja sann matarsa da d’iyarsa imaninsu abin duniya ne.. Tuni suka nemo Sagir suka basa dukiya dan ya nemi auren yarinyar su samu su kawar da wann mutumin da ahalinsa wanda basu San dalilin Abubakar na saka hoton mutumin cikin Yarjejeniyar ba.

A wann lokaci kuma aka saka auren Safeenah da Mu’azzam.. Wani rana Ikram ta shigo d’akin Mommy tana nemanta zata tambayeta yanda Ta aje maganin Mamy don lokacin bata magani yayi.. Nan Ikram taji kaman Mommy waya take ga wani dogon envelope saman gado.

SameenaAleeyou📚
*GIDAN ARO*

*79*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Mommy taci gaba da fad’in “Kana jina Muttaqa, dole ai auren nan.. Ta haka ne kawai zamu San duk wani Sirri game dasu.. Auren nan fah dole ne ayi shi..” Ta murmusa kafin tace “Haba babu wanda zai San wann sirri da zasu sani da Sun sani tuntuni bazan tab’a bari wani yaji wann sirri ba..” Mommy ta dasa aya sakamakon jiyo kaman motsin mutun da tai cikin d’akinda dan balcony take tsaye tana amsa wayar.

Saurin datse wayar tai kafin ta juyo ta dubi Ikram da har Ta k’araso wajen k’ofar Balcony d’in.

Mommy Ta d’an tsareta da idanu. Ikram tai saurin girgiza kai tace “Mommy kiyi hak’uri banyi nufin na saurari wayarki ba.. Amma Mommy wane sirri ne wann kike fad’i a waya babu wanda zai sani..?”

Mommy tai raurau da idanu cikin sanyin jiki dan tasan Ikram da bak’ar naci da son jin k’waf. Akwaita da bak’in curiosity tana son sanin diddigin komai yawa yar jarida, yawan fad’ansu da Meema kenan.. Meema bak’in gulma da shiga abinda ba huruminta ba Ikram tambaya da son sanin dalilin faruwar abu. Ga wa’azin gulma da iyayi a cewar Meema. Sam basu wane faye shan inuwa guda ba. Kiki ce take zama taji nasihan Ikram musamman akan sallah, dan idan suna zaune gaba d’aya lokacin sallah yayi bata tashi Ita kad’ai sai tayi masu magana cewa su tashi suyi ko bazasu tashin ba. Meema takanyi tsaki Ta fara fad’in toh sannu musulma mukam jikokin arna ne ai.. Safeenah kaw sabida Ta samu karbuwa wajen Yayanta take wani abin. Bayan abinda ya sami Ikram kaw Meema sai tafi kowa damuwa da shiga tashin hankali, tana jin an kira sallah sai ta tuna Ikram sai kaga ta tashi ta nufi yin sallah..

Mommy Tai shiru tana nazarin abinyi tasan dai wann yarinya mai uban San jin k’wak’waf bazata daina tambayarta ba. Muryar Ikram d’in ya kuma katse mata tunani “Mommy I hope we are not in danger.” Ta k’arashe maganar idanunta na sauk’an akan doguwar envelope d’in da aka rubuta BAT a saman.

Mommy tai saurin zama saman takardan hawaye na ciko idanunta.

Ganin haka yasa jikin Ikram yin sanyi, Ta matso kusan Mommy Ta zauna daga gefenta had’ida d’an dafata kad’an “Mommy are you alright..?”

Mommy ta share hawayen da suka zubo mata tace “Ikram inafah lafiya..”

Cikeda damuwa Ikram tace “Mommy meke faruwa..?”

Mommy ta d’ago hawaye tab idanunta “Akan ‘yar uwarki Safeenah ce.. Ashe wai biye biyen maza take Dikda an saka aurenta da Mu’azzam.. Yanzu idan Mu’azzam yasan haka nayi imani fasa aurenta zai dama ba sonta yake ba Kinsan Daddynku ya had’a auren.. Wllhi dik na damu.. Wann shine yasa kikaji nace bazan bari wani yasan sirrin ba.. Toh amma zargi ne da kokonto.. Kirana akai akace tana biye biye maza ban tabbatar ba Ikram.. Ga aurenta ya matso..”

Ikram tai shiru tana nazarin maganganun Mommy sai ta tuna zamansu a Salford da Safeenah yanda take yawan kawo masu maza gida suna kwana har suka samu sab’ani daga bisani ta sanar da ita daina kuma bazata k’ara ba musamman da Daddy ya soma yunk’urin had’a aurensu da Mu’azzam.

Ta sinkayo muryar Mommy tana fad’in “Ikram taimako zaki min, nasan Kema Bazaki so Safeenah ta lalata aurenta tun kafin tayi ba..”

Ikram ta dubi Mommy dake hawaye cikeda tausayawa. Lokaci guda Mommy Ta share hawayenta kafin ta d’aura hannunta saman na Ikram tace “Ikee please help me.. Ki taimakeni..”

Ikram tai saurin girgiza kai tana dubanta cikeda tausayawa “Haba Mommy kin wuce neman taimako wajena.. Umarni kawai zaki bani.. Mommy ke fa uwace a wajena.. Abinda kikewa Mamy bazamu iya biyanki ba saidai muyi miki biyayya kaman yanda zamuyiwa Mamy.. Tin tasowarmu kike kula damu da mahaifiyarmu.. Mommy dan Allah ki daina cewa na taimakeki ina jin nauyin hakan matuk’a..”

Mommy ta kuma share hawayen makircinta kafin tace “Ikram so nake ki saka min ido akan Safeenah... Idan da gaske tana bin maza dole mu taka ma hakan birki tin kafin Ta tafi gidan Mu’azzam, nasan bazaki so hakan Ta kasance ba.”

Jiki a sanyaye Ikram Ta jinjina kai kafin Mommy taci gaba da fad’in “Bakiji zafin abin nan da nakeji ba amma babu yanda na iya ne.. Kullum so nake yaran nan su dinga koyi dake amma ko wa’azi kike masu isgilanci suke.. Ikram kiyita hak’uri dasu ‘yanuwanki ne gaba d’ayansu.”

Ikram ta murmusa kad’an tana girgiza kai “Haba Mommy ni dasu duk d’aya ne. We are all humans and we make mistakes.. Mafiya kyaun masu laifi cikinmu sune masu tuba.

Mommy cikin zuciyarta take fad’in shegiyar uwar iyayi da kilibibi. A fili kuwa jinjina mata kai tai kafin taci gaba da fad’in “Ki kula da wayarta abinda ke shiga yana fita.. Duk abinda kika samu ki sanar dani.. Amma kar kiyi yanda zata fahimci muna bibiyan al’amaranta..”

Ganin Ikram d’in ta d’anyi shiru yasa Mommy murmusawa tace “Ni mahaifiyarta ce kuma Kema ‘Yaruwarta ce abinda muke ba bin diddigi bane taimakonta Zamuyi daga halak’an da take k’ok’arin kai kanta.. I hope zaki taimaka min Ikram.” Ta k’arashe idanunta na rau rau.

A hankali Ikram Ta jinjina kai tace “Mommy zanyi duk yanda kika ce.. We will work together, I promise.”

Mommy Ta murmusa harda rungumar Ikram kafin ta tambayi maganin mahaifiyarta.

Mommy tai saurin girgiza kai tana fad’in “A’a haba ni zan bata maganinta.. Tashi kije kawai ki fara abinda na umarceki.. Kar ki mance this is our little secret.”

Ikram Ta jinjina kai tana sakarwa Mommy murmushi kafin Ta fice.

Mommy ta rakata da mugun kallo tana sakin huci “Shegiya uwar shishigi da iyayi.. ya k’are miki.. Daga yanzu kin gama shishigi da shiga abinda babu ruwanki.” Ta k’arashe tana mai ciro wayarta.

Bugu biyu Danger ya d’aga “Muttaqa kana jina..”

Daga d’aya b’angaren Danger yace “Ina jinki babbar Ya uwa mabada mama.. Mai kike so Ai yanzu.?”

Mommy Ta jinjina kai tace “Ina yaron nan Sagir..?”

Danger yace “Yana nan ana shirye shirye dan har iyayen yarinyar sun amince da batun aure..”

“Ba wann na kiraka mu tattauna ba.. Magana ne akan wann yarinyar Ikram.. K’anwar Mu’azzam, tana nema ta tsaya min a wuya Ta hanani had’iyan miyau.. Itace babbar barazana na maganar da nake maka yanzu.. Tana da son bin diddigi da sanin komai.. Idan bamu kawar da Ita ba toh kuwa Tabbas asirina yana gab da tonuwa..”

Danger ya bushe da dariya yace “Haba kar wata mitsitsiyan yarinya Ta baki tsoro.. Idan kinaso yau d’in nan sai na shigo har cikin gidan na farka wuyanta..”
Chapter 159 · 0% Book details