← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 175

Sashe 20

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan kika fita haka mutumin da yake chasing d’inki zai ganeki.. Bari na miki dabara yanda bazai ganeki ba..” Ya k’arashe yana mai cire malfar kansa.. Lokaci guda ya d’aura mata akai yace “Yauwa he won’t be able to recognize you now.. Kina iya tafiya..” Ya k’arashe yana mai sakar mata murmushi..

Murmushin itama ta sakar masa tana mai furta ta gode..

Yanda take murmushi tana sanne ido ya mugun bawa Musaddiq dariya, Aiko nan ya tintsire da dariya.. Take Ajidde ma ta tintsire da dariya tana kuma duban fuskarsa mai lullub’e da hazon k’ura.. A haka ta fice tana dariyarsa yana dariyarta..

A b’angaren Mu’azzam kuwa tinda yabi bayan yarinyar bai cimmata ba Sai ya yanke shawarin tambayan securities na gidan gonan Ko sunga yarinyar da yake nema.. Saidai kafin ya isa wajen securities ya hango Daddy da Uncle Salman sun fito daga wani babban Office suna tattaunawa Uncle Salman d’in na nuna ma Daddy wasu documents.. Ko ba’a ce ba Business suke tattaunawa..

Suna hangosa fari’ar Daddy ya k’aru, yama daina sauraren Uncle Salman wanda shima tuni ya tsaya da bud’e takardun yana duban D’an d’anuwan nasa wanda sam inuwansu Bai jituwa..

Mu’azzam na K’arasowa Daddy ya tafi ya d’an basa light hug yana fad’in “A’a Inspector sauk’an Yaushe..?”

Mu’azzam na murmushi ya d’an sadda kai yana gaida Daddy.. Su duka biyun annuri ne saman fuskokinsu..

Uncle Salman ya d’anyi gyaran murya yace “Sirki na rungumar Sirki nan dai ba Abuja bane..”

Murmushi bai bar saman fuskar Daddy ba yake fad’in “Mu’azzam D’ah na ne ba Sirki na ba..”

Mu’azzam ya d’an kaikaito yana duban Uncle Salman, irin duban da yake masa tin yana yaro shine dai saman fuskar tasa.. Ya gaishesa cikeda girmamawa yana tambayan ya samesu lafiya..

Uncle Salman yace “Lafiya lou Mr Officer.. Saima bautan dukiyar ka da nake Kanyi wanda Yayana ya hana a cire maku Shares d’inku tun kafin rashin ‘yaruwarka..”

Take annurin fuskar Daddy ya d’auke cak.. Ya dubi Uncle Salman yace “Salman ya isa haka..”

Uncle Salman ya d’an tab’e baki kad’an yana maida hannayensa baya..

“Ni zan shige Meat Factory aiki na jirana..” Uncle Salman ya fad’i yana mai k’ok’arin shigewa.. Lokaci guda kuma ya kaikaito ya dubi Mu’azzam yace “Ina maka Barka da zuwa D’ah na Mu’azzam..!” Yai maganar murmushi saman fuskarsa.

Murmushin Mu’azzam ma ya sakar masa yana mai jinjina kai ba tareda yace komai ba..

Uncle Salman na shigewa Daddy ya kamo kafad’an Mu’azzam guda yana fad’in “Mu k’arasa ciki Inspector..”

SameenaAleeyou 📚

*GIDAN ARO*

*13*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Inne tana ganinsa Ta soma masa lale kaman ta goyasa dan murna, Aunty Shemau ma na zaune wajen tai masa Barka da zuwa cikeda kulawa. Take ta tina wayan da sukaida Mommy, bazata tab’a bari Mu’azzam d’in ya fahimci wani abu ba.
Kakarsa sai nan nan dashi take dan Farin ciki, tuni ta soma masa tayin abinci daban daban harma tambayarsa take ko akwai abinda yake so a girka masa a gurguje. Mu’azzam yace “A’a Inne zanci duk abinda ya samu, amma zanyi wanka na duba Mamy first idan yaso sai muci dinner gaba d’aya..”

“Har dare bakaci komai ba, yammacin da saura fah..”

“No Inne babu komai ai ba wani yunwa nakeji ba ma.. Zan duba Mamy sai na d’an huta..”

Mik’ewa tai tana fad’in “Mutum yayi tafiya bai saka komai cikinsa ba inyi.. Badai a gidan nan ba..” Ta k’arashe tana mai kiran ma’aikatan.

Mu’azzam yabita da kallo murmushi saman fuskarsa zuciyarsa Cikeda k’aunar ahalinsa.

“You must be jet lagged.” Musaddiq ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana mai k’ok’arin k’arasowa cikin parlorn.

Juyowa Mu’azzam yai sanda Musaddiq d’in ya k’araso fuska fal fari’a sukai handshake suna d’an hugging juna.

“Wai dama kana tafe.. Kuma shine baka fad’a mun ba.. I would’ve arranged something for you. You know this place is boring and annoying..”

Da mamaki Mu’azzam ke duban Musaddiq dake sanye da uniform na ma’aikatan gidan gona“I can see you’re better off here.. And to be honest, naji dad’in ganinka haka da uniform kana aiki..”

Musaddiq ya fuzar da fuci kad’an yana ‘yan waige waige dan ya tabbatar Inne bata wajen “Ai ni kawai matar nan ta gama dani.. Wllhi wnn jarabbebbiyar tsohuwa Ta gama dani.. Musaddiq Marwan Gamji no longer exists.. I guess fate has decided for me.. Ni kuma kalan nawa K’addaran kenan..” Yai maganar sanda suka jera suna tafe hanyar d’akin Aunty Nuratu..

Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Haka shine da kyau Musaddiq, kaga one day you’ll takeover the family business. After all, Wannan shine mafarkin da a Kullum Daddy yake.. Wani daga cikinmu ya kula da kasuwancin Ahalin.. Saidai ni tuni Allah ya k’addari ba d’an kasuwa bane kaman yanda Daddy yaci min buri ni D’ansanda ne.. Naji dadi sosai da naga kai d’in zaka cika burin Daddy.. I’m so proud of you Musaddiq..”

“Kawai ka fito fili kaima kace kana Farin ciki da k’untata rayuwata da akai..” Musaddiq yace yana kuma b’ata fuska

Murmusawa wann karon Mu’azzam yai ya kaikaito yana duban Musadddiq sosai “Watarana zaka fahimci Inne gata ta maka Musaddiq.. We all love you, and we want what’s best for you..” Yai maganar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.

Gajeren murmushi Musaddiq d’in ma yai yace “Sai ka shafe watanni Abuja kaji bana nan sannan ne zakace a dawo maka dani and your Grandma bata kyauta ba data d’auke ni..”

Mu’azzam ya d’an daga fuskarsa suna ci gaba da takawa a hankali, ba tareda ya dubi Musaddiq d’in ba yace “At least zan d’an huta da rashin jinka..”

“Au haka kace. Zamu gani ai.. I know rashina a gareka tamkar rashin police force ne..” Cewar Musaddiq daidai sanda yake tura k’ofan d’akin Aunty Nuratu sallama saman bakunansu.

Aunty Shemau suka tadda ta gama kintsa Mamy ta d’aurata saman wheelchair.. Ta fad’ad’a murmushinta tana duban Mu’azzam d’in “A a Mu’azzam ka shigo, Aiko har na gama shiryata zan kawota wajenka.. Sai gashi ka shigo ma..”

Cikeda jin dad’in yanda Aunty Shemau ke kulada mahaifiyarsa yace “A’a dama zan shigo Aunty.. Sannu da d’awainiya fah..”

Aunty Shamau tai saurin katsesa da fad’in “A’a Haba dai Mu’azzam wani d’awainiya kuma.. Kawai na d’aura daga yanda ‘yar uwata Aunty Hajara ta tsaya ne. Aunty Nuratu ai ‘yaruwa ce a garemu.. Ka daina mana godiya kaman wani hidiman muke.. Ciwo ai na kan kowa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad’unta..”

Gaba d’aya suka amsa da Ameen daidai sanda Mu’azzam ya k’araso gaban wheelchair d’in ya duk’a Aunty Shemau na kuma gyara mata kanta da ya tank’washe a karkace.

Mu’azzam ya zuba mata idanu zuciyarsa fal k’aunarta gauraye da tsananin tausayinta, Allah sarki inama wani na iya yaye ma wani cuta da ya bada duk abinda ya mallaka koda rayuwarsa ce dan mahaifiyarsa Ta sami lafiya.. Saidai ba haka abin yake ba. Allah shine yake jarabtan bayinsa da cuta ba Don ya k’isu ba saidai dan ya jarabci imaninsu da wannan cutan sannan ta kuma zame ma bayinsa na k’warai kankarewar zunubi..

Inne ce ta shigo tana tambayar ko mai maganin ta iso.?

K’irjin Musaddiq ya buga dan sai yanzu ya tina da Ajidde da yanda sukai..

Inne taci gaba da fad’in “Shemau ki kirata muji ko lafiya bata iso ba har yanzu.. Ni bana son ana sako shiririta cikin lamarin jinyar nan..”

Aunty Shemau ta d’an daburce tana fad’in “Ai Inne tace tana tafe.. Inaga abin hawa ne bata samu ba..”

Musaddiq yayi caraf yace “Wait. Wai mai maganin Mamy.. Ai kuwa tazo amma saidai akwai maganin data mance bata taho dashi ba wanda za’a bata yau d’in.. So sai ta koma, and I don’t think zata iya dawowa yau dan wajen da take zuwa akwai nisa daga nan.. And kaman hadari ne a garin..”

Duk suka juyo suna dubansa kafin Inne tace “Wannan ai shirita kenan..” Inne ta fad’i tana duban Musaddiq. Taci gaba da fad’in “Kuma sai ta rasa nawa zatai bayani sai kai..”

“Toh ai ni ta samu Inne shisa ta fad’a mun..” Baikai aya ba tace “Kai rufe min baki..” Ta dubi Aunty Shamau tace “Shemau ki kira matar nan kiji bayani daga bakinta dan ban yarda da zancen Gidado ba.”

Aunty Shemau ta jinijina kai tana fad’in “Toh Inne zan kirata..”

Shidai Mu’azzam bai bi tankasu ba hannun mahaifiyarsa rik’e cikin nasa har lokacin..
A haka har d’akin ya rage saura shi da mahaifiyarsa.. Addu’o’i ya dinga mata har Shemau ta shigo ta taddasa. Nan take sanar dashi mai magani tace ko zuwa gobe za’a iya bata idan Allah yakai rai dan lokacin ma ruwa ake tsulawa..

Ta kuma k’arasowa tana fad’in “Kaje ka huta kaci abinci Mu’azzam gani nan ga Hindu zamu kula da ita...”

Gajeren murmushi ya d’anyi had’ida mik’ewa yana ma Aunty Shemau godiya..

Yana ficewa Shemau ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da fuci a hankali.
Ta maidoda dubanta ga Aunty Nuratu tana aika mata mugun kallo

“Nakasasshiyar banza.!” Ta fad’i tana mai hankad’a wheelchair d’in da Aunty Nuratu ke kai..
**

A b’angaren Ajidde kuwa koda ta koma gida ma Kyallu ba taro ba Sisi jibaganta tai Ta jefata d’akin Tumakai tace ta Kwana dasu, D’akin da Kyallu ke aje dabobbinta harda turke tayi ma Ajidde Wanda idan tai mata laifi take d’aureta a nan itama Ta Kwana tareda dabbobin.. Haka tayi lamo jikin turken da Kyallu ta d’aure mata k’afafu tana rungume da hular da ma’aikacin Gidan Gonar ya bata wanda bata San koda sunansa ba. Saidai tuni Ta masa lak’abi da Kuran Tashe..

Dikda azaban da take ciki hakan Bai hanata sakin murmushi ba sanda ta tina had’uwarta da mutumin wanda ko sunansa bata sani ba.. Tanaji can k’asar zuciyarta tana son ta sake ganin wannan fuskar tasa mai lullub’e da hazon k’ura wanda ya sanyata dariya da nishad’i har ya mantar da Ita ukuban da Inna Kyallu ke mata..

Washe gari bata aiki Ajidde ba da kanta tai shiri Ta nufi gidan dan bama Majinyaciyar maganinta..

Kyallu tana fita Ajidde ta samu ta k’ok’arta ta tsinke Turken data d’aureta. Gefe da Gidansu akwai wata mata wacce malama ce kuma har matan aure tana koyarwa, wasu lokutan idan Kyallu Ta fice tsiddabarunta da bokancinta gidan Malama Hafsatu take zuwa domin ta taimaka mata da abinci..
Chapter 20 · 0% Book details