Sashe 162
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaunar da ita saman kujera yai yana mai rage mata mayafin kanta, ya k’arasa ya kunna air conditioning. Tana ganinsa ya fice bata iya furta komai ba Sai lumewa da tai cikin kujeran tana mai lumshe idanunta wasu hawayen na kuma siraro mata. Jim kad’an Ta gansa ya shigo rik’e da bottle water.
Ya zauna gefenta ya bud’e goran ruwan yace “Have some.”
Ba musu ta bud’e bakinta ya shiga bata ruwan a hankali. Ta lumshe idanunta bayan ta kurb’a.
Mu’azzam Ya d’aura hannunsa saman nata yana d’an Shafa tafin hannun nata a hankali alamun yana k’ok’arin yai calming d’inta.
Kallo guda zakai masa ka fahimci danne nasa yake domin ya samar mata da natsuwa. Ganin ta d’an nastu ya sanyasa matsowa kusanta sosai ya shigar da ita cikin jikinsa har lokacin bai daina murza tafin hannunta a hankali ba. A haka yakeji bugun zuciyarta na daidaita har yaji ta daina sakin ajiyan Zuciyar. Saidai yanda tai Lamo cikin k’irjinsa zaisa ka fahimci ko motsata bazataso ai ba.
Agogon dake d’aure hannunsa ya d’an duba kafin yai gyaran murya kad’an yace “Baby zanje Sallah.. Ki zauna a nan kinji I’ll be right back.”
Ta d’ago tana dubansa da pale eyes d’inta “Tsoro nakeji..” Ta fada kaman zatai kuka cikin yanayi mai tabbatar da tsoron take ji. Lokaci guda ta k’arada “Matar tana nan a nan.. Wacce Ta kashe Abba.. Zata kashemu.. Tsoro nakeji dan Allah..”
Cikeda tausayawa ya tsareta da idanu kafin ya kamo hannayenta cikin nasa “Bazata miki komai ba, kuma bazata sake cutar da kowa ba da izinin Allah kinji koh.. Ki kwantar da hankalinki.. Kinga ba ke kad’ai bane.. Nasan baki so wani abu ya sameki ko babynmu koh..” Ya k’arashe yana kai hannu kad’an saman cikinta.
Ta dubesa kad’an sai kuma ta jinjina masa kai.
Kaman wanda ya tina wani abin Sai ya mik’e tsaye yana mai kuma kamo hannunta “Taso muje.”
Nan ma babu musu Ta mik’e yana mai rufa mata mayafinta.
A tare suka fice, yanda suka tadda Mama Hindu da Aunty Larai zasu shige sashen Inne dan dama tin isowarsu Mama Hindu suke sashen. Ya k’arasa da ita ya dank’a masu amanarta dan shikam yau sai ta Allah.. Sallah ne kawai zai dinga fitar dasu amma Sai yaga yanda hali ta kaya da Mommy da abubuwan da Ta aikata.
A parlor suka tadda Ajidde sai lissafin awannin da suka kwashe saman kwalta take dan ita dai zata iya cewa bama ta tab’a yin wata tafiya ba balle mai nisa irin wann.. K’arewa jiya har kwana sukai a garin Jos dan dole suka yada zango a jos sabida yanayin hanya da kuma dare.. Shiyasa yau d’in suka iso garin da wuri.
“Yauwa Mama Hindu sa’i goma sha nawa kenan.. Gwara na rik’e da kyau dan na labartawa Inna Kyallu..” Shiru tai sakamakon hangota da tai tareda Sadiya da kuma wata matar. Dan ta gane Sadiya kam. D’aya matar ce bata ganeta ba.
Ajidde ta gaisar da Aunty Larai kafin ta dubi Sadiya dake sakar mata murmushi suka gaisa.
Mama Hindu tace “Toh Sarkin shiririta ki tashi haka nan kiyi sallah koh..”
Ajidde ta jinjina mata kai tana mai mik’ewa. Ita alla alla take suyi hiran yaushe rabo da matar Kofur Zalimu ta labarta mata yanda Aunty Nuratu ta mik’e rana guda cikin ikon Allah amma saidai ta kula kaman wani abu na damun Sadiyar sabida yanayin da ta ganta ciki hakan yasa tai shiru Ta d’an kama kanta itama.
Ana a haka Inne ma ta shigo yin sallah. Suka gaisa da Aunty Larai dan dama d’iyar k’awarta ce.
Sadiya dake zaune saman darduma k’arfin hali kurum take dan sallar ma da k’yar Ta iyayi, gaba d’aya ji take kaman jiri zai kifar da ita, ga wani irin rawar d’ari da take kaman zazzab’i ke shirin sauk’o mata.. Ga haraswa da keta k’ok’arin yunk’uro mata. Aiko babu shiri ta mik’e ta nufi band’aki saidai kafin ta isa ta soma k’waza amai. Suka yo kanta suna mata sannu.
Aunty Larai ta rik’eta har ta gama, sai jero mata sannu suke. Inne na tambayan dama bataji dad’in jikin bane.
Aunty Larai tace “Eh Inne dama kwana biyun nan jikin gashi nan ne dai kawai.. Amma Alhamdulillahi.” Ta k’arashe da murmushi.
Murmusawa Inne tai cikeda Farin ciki Hajara ta kashe Dan Mu’azzam tun yana ciki baizo duniya ba Sai ga wani nan Allah ya kuma basa, Allah kenan mai kyauta da k’ari a lokacin da yaso.
Inne tai mata fatan samun lafiya tace da Aunty Larai ta k’arasa da ita band’aki ta taimaka mata ta kintsa. Aunty Larai ta amsa tana mai shigewa da ita. Mama Hindu ma fari’arta ya k’aru sanda ta k’araso tana gyara wajen.
Suna fitowa daga band’akin suka tarar Inne da kanta taketa karkad’e mata saman gado tana fad’in Larai ta k’araso da ita ta kwantar ta. Sadiya kam duk kunya ya dabaibayeta ganin yanda suketa riritata daga yin amai guda d’aya.
Aunty Larai ta taimaka mata Ta kwanta saman gadon dan k’arfi kam bata dashi ga zazzab’i da takeji na taso mata. Haka tai lamo saman gadon abubuwan da suka faru sai Yawo a kanta suke.
Inne kaw tuni ta umarci Mama Hindu ta nemawar Sadiya abinda zata saka a cikinta. Mama Hindu kaw ta amsa cikeda kulawa kafin Ta fice.
*
A can parlorn Daddy ma Uncle Salman da Daddy suka mik’e zasu fice masallaci. Mommy tabi Daddy da kallo yanda yake kiran ma’aikatan gidan da kansa jikinsa har wani rawa yake yana sanar dasu a shirya section d’in Nuratu. Ji tai kaman ta shak’o Nuratu da ‘Yaruwarta ta murk’ushesu gaba d’aya.
Akan idanunta suma suka mik’e suna rik’e da juna suka fice. Kowa ya fice yin sallah aka bar Mommy Ita kad’ai duk’e a parlor.
Take Mommy Ta soma tunanin Ta fece a guje koda Yansandan nan zasu damk’ota.. Balle ma tasan bazasu harbeta ba.. Ta yunk’ura zata mik’e amma mai saiji tai an tokareta ta koma da baya tana sakin k’aran azaba had’ida furta “Kamin rai Mu’azzam.. Nasan kai ba mugu bane.. Ka min rai Kayi mun aikin Gafara.!” Muryarta ne ya carke sakamakon ganin da tai babu kowa wajen sai ita kad’ai. Ta shiga jada baya zuciyarta naci gaba da yankewa, sai rarrabe idanu take a tabganememen parlorn.
Tana nan zaune ta soma ganin labulayen Windows suna kad’awa su kad’ai. Mommy Ta soma firgita tana waige waige. Can ta hango wani dogon abu a k’asa kaman maciji yana nufota.. Ta saki k’ara ta mik’e a guje zata b’uya amma Sai taji kaman ana janyota baya.. Aka dawo da ita baya aka d’agata aka kwad’ata k’asa da k’arfin gaske. Ta kuma bud’e baki zata saki k’aran azaba taji kaman an danne mata bakin an hanata ihu ga azaban bugata a k’asa da ake. Can anjima aka k’yaleta tana fidda numfashin azaba da k’yar. Ta soma k’ok’arin mik’ewa zata rarrafa taji wani irin iska mai kaman guguwa ya soma majajjawa da ita nan cikin parlorn saman chandelier irin k’wan wutar nan dake mak’ale tsakiyar parlorn taji kaman an azata akai. Bakinta na rufe balle ta saki ihu.. Saitin kunnuwanta taji wani irin shewa mai kama da dariya maras dad’in sauraro... Sai taga sama kaman ya juye mata k’asa nan taji an kuma jefota daga saman an kwad’ata k’asa da k’arfin gaske. Aka bud’e mata baki ta saki ihu tana fad’in “Dan Allah ku rufa mun asiri.. Wayyo Allah ma shiga uku zan mutu.!”
Wani irin dariya taji an fashe dashi har ana shud’ewa kafin aka soma mata cakulkuli wanda banda tsantsan azaba babu komai cikinsa.. Sai sakin k’aran azaba take tana neman hanyar gudu.. Nan taji an soma d’auketa da wasu irin mari masu azaban zafi Ta ko wani b’angaren fuskarta.. Mommy ta galabaice ta gigice.. Ta yunk’ura zata mik’e tana haki sai kuma taji an jayota k’asa da k’arfi an danneta nan ta hango kujera ya mik’e ya nufota.. Ta saki k’ara tana fad’in kumin rai... Bata kai aya ba Ta soma hango wasu abu kaman kunamai bak’ak’e k’irin suna nufota.. Mommy ta tak’ure k’uryar parlor tana sururtai tana fad’in Su k’yaleta Su mata rai. Can taji an kuma d’agata ana majajjawa da Ita a tsakiyar parlorn, Sai kwad’ata ake ana bugunta. Kan kace mai tayi laushi ta kwance tsakiyar parlorn tamkar sunammiya.. Koda babu ‘yansanda dake tsaron gidan bazata iya ficewa a halin da take ciki ba balle ta gudu. Iyaka Laushi Mommy tayi Laushi, fuskarta kaw har rinewa yai alamun azaba kai kace rini aka bud’a mata tashi guda. Tai shame shame nan tsakiyar parlorn tana fidda numfashi da k’yar.
**
A haraban gidan jikin parking lot Mu’azzam ya hangi Daddy da Uncle Salman bayan sun fito daga masallaci.
Uncle Salman ya ciro wayar salulansa yana duba lokaci, nan hoton Shemau dake fuskar salulan ya bayyana, domin kuwa Dikda abinda ya faru Uncle Salman bai cire hoton Shemau a fuskar wayarsa ba. Yai tsaye yana duban hoton Daddy na hankalce dashi.
Murmushi kad’an Daddy yai kafin yace “Har yanzu kana k’aunarta.”
Uncle Salman ya jinjina kansa a hankali alamun eh.
Daddy ya jinjina kansa yace “Kayi saurin yanke hukunci ba tareda kayi bincike ba.. Ka natsu ka fahimci yanda al’amarin yake sai ka yanke hukunci na k’arshe.. Shemau tana tsananin k’aunarka kuma duk abubuwan da ta aikata tayi su ne domin ta birgeka.. Bayan abubuwan da suka faru na tabbata da kai da Shemau Kun d’auki darasin rayuwa.. Yanda Hajara ta buga wasa daku ya ishemu izna baki d’aya.. Allah ya ganar damu yasa mufi k’arfin zukatanmu.”
Uncle Salman ya amsa da Ameen D’anuwana. Lokaci guda ya k’arada “Ka yafe mun duk abubuwan da nai maka a baya.. Sabida abin duniya da San zuciya irin nawa sun rufe mun ido.. Ka yafe mun D’anuwana.”
Daddy ya murmusa had’ida girgiza kai “Babu komai Salman, abu mafi mahimmanci shine Allah ya bayyana gaskiya sann ahalinmu zai sake dunk’ulewa waje guda.. Allah ya yafemu gaba d’aya.”
Uncle Salman ya murmusa kafin ya k’araso ya rungume Daddy.
Mu’azzam daketa sakin murmushi k’arasowa yai had’ida yin gyaran murya kad’an “Can you two create a space for me..? Let me represent my Dad.”