← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 175

Sashe 140

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai lokacin Mommy Ta fashe da kuka tana nuna Daddy dake duk’e wajen yana hawaye take furta “Ka cuceni Marwan.. Ashe Nuratu tsohuwar masoyiyarka ce shine ka aurota ka kawo mun ita gida na shafe shekarun aurena Ina jinyarta.. Ashe dama Nuratu ce dalilin da yasa baka tab’a furta mun kalman so ba.. Ashe dama itace wann matar da Ta sace zucuyarka da a kullum kake ce mun mace d’aya tak ka tab’a so nima kuma rabon ‘ya’ya ne yasa ka aureni.. Marwan na rayu da k’unci cikin gidanka, na rayu tamkar Ina rayuwa da gangar jikinka ruhinka da zuciyarka yana tare da Nuratu.. Maiyasa na kasa fahimtar hakan.. Idan ban mance ba tin bayan da ka auri Nuratu ka sauya, Tun bayan ka auri Nuratu ka soma sakin jiki dani.. Meye dalili shine ina kular maka da ita.. Ashe itace wann matar da ka kasa mancewa ka kasa cireta cikin zuciyarka.. Ta yaya zaka rayu da soyayyar matar D’anuwanka cikin zuciyarka..? Ka mance mai ka sanar dani a lokutan baya da nake tambayarka wacece wann matar da tasa na kasa samun Farin ciki daga gareka.. Ce mun kai Ta mutu a zahirinka amma cikin zuciyarka soyayyarta mai wanzuwa ne wanda bazai tab’a gushewa ba har ka koma ya mahaliccinka.. Ka sanar dani cewa ita d’in Haske ce da ta haskaka zuciyarka.. Sann daga lokacin data rabu da kai zuciyarka ya disashe wann hasken ya daina haska zuciyarka.. Ashe dama Nuratu ce wann Hasken..? Ashe ni ce aka maida shashasha a nan.. Ni ce babbar shashasha ka kawo mun matar da na jima Ina rayuwa da ita matsayin kishiya ta zuciya da ruhi daga baya ka aurota ka kawota na kwashe shekaru Ina jinyarta..!” Taci gaba da kuka tana furta “Kaida D’anuwanka Kun shashantar dani.. Kunyi amfani dani, shi da matarsa sunyi amfani dani dan su cimma burinsu kaima kayi amfani da soyayyar da nake maka ka kawo mun tsohuwar masoyiyarka ina maka jinyarta.. Wacece aka cuta aka zalunta a nan..? No wonder kake k’aunar duk abinda ya danganci Nuratu.. No wonder kake wa Mu’azzam wane irin soyayya wanda bakama ‘Ya’yanka na cikinka irinsa ba.. Ashe shid’in D’an masoyiyarka ce.. Ashe soyayyar da kake wa mahaifiyarsa shi ne ya shafe shi.. Ta yaya zaka mun haka..? Ta yaya zaka mun haka Marwan..!”

Musaddiq dake tsaye daga k’ofa yaji komai cikin sauri ya k’araso ya rungume mahaifiyarsa dake kuka sosai. Hawaye na gangaro wa Musaddiq d’in lokaci guda yana duban mahaifinsa yana girgiza kai disbelievingly.

Uncle Salman ya k’arasa gaban Mu’azzam yana fad’in “Kaji duk abinda matarsa ta fad’i.. I’m sure yanzu zaka yarda dani..Zaka yarda cewa Marwan shi yake da motive na kashe Mahaifinka ba ni ba.!”

“Ya isa.! Ya isheku haka..! Ya isheku haka..!” Mu’azzam ya fad’i cikin wane irin murya yana mai dubansu da idanunsa da suka koma jazir ruwa na fitowa daga cikinsu Wanda Baida tabbacin idan wann ruwan hawaye ne.

Yakai dubansa ga Daddy dake duk’e wajen yana hawaye. A hankali ya soma takawa ya isa gaban Daddy.

Daddy ya d’ago idanunsa masu zuban ruwa yana duban Mu’azzam d’in.

“Tell me.. Da gaske ne..? Shin.. Da gaske ne.. Ka fad’a mun da bakinka..!”

Daddy yaci gaba da girgiza kai yana hawaye.

“Just answer me Uncle Marwan..!” Mu’azzam ya fad’i hawaye na tsartowa daga idanunsa.

Daddy ya mik’e da k’yar yana duban Mu’azzam d’in hawaye naci gaba da gangaro masa, ya mik’o hannunsa dake tsananin rawa yana k’ok’arin kamo hannun Mu’azzam d’in, saidai Mu’azzam bai bari Daddy ya rik’e hannunsa ba.

“Just.. answer.. my question..!” Ya fad’i cikin rarrabewan kalamai yana duban Daddyn da fuskarsa da Ta gama rinewa zuwa ja.

Daddy yaci gaba da girgiza kai yana furta “Mu’azzam.. I.. I would never kill your father.. He was my brother.. D’an uwana ne kuma mafi soyuwa a gareni.. Kuma babban abokina gareni..!” Hawaye suka ci gaba da kwaranyowa daga idanun Daddy sanda yaci gaba da fad’in “D’anuwana ne da nake matuk’ar k’auna wanda zan iya sadaukar masa da komai nawa.. You have to believe me Mu’azzam..”

Cikin zuban hawaye Mu’azzam dake girgiza kai yana duban Daddy yake fad’in “But you still chose to kill him dan ka kasance da matarsa.. How could you..?!” Yai fasali yana jinjina kai k’irjinsa naci gaba da harbawa, lokaci guda yake furtawa a hankali wann karon “You know.. I.. I trusted you.. I loved you like my own father... I believed in you... I never doubted you..!”

Daddy dake tsananin hawaye yai k’ok’arin kamo hannayensa yana girgiza kai yake fad’in “Mu’azzam..”

Fincikan hannayensa Mu’azzam yai yana duban Daddy.. Kaman mai son cewa wani abu sai kuma ya soma dubansu d’aya bayan d’aya yana fitar da numfashi a hankali.. lokaci guda ya juya yasa kai ya zai fice cikin sassarfa..

Sai kuma ya juyo yana duban Daddy yana sauk’e numfashi a hankali “You’ll never see us again.. Bazaka sake ganina da mahaifiyata ba... And this family.. Wann ahalin ya riga ya rushe..!” Yana ida fad’in haka yasa kai cikin sassarfa ya fice Yana k’unshe bakinsa da tafin hannunsa guda.

Daddy yai k’ok’arin bin bayansa yana kiran sunansa amma bai tsaya ba.. Cikin sassarfa ya nufi yanda motarsa ke ajiye ya shige ya fice daga gidan a guje.

Daddy ya dawo da baya yana duban Mommy wacce Musaddiq ke rungume da ita yana ma mahaifin nasa wane irin duba na I don’t know you anymore.

Ya nufosu zai magana Musaddiq ya dakatar dashi “No.. Don’t come near my mother.. K’uncin da ka jefata ciki tsawon shekaru is enough..” Ya dubi Mommy dake kwance cikin jikinsa tana hawaye yace “Muje Mommy.. Muje ki huta.. This isn’t good for your blood pressure.. Muma zamu tattara mu bar wann ahalin.. Ahalin ya riga da ya ruguje.!” Daga haka Sa kai sukai suka wuce yayinda Daddy ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa.

Ya bud’e idanunsa yana duban Uncle Salman dake tsaye yana sakin huci. Lokaci guda yake nunasa da yatsa “Burinka ya cika ka tarwatsa mana kan ahali.. Ahalin da na jima Ina karewa..!” Daddy yaci gaba da nunasa da ‘yar yatsa yana fad’in “Ka sani Salman, Idan wani abu ya sami Mu’azzam bazan tab’a yafe maka ba..!” Daga haka bai kuma cewa komai ba ya nufi upstairs yana jan jikinsa da k’yar.
**

Koda Safeenah ta iso ‘Yansandan ne sukai yunk’urin dakatar da ita saidai securities d’in gidan suka sanar dasu cewa ‘yar gidan ce. Hakan yasa suka k’yaleta ta shige.

Tana shigowa gidan tai tsaye haraban gidan tana k’are ma gidan kallo.. Take ta soma tuna abubuwan da akai mata a cikin gidan, bayan cire mata cikinda Mommy tai sann suka d’auketa suka kaita gidan mahaukata a maimakon gidan Mu’azzam. Hawaye suka gangaro mata. Nan ta dubi b’angaren sashen Inne ta hangi wutan sashen a kunne.. Kenan Inne tazo gari. Take taji kuka na zuwa mata sanda ta tina Mommy ta hanata sanar da Inne cewa Tanada ciki dan kawai ta cimma burinta akan cikin.

Sashen Inne ta nufa, ta murd’a k’ofan parlorn kafin ta shige, tai tsaye a parlorn na d’an lokaci kafin ta soma takowa cikin parlorn a hankali. Saman kujera Ta kwanta had’ida rungume throw pillow cikin k’irjinta, hawaye na gangaro mata Ta lumshe idanunta, abubuwan da suka faru sunata kuma dawo mata. Daga nan bacci yai gaba da Safeenah a nan parlorn Inne yanda tai kwance saman kujera.

Washe gari da safe Inne ta nufo parlor tana fad’in “Mutane sai suyita bacci dan Rashin abin yi.. Sun riga da Sun saba da wann baccin asaran.. Aiko tinda nazo kuma kunsan babu wann baccin asaran..” Birki tai tana duban mutum kwance saman kujera.

“A’a ikon Allah.. Toh Wanene wann..?” Ta tambaya tana k’arasowa

Ta k’araso sosai tana duban matar dake kwance parlornta.

Takai hannu tana k’ok’arin juyo da fuskarta take fad’in “Wacece a nan.. Maryam ko Karima..” Shiru tai sakamakon ganin fuskar Safeenah ya bayyana.

“A’ah.. Safeenah.. Ke Safeenah.. Tashi mana..!” Inne Ta fad’i tana d’an jijjiga Safeenar.

Safeenah ta soma bud’e idanunta da k’yar tana duban Inne.

Inne baki sake take dubanta “Ke lafiya..? Mai kike a nan..?”

Safeenah ta dubi Inne sai taji kuka na zuwa mata.

Inne ta zauna gefen Safeenan tana fad’in “Mai kike a nan sassafe.. Ya na ganki haka.. Inji ba wani tashin hankalin bane..?”

Kuka Safeenah ta fashe dashi had’ida fad’awa jikin Inne.

Yanzu kam abin ya soma damun Inne.. Tasan shiririta irinta Safeenah amma ganinta haka ya d’aga mata hankali “Ke Safeenah.. Meke faruwa ne wai..? Ina Modibbon.. Wani matsalan kuka samu..?”

Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “Inne.. Inne Kinsan inada ciki..?”

Inne ta d’ago ta kad’an tana dubanta sai kuma ta murmusa tace “Kan wann kikazo nan Kina kuka..? Banda abinki Safeenah wann ai abun Farin ciki ne.”

Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye “Inne Mommy ta cire cikin.. Mommy Ta bani maganin cire ciki..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.

Cikin tsananin mamaki Inne ke dubanta. Ta girgiza kai cikin rashin gane me Safeenar ke son sanar da ita.

“Ban.. Ban fahimceki ba Safeenah.. Hajara ce ta baki magani zubda ciki..”

Safeenah ta jinjina mata kai tana hawaye lokaci guda take sanar da ita yanda abun ya kasance da yanda suka d’auketa suka kai gidan mahaukata suka ajiye a cewarsu kwanyarta ya tab’u.

Inne tayi kusan minti biyar tana zaune wajen tamkar wacce aka dasa, sai juya maganganun take cikin kwanyarta “Ke Safeenah, nasan shashanci da shiririta irin naki.. Hajara tana cikin hayyacinta zata aikata abinda kikace Ta aikata..?”

Safeenah Ta jinjina kai tace “Shiyasa da nace zan sanar dake inada ciki nasan zaki sa Mu’azzam ya maidani D’akina amma sai Mommy tace kar na sanar dake sabida tana son ta cimma k’udirin ta akan cikin..”

“Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! A cikin gidan nan akai wann ta’addancin.. A cikin gidan Marwan aka kashe jinina.. Akan idanun Mu’azzam kuma babu wanda ya d’auki mataki akan abinda Ta aikata.. Toh ai ba kece ya kamata akai asibitin mahaukata ba ita Hajaran itace ta cancanci a kaita asibitin mahaukata.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye bata daina jinjina lamarin ba ta nufo waje.

Safeenah ta take mata baya.
Chapter 140 · 0% Book details