Sashe 80
Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Faty ta murmusa kad’an ta zauna tana fad’in “Bata lokaci soyayya ke d’awainiya da ita.. She will come back to her senses soon.. Ina d’aya matar tasa ne Wai..?”
Mommy Ta tab’e baki tace “Toh wa yasan masa ne Wai Kinsan bazai sanar da Safeenah komai ba dan bai d’auketa da daraja ba..”
Hajiya Faty Ta jinjina kai tace “We need to do a background check on her.. Musan ‘yar wacece kuma daga Ina take sannan ina iyayenta suke dan Kinsan dai Safeenah bayi zatayi ba wannan fad’anta ne amma dole mu dafa mata tinda ita namiji ya lashe zuciyarta.”
Mommy Ta jinjina kai tace “Kin kawo shawari.. Zan bar miki wannan a hannunki ki gano mana wacece ita sai musan ta yanda zamu b’ullo wa al’amarin.”
“Bakida matsala idan dan wanann ne k’awata.” Hajiya Faty Ta bata amsa tana mai d’aura k’afarta d’aya bisa d’aya.
**
Chief ya d’aga wayar ya k’ara a kunnensa yana furta “Yes BAT bakada matsala, komai ya tafi as we planed.. Mu’azzam Bazai tab’a samun sakamako mai inganci ba.. Yes munyi tempering samples d’in kaga hakan na nufin result d’in bazai matching ba..” Ya murmusa kafin yace “Bakada matsala BAT. We did a clean job.. I trust Maleeka, she’s good at everything.. Tana d’aya daga cikin best agents d’inmu a FCID. Yes alright shikenan sai na jika BAT..” Daga haka katse kiran yai kafin ya dawo yanda Maleeka ke kwance saman gado.. Alert ya nuna mata na naira dubu d’ari biyar ya shigo wayarsa.
Maleeka Ta zaro idanu waje tana kame baki.
Chief ya fashe da muguwar dariya kafin yace “Idan kika ci gaba da bamu had’in kai kina aiki damu yanda ya kamata haka Zakita receiving alert babu k’akk’autawa.. BAT yace a baki wannan tukurci ne for the job well done..”
Maleeka ta fuzgo wayar hannun Chief tana kuma karance alert d’in lokaci guda Ta saki murmushi tace “Idan ka rasa soyayya sai ka kama Kud’i dan kar kayi biyu babu.. Mecece duniyar dama soyayya ne da kud’i.. A rashin d’aya sai ka samu d’aya domin kaji dad’in baje kolinka..” Suka b’uge da dariya Chief na shafa k’atuwar tunbinsa wanda kaman zashi labor room, lokaci guda ya hauro saman gadon yanda Maleeka ke kwance.
**
Ko parking mai kyau bai ida ba ya fice daga motar, ya shiga tafiya cikin sassarfa ya nufi b’angaren Daddy..
Ko sallama Musaddiq bai ba ya tura k’ofar parlorn ya shiga.. Daddy na zaune tsakiyar parlorn yana shan shayi dan ko dinner bai samu yaci ba Musaddiq ya shigo parlorn cikin tsananin b’acin rai.
“This has to end now Daddy.. Bazai yuwu akan Mu’azzam a tsaya ana wulak’anta kowa a gidan nan ba.. Especially Mahaifiyarmu.. Daddy I’m so disappointed.. Absolutely disappointed.. How could you hit our Mom kawai akan b’acin ran Mu’azzam.. Just yesterday ka hanani sanar dashi wani abu da ya shafi ahalinmu ba Don komai ba Sai dan gudun b’acin ransa.. And bai jima ba kanaji kana ganni Daddy Mu’azzam ya shigo har cikin gidan nan da ‘Yansanda yai arresting Safeenah.. Yanzu kuma Daddy ka d’aga hannu ka mari mahaifiyarmu duk akan gudun b’acin ran Mu’azzam.. Who the hell is he.. Shi waye da baza’a b’ata masa rai ba..! Shi waye da kowa zai sadaukarwa mai girma sabida gudun b’acin ransa.!” Yai fasali gumi na kuma tsartsafo masa yana kuma zaro idanunsa da suka kad’a sukai ja sosai “Daddy na rantse da Allah idan Bakaje ka basa Mommy hak’uri ba, ka d’auko Ta ka dawo da Ita gidan nan.. I’ll expose everything.. And when I say everything.. Ina nufin duk abinda na sani.. Idan yaso zuciyar Mu’azzam ya kumbura kuma ya fashe sabida bak’in ciki da k’unci..!” Yana ida fad’in haka yasa ya fice.
Daddy da ya rapka uban tagumi yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa.. Meke shirin faruwa da ahalinsa ne..? Mene abubuwan da suke faruwa.. Yanzu Hajara saida ta bak’anta Mu’azzam wajen D’anuwansa Musaddiq.. Yau shine Musaddiq ke masa barazana har yana cewa zai sanar da Mu’azzam tattaunawar da yaji sunayi da Salman.. Lallai shaid’an ya shigo masa kan ahali.. Bazai bari ahalinsa ya tarwatse ba.. Jiki babu k’wari Daddy ya mik’e ya haura sama. Ya shirya tsaf kafin ya sauk’o ya nufi b’angaren Musaddiq.
Zaune ya tadda Musaddiq d’in hannunsa rik’eda pills yana k’ok’arin afawa bakinsa sai sakin huci yake.
Daddy ya k’arasa da sauri ya buge hannun Musaddiq k’wayan suka watse k’asa.
Cikeda tausayawa Daddy ke duban Musaddiq d’in.. Ya shiga girgiza kai yana duban yanda Musaddiq ke hawaye cikin tsananin k’unan rai.
Daddy ya girgiza kai yace “Akan abinda ya faru shine kake k’ok’arin maida kanka ruwa Musaddiq..? Maiyasa..? Akan na samu matsala da mahaifiyarka..?”
Musaddiq baice komai ba Sai hawayen dake ci gaba da fitowa daga idanunsa.
Daddy yaci gaba da fad’in “Musaddiq mahaifiyarka ce ta turoka ka rama mata abinda bai mata.. Shin Ita tace kazo kamin rashin kunya abinda ba d’abi’arka ba..?”
Musaddiq ya d’ago idanu masu zuban ruwa yana duban Daddy “Mahaifiyata ce Daddy.. Kuma dole nabi bayanta a lokacin da ahalin da take tink’aho dasu suka guje mata.. Daddy Menene matsalar Ahalin nan..? A koda yaushe matsalar guda d’aya ce shine Mu’azzam... Baga kai ba baga Inne ba.. Duk Kun d’auki son duniya Kun d’aura masa.. Shin Daddy mu ba ‘ya’ya bane.. Why always him..?” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.
Shiru ne ya d’an biyu tsakani kan Daddy a k’asa, kafin ya girgiza kai yace “Kar ka bari Shed’an ya sanya maka hassada cikin zuciyarka d’ah na.. Ba haka abun yake ba.. Banfi son Mu’azzam ba, dukanku Ina sonku daidai gwargwado.. Haka Inne ma na tabbata tana k’aunarku gaba d’aya.. Idan kaga anfi son wani ba shi d’in akafi so ba kyawawan mu’amalarsa da d’abi’unsa ake so.. Zuciya tana son abu mai kyau ne Musaddiq ba gurb’atacce ba.. Kai shaida ne lokacin da ka koma Fufore da yanzu ka duba Alak’arka da Inne kasan akwai banbanci.. Inne tana nuna maka asalin k’aunarta gareka a halin yanzu.. Ashe ba kaid’in bane bata k’auna.. A’a so take ka gyara d’abi’unka shiyasa take nuna tsauri akanka..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Musaddiq duk abinda nakeyi ba inayi bane don Mu’azzam.. A’a inayi ne domin ahalinmu.. Ko wani ahali sunada nasu k’alubale da suke fuskanta amma bana fata Allah ya jarabcemu da k’alubale na tarwatsewar ahali ko gaba mai muni ya shigo tsakani wanda wasu lokutan zaka samu ya shafi har ‘ya’ya da jikoki.. Musaddiq sabida wannan dalilin naketa k’ok’arin naga kan ahalinmu bai tarwatse ba.. Sannan na tabbata mahaifiyarka bata sanar dakai mai Ta aikata ba.. Amma naji dad’i da baka sani b, kuma bana so ka sani.. Sannan koda bakace naje na dawo da Hajara ba zanje na dawo da ita dukda cewa ita ta sallami kanta bani na sallameta ba..” Ya mik’e yana gyara tsayuwarsa still idanunsa kan Musaddiq d’in.
Daddy ya d’an kuma gyaran murya kad’an kafin yace “Ya kamata ka koma Fufore, zamanka a nan bazai haifar maka da komai ba illa ya kuma maidaka cikin Rayuwar da ka riga ka baro a baya..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige.
Musaddiq yai saurin ambato sunansa.
Daddy ya juyo yana dubansa.
Ya k’araso yana sadda kansa k’asa, a hankali ya furta “Kai hak’uri Daddy ka yafe mun..”
Daddy ya saki murmushi kafin ya d’an buga kafad’an Musaddiq kad’an yace “Babu komai Abubakar Allah shi maku albarka gaba d’aya.” Daga haka Sa kai Daddy yai ya fice ya nufo k’asa ya shiga motarsa dan already driver d’insa ya tafi, da kansa ya tuk’a motar ya tafi d’auko matarsa dake gidan Hajiya Faty.
**
FUFORE
Aunty Shemau Ta dubi mijinta dake zaune gefen gado yana duba wasu takardu.. Lokaci guda ya d’ago mata takardun yace “Takardun irin wad’annan ne.. A gabana Yayana Abubakar ya saka hannu cewa baison k’wandala na Kampanin, kuma zaiyi resigning daga wannan ranan.. Zai nemi nasa daga scratch..”
Aunty Shemau Ta girgiza kai cikin rashin fahimta kafin yace “Amma Maiyasa zai haka bayan Dukiyar nan mahaifinku ne ya bar maku..”
Murmusawa Uncle Salman yai kafin yace “Bakisan kalan Zuciyar Yayana Abubakar ba, yana da matuk’ar zafin zuciya da gudun duk abinda zai kawo masa magana ko raini..Yanda kika ga D’ansa Mu’azzam haka yake.. Maganganun da nake jifansa dasu kan cewa yayi tsaye akan dukiyar mahaifinmu yana son ya handame komai shiyasa yak’i barina na girma a Kampanin wann kalaman su suka tunzurasa yace na basa takarda da alk’alami ya saka hannu cewa daga wannan ranan baya buk’atar ko k’wandala na daga abinda mahaifinmu ya bar mana sannan zai tashi ya nemi nasa bazai kuma dogaro da abinda aka bar mana ba.. Shemau wad’annan takardun nake nema wanda D’anuwana Marwan ne ya b’oyesu na tabbata.. Sabida bayan rasuwar Yayanmu da aka Zo ana maganar rabon Gado sai cewa yayi babu yanda za’ayi a cire iyalan Yaya cikin Company.. Ni kuma sai na sanar dashi ga abinda Yayanmu yayi ya rubuta cewa baya son k’wandala amma sai Marwan yace “Gado Allah ne ya riga ya raba abunsa.. Ko Yaya yana so ko baya so yanada gadon mahaifinmu tunda mahaifinmu ya rigarsa rasuwa, sannan kasonsa za’a dinga bawa Iyalansa koda basa so... Bazai tab’a yarda da wannan yarjejeniyar ba kuma bazai bari na raba mana kan ahali ba.. Kinga idan na samu takardun nan ni kuma zan kai Kotu na tabbatar cewa iyalan Yayanmu basuda gado dan mahaifinsu shi da kansa ya ciresu daga cikin gadon.. Harma yayi furuncin idan inason nasa kason na had’a gaba d’aya shida Iyalansa basa kwad’ayin wannan dukiyar.. Kinga kuwa ai Shemau baki shi ke yanka wuya.. Zafin ransa ya jawo yayi wannan rubutun ya cire iyalansa daga cikin Dukiyarmu.. A yau idan na sami takardan yajejeniyar nan zan tafi Kotu kuma dole a daina cire kason su Mu’azzam a cikin Company dan Ubansu da kansa ya ciresu.. Balle ma Mu’azzam idonsa baya kan dukiyar na tabbata Marwan shima amfani yai da wanann damar yake handame nasu kason dan har yau bai d’aura Mu’azzam a hidimar Company ba.. Sannan shi Mu’azzam d’in idanunsa baya kan dukiyar sam.. Dan da alama Mu’azzam bai rage wa mahaifinsa komai ba na rashin son abun Duniya..”