← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 175

Sashe 37

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya d’aura hannunsa guda saman kud’ad’en da ake bin Su Sadiya bashi yace “Wannan bashin da ake bin Sadiya da mahaifiyarta ce.” Ya kuma d’aura d’aya hannunsa kan Naira dubu d’arin yace “Wannan muma Naira dubu D’ari ce Sadakin D’ah na Mu’azzam ga d’iyar da aka mik’a maka jagorancin ragamar aurenta Wato Sadiya..”

Kafin Malam Liman ya kuma wani magana Uncle Salman ya zaro Doguwar takarda ya mik’awa Malam Liman “Wannan takarda ce kuma shaida ce dake tabbatar da cewa d’ah na Mu’azzam lafiyayye ne baida wata cuta da zata hanasa aure, sannan genotype d’insa AA ne wanda a k’a’ida zai iya auren mace mai ko wane irin genotype koda kuwa SS ce domin na sani a akasarin masalattanmu ana ci gaba da wayar da kai cewa idan za’ayi aure a auna jini asan wani irin jini mutum ke d’auke dashi domin guje ma tsautsayi na samun yara da za’a Zo aita faman jinya suna shan wahala iyayen na shan wahala wanda ansan akwai k’addara amma idan akwai hanyar da za’a iya bi a kiyaye faruwar hakan yin hakan shi yafi alfanu dan ko a musulunci akwai rigakafi kuma an amince da hakan..”

Tinda Uncle Salman ya soma magana Malam Liman ke dubansa, ya d’an girgiza kai yace “Alhaji idan na fahimceka kaima ka biya bashin ne domin ka amsar wa d’anka auren Ita Sadiya..?”

Uncle Salman ya jinjina kai yace “K’warai kaw Malam Liman, ai idan ban b’ata ba dama aurarta zakayi ma Alhaji Isyaku ko ba haka ba..”

Malam Liman ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Amma Ai da yardar ita yarinyar da mahaifiyarta mukai za’a bada aurenta ga Alhaji Isyaku amma bamuyi dasu za’a aurarta ma d’anka ba.. Alhaji Aure ai ba abun wasa bane..”

Uncle Salman ya murmusa yace “K’warai kuwa aure ba abin wasa bane shiyasa na gabatar maka da komai tin kafin ka tambaya.. Sannan na tabbata Ita yarinyar dama auren sadaukarwa zatai dan a biya masu bashi da don soyayya ba.. Bana ko haufi yarinyar bata son Alhaji Isyaku.. Amma fah idan bazaka bamu auren ba muma zamu tattara i namu i namu.. Allah bamu Alheri..” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin janyo kud’ad’en..

Liman ya tsunduma tunanin alk’awarin taimaka masu Sadiya da yayi, yana tsoron kar wannan itace damarsu ta k’arshe kuma ta kufce masu.. Idan yarinyar da mahaifiyarta suka tafi gidan yari baijin zai tab’a yafe ma kansa bayan alk’awarin taimaka masu da yayi.. Sannan mahaifin yarinyar marigayi yana d’aya daga cikin members na committee na masallacin, bazaiso Hakan Ta faru ga ahalin marigayi ba.. Toh amma idan ya aurarta ga wannan matashi ba tareda saninsu ba shin yayi daidai..? Gaba d’aya kan Malam Liman ya cunkushe ganin dama na k’arshe na k’ok’arin kufce masa.. Take yaji b’angare mafi girma na zuciyarsa tana fad’in Kar ka bari mutanen nan su fice daga masallacin nan bakada Sauran zab’I, zaka jima kana jin ciwo idan Tabawa ta kai iyalan marigayi gidan kasu..

Lokaci guda Malam Liman ya dakatar dasu.. Mu’azzam ya saki murmushi da gefen bakinsa.

Take Malam Liman yace ya amince idan zasu sauk’e masu Sadiya nauyin bashin nan..

Uncle Salman ya juya ya dubi sauran tsirarun mutanen dake haraban masallacin dan dama ba cikin masallaci suke ba zaune suke haraba yace “Bayin Allah ku zama shaidu..!”

Nan take cika cikan aure suka had’u, aka samu waliyi, Wakili, Siga da kuma Sadaki da shaidu nan aka d’aura auren Mu’azzam Marwan Gamji da amaryarsa Sadiya Ibrahim kan sadaki Naira dubu d’ari lakadan ba ajalan ba.

Assad Daskarewa kurum yai dan ya kasa yarda da abinda Mu’azzam ya aikata kawai dan ya cimma burin bincikensa.
“You.. Are a Savage Mu’azzam Gamji.!” Assad yace yana mai girgiza kai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam d’in ya aikata.

Ana haka Wasu matasa ne suka shigo masallaci a hargitse.. Gaba d’aya su Malam Liman suka mik’e harmadasu Mu’azzam suna duban matasan daketa faman haki.. Malam Liman ya soma tambayarsu “Kai lafiya.. Lafiya kuka shigo masallaci haka nan.. Subhanallahi..!”

D’aya daga cikin samarin ya duk’a yana haki “Malam Alhaji Isyaku Chanji ne..!”

Malam Liman ya juyo ya dubi su Mu’azzam kafin ya dubi saurayin yace “Subhanallahi.. Mai ya sami Alhaji, taron nan fah isowarsa muke jira Allah baiyi za’ayi auren dashi ba.. Dan dik munyi zaton janyewa yayi..”

“Malam wllhi wasu mutane ne mukaga Sun sakasa a mota sunyi wancan hanyar dashi.” D’ayan ya fad’i yana haki.

Malam Liman dasu Mu’azzam suka dubi juna cikin kad’uwa, Sai kuma Liman ya dubi Matashin yace “Wasu mutane ne kenan suka d’aukesa.”

“Malam ina tunanin ‘yan Garkuwa ne domin duk sun rufe fuskokinsu da bak’ak’en yadi babu wanda yake iya ganin fuskokinsu..”

“Subhanallahi..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!” Abinda Su Liman ke iya fad’i kenan..

Wannan karon Assad ne ya k’araso yana tambayar saurayin ta Ina Su Alhaji Isyaku sukai..

Malam Liman yace “Ai kuwa kafin a watse daga taron nan ya zama dole a sanar da ‘yansanda.”

Mu’azzam ya dubi Malam Liman yace “Kar ka damu Malam ni d’ansanda ne zamu kula da wannan..!” Lokaci guda ya ciro wayarsa yana neman backup dan dama yasan masu bibiyan Su Sadiya ba lallai Su k’yale Alhaji Isyaku ba muddin sukaji zai aureta tinda yarinyar da ahalinta suke targeting.. Lokaci guda ya fice a harabar masallacin waya manne kunnensa.

A can gidan Alhaji Isyaku kaw labari ya isa masu cewa anga wasu mutane fuskokinsu rufe da bak’ak’en masks sun sace Alhaji Isyaku hankalin Maman Sabeera da Sabeera ya kuma tashi.. Babu shiri Sabeera ta fice ta taho gidansu Sadiya.

Masu kid’an Tabawa suna tsaka da kid’a su Tabawa na rawa Sabeera ta shigo a birkice, tayo kan Sadiya Ta cakumota tana jijjigata take fad’in “Ina mahaifina Sadiya..? Ki fad’a mun su wanene suka sace Babana.. Ki fad’a mun Sadiya..!”

Toh fah Wannan shine ana wata ga wata Wai an sace Alhaji Isyaku Ango. Cak sautin kid’an k’waryar ya daina tashi, su Tabawa kaman wad’anda aka zare masu battery tuni suma suka dakata da rawar da suke.. Kowa ya juyo yana duban Sabeera dake jijjiga Sadiya tana fad’in ina Takai mata mahaifi.

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*22*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Su Tabawa da ayarinta tuni suka fice Tabawa tana fad’in “Ku tashi muje zama bata ganmu ba an sace ango.. Wayyo Allah kud’ad’ena. Na shiga uku ni Tabawa waye zai biya bashin nan yanzu.. Wayyo Allah na shiga ukku. Gaskiya Sadiya farar k’afa gareki.. Ace aure biyu ana fasawa kaman bakin uwa.. Koda yake dama ‘yar bakin uwar ce ke.. Matsiyata masu bak’in k’addara..!” Haka Tabawa ta dinga ihu a lungun hannu aka tana tsine masu Sadiya, Ita damuwarta ba b’acewar Alhaji Isyaku bane bashin su Sadiya ne da zai biya shine damuwarta..

A nan cikin gidansu Sadiya kaw kuka kawai Sadiyar take tana duban Sabeera dake ci gaba da jijjigata wacce itama kukan take, cikin kuka Sadiya ke furta “Sabeera ban sani ba.. Wllhi ban San komai ba, ki yarda dani ina zan d’auki Mahaifinki na kaisa..”

Cikin kuka Sabeeran ma ke girgiza kai tana ci gaba da jijjiga Sadiyar take fad’in “No you are a liar Sadiya.. You lied to me once.. What makes you think zan yarda dake wannan karon.. You are nothing but a gold digger, I was so stupid that I couldn’t see your true color tuntuni.. I no you never loved my father.. Sabida kud’insa ne kika amince da aurensa.. Kawai kud’insa kike so shiyasa kika sa aka sace shi Dan kar ki aure shi dan ki karb’i kud’ad’e masu yawa daga wajensa.. I feel like I don’t know you Sadiya. Tinda kikayi tarayya da D’antadda irin Sagir, zakiyi da ‘yan Garkuwa ma. You planned all this Sadiya.. Just admit.. Why can’t you admit it already..!” Ta k’arashe tana mai tura Sadiyar da k’arfin gaske.. Sadiya bata fad’a ko Ina ba Sai jikin Mu’azzam da shigowarsa kenan gidan.. Hannayesa duka biyu yasa ya tallafota.

Sadiya ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban mutumin data fad’o jikinsa wanda ba kowa bane face wannan D’ansandan wanda sukai karo kwanaki kuma shine mutumin dake bincike kan mutuwar Sagir.

Su duka biyun suka k’ura ma juna idanu.. Lokaci guda taji ya rik’o hannunta yana fad’in “Let’s go, you are no longer safe here.. Let’s go now..!” Ya k’arashe yana k’ok’arin janyo hannunta da k’arfin gaske.

Sadiya da tsananin tsoro ya gama cikata Ta soma k’ok’arin k’wace hannunta tana fad’in “Wait.. Ina zamuje..? Ina zaka kaini.. Just let me go.. Ka sakar min hannu.. Ka sakeni Ina zaka kaini..!” Ta finciki hannunta da k’arfin gaske tana huci take dubansa, lokaci guda take furta “Just because you are a Corp doesn’t mean you can arrest me without any allegation. Mr Inspector..!”

Mu’azzam dake tsananin huci yana dubanta, lokaci guda ya kuma takowa gabanta, wani irin duba yake mata wanda za’a iya kiransa da duban tsana “You wanna know who am I to you..?” Ya kuma matsowa kusanta sosai kafin yace “Well, I’ve every right over you.. Idan nace maku ni ne mutumin da ya biya bashin da kuka ciwo ma kanku fah..!”

K’irjinta ne yai wani irin bugawa tana dubansa da idanunta wanda har yanzu hawaye ne kwance cikinsu. Lokaci guda kuma taji wani irin k’arfin zuciya na zuwa mata bayan tulin iftil’ai na rayuwa data gani.. Hawaye ne a cikin idanunta amma murmushin takaici ta sakar masa tana duban cikin idanunsa ba tareda wani tsoro ko d’ar ba tace “A cheap low life police officer like you.. Wanda bai dogara ga komai ba face cuku cuku da karb’an cin hanci da rashawa bashida wad’annan kud’ad’en da kake mafarkin ka biyasu a matsayin bashi na ni Sadiya.. Ka fahimta..?!!” Ta k’arashe tana sakin huci.

Da mugun mamaki Mu’azzam ke dubanta idanunsa na kuma kad’uwa,wani wulak’antaccen kallo yake mata daga sama zuwa k’asa yana tuna duk maganganun da ake fad’i na rashin kamun kai gameda da Ita ya kuma tuna maganan da yanzu Ta fad’i masa cewa cheap low life police Officer mai karb’an cin hanci da rashawa irinsa bai isa ya biya bashin da ake binta ba. A hankali yake kad’a kai idanunsa na kuma yin jazir “You’ll repeat this..! Zaki maimaita wannan idan sunana Mu’azzam Abubakar Gamji.. Zaki maimaita..!”
Chapter 37 · 0% Book details