← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 175

Sashe 44

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallar asuba da batayi bane ta soma tinawa.. Babu shiri ta nufi wata k’ofa dake nan cikin d’akin wanda takeda tabbacin bathroom ne. Aiko tana tab’a k’ofar ya bud’e, kaman yanda take zato bathroom d’in ne komai na buk’ata akwai a ciki sannan komai Sabo ke sealed ba’a bud’e ba.. Harta toothpaste da toothbrush dik sabbi ne jere a wajen. Ta tab’e baki kad’an ba tareda tace komai ba.. Ita a halin yanzu babu abinda take so face ta ganta a gida.. A gurguje tai alwala ta fito tana tinani ina zata kalla ya zamto mata alk’ibla.. Bata ida tinanin ba ta hangi k’aton darduman turkey an shimfid’a ready to pray.. A ranta tace k’ila mata mai d’akin ne ta shimfid’a.. Sauri sauri ta isa saman darduman ta tada sallah.. Koda ta idar mik’ewa Tai tana kuma bin d’akin da kallo wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, harta wardrobe d’in da yake transparent tana iya hango kaya jere cikinsa. Ta d’an tab’e baki a hankali kafin ta nufi k’ofa tana tinanin toh ina ne nan..

A hankali ta tab’a k’ofar d’akin ta bud’e.. Nan taga corridor ne madaidaici da k’ofofin da bazasu gaza guda uku ba. Tana tafe ta hango stirs wanda zai sauk’arta k’asa kenan. Nan take ta nufo staircase d’in zuciyarta bai daina yankewa ba. D’aga idonta da zatai ta hango wani k’aton hoto da akayisa in full kaman ka kira mutanen ciki suzo.. Mu’azzam ne da wannan Matar da taga hotonta a d’aki.

Take ta tina walak’acin da ya mata a daren jiya. Ganin fuskar tasa take kaman wani bak’in kumurci. “Rascal..!” Ta fad’i a hankali tana aika masa mugun kallo dukda kuwa cewa Sunyi kyau sosai kaman ka sure ka gudu, ko ba’a ce ba hoton ran aurensu ne dan sunyi shiga ne irinta Amarya da ango. Dikda manyan kayane a jikinsa tsaf ta ganesa, sky blue shadda da akai mata d’inkin babbar riga mai gajeren hannu daga ciki sai hular dake kansa navy blue zanna bukar mai k’anan zane tasha tangaran sai k’yalli take. k’afarsa rufe cikin bak’ak’en covers.. Yayi kyau sosai dan ba k’aramin karb’ansa manyan kayan sukai ba. Ita kaw matar bridal gown ne jikinta all white tayi kyau sosai itama fuskarta cikeda annuri wanda da gani zaka fahimci tana tsananin k’aunar mijin nata..

A fili Sadiya tace “Bakiyi dacen miji ba.”

Sadiya ta k’ura masu idanu tana tinani Wato gidansa ne kenan nan.. Toh ina matar tasa..? Rashin samo amsar da batai ba ya sanyata tab’e baki a hankali tana mai kuma dubansa cikin hoton, dan a hotonma fuskar nan tass babu wani annuri.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta furta a fili “Mugun banza azzalumi.!” Tai maganar tana dungurinsa cikin hoton.

Mu’azzam dake zaune dining area dik yana kallonta ta cikin k’atoton mirror d’in da aka k’awata dining area d’in dashi.

Yi yai kaman bai ganta ba kuma baiji mai take cewa ba, yaci gaba da abinda yake yana kallon yanda take sakin huci tana dungurin hotonsa tana fad’in mugun banza

Yai murmushi yana dubanta ta mirror, saida yai sipping tea d’in sau biyu kafin ya bud’e murya yace “Welcome to GIDAN ARO.. Where everything here doesn’t belong to you..!”

Sadiya ta juyo a razane dan sam batasan da mutum a wajen ba.. Mu’azzam ya taso yana takowa a hankali har dai ya k’araso kusanta.. Hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa yake furta “Take your eyes off my photo, I’m not the rich husband you’re looking for..!” Yai maganar yana mai mata nuni da hotonsu shida Safeenah da idanunsa.

Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Correction Mr Inspector, bani na kawo kaina nan ba, as a matter of fact kidnapping d’ina akai.. Zan fi kowa Farin ciki idan ka maidani yanda ka d’aukoni.!”
Ta k’arashe cikin tsimewa itama.

Ya murmusa kad’an da gefen bakinsa yana mai kuma takowa gabanta.. Lokaci guda ya tsime kaman dai bashine mai murmushin ba. Nan yaci gaba da furta “If you cooperate with me and do exactly as I say zaki koma yanda kika fito, because I don’t intend to keep you here for good.. Like I told you gidan nan tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Kinsan ance ba’a baje Koli a a GIDAN ARO.. Toh kar kiyi gangancin baje naki kolin domin dik gidan da akace na aro ne any moment any time za’a iya sallamanka without notice..”

Ya k’araso jikin hoton yana mata nuni da Safeenah “Kin ganta nan, she’s the lady of this house.. Aro aka baki na wutin gadi..”

“Ban nema ba balle a bani Aro.. So don’t delude yourself.!”

Da mamaki yake dubanta, dik ajiyeta a wannan store d’in da yayi jiya a matsayin warning ashe bai shiga kanta ba. Ya kula bakinta sam bai mutuwa. Ya tina yanda daren jiya baiyi bacci ba har saida ya dawo ya d’auketa cikin hannunsa ya kaita d’aki ya kwantarta ya tabbata ta samu sound sleep. Da yasan wannan bakin tsiwar nata bazai mutu ba da barinta yai a wannan d’akin ta Kwana ko zatafi shiga hankalinta.

Takowa kusanta yake tana jada baya, bai tsaya ba har saida ya k’araso kusanta sosai ya tabbata bata da sauran wajen gudu kafin yai mata rumfa da kansa ya bud’e duka hannayensa ya tareta dasu yanda ko k’wakk’waran motsi bazata iya ba “Mai Kikace.. Maimaita abinda kika fad’a.!”

Kasa magana tai Sai k’walla dake k’ok’arin ciko idanunta.

Dubanta yake tin daga fuskarta mai cikeda rauni gauraye da tsoro kafin ya murmusa kad’an yace
“Be careful how you speak to me.!” Yai maganar yana duban d’an bakinta wanda kaman ba daga nan maganganun ke fitowa ba.

Saida ya tabbata tsoro ya shiga jikinta kafin yaci gaba da fad’in “Kar ki damu everything here is free of charge.. You can sleep in my wife’s bedroom, free of charge.. You can use her kitchen, free of charge.. You can watch her television, free of charge.. You can have all the luxury here free of charge.. You don’t need to pay with your body.. Kaman dai yanda kika saba..!” Ya k’arashe yana mai dubanta daga sama zuwa k’asa.

K’walla masu zafi suka ciko idanunta.. Ta lumshe su a hankali hawaye suka gangaro mata.

“I can’t take this insults anymore.. Tell me.. Ka sanar dani mai kake nema wajena.!”

Ya murmusa kad’an kafin yace “Worse abinda zai faru dani a rayuwata shine a ganni tareda ke... Amma idan har sai nayi hakan na gano makashin ‘yaruwata, zanyi.. Zanyi dan na gano gaskiyar komai yanda akai aka samu gawan ‘yaruwata tareda watsettsen saurayinki who was about to marry you.!”

Sadiya ta murmusa hawaye na gangaro mata lokaci guda tace “Ashe K’anwarka ma tanada connection da Sagir tinda har aka gano gawansu tare.. Ashe bani kad’ai bace dai watsettsiya...!

Katseta yai da fad’in “Don’t you dare mention my sister..! I forbid you..!” Yai maganar yana mai nunata da yatsa hannunsa har rawa yake.

Taji tsoron yanayin da taga ya shiga, lokaci guda kuma sai taji kaman bata kyauta ba ganin cewa k’anwar tasa ta rasu bai kamata tai magana irin haka akanta ba koda Mu’azzam ya gaya mata maganganu marassa dad’i.. bata iya k’ara furta komai har ya fice daga gidan cikin sassarfa..

Haka Mu’azzam ya fice da tinanin maganganun Sadiya cikin zuciyarsa. Cewa k’anwarsa tana da connection da Sagir.. Bazai tab’a yarda Ikram tana da connection da wannan d’anta’addan ba... No no no baima so ya amince da hakan.. Wasu irin hawaye ne yaji suna k’ok’arin ciko idanunsa.. Maiyasa all of the sudden yaji ya fara tunanin binciken k’wak’waf da yake yi.. Ji yake cikin tone tonensa zai digging abinda zuciyarsa bazata iya d’auka ba.. Hawaye ne yaji from no where suna gangaro masa.. Ya shiga girgiza kai yana furta “No no.. Sace Ikram akayi.. Batada wani connection da wannan mutumin.. Babu wanda yakeda connection da wannan d’anta’addan dik cikin ahalina...” Birki yai had’ida kifa kansa saman steering yanaji zuciyarsa na barazanar tarwatsewa.

A b’angaren Sadiya kaw yana ficewa itama Ta nufo waje da zummar ficewa daga gidan.. Saidai tana sako k’afa taga k’artan karnukan nan suna nan a harabar gidan suna shawagi..

Ta koma da baya had’ida jinginuwa jikin garu Ta lumshe idanunta hawaye na gangaro mata. Umma da ‘yanuwanta kawai take tunawa tasan dole suna cikin damuwan rashinta.

Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’e ta komo cikin gidan, ga wani irin yunwa dake azalzalanta.. Nan saman dining table d’in taga mug na tea, da alama dai shima a nan yaci karin kumallon nasa.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta nufi hanyar da take tinanin kitchen zai kaita.. Aiko kitchen d’in ne wadatacce wanda shima aka k’awatasa da kayan alatu irin na zamani kana gani kaga gidan Amarya. Tai tsaye tana k’are ma kitchen d’in kallo sai kuma taji hawaye na k’ok’arin ciko idanunta, bata son tab’a duk wani abu da ya shafi wannan gidan amma batada wani zab’i cin abinci dole ne a wajen ko wane rayayye abin halitta.. Fridge ta bud’e tagansa shak’e da abubuwan buk’ata.. Ala dole ta had’a mai zata had’a dan ta saka a cikinta.. Saida ta koma d’aki ta d’auki sabbin abubuwan da takeda tabbacin shi ya aje su kafin tai brush ta fito taci sandwich d’in data had’a Wanda take jinsa kaman magani take taunawa.
Zama tai ta rapka tagumi tana tinanin rayuwa da yanda yake zuwa mata.. Mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna buk’atar ta bazataso taita zama a wannan kurkukun ba.. Zatayi k’ok’ari taga Ta bar wannan gida Ta koma ga ahalinsa as soon as possible.

**
A b’angaren Mu’azzam kaw saida suka had’u da Assad ya basa update cewa basu iya gano masu lambobin da ake tura masa sak’o dasu ba.. Lambobin basa kan waya sannan ta iya yuwa ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in yayi disposing d’insu. Nan yake sanar dashi tareda Maleeka sukai k’ok’arin gano mai lambobin amma basu samu ba.

Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Maleeka kuma.?”

Assad ya jinjina kai yace “Kasan itace computer guru.”

D’an Jim yai sai kuma ya jinjina kai ba tareda yace komai ba.
Chapter 44 · 0% Book details