← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 175

Sashe 2

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutumin ya kuma murmusawa kafin yace “Mr Officer, if you think you’re goin to get something from me you’re quite mistaken..” Cak ya katse maganar nasa sakamakon ganin hoton da ya aje masa saman table d’in..

“Im gonna ask you for the last time.. Tell me everything you know about this guy..!” Mu’azzam ya k’arashe yana mai matso da fsukarsa dab kusan na mutumin yatsarsa manuniya na saman hoton yana nuna hoton da Ita....

K’uri mutumin yai yana dubansa kafin ya saki murmushi kad’an yace “You won’t get anything from me, Mr Officer..?”

Wani irin zabura Mu’azzam yayi saida yai fatali da table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin.. Ya finciko wuyan mutumin ya matse ya had’uda da garu yana mai ci gaba da sakin huci “I am not playing games with you.. Now tell me.. Ka fad’a mun mai ka Sani akanshi..? Wanene shi..?”

Mutumin da yaji matsa idanunsa sun firfito waje yana neman hanyar da zai shak’i iskan numfashi ya fitar da k’yar yake jinjina kai ma Mu’azzam alamun ya sakar masa wuya zai fad’i abinda ya Sani...

Jifa dashi Mu’azzam yai yana yarfe hannunsa kafin ya isa gabansa ya d’an duk’a kad’an “Tell me..” Ya fad’i idanunsa akan mutumin..

Da k’yar mutumin ya d’an iya mik’ewa ya zauna dirshan a k’asa kafin ya soma fad’in “Baida kowa.. D’an ta’adda ne.. Baida kowa a garin nan, sannan bansan daga Ina yake ba.. Amma nasan a nan yake running businesses d’insa..”

Cikin zak’ewa Mu’azzam yace “Ya akai kasan d’anta’adda ne...?”

“Sabida ni kad’ai yake zama yayi min firan da bai wuce mintoci....”

Ya jinjina kai kafin yace “What was his business..?”

Girgiza kai mutumin yai kafin yace “Komai ma business d’insa ne as far as wannan kasuwancin ta’addanci ne...Iyakacin abinda zan iya fad’a maka kenan..”

Mu’azzam ya kuma gyara tsugunonsa idanunsa nakan mutumin kaman mai tsoron kar yayi losing sight d’insa kafin yace “Baida kowa.? Baida tak’amammen aboki ko wani abu mai kama da haka.. Tell me..”

“As I told you , mutumin nan ganinsa kawai muke yazo ya sai sigari yasha ya k’ara gaba.. Amma wata rana naji yana waya kaman da wacce zai aura ne..”

“Wacce zai aura..?” Mu’azzam ya tambaya cikin son jin yaji komai.

Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai wacce zai aura.. Dik a wanann daban ni kad’ai yake zama yayi hira dani da bai wuce na tsawon minti uku zuwa biyar.. “

Tura masa kujera Mu’azzam yai yace “Tashi ka zauna sannan ka sanar dani firan taku..”

Saida mutumin ya d’an fuzar da huci kafin yace “Amma Rankaidad’e bazaka bari a ajiyeni a police station ba dan ka gani da idanunka shago na bana sayar da komai, bana sayar da tabar wiwi sannan bana sayar da k’waya.. Karan sigari kawai nake saidawa Rankaidad’e.. Dan Allah ka taimakeni kar a ajiye ni a nan.. Bana komai illegal I promise..”

“Kar ka damu idan muka tabbata baka running wani illegal business na maka alk’awari bazamu ajiye ka a nan ba.. Yanzu ka fad’a mun hiranku na k’arshe da wannan mutumin..”

Saida ya gyara zamansa kafin ya soma fad’in “A satin da ya gabata yazo k’ofan shago na, as usual ya sayi sigari na kyauta masa lighter.. Kaman ko yaushe bai shiga cikin mutanen dake zama a daban k’ofan shago na ba.. Ya koma gefe ya soma zuk’ar sigarinsa.. Ya gama shan sigarinsa yazo wajena karb’an canji dan dama sanda ya sayi sigarin ban basa canji ba dan babu canji, nace masa ya gama sha kafin a samu canji.. Toh tsayuwarsa yana jirana na had’o masa kan canji na basa yai daidai da fara ringing d’in wayarsa..Ya ciro wayar yana amsawa. Cikin maganganun nasa a waya na fahimci da wacce zai aura yake waya.”

Mu’azzam yace “Bakaji wani abu ba gameda budurwar tasa.. Maybe a ina take kokuma wani abu mai kama da haka..?”

“Inspector I told you I was only his smoking buddy.. How would I know all the details..!”

Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Do you really want us to play this game..? I can assure you I know exactly when to throw my card..” Ya k’arashe yana mai waina zobensa saman table. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Nasan baka Sani ba, but I do know a lot of things about you.. I know about your criminal records.. Nasan abubuwan da kake aikatawa wanda zasu kaika jail ka shafe shekaru da Dama.. But If you cooperate with me, zanyi iya k’ok’arina a kotu to make sure anyi reducing sentences d’inka.. So ina shawartanka don’t let me lay my cards first.” Ya k’arashe yana tsaida zoben dake faman wainuwa saman table da yatsarsa guda...

Murmushi mutumin yayi yana mai jinjina kai dan yasan business na drugs da yakeyi zai iya kaisa gidan yari.. Yai k’uri wa Mu’azzam yana dubansa wanda babu alamun tsoro Ko d’ar a tattare dashi.. Kaman bazaice komai ba Sai kuma yace “I need protection..”

Mu’azzam yai masa k’uri yana dubansa kafin yace “So you do know something..?” Yai maganan yana jinjina kansa yana kuma tabbatarwa plan d’insa really works.. Gyara zamansa yai had’ida d’aura k’afa d’aya bisa d’aya still yana fuskantar mutumin yace “I knew it.. I was right all along..”

K’uri mutumin yai masa gajeriyar murmushi saman fuskarsa “But you need to guarantee my safety first, Inspector..”

Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai furta “We will give you protection here.. I promise.. Just tell me what you know..”

Ya jinjina kansa a hankali idanunsa akan Mu’azzam sann ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya ciro k’aramar takarda a nannad’e.. Lokaci guda ya mik’a ma Mu’azzam yace “Wannan zai iya amsa maka duka tambayoyin ka.. Duk abinda kake so ka Sani gameda mutumin nan..”

Mu’azzam yasa hannu ya amshi takardan ya warware.. Address ne na wani gida a jiki..

Ya d’ago yana duban mutumin da alaman tambaya..

Jinjina masa kai mutumin yayi yace “Kaje wannan Address d’in zaka sami amsoshin da kake nema...”

Mik’awa tsaye Mu’azzam yayi yana juya address d’in wanda yake a garin SULEJA...

Bai kuma ce ma mutumin komai ba yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa.. Mutumin na kiransa yana fad’in yaushe za’a sake shi ya tafi gida.. Inaa ko zarafin juyowa Muazzam baiba balle ya amsa Sa.. Yana fitowa ya tadda Assad yana jiransa.. Cikin sauri Assad ya take masa baya yana fad’in Ina zasuje..

Bai tsaya amsa Assad ba har saida suka k’araso yanda motocinsu Ke ajiye.. Ya dubi Assad yace “You drive..”

Assad yace “Destination.?”

Takardan dake hannunsa ya d’an warware ya nuna masa..

“Suleja..?” Assad ya maimaita a hankali kafin ya girgiza kai kad’an yana mai capke d’an makullin da Mu’azzam d’in ya jefo masa..

“Do we have a mission there Inspector.?” Cewar Assad dake k’ok’arin key wa Mota..

“Idan munje zaka gani..” Mu’azzam ya basa amsa yana mai kuma duban takardan dake hannunsa..

Maleeka da tin fitowarsu take hangensu, Ta nufo waje cikin sauri amma saidai bata cimmasu ba, cikeda takaici take ciza baki kafin Ta koma cikin building d’in..

**

SULEJA

Wata matace zaune tsakar gida tana tsintar wake, yara guda biyu maza zaune gefenta saman tabarma suna cin abinci.. D’aya bazai gaza shekaru 12 ba d’ayan kuma bazai gaza 9 ba.. Sai cin abincin suke hannu baka hannu k’warya alamun yunwa taci ta cinyesu...

“SADIYA..! SADIYA..!! Ke SADIYA..!!” Matar Ke fad’i daga nan yanda take zaune tana tsintar wake..

Ganin wacce ta kira d’in bata fito ba ya sanyata yin k’wafa tana mai gyara zamanta saman kujerar had’ida daidaita zaman parantin da waken Ke ciki saman cinyarta “Kar Allah Sa ki fito daga cikin d’akin nan.. Idan yunwa ta azalzaleki zaki fito.. Ke kanki farau ake saka aure a fasa..? Ai ke abinma ki gode ma Allah ne da yanzu kin je kin auri wanda ba’a san danginsa ba.. Wa yasani ma ko d’anta da ne Ko d’an fashi da makami ne, ko kuma ma Dan garkuwa ne da mutane.. Ki gode ma Allah baki da rabon shan wahala ne tinda gashi har shagulgulan bikunku aka fara d’aurin aure kad’ai ya rage aka nemesa aka rasa sa, Allah kad’ai yasan shid’in wane irin mutum ne dan ko danginsa bamu tab’a gani ba sai wannan Kawun nasa.. Da yanzu kin aure shi d’in Allah kad’ai yasan irin masifar da zai janyo miki, ke da gidanki saidai ki rayu ciki tamkar kina a GIDAN ARO ne..” Ta k’arashe tana bushe waken dake cikin parantin...

Tana busar waken take ci gaba da furta “Ni duk bama wannan ba uban bashin da mukaci ne na fitan biki ya tsaya min a wuya da yanda zamu kwashe da d’inbin mutanen dake binmu bashi... Oh Allah dai ya fiddamu..”

Bataji sallamar ba sai Muryar data jiyo tana furta “K’warai kuwa Uwani gwara ki nemo hanya tun wuri dan yau bani fita cikin gidan nan sai kin lale min kud’ad’e na.. Yo Ai ni bani nace kiyi bukin k’arya ba.. Harda cewa d’an gidan Babban k’usa a k’asar Amurka ‘yarki zata aura.. Toh maza maza idan ma guduma ne ba k’usa ba a fiddo mun kud’ad’ena yanda suka shiga suka fita ehe..” Ta k’arashe tana wane irin jijjiga

Mata mai tsintar waken murmushi ta saki wanda hausawa Ke ce ma kafi kuka ciwo
“Tabawa kece tafe, k’araso k’izauna mana, ga wajen zama..”

“Ank’i a zauna d’in.. Nace bazaa zauna d’in ba.. Yo ni naga wajen zama ne a nan..”

“Haba Tabawa mu shiga daga ciki sai muyi maganar..”

“Bazan shiga ba..!” Tabawa Ta fad’i tana mai fatali da parantin waken da matar Ke tsincewa Ai ko sai cikin abincin da yaran ke mamuk’a...

Wane irin kuka k’aramin ya fashe yana birgima yana fad’in sai an biyasa abincinsa da aka b’ata...

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*02*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tagumi Ta rapka tana duban yaran yanda suke kukan basu k’oshi ba.
“Oh ni Uwani naga takaina, yanzu ta Ina zan samo kud’ad’en nan..”

“Umma bamu k’oshi ba..” K’aramin yaron ya fad’i yana mutsuke ragowar hawayen dake idanunsa..

Janyo yaran tayi jikinta tana lallashi tana fad’in suyi hak’uri yanzu zata girka masu ragowar waken data tsince..
Chapter 2 · 0% Book details