← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 175

Sashe 114

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tai zaune tana tinanin ina ta yar da sisin kobon. Wann sisin kwabon shi kad’ai ne abinda yake tuna mata bayanta. Bazataso ta rasa sa ba. Mik’ewa tai ta janyo akwatin da suka tara kayayyakinsu na wancan gidan. Addu’a kurum take Allah yasa yana ciki. Ta shiga bincikawa tana duba cikin akwatin.. Babu wann sisin kwabon babu alamunsa. Tai zaune tana tinani.. Watak’ila a Suleja ta yasar shi.. Shikenan Ta rasa abinda yai mata saura na bayanta. A hankali ta koma ta zauna tana girgiza kai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta “A’a a’a bazan rasa wann sisin kwabon ba.. Shine kad’ai saura mun.. Zanci gaba da nemansa cikin kaya har Allah yasa na samu.. Nasan yana nan mak’ale wani wajen.. Zanci gaba da dubawa sannu a hankali har na sameshi..” Ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka gangaro mata.

**

Ta yanda Mommy take shiga bata nan take fita ba “Sabida bakida hankali ke shahshasha ce wacce ta rako mata duniya koh.. Shine kika d’ibi k’afafu kika tafi gidansa kikaje kina haukar nan naki da bazaki daina ba koh.?!”

Safeenah ta turo baki tana jin zuciyarta na tashi kaman zata amayo da cikinta. Yamutsa fuska tai tace “Mommy dan girman Allah ki barni naji da abinda ke damuna.. Ni wllhi ganin matar Mu’azzam da nai ya haifar mun da tashin zuciya.. I already have headache dan Allah ki k’yaleni haka nan Mommy, Please..!” Ta k’arashe tana mai d’ago wa mahaifiyar nata hannu.

Cikeda takaici Mommy tace “Ai idan baki cire wann jarababben cikin zuciyarki ba haka nan zaki k’are da wahala.. Jarababbiyar banza ‘yar wahala.”

“Mommy idan dai akan my Halal ne ki kirani da sunan da kikaga dama wllhi wllhi babu abinda zai rabani da mijina.. Ko shi Mu’azzam d’in bai isa ya raba aurenmu ba.. So ki daina bama kanki wahala kan My Halal.”

Throw pillow dake gefenta ta jifawa Safeenar dan takaici “Kinci ubanki keda Halal d’in.!” Hakan yai daidai da mik’ewar Safeenah a guje ta nufi guest toilet tana k’waza amai..

Mommy ta bita da kallo baki sake ita ta ma mance Safeenah ciki gareta.

Sallaman Mu’azzam ya dawo da hankalin Mommy..

SameenaAleeyou📚

*GIDAN ARO*

*58*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Zabura Mommy tai babu shiri ta nufo k’ofar tana k’ok’arin taresa take fad’in “Mai ya kawoka gidan nan.. Kai yanzu idan kanada kunya sai ka kuma tako k’afarka cikin gidan nan bayan dik kalan rashin mutuncin da ka fesa mana.. Idan gaisuwa ce ya kawoka ni Hajara na yafe bani buk’ata a k’ara gaba ehe.. Idan kuma k’anina mahaifinka kazo gaidawa shima kasan yanda zaka samesa.. Kaje can company ka samesa amma ba gidana ba.. Sann Idan tak’amarka shine nan d’in gidan mijin mahaifiyarka ne Toh itama bata a nan gidan balle kace zakake shigowa kanka tsaye duk sanda kaga dama.!” Ta k’arashe tana huci tayi famkam famkam Ta cike k’ofar gaba d’aya.

Mu’azzam baice mata komai ba Sai dubanta da yake cikeda mamaki. Wai Mommy ke masa duka wad’ann abubuwan. Matar da a baya bata nuna masu komai ba face zallan k’auna.. Abubuwan da take masa shi gani yake yayi yawa ace duk kawai kan laifinsa k’wara d’aya take hukuntasa haka. Ya fara shakkun k’aunar da Ta nuna masu a baya shida ‘yaruwarsa da mahaifiyarsu.

Musaddiq ya k’araso yana girgiza kai ganin ko damuwa da cewa gidan akwai ma’aikata sann ga k’annensa Mommy batayi.. Ita kawai damuwarta ta tozarta Mu’azzam.

“Mommy dan girman Allah wann wane irin abu ne.. Mommy will you please..”

Dakatar dashi Mu’azzam yai ta hanyar d’aga hannu kafin ya dubi Mommy na d’an lokaci kaman mai karantarta. Sai jijjiga take nan bakin k’ofar tana addu’a cikin zuciyarta Allah hana Safeenah fitowa daga band’akin nan a yanayin da take.

Ya d’an d’ibi dak’ik’ai a haka kafin ya jefa hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ba tareda ya furta komai ba ya juya ya fice daga parlorn.

Musaddiq ya dubi Mommy kawai had’ida girgiza kai kafin yasa kai ya shige.

Tabi bayansu da kallo tana jinjina kai “Ba yanzu ba Mu’azzam.. Bazan bari kasan cewa akwai gudan jininka kwance cikin Safeenah ba sai zuwa lokacin da na tsara.. Shiri na musamman nake maka my dear stepson or should I call you my dear Son-in-law.” Tana gama fad’i Ta murmusa a hankali kafin Ta juyo tana duban k’ofan bathroom d’in da Safeenah ta turo ta fito dik a galabaice. Fuskarta ya kuma yin haske na musamman, kana ganinta kaga mai k’aramin ciki.

Dikda jiwa dake k’ok’arin d’aukanta bai hanata nufan k’ofa tana fad’in “My Halal.. Mommy kaman naga My Halal yazo..!”

Janyota Mommy tai a fusace ta zaunar saman kujera “Zauna dan Ubanki babu yanda zakije.. Mahaukaciyar banza.”

Safeenah ta turo baki tana duban Mommy “Mommy Nifa bazaki min wann fir’aunanci na d’auka ba ehe.. 21st century fah muke.. Da a k’asashen waje ne nayi imani da na makaki kotu.. Saidai kawai kiga sammaci..”

Mommy ta saki baki “Ni kike ce zaki maka Kotu kan wancan watsettsen.? Eh lallai Safeenah yayi.. Wato Ina karb’ar miki ‘yanci baki gani.. Toh maza tashi tashi ki bisa d’in kiji bak’ak’e.. Matarsa ta kwance miki Karnuka shi kuma saidai ya kwance maki mari masuji da lafiya.. Idan ke shashasha ce ki tashi kije..!”

D’an lumshe idanunta Safeenah tai tana dafe kanta dake d’an sara mata. Ga k’amshin turaren wutan dake tashi a parlorn sam bai mata dad’i ba. Batabi takan Mommy ba ta shiga kiran ma’aikatan gidan tana tambayarsu wane irin turare suka saka yau a gidan. Dik suka ce wanda aka saba sakawa ne.

Tsaki tai ta shiga masu masifa tana fad’in kar su sake saka wann turare mai warin a gidan. Ma’aikatan wann ya dubi wann wancan ya dubi wancan. Da gani zaka fahimci akwai zance a bakunansu.

Mommy tai masu izinin tafiya tana fad’in su canza turaren.

Haka suka wuce suna ‘yar k’us k’us anya ba ciki ne da Safeenah ba. ‘Yar dattijuwar cikinsu tana fad’in ai da ganinta kaga mai ciki, d’ayar fad’i take da safe ta kai mata tea d’in data saba sha dik safiya Ta watsar tace is too concentrated kar Ta sake kawo mata.

Dattijuwar ta murmusa tace “Allah yasa wann rabo yasa a maida Safeenah d’akinta.”

‘Yanmatan tab’e baki sukai ba tareda sun amsa da Ameen ba dan dama haushi take basu.

Suna tsaka da zancen sai ganin Mommy sukai k’ofan kitchen d’in tana aika masu firgitaccen kallo. Gaba d’aya suka natsu suka shige taitayinsu.

Mommy ta tako cikin kitchen d’in cikeda isa da mulki tana dubansu d’add’aya “Naji duk abubuwan da kuke cewa munafukai.. Aikin da kuka iya kenan dama. Toh wllhi kunji na rantse maku idan kuka kuskura naji zancen nan ya fita kaf zan koreku na canza ma’aikata.. Ko Safeenah ce ban yarda ku sanar da ita abinda gulmanku ya raya maku ba balle wani cikin gidan nan.. Dik abinda take so ku girka ku bata bakinku alekum.. Idan kuka sake naji zancen nan wani waje kunsan sauran.!” Ta k’arashe tana mai gyad’a kanta alamun jaddada kalamanta kafin tasa kai ta fice.
**

Mu’azzam kaw suna ficewa shida Musaddiq ‘yar nasiha yaima Musaddiq d’in kan hak’uri da iyaye especially Mommy.

Musaddiq ya d’an fuzar da fuci yace “Wai baka ganin Mommy Ta tsira abubuwan da batai ba a baya ba. Batayi wad’ann abubuwan zamanin k’uruciya ba sai yanzu da girmanta muma da girmanmu.. Haba Mu’azzam wann ai rashin dacewa ne.”

Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na Sani Musaddiq. But still Mommy mahaifiyarka ce.. Kar kace zaka d’aga mata murya ko zaka mata tsawa.. Iyaye ko ba musulmai bane ba’a d’aga masu murya Musaddiq.. AlQura’ani mai girmama wajaje da dama yayi umarni da cewa a kyautata ma iyaye. Wann zai tabbatar maka iyaye ba abun wasa bane.. Girman hakkinsu ya shige abinda za’ayi wasa dashi.. Musamman uwa wacce takeda girman hakki akan D’anta kaso uku kafin uba wanda yake da guda d’aya kaman yanda yazo a hadisin Annabin rahama (S.A.W).” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko nasiha zakai ma iyaye kwantar da kai ake da lallami da kwantar da murya da lallashi.. Ba’a yima iyaye ihu Musaddiq.. Sai Mommy ta d’aga maka k’afa ka shiga Aljannah.. Kaje ka bata hak’uri anjima kuma ka lallasheta.. Ni nasan ba halinta bane kawai zafin abinda naima d’iyarta Safeenah ne yasa take duk wad’ann abubuwan.. But I believe Mommy tanada zuciya mai kyau tinda ta rik’emu bisa gaskiya da amana ta kuma d’auki tsawon shekaru tana jinyar mahaifiyata. Wacce duk zatai haka akwai goodness a cikin zuciyarta.”

Musaddiq ya d’an jinjina kai kad’an yana had’e fatun bakinsa “Shikenan zanyi yanda kace.. Zan bata hak’uri..”

Mu’azzam ya murmusa yana dubansa, Sai ya tuna sab’anin da suka samu a Gidan Gona. Ya kuma murmusawa yana jin dad’in yanda al’amra suka soma daidaituwa tsakaninsa da D’an uwan nasa. Ya d’an bubbuga kafad’ar Musaddiq d’in guda kafin suka soma tafiya suka nufi b’angaren Musaddiq d’in Mu’azzam na fad’in “muje mu buga PS mana na d’an lallasa maka kad’an.”

Video game din suka d’anyi tare wanda suka jima basuyi ba, Musaddiq d’in sosai yaji dad’in samun time da D’anuwansa da yayi wanda suka kwana biyu basuyi hakan ba.

Haka Musaddiq ya lallasa wa Mu’azzam a game d’in. Mu’azzam ya aje control pad d’in yana d’ago hannayesa biyu alamun surrender.

Musaddiq ya dara kad’an yana fad’in “Haba Officer ka bada gari kenan..?”

Mu’azzam ya tab’e baki kad’an yana d’aga kafad’unsa “Ni yanzu bayan bincike I guess babu abinda na iya.” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye.

Musaddiq na nan rik’e da control pad d’in yana ci gaba da darawa idanunsa kan TV. Mu’azzam ya d’an matsa gefe yana duban D’anuwan nasa. Take tunanin B.A.T ya fad’o masa. D’an kauda fuska yai yana k’ok’arin kauda tunanin. Kaman ance ya dubi saman kujerar dake bayansu ya hango hular Musaddiq mai d’aukeda B.A.T ya k’arasa a hankali ya d’auki hular yana juyata.

Musaddiq dake ci gaba da buga game d’insa d’an juyowa yai yana duban Mu’azzam rik’eda hularsa ya k’ura mata idanu.
Chapter 114 · 0% Book details