← Book details Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 175

Sashe 55

Gidan Aro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy ficewa yai a parlorn dan ya kasa controlling Safeenah da mahaifiyarta wanda gaba d’aya sun fice a giya sabida abunda Mu’azzam ya aikata masu.

Aunty Shemau kaw tsananin mamakin Mu’azzam ne ya mugun cikata. Ita batai tsammanin rashin mutuncin Mu’azzam ya kawo nan ba.. Wai matarsa ce ba Karuwa ba.. Ikon Allah Toh yaushe akai auren..? Yaushe ya aureta har ya kaita gidan Safeenah.. gidan da akai ma Safeenah jere.. Kuma ko kunyar cewa matarsa ce baiyi.. Ita yanzu kam ta fara razana da al’amaran Mu’azzam.. Harga Allah tsoro ya fara bata koda wasa batai tsammanin yakai wannan matakin a rashin mutunci ba.. Ko a labarai bata tab’a cin karo da D’an iskan miji irin Mu’azzam ba ka d’auki wata mata ka Kai gidan Amaryar ka da iyayenta suka zuba mata dukiya sukai mata jere ko tarewa matar batai ba. Lokaci guda tausayin Safeenah na rufeta, bata tab’a ganin Amaryar da aka ci mutuncinta irin Safeenah ba.. Ace aure ko tarewa Bakiyi ba. Bama kiga kalan gidanki ba har an auri wata mace an kaita ta rigaki sanin gidanki da mijinki da kayyakin ki.. Ikon Allah wannan kayan mamaki da yawa yake. Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tana mai ci gaba da danna Safeenah dan Mommy kam tuni tabi bayan Daddy tana jaddada masa tafiya Kotu, dan cewa tai bataga Uban da zai hanata maka Mu’azzam a kotu ba sakamakon cin mutuncin da yai ma d’iyarta.

Safeenah ta mik’e ta d’au crutches d’inta Ta nufo waje.. Aunty Shemau ta biyo bayanta tana fad’in “Feenah ina zaki.. Bakida lafiya ki zauna a gida..”

Ko tsayuwa amsa Aunty Shemau batai ba.. Kiki da Meema hayaniyar ya fito dasu, Kai kana ganin gidan kawai Kasan babu lafiya. Meema kaw da ta lab’e taji komai mamaki ya kasa sakinta ita kanta yanzu al’amarin Ya Mu’azzam ya daina bata mamaki ya koma bata tsoro.. Wai matarsa ce ba Karuwa bace.. Ikon Allah kayan mamaki baya k’arewa a wannan ahali nasu.

Meema tai saurin rik’o Safeenah da tuni ta d’uko car keys d’inta tana fad’in “Adda Feenah what are you doing..? You can’t drive like this.. Dan Allah kiyi hak’uri abi komai a sannu.”

Cikin tsananin huci Safeenah ke fad’in “Let go of me Meema.. I’m not listening to you today.. Ki sake nace Meema..!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na tsartsafo mata.

Babu shiri Meema Ta saketa ta shiga bin bayanta tana kiran sunanta. Kiki ma makarantar da bataje ba kenan ta soma bin bayan ‘yanuwan nata.. A haka har suka iso parking lot yanda motar Safeenah ke ajiye tana k’ok’arin bud’eta.. Meema taci gaba da rok’onta tana fad’in “Addah Feenah please you can’t drive like this.. Ki kalli condition d’in da kike ciki fah.. K’afarki babu lafiya how can you drive like this.. Ok bani key d’in I’ll drive you ko ina kike son zuwa..”
Ta k’arashe tana mik’o hannayenta biyu alamun Safeenah ta bata key d’in.

Huci kurum Safeenah take tana duban Meema. Lokaci guda ta dank’a mata key d’in tace “Take me to her..!”

Meema Ta juyo da dubi Kiki dake tsaye bayansu tana zaro idanu waje dan tsoro sabida tsananin tashin hankulan da suka tsinci kawunansu ciki a gidan.. Kai da ganin yanayi Safeenah Kasan zata iya aikata koma menene.

Kiki ta girgiza wa Meema Kai alamun kar ta kai Safeenah wajen matar da suka ganta tareda Ya Mu’azzam dan tsaf zata iya illatata komai ka iya lalacewa. Dama Kiki akwai tsoro.

Tsawa Safeenah ta dakawa Meema “I said take me to her Meema..!”

Lokaci guda Meema ta shiga jinjina kai kafin ta bud’e driver’s side Ta shige Safeenah ta shige mazaunin mai zaman banza..

Girgiza kai Kiki take tana furta “Oh no.. This is not good.. I must do something to stop them..!” A guje Ta koma cikin gidan tana k’walla kirawa Yayanta Musaddiq.

A main k’ofan fitowa daga gidan sukai kusan karo da Musaddiq yana mata fad’an shi sa’anta ne da zatake masa kiran tasha.

Kiki ta shiga girgiza kai tana fad’in “Ya Musaddiq Addah Feenah da Meema sun tafi gidan Ya Mu’azzam . Addah Feenah tace sai ta kashe matar da muka ganta tareda Ya Mu’azzam..! You need to stop them before Addah Feenah does something terrible..!”

“Damn it..!” Ya furta yana mai komawa cikin gidan.. Sauri sauri ya d’auko car keys d’insa ya fito zaibi bayansu.. Mommy ya gani tsaye gabansa tana sakin huci “Koma babu yanda zakaje.. Ka koma ka k’yalesu suje sucimin uwarta.. Idan kabi bayansu ka taresu ban yafe maka ba Musaddiq..!”

Musaddiq ya girgiza kai yace “Mommy idan sukaje suka kashe ‘yar mutane kamasu fah za’ayi, kulle yaranki za’ayi a prison.. Dan Allah ki bari na dakatar dasu kafin azo ana danasani gaba d’aya.. You don’t want your daughters to go to jail.. Do you..?”

“Kafin su tafi gidan yari sai shegen nan Mu’azzam ya tafi dan dik abinda ya faru shine sila shi ya jawo.. Dan haka na basu goyon baya d’ari bisa d’ari suje suci uwarta kafin shima mu tafi kotu ya amsa nasa..!”

“Mommy..!” Bai kai aya ba Ta katsesa da fad’in “ka sake kiran Sunana sai na tsine maka.. Shashasha kawai wanda baya kishin ‘yaruwarsa..!”

Kiki dake tsaye gefe kuka itakam ta fara dan tashin hankalin yayi yawa..

Cikin sauri ta sad’ad’a ta fice ba tareda Mommy ta ganta ba. Bazatso Addah Feenah ta kashe wannan matar a kaita gidan yari ba.. Zatabi bayansu tai k’ok’arin dakatar dasu koda bazata iya ba.

Mommy kaw tana nan tana jaddadawa Musaddiq cewa yana fita daga gidan sai ta kwashe masa albarka.

A parlor Aunty Shemau ta tadda Daddy asthma attack d’insa ya tashi sai numfashi yake da k’yar oxygen na neman gaza masa.. Ta saki kururwa tana doka kiran Mommy..

A tare Mommy da Musaddiq suka nufi cikin gidan a guje hankali tashe.

**

A can Headquarters kuwa Assad sai juya wayar da Sabeera Ta basa yake yana kuma dubawa. Ya d’an tsareta da idanu kafin yace “Zan so ki tsaya ki bada statement d’inki a gaban Mu’azzam..”

Sabeera ta girgiza kai tace “Rankaidad’e Kasan yanda yanayin wannan case d’in yake, yanzu haka ni da na kawo wayar nan ta yuwu rayuwata na cikin had’ari.. Da fari jefar da wayar nayi niyyan yi dan bana son wani abinda zai had’ani da case d’in nan duba da yanda Aminiyata keta faman shan wahala dik a sabida tarayyarta da Sagir. Da ace Nasan yanda zan sami Sadiya da bazanzo ofishinku ba, da kai tsaye wajenta zanje na kai mata wayar. I don’t want anything to associate me with this case.”

Assad ya murmusa kad’an kafin yace “I understand where you are coming from.. And believe me wannan abinda kikayi zai taimaka mana matuk’a wajen solving case d’in nan.. I must thank you.. Mun gode k’warai.. Ba k’awarki kawai kika taimaka ba harda entire NPF kika taimaka.. Idan aka kamo accomplices d’in Sagir an rage mugun iri cikin al’umma.. Thank you miss Beautiful..” Ya k’adashe yana sakar mata murmushi.

Murmushin itama tai kad’an tana mai sadda kanta k’asa. Cikin d’an daburcewa sabida irin kallon da yake jifanta dashi Ta mik’e tana fad’in “I.. I must leave now.. Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai sa kai..”

Saurin bin bayanta yai yace “Wait.. Barin saka a kaiki..”

Tai saurin girgiza kai tace “No banso a ganni da wani d’ansanda balle naja ma kaina attention.. But thanks anyway.. I can manage..”

Assad ya jinjina kai yana dubanta “You take care..!” Ya fad’i sanda take ficewa. Ta jinjina kai a hankali kafin tai saurin ficewa daga wajen.

Yana nan tsaye Yusu ya k’araso ya samesa suna magana k’asa k’asa dan basu so wani ma yasan sun sami wayar Sagir a hannunsu har Sai Mu’azzam ya iso..

Aiko nan suka hangosa yana tafe ya kwab’e suit d’insa yai folding hannayen long sleeves d’insa wanda itace ‘yar cikin suit d’in nasa.. Da gani yanda yake tafiya Kasan ya shirya ma binciken.

Yana k’arasowa suka nufi building d’in suna tattauna batun.

Maleeka da k’arasowarta kenan nan ta hango Mu’azzam ya dawo aiki wani irin murmushi ne ya kufce mata ta k’araso gudu gudu tana d’ago masa hannu take fad’in “Sir....!”

A tare suka waigo suna duban Maleeka dake nufosu.. Team d’in nasu sun had’e gaba d’aya. Yusuf da Assad suka saki murmushi suna duban Maleeka wacce suka rasa walwalanta tin bayan dakatar da Mu’azzam da akai. Sai yau suke ganin murmushinta.

Ta k’araso da sauri tana k’ok’arin saita kanta gaban Mu’azzam wanda ya tsime sosai yana dubanta “I.. I’m sorry Sir.. I just want to say welcome back.. Munyi kewarka sosai.. Welcome back Sir..!” Ta k’arashe tana rungume files d’in dake hannunta cikin k’irjinta.

Duk sukai tsaye suna duban Mu’azzam da ya tsareta da idanu wanda ba Maleeka dake Ta faman rarrabe idanu cikin tsoro tana addu’an Allah Sa ba wani laifin tai ba harta da su Assad saida suka d’anyi pause suna dubansa.

Murmushi ya sakar mata da gefen bakinsa kafin yace “Thank you..”

Daskarewa Maleeka tai tana jin Wai Mu’azzam ne ya ce da ita thank you har yana sakar mata wannan tsadadden murmushin nasa..

Bai kuma bi takanta ba yasa kai ya shige su Assad na biye dashi suna murmushin Daskarewar da Maleeka tai.. Lokaci guda Mu’azzam d’in ke fad’iwa su Assad “Let’s go.. To the tracking room and see what we can find inside..”
Yusuf da Assad suka jinjina masa kai suna tafe cikin sassarfa.

Saida har suka shige kafin Maleeka ta saki d’an k’aran murna tana cilla hannayenta sama “Yes yes.. He will fall for me eventually.. I’m sure of it.. Well done Maleeka kici gaba da hak’uri har ki saye zuciyarsa..” Daga haka saurin shigewa tai tabi bayansu.

**

Meema tana ida parking a k’ofar Gidan Safeenah ta k’arasa tana buga gate d’in da sandar crutch d’inta. Bugu take da iya k’arfin da Allah ya hore mata Meema na fad’in Addah Feenah take ita easy..!”

Bata ko saurari Meema ba tace “Ki d’auko min ultra pad d’in nan cikin mota nayi imani nata ne na gani wajensa ranan.. Ma ita ya saya zai kawo.. Wllhi I’ll make her eat it.. Sai na sakata Ta cinyesa.. Ki wuce nace ki d’auko mun Meema..!”
Chapter 55 · 0% Book details